Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 31

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*31*

Da misalin karfe 8:00am wasu mata suka nufi bangaren yarima nan Fauzan ya dakatar dasu duk da yasan cewa al’adarsu ce hakan amma shi bazai bari a gano sirrin uban gidan nasa bah donhaka ya hanasu shiga yace su Jira a nemi izini nan ya dauki waya ya kira yarima tayi ringing Bai d’aga ba, yace suje su dawo anjima yarma na bacci nan suka koma suka sanar da Fulani murmushi tayi tasan dama Hakan zai faru donhaka ta Bada umarni a bari sai anjima, nan kuwa Yan gulma sun Kaiwa gimbiya Suhail labari take magana ya fara tashi cikin masarautar daga karshe Suhail tace kodai ana boyewa yarinya Bata kawo budurcinta bane . Ayman kuwa dama yasan al’adunsu yadda yake Amma shi bazai taba dauka ba tunda ba addini bane wannan Wani bangarene na rayuwarsa Babu Wanda ya Isa yagano sirrinsu sai dai kowa ya Fadi abunda yake so. Yayi wanka ya shirya ita kuwa tana bacci tun bayan sallar asuba ta gefen Ido ya kalleta sannan ya fice daga d’akin, a falo ya zauna sannan ya kira Fauzan ya shigo suka gaisa ya nemi da ya kira jakadiya tazo ta raka amarya bangarenta sannan a taho mata da wasu kayan da zata saka kada a Bata Wanda masarautar ta tanada saboda wannan Rana , gyada Kai Fauzan yayi ya tashi ya fice cikin zuciyarsa kuwa Yana jinjinawa Ayman abubuwan dayake shine dai dai saboda masarautar tasu ba abin yarda bane .
Aman ya samesa Yana ta masa shakiyanci yaki kulasa Yana cewa ” nan da one month ne dai Nima zan dandani abinda ka dandana kake Wani daddaga min shoulder a dole Ka zama babba koh, ba mamaki ma zee ta riga matarka samun ciki kasan ni ba ragon namiji bane ” murmushi Ayman yayi kamar zaiyi magana ya fasa daga nan suka wuce fada gun sultan don gabatar da gaisuwa . Waziri babba ya Kalli Ayman yace ” naji dad’in abunda ka aikata dama tuntuni nake son a soke wannan al’adun amma Abu ya gagara Allah ya Maka albarka ” ya juya wajen sultan yace ” Allah ya baka nasara na shirya dukkan tukuicin da zaa gabatar a masarautar Singa ba sai anyi Wani taro ba tunda yarima baya bukata ” murmushi sultan yayi ya Kalli dan nasan dama yasan zaa rina Ayman akwai sirri da rashin yarda yace ” shikenan yarima Mai jiran gado duk yadda kace Hakan zaayi Allah ya basu zuria dayyaba ” “Ameen ya rabbi waziri Babba da Aman suka amsa ” a yayinda waziri karami ke faman hararin waziri Babba kasa kasa gulma na cinsa ya rasa ya zaiyi wannan labarin ya iso kunnen Suhail gashi yanzu suka iso fada bare a ce zasu tashi ya Kai mata rahoto, tamkar sultan yasan me a ransa yace ” waziri karami ka shirya da Kai zaayi tafiyar zuwa fadar Singa na baka jagorancin wannan tafiya ” Yana kefkefta Ido yace ” godiya nake ranka ya dade Allah ya Kara lafiya ” Ayman ya tashi cikin girmamawa ya musu sallama cike da Jin kunya ya tafi yayinda Aman ya mara masa baya, daga nan bangaren Fulani suka shiga suka gabatar da gaisuwa Yan uwa na tsokanarsa shi dai sai murmushi baya ce musu komai a yayinda Yan mata ke kyasawa Aman kuwa Mayen mata tuni ya fara yaudarar wata Hibba ya karbi number ta .
Gimbiya Failuzaa tayi wanka sai faman murmushi take idan ta tuna abunda ya faru jiya Gani take tamkar a mafarki Bata taba tunani haka abin zaizo mata da sauki ba, ta shirya cikin kayan da jakadiya tazo mata dasu nan suka tafi fada gun sultan tayi gaisuwa sai bangaren Suhail tana ta haba haba ta ita tana Neman Janta a jiki jakadiya ta kasa ta tsare Babu damar ayi Wani munafunci daga karshe suka mata sallama suka tafi bangaren Fulani inda Suhail ta Aiko mata da kyaututtuka na maraba da shiga masarautar, Sabrin kuwa kishi ya Hana taje inda Failuzaa take dama tana fama da kanta haihuwa ko yau ko gobe. A bangaren Fulani suka yada zango a nan ta samu tarba Mai kyau aka gabatar mata da kayan Karin kumallo Wanda a ka’ida da Ayman ya kamata suci tare amma ya koma part nasa tare da Aman. Haka aka shirya kayan tukuicin da zaa Kai masarautar Singa tare da sauran Yan uwa don nuna farinckn kasancewar gimbiya Failuzaa cikin ahlinsu da Kuma tukuicin budurci .

Related Articles

*Abuja Nigeria*

Yau Ake visiting a makarantar su hajjo duk inda ka duba motocine birjik iyaye sun kawowa y’ayansu ziyara wasu kuwa samari da Yan mata sai Kuma mazan da suka kawowa matansu ziyara, hajjo tana sanye da uniform nasu da karamar hijab half Sunna Wanda ya Kara fito da kyaunta tana faman raba Ido tana Neman inna da aka ce mata ta iso tana jiranta. Horn ta jiyo daga bayan ta nan ta juya inna ce gaban mota sai da gaban hajjo ya Fadi kar dai a ce anyi auren , a hankali ta taka zuwa wajne motar kirar hummer uncle Yusuf ne a mazaunin driver sai inna Dake gidan gaba . a saitin window ta tsaya Ina wuni uncle ” lafiya my dota ya kike ya karatu” ” lafiya Alhamdulillah, inna sannu da zuwa” murmushi inna tayi tana karantar yanayin y’ar tata har ta hango matsalarta ” ya karatun Ina fatan ba matsala” Babu komai alhmdllh idan akwai Wani abu zan kiraki, ki gaida maman Nana”
“Au korata kike yau Kuma ” murmushin karfin Hali tayi tace” ah ah inna naga ba ke d’aya bace ” ” toh shikenan Allah ya taimaka, “daga haka inna ta cire kudade masu yawa ta Mika mata sannan ta Bude motar ta fito , provision din da suka zo mata dashi ta fitar ta ajiye mata . Uncle Yusuf ya cire kudi ya Mika mata taki karba sai da inna ta saka Baki , inna ta rike mata wasu ledojin tace ” muje na tayaki ” hajjo batayi magana ba suka fara tafiya inna ta murmusa ” sanyin idaniyata fushi kike dani koh” ta shagwabe fuska tace ” inna yanzu aure zakiyi ” murmushi tayi dama tasan matsalar kenan ” Ina son kisani cewa komai daga Allah ne idan ya kaddarawa bawa Abu Babu Mai hanawa Kuma Ina son kisa a ranki cewa dama Allah ya rubuta sai na auri kawunki ki tayani da adua da fatan alheri”
“Amma inna kince Baki taba son Baba nah ba ” murmushi inna tayi tare da girgiza kai batace komai ba, ” yanzu inna wannan din soyayya kuke dashi ” ” gidanku…” Dariya hajjo tayi kamar zata Fadi ta koma baya saboda tasan inna zata iya Kai mata duka sai yanzu taji sanyi cikin zuciyarta tun bayan dawowarta don Gani take tamkar inna ta daina sonta Amma yanzu hankalinta ya kwanta . A bakin gate din hostel suka tsaya don baa bari a shiga Bless ta kira tazo ta taimaka mata suka shigar da kayan bayan sun fito inna ta mikawa Bless 2k ta karba tana godiya, zama sukayi bisa wasu kujeru Bless ta tashi ta Basu waje nan inna ta cigaba da kwantarwa tilon y’ar tata hankali ita kuwa sai zuba shagwaba take duk abubuwan take idanunsa na kanta sai faman murmusawa yake dama yaso zuwa wajenta Amma ganin mahaifiyar tata yasa ya fasa zuwa. Kamar bazasu rabu ba inna sai da ta tabbata ta kwantarwa hajjo hankali ta lallabata hade da nasiha kafin sukayi sallama ta rakata bakin mota tana d’aga musu hannu suka tafi, ya Yusuf ya kalleta yace ” like wannan yarinyar tana taya mahaifinta kishi koh, naga Bata sake jiki dani” murmushi inna tayi tace ” yaranta ne dai Amma a hankali zaku Saba ai ” hmm fav wato sai da kikasan yadda zakiyi kika lallaba abinki don naga yanzu tafi fara’a akan lokacin da mukazo , wllhi shiyasa nake Kara sonki magirah kin iya tafiyar da komai yadda ya dace . Don Allah ki nunamin kauna da kulawar da na rasa a baya please” hmmm Yaya kenan yanzu fa girma yazo ” ” ah ah wallahi ban yarda ba nidai a cire kunya a biyani bashin Soyayya ta ” dariya take kasa kasa ya langabe Kai ” haba mana favorite nine fah kinsan Ina sonki har abada ” nidai ka daina just concentrate kana driving please ” yawwa kwana nawa ya rage a daura auren nasan this week zaki gama idda koh ” murmushi kawai take Bata sake magana ba ya kalleta ya cire Ido ya Maida hankali akan driving din da yake a dole yayi fushi tana kallonsa tana murmushi.
Hajjo ta koma ta zauna bisa kujerar da suka zauna da inna dazun tana faman murmushi wato inna tana sonta itama tana son innarta Allah ya bar mata inna duk duniya Bata da kowa sama da ita, nan tarihin rayuwar innar ya fado mata yanzu dama inna y’ar sarki ce Amma Bata taba fada mata bah, wata zuciyar ta Bata amsa da cewa tana jiran sai kin girma Amma yanzu she is 16 ai ta gama girma ya kamata tasan komai Kuma tana bukatar zuwa gun dangin mahaifinta Amma sai ta gama makaranta don ta tabbata inna bazata bari ta tafi yanzu ba gashi ance next year zata rubuta WAEC da NECO.
” Assalamu alaykum beauty” da sauri ta d’aga Kai tana kallonsa ita yake kallo sun kurawa juna Ido tayi saurin dauke nata , ” zan iya zama kusa dake please if you don’t mind ” shiru tayi tana son tuna fuskar tasa tabbas akwai inda suka taba haduwa . ” Talk to me can I sit please” toh ni zan hanaka zama ne ” ta amsa a yatsune , Yana murmushi ya zauna qamshin turarensa ya cika wajen.

Back to top button