Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 31-32

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*31&32*

 

…….sai wajen k’arfe d’aya saura suka iso gida”ada Amaan taso tayi masa bore saidai yadda taga ya had’e girar sama data k’asa yasaka ta nutsu ta Amshi ledojin dayake mik’o mata”idan kin shiga ciki kiyi wanka da sallar Azahar kina jina?”kanta ta gyad’a masa still tana tsaye”ganin bata Alamar tafiya yasaka shi cewa”kije mana”to hamma nika d’ai?”girgiza kansa yayi fuska bbu walwala yace”Amaan meyasa kike son bani wahala ne?”ya kikeso nayi da raina?”fasa sallar zanyi na biyoki kikeso kome??”to mema zan miki idan na biyoki d’in?batace masa komai ba ta wuce kawai”sai kuma yaga kamar be kyautaba”yatab’e baki yana nufar bakin get da nufin Ak’afa yatafi masjeed d’in dake layin…. Amaan da sallama ta shigo had’ad’d’en parlourn Ammi”k’amshin girkin Ammi yakaima k’ofofin hancinta ziyara”Abdallah na zaune yana chats”da k’yar ya Amsa sallamar tata”sbd tafara bashi haushi sbd ita yayansa nasamun matsala da mutane”Ammi fa?”ta tambaya tana kallonsa”kin bani Ajiyar tane?”yafad’a fuska bbu walwala “batace masa komai ba ta wuce d’aki”kayan jikinta ta rage ta wuce bath room tayi wanka da Alwallah”bayan ta fito tayi sallah ,sannan ta shirya cikin wasu rida da wondo golden irin na k’asar turkish”saita aza hijab saman kayan”gashin gaban goshinta duk yafito”tana zaune kan sofa bayan tagama cin kayan mak’ulashen data shigo dasu ,sai cillah teddy d’in ta sama takeyi tana dariya Ammi ta shigo cikin d’akin da sallama”Ammi ya jikin naki?”Alhmdllh Amaan kun dawo ne?”Eh tun d’azun “shine nace kina Ina? wai Abdallah na bashi Ajiyarki ne? d’an jim Ammin tayi sbd ta fahimci Abdallah najin haushin Amaan”yakuma sanar mata Abinda yafaru sbd jajen rashin zuwan Dr Mansoor datayi”ta kuma sha Alwashin zubama shariff Ido game da Abinda yafaru tsakaninsa da Dr mansoor tana zaune zaizo mata da maganar….kinga shareshi kawai Amaan yana fushine sbd nace yaje masallaci “yanzun tunda kinyi sallar kije kiyi wanke wanke gobe insha Allah su jummai zasu dawo”Anjima ni Asibiti zanje naga likita”daga haka ta nufi bath room”Amaan dake sauraronta ta Ajiye teddyn ta d’akko d’an kwali ta goyata kafin ta fita”tana k’ok’arin shiga kitchen shariff yashigo cikin parlourn”kallo be ishetaba ta wuce ciki”yana lura da ita shima saiya d’age kafad’a, Alamar saime idan tak’i kulashi?ya wuce samansa bebi takan kowa ba”Amaan bayan ta gama wanke wanken ta fito parlourn Atare da Ammi sukaci Abinci”tana kallon Abdallah ta nuna kamarma batasan dashi ba”sbd shima yabata haushi….wajen k’arfe 3 na yamma Ammi na zaune a parlourn Amaan tayi matashin kai da cinyarta tanata yimata surutu da shagwab’a shariff yayi sallama yashigo cikin parlourn “yasha wankan k’ananun kaya”da Alama ta k’ofar baya yabi yafita d’azun”Ammi ce ta kallesa ta Amsa sallamar tasa”dama Ammi ga wani doctor nan dayafi mansoor sanin Ainahin irin ciwon ki zai shigo ya dubaki”to shikenan babu damuwa ya shigo bara na saka hijab”Amaan tashi zaune”shariff yasaci kallon ta…..yaga gaba d’aya kamarma batasan dashiba Acikin parlourn”yanaso yace”ta tashi ta koma ciki Amma miskilancinsa da zafin kansa ya hanashi furta hakan”sai y’an harare harare yakeyi yaja yayi tsaye”duk Ammi na lura dashi”ta mik’e tsaye ta wuce d’aki”Amaan kuwa maida hankalinta wajen teddy d’inta tayi…shi kuma yaja k’aramin tsaki yafita”be jimaba suka shigo tare da wani likitah Amma ba yaro bane”Amaan ta Amsa sallamar sa tana gaishe da doctor d’in “batare data yadda ta kalli mutumin nata ba”Ahaka Ammi tashigo cikin parlourn da sallama “bayan ta zauna suka gaisa”Amaan ta mik’e tsaye ta wuce d’aki “har doctor d’in yagama duba Ammi bata fito main parlour ba”daga karshe har dare bata fitoba tana d’aki….washe garin ranar shariff babu wanda yasan yafita”ko Ammi saida gari yayi haske yasameta kitchen suka gaisa”sosai ya k’ullaci Amaan Azuciyarsa”yana zaune a office fuskarsa bbu walwala ko kad’an yanata danne danne mus’ab yashigo”tunda yaji muryar sa yakoma had’e rai “sbd yasan confirm sai yamasa zancen Dr Mansoor” shidai mus’ab d’an murmushi kawai yayi yaja kujerah ya zauna yana fad’in barka da Asuba Abokinah”barka dai”shine Abinda sheriff yafad’a iya lab’b’ansa yana cigaba da Abinda yakeyi”shiru na second 50 yaratsa can mus’ab yace”Atak’aice nazo muyi mgn bazan damu da duk yadda zaka fassaraniba”na rasa se yaushe zaka canza shariff?”yanzun fisabilillahi Abinda kukayi kaida mansoor kun kyauta kenan?”uzuri guda na masa shine”besan wacece Amaan ba da yanayin datake ciki shiyasa yace”yana sonta”kai kuma uzurin dana maka sbd kasan yanayin datake ciki shiyasa baka bashi fuska ba”kuma sanar masa wacece ita kamar tona Asirin tane danaka”yaka mata dan Allah kayi hak’uri komai ya wuce karka rik’esa Arai sbd wata wacce kasani cikin k’ank’anin lokaci”koda yasanar mun har korarsa kayi duk banji dadi ba”meyasa sbd Amaan kake irin haka?gashi ka hanashi yaduba Ammi…..ka gama?”cewar shariff cikin k’ank’ace ido”ban saniba”sai Abu na gaba nasan jiya ka hau face book kaga wannan shed’aniyar Agolar (Ibtihal)ta gidan ku tayi post d’in pics naku kaida Amaan a face book ko?kuma kowa nayin comments yadda yaga dama”wasu su fad’i Alkhairi wasu su fad’i sharri”nine na fito na kareka…..enouph mus’ab! duk nagani Ajiya ta aza pic namu muna can ice cream “ban kuma damu da kome mutane zasu fad’a ba”idan yanzun naga damar fita da Amaan saina fita da ita duk inda nakeso bbu shegen daya Isa ya hanani”bana biye ta mutane, musammun da kowa yasan matsayin aikinah yanzun”so pls muma rufe wannan zancen banaso….shiru mus’ab yayi zuciyarsa na sanar masa Abinda yake zargin shariff yatabbata kenan?”dan yajima yana zargin kodai son Amaan yakeyi”dukda yana fatan hakan saidai yafiso saita sami lafiya…..idan kagama tunanin gulmar pls zaka iya tafiya”murmushi mus’ab yasaki yana fad’in kamar kasani gulmar mutum biyu nakeyi nida zuciyata “banza shariff yamasa yasharesa”saida mus’ab yagama tsokanarsa sannan yabar office d’in “shi kuwa sai wajen 6 yanufo gida…..wasa wasa tun shariff na d’aukar Amaan zatazo ta masa mgn harya cire rai”gaba d’aya bbu ruwanta dashi”har gaidashi batayi”tun Ammi bata luraba har dai tafara lura”ta kumayi mamaki”saidai tasaka musu Ido kawai”idan Amaan tasan yana gidan bata fitowa tana k’unk’ume Adak’i”idan tana zaune Awaje ya shigo zatabar wajen” wani zubin tayita kuka idan tana tunanin to ita wacece?”Ina iyayenta?”kodai Ammi itace mahaifiyarta?”to Ina babanta?”duk irin wannan tunane tunanan ke d’aure mata kai idan tanayi saita kama kuka”rubutunta na wajen mlm kuma Abdallah kullum sai yaje ya Amso yabama Ammi ta bata tasha ta shafe jikinta”idan taji muryar shariff har lab’ewa takeyi tayita lek’ensa”shi kuwa uban gayyar tun be damuba da fushin da Amaan keyi dashiba harya fara damuwa”zafin kansa yasaka ba’a ganewa…… Ayau yakama satday”kuma Ayau sadeeq zai dawo gida Nigeria A matsayin babban likitan mata”duk yawanci y’an gidan murna sukeyi harda Amaan dabata sanshi ba”Atare da ita da masu Aiki da Ammi Akayi girki yau”wajen k’arfe 2:35 pm Amaan na kwance saman cinyar Ammi sbd dukta gaji sunsha aiki”driver yatafi d’akko sadeeq Airport”Abdallah nata cin magani ya shigo cikin parlourn “sbd be wani murna da dawowar sadeeq”ga haushin yasaka yabar side nasa Angyara masa zai koma sashensa shi Ancanza masa wani side d’in….baka iya salama bane?”cewar Ammi tana hararar sa”kamar zaiyi kuka yace”dama nina san kowa baya k’aunata gidan nan”kina gani Ammi wannan mugun yaya sadeeq d’in ya Amshemun d’akina bakiyi mgn ba “sannan ita kuma wannan kinfi damuwa da ita akaina”murmushi yasub’uce ma Ammi tana fad’in Abdallah baza kayi hankaliba ko?”sadeeq shekara 10 yabaka sbd kana binsa shine ka rainashi ko?”wlh kayi Ahankali kasan dai dama idan yasameka laftarka yakeyi ko”sbd haka idan kamasa rashin kunya bbu ruwana wlh jibgarka zaiyi”turo baki yayi ya kauda kansa yana fad’in ke kuma Anty Amaan kije inji yaya shariff yana a parlourn sa”saida Amaan taji fad’uwar gaba”dandanan idanuwanta suka kawo ruwa tak’iyin mgn”Abdallah ya juya yabar parlourn”Ammi na kallonta ta shafi kanta tana fad’in tashi kije yayanku na kiranki” Amma karki jima kinjiko?”kije kuma kisaka hijab”Ammi nifa dukana zaiyi ko?”ta fad’a hawaye na zubo mata”bazai dokeki ba Amaan sbd yasan bana so”dama kin masa wani laifi ne?”shiru tayi tak’i mgn “tashi kije kisaka hijab kiji kiran meye yake miki?”batace komai ba ta tashi ta wuce d’aki…… shariff dake zaune kan 2 seeter yana kallon komai ta CTV camera”yatab’e baki yana rufe laptop d’in dake ga bansa”ya kumasha Alwashin Abdallah zai sani idan yahad’u dashi”ita kuma Amaan Ai zatazo ta sameshi”kasancewar yau Antashi da rana sanyin yad’an rage”yana sanye da wondo 3 quarter fari da farar t shirt me gajeran hannu wacce ta fidda shafe d’in murd’add’en jikinsa”mik’e dogayen k’afafuwansa yayi saman center table yana girgiza su”ya jingina bayansa Ajikin kujerar ya lumshe sexy eyes d’insa…..cikin sand’a had’e da tsoro Amaan ta turo k’ofar d’akin ta shigo”hawaye shab’e shab’e kwance saman baby face nata”tayi sallama cikin muryar kuka”shariff ya Amsa Azuciyarsa yana binta da kallon k’asan Ido”nesa dashi ta duk’a Ad’arare,yayinda tabar k’ofar Abud’e sbd idan zai daketa zata samu hanyar guduwa”hamma Ina wuni? shine Abinda Amaan ta fad’a cikin rawar murya “kaman dama jiranta yakeyi ya bud’e idanuwansa k’yam ya’azasu saman kyakykyawar fuskarta”ta kawar dakai gefe gabanta nata fad’uwa”idan ba’a wuniba zaki ganni ne? to bana son ita gaisuwar taki ki rik’e Abarki”kin maidani Abokin adawarki ko? girgiza kanta tayi”yes tunda kina gaba dani kinfi k’arfin kimun mgn koki gaisheni, to yayi kyau…..dan Allah kayi hak’uri hamma na dena wlh”kaine kake ja ko?”sai nayita bin kanka Ina maka mgn baka Amsani”bazan Amsaba”kije kici gaba dayin gabar dani kiga zandena rayuwa ne sbd kin dena mun mgn?”ya
fad’a Atsawace”ta rintse Ido jikinta na rawa”yaja tsaki “hamma kayi hak’uri nima bansan nayi maka laifin ba”bansan meke damuna ba”dan Allah kasanarmun wacece ni da iyayena?ko kuwa Ammi itace mahaifiyata??….tsuramata Ido kawai yayi yana bin d’an bakinta da kallo k’asan zuciyarsa najin tausayinta “saiya sassauta murya yace”Ammi itace mahaifiyarki”Abbanmu yarasu”yau sadeeq zai dawo nasan kinji Ana maganar?”iyakarki dashi gaisuwa cikin ladabi”bayan haka ko fira ban Amince kiyi dashi ba”daga haka yayi shiru “Ahankali tace”to hamma zanyi Amma kaima kadena k’yaleni idan Ina maka mgn ko?”umarni kikazo ki bani?”shiru tayi dan bata fahimci me yake nufi ba”oya tashi kibani waje”batace komai ba ta mik’e tsaye…. yad’an kalleta yace”zo nan”yafad’a yana nuna mata gefensa”tazo bbu musu ta zauna”meyasa kike kuka?”bbu komai fa”ta fad’a tana share hawayenta “saidai ya lura tak’i yadda ta kallesa”ya fahimci time d’in datake hayyacinta tanada kunya”wai wannan d’ararewar da kikeyi duk na meye ko yau kika fara gani nane? batayi mgn ba kanta na’asunkuye”tashi ki kamun ruwa a fridge”nima zan sha ham ma”to jeki kawo”dato ta Amsa ta tashi tsaye ta nufi wajen fridge d’in”goran ruwa da cup data gani Asama ta d’akko tazo ta duk’a gabansa ta zuba masa ta mik’o masa”sai k’in Amsa yayi yanuna mata d’an bakinta wai tafara sha”nok’e kafad’arta tayi tace”kaifa zaka fara sha hamma sbd kaine babba ko?”beyi mgn ba fuska asake ya Amsa da Alama kalamanta sun masa dad’i”duka ya shanye yana fad’in k’aromun pls”batayi mgn ba ta Amsa ta k’ara masa”rabi yasha yanufi bakinta da sauran”babu musu ta Amsa ta shanye”sun isheki?”uhmm”beyi mgn ya d’auki wata chacoolate dake gefensa ya b’alle daga ledarta yana fad’in zoki zauna kisha”to hamma Amma Ammi tace karna jima”beyi dai mgn ba yamik’a mata”ta Amsa tana masa godiya “yana kallon yadda take sha tana lumshe Ido Alamar tayi mata dad’i sosai”besan lokacin da murmushi yasub’uce masa ba”sautin murmushin nasa yasaka Amaan ta bud’e idanuwanta suka sark’e da nashi”itama batasan lokacin datayi murmushin ba”hamma! uhmm”yanzun zaka dinga mun mgn ko?”kema zaki dinga yimun? yafad’a yana gyara zamansa yanata kallonta “saidai tayi k’asa da kanta”Ahankali yace” yau bakiyi wanka ba?”Allah nayi da safe”to Anjima ki k’ara yi”nidai Allah sanyi ke Akwai”shiyasa nace ke k’azama ce ko?”kai hamma Allah inada tsabtata”saifa yau na tab’a shigowa d’akinka”shima nine naso hakan”to Ai yanzun zandinga zuwa gaisheka ma”Amma saina k’wank’waso ko?uhmm”nizan wuce amma katashi ka rakani”bece komai ba yatashi tsaye ,itama ta mik’e suka kalli juna ta turo baki tana fad’in kanada tsayi hamma”ke kuma y’ar guntuwa ce ko?”yafad’a yana jan karan hancinta”ta nok’e kafad’arta wai ita tanada tsayi”shidai yana dai kallonta yana neman Abinda yasanyasa farin ciki yasara”sbd jin zuciyarsa yakeyi wasai….yana wannan tunanin yaji Amaan Agefen sa har jikinsu na gugar juna”ihun murna tayi tana fad’in yeeeeeeeeeeee! na kusan taddoka tsayi hamma”da sauri ya matsa yana jin wata iriyar hajijiya najansa da sauri ya zauna gefen kujera yana tattaro kalmar jeki gani nan”batayi musu ba ta nufi k’ofa tana fad’in hamma wannan Abin yamun dad’i sosai”pls kadinga siyamun irinsa”Amaan! zonan”yafad’a murya akasale”ta juyo batare data kallesaba”jeki d’aki suna nan saman bed ki d’akko kizo muje na rakaki ku gaisa da sadeeq ga kiransa nan nasan ya dawo yanzun”yak’are maganar yana kallon babbar wayarsa dake hannunsa….✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button