Hausa NovelsYar Aikin Karuwai Book 2 Hausa Novel

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 41-45

Sponsored Links

Nawwar da kyar ya bari ma na ajiye kayana,nima nayi missing dinsa,yace ko kice kinyi missing dina haka ake soyayyar ko Dan Baby Ina missing din romance naka babu sabo da kinga danginki ni an sani a kwandon shara shike nan sabo da Allah,ai kaima kasan nayi fada ma bata baki n…bakinsa na tsinta cikin nawa Yana tsotsa na Fara maida Masa da matartani,a hankali ya rabani da kayan jikina ya zare nasa na makale shi kafafun mu suna nema su gaza daukanmu, a hankali muryata tana rawa nace standing position zamuyi, kirjina masu tafiya da imaninsa su yake Sarrafawa yana matsawa Yana tsotsa,gigicewa nayi na Shiga Yi Masa salo mun fita a hayyacinmu,Ni ke riding nasa yau,Ji yake dama mu dawwama a haka, wani Kara kaunata,Nishi muke Muna furtawa juna kalamai,Nawwar ba dai sanin ta kaina ba duk yanda na Kai da rashin butaka sai ya min abu kadan shike nan na zurma,mun Dade muna murza juna sannan ya shigeni cikin nutsuwa da salo irin na matasan birni,yau ranar ta musamman ce,mun jiyar da juna dadi.

Auta Exam dinsa waec ta fito tayi kyau,takardar da yayi printing out ya kawowa Baffa yace Baffa ga result din,Baffa ya karba yayi masa addua yayi kyau Autana, Auta yace Baffa Alkawarina, Inshaallah za a cika maka yanzu kudi za a Kai ai,fatan dai Kun daidaita da Sahar din,yace ae ai ta sani sai dai na sake fada Mata idan an gama komai bayan na fara University sai ayi bikin,yace wato dai Auta Kai baza ka je kasar waje karatun ba? yace idan na Fara a nan in nayi auren sai na tafi da ita can,to cewar Baffa.
Sahar din da Auta yake so ta girmeshi zata Kai sa’ar Rabi da Cele gata katuwa ce amma yace shi itace dai daidai shi,itama gandamemiya da ita ta nace sai Auta,Uwarta Kuma tace Matukar tana raye baza ta auri wannan yaron ba gwara ta samo Babba me hankali,Babanta ma bai yarda ba amma ita tace sai Auta shi take so.

Papa aka tura yaji Yaya ake ciki,Baban Sahar yace kuyi hakuri bawai dan jikinsa bai Kai bane wani ma in ya ganshi zai ce ya Kai 28 haka ya girma da yawa a jiki amma shekarunsa 23 bazan iya aurawa yata yaro ba gwara Babba Wanda yasan mutuncin mace Wanda yasan darajar mace,Papa iya haushi yaji sabo da ko Yaya aka ki jininka sai kaji haushi yace shike nan ba damuwa Allah ya hada kowa da rabonsa. Baban Sahar yace Ameen Suma ba laifi suna da rufin asiri.
Papa Yana dawowa ya samu Mami a dakin Baffa tana zuba Masa abinci,Baffa yace ka dawo? yace ae ya samu waje ya zauna yace a Kira Auta yaji da kunnensa aka kirashi Auta yazo Kuwa Papa ya zube zance yanda sukayi,Auta yaji wani bakin ciki harda hawaye,su Baffa dariya ta kamasu Auta na kukan soyayya, Papa yace Dan banzan yaro ba a sonka kana likewa,Auta yace ai ita bata da laifi tana so na ni Zan jirata ko shekarun ne sai na Kara,Baffa yace wlh baka Isa ba ka Nemo mace tun wuri idan ba haka ba wlh sai na aura maka me rabo wannan rashin kunyar taka bada mu ba bazan dauka ba,Auta yace Ni fa nace Ina so ayi min Kuma nace na fasa ui yanzu,Baffa yace bafa na Wasa dakai ka Nemo mace idan zaka Nemo zuwa ka Fara University gashi nan na biya maka awolowo University soon zaka Fara zuwa wani satin.

Tashi yayi ya tafiyarsa Mami bata ce komai ba sai yanzu tace ai dole ayiwa Auta aure, Auta da alama mace yake bukata ai ko yaki wlh sai an masa aure Ina Zan iya wannan iskancin nasa na zabe zabe a haka har ya lalace,Baffa yace kyale dan jakar uba ai na sama Masa Office ya daina yawon banza da kallon ball ko Yana school weekend sai yaje Office,da bangaren Nawwar Zan kaishi amma naga fada zasuyi gwara na barshi a bangarena.
Bangaren Auta dakinsa ya shiga yana takaici ya rasa Sahar, kiranta ne ya shigo wayarsa bai fasa dagawa ba yace hello,Sahar kuka take yi wiwi katuwa da ita ko kunya tace Nawaf dan Allah karka canja wata ka dan jirani ko su Daddyna zasu hakura,Auta yaji tausayin Kansa sabo da ba karamin yaki yayi ba kafin ya samu soyayyar Sahar gata lokacin tana ss3 su suna jss1 har ta Gama degree dinta tsaf Auta yaje Suka Fara soyayya ga yara da iya soyayya su ba aura zasu Yi ba sai su kwacewa babban mutum budurwa sabo da suna da time Basu da aikin yi duk wata kulawa za a bawa mace shi yasa Auta Yana shiga neman Sahar duk ya kori manyan samarinta.

Yace Sahar kiyi hakuri haka Allah yaso idan da rabo Zan aurenki amma su Mami sunce aure za a min kiyi hakuri ki yiwa iyayenki biyayya nima Zan yiwa nawa biyayya muyi Addua Kawai,ya lallaba Sahar sai da Suka gama waya ya jefar da Wayar yace bazan sake fitowa ba abinci ma bazan ci ba gwara na mutu na huta ya sawa kofarsa key sabo da Auta ya sa rai ya samu Sahar an gama Yana sonta shi Kam,Mami taga Auta Shuru Shuru har dare tun safe bai fito ba, Dakinsa ta nufa ta murda a kulle ta Kira sunansa Auta,ciki ciki ya amsa haushin kowa yake ji,Zo ka bude min kofa yaki budewa,tayi tayi sai da kyar sannan ya tashi ya bude Jin Mami tace sai taci mutuncinsa,Kofa ya bude Idonsa duk ya canja alamar kuka yayi,dariya ma ya bawa Mami,tace Autana kukan Soyayya kayi ne? Yace kukan soyayya ai sai mata,hmm to mu fa ba laifinmu bane iyayenta ne Suka ce basa sonka kayi yaro,Auta yace ai ba haka ake neman aure ba daga zuwa sai a kyale su ai sai an lallaba su tukun an musu Nasiha Kawai daga zuwa sau daya shike nan sai ace na hakura ai dama ni nasan ba’a so na,ni bazan auro kowa ba a barni Zan jirata ko zasu yarda su hakura,Mami ta kalle shi Kawai tace babu fa wata Sahar da zamu jira mu wallahi aure za a maka Kama sani wannan iskancin naka bada mu ba,Muje kaci abinci amma ka cire wata Sahar a ranka Wanda bai son mu muma bama sonsa,Mami ta jashi zuwa palonta,da kanta ta zauna tana bashi abinci a baki sabo da Auta ne su Sultana suna ta Masa dariya,Nawwar ne ya shigo gaida Mami ya samu Mami tana bawa Auta abinci a baki,kallonsu yayi yace wannan katon yaron lallai Mami kema,Kai kyale min da Soyayya zata halaka min dana yayi yajin abinci ya kulle Kansa a daki,Mami ta bawa Nawwar Labari,dariya Nawwar yayi yace Auta Wai yasan soyayya Kai duniya gaskiya ayi Masa auren Mami ga kannen Rabia,Auta yace ni fa bana so Cele nake so wlh Indai ba Cele ba to sai dai a barni na zabi wata Ni bana son yarinya kwaila,Nawwar ya kalleshi yace Omaira ai katuwa ce,yace da sauranta bata nuna ba,Mami ce ta make shi tace kaji ko Nawwar wlh aure ko Yana so ko baya so shekara bazai Kara ba Mata ba,Nawwar yace uhm ni ka shirya ma na aikeka Kano gobe zaka Kawai wani takardu,Auta yace to Yana murna ya samu kafa idan ya tafi sai ya zauna ya huta shi bazai kula wata mace ba ma yanzu.
Nawwar na Kira a waya nace Baby Ina ka zauna ne ka taho gida Kai nake jira bacci zanyi,mikewa yayi da sauri yace Mami sai da safe ya fice Yana waya,Auta yace wlh an shanye Yaya itace fa ta Kira na tabbata ko kece bazai wannan saurin ba,Mami tace karfa kaima aga haka Idan kayi aure,Allah ya kiyaye ni da nake tsayayyen mutum ai ba kamarki Mami,Mami tace da zai yuwu ma ai da ka min part Dina na koma,Murmushi yayi yace sai dai ki tafi gidan Nawwar shine babba ai ba kya zo gidana ba,au haka zaka min Auta gidan naka ma bazan zauna ba? to me Zaki Yi a gidan yara mu da idonmu yake a bushe,Mami tace ka nuna min matsayina Auta kishi nake wata zata kwace min Autana,Auta yayi dariya yace wace ma ta Isa ai Kuwa a canja ta,haka Suka Yi ta hira da Mami,Sultana da Nasira ma sun samu mazajen auren su.

Washe gari Auta ya tafi Aiken Nawwar Kano gashi an hanashi kwana ba yanda ya Iya Yana zuwa ya nemi mutumin yace zai turo driver ya dauke shi,Auta yace Kar ya wahalar da Kansa kawai ya Masa kwatance yace yazo Office din da Kansa,Napep Auta ya shiga yaje ya Kai takardun ya fito zai shiga Napep wani matashin mutum zai kai 34yrs ya fanfaro da gudu ya zaga bayan Auta ya buya,Wata tsohuwa tukuf ta biyo shi da bulala tana cewa Baso wato Dan ubanka baka ji baza ka Daina Shaye shayen nan ba yanzu madarar sukudayin din nan kake sha baza ka daina ba, Auta yana kallon ikon Allah katon gardi haka yana buya a bayansa ko kunya baya ji, tsohuwa taci gaba da cewa to ni makwafciyarku ce akwai hakkin makwaftaka a kaina da ku, wallahi Salma baza ta auri wani abokinka ba Dan Shaye Shaye ba,kullum ka dinga kwaso samarin Yan wiwi kana zaluntar yarinya kana dukanta kace sai ta auri wani,Idan an hanaka sai ka kawo wani,itace fa aka baka ka aura wanne hauka ne haka Salma ce ta fito da gudu tace yawwa Inna bazan auri zabin Yaya ba ko zai karshe ni ai ya San shi nake so,yarinya tana murguda baki tana hararar Wanda aka Kira da Baso boye a bayan Auta, Salma ce tazo ta tsaya a gaban Auta ta kaiwa Yayan nata duka ya kauce ta samu Auta,Shima Baso ya kawo hannu ta bayan Auta zai daki Salma ta matsa da sauri ya samu Auta,Auta yaji zafi ya matsa gefe suka bishi Baso yana buya a bayansa ya zuro hannu Salma ma ta kawo nata suka sa Auta a tsakiya suna fada in ya matsa Baso ya sake binsa ya buya a bayansa suka shiga zagaya Auta, Salma ce ta gaji tace zaka dawo ne muje Inna suka juya tare da komawa gida tana cewa wallahi kullum sai ya dake ni na gaji kullum kamar jaka.

Baso da muryar yan daba ya Kalli Auta tare da daga masa hannu yace ahhh Abdul’aziz na manta ban gaishe ka ba ina kwana, Auta dariya ta kamashi lallai kwaya bata yi ba,wani Dan yaro baifi 5yrs ba yazo zai wuce nan Baso ya dagawa yaron hannu yace a’a yaro ban gaishe ka ba ina kwana? Yaron ya tsaya yana kallon Baso,Nawaf ya Kalli Baso gaba daya Shaye Shaye ya haukata shi,ya sake kallon Nawaf yace Abdul’aziz bafa mu gaisa ba ina kwana? Auta yana sani ya Mika masa hannu yace ka tashi lafiya yawwa ina kwana Dan Allah ban dari biyar nan,Baso yace Allah Man? Kasan ina da Hali na kirki Dana tsiya ya zaro wata tsohuwar dari biyar ya mikawa Nawaf yace ungo Allah ya baka,Auta yace tsokanarka nayi fa ni na gode, wallahi sai ka karba karya kake Oga dole sai ka karba ko na maka dukan tsiya a nan,Nawaf yaga Baso tsakani da Allah dukansa zaiyi yana wani tangal tangal a hanya,hannu yasa ya karba,yace yawwa abokina kaga gidanmu can muje,Nawaf yace kayi hakuri gida zanje,hannu yasa ya fisgo Auta gidansu a gefen kusa da hanya yake,wani gida kamar shagon Samari dakuna guda biyu sai wani daki kamar kango sai yar Katanga da kitchen na langa langa bandakin ma rabinsa na langa langa ne,kofar gidan Kuma ko kofa Babu sai buhun Leda, Nawaf ya bishi suka shiga ko ina tsaf neat,Salma tana wanke wanke a tsakar gidan ga wani mahaukaci a gefe yana zaune yana wasanni yana soshe soshe gashinsa duguzaza da kasumba babban mutum ne zai kai 47yrs, Auta yana ta kallon mutumin,Baso ya dakkowa Auta benchi dogo ya goge masa yana tangadi yace zauna master,Auta ya zauna shi dai,Salma tana aikinta Baso ya daka mata uwar tsawa ta mike jiki na bari yace kawo masa ruwa,Auta da sauri yace na gode Dan Allah, kai ba a mana musu a nan yawwa ke kawo masa ruwa sai ka sha,Nawaf yayi shuru Salma ta kamfato masa ruwa a randa,Auta ya Dan dodana bakinsa a bakin kofin kamar yana sha yace yawwa Alhmdllh na koshi kai har naji Dadi kishirwa ta tafi,Salma tana kallon wayon da Auta yayi tayi shuru dai.

Auta yace wannan Mahaukacin fa? Salma tace ae a gari ya tsinto shi,Baso ya daka mata tsawa yace zan ballaki munafuka jibarki kina fama da koshoko me zan ci dake Baba ya mutu ya barmin masifa wlh bazan aureki ba bana sonki,Salma taji kuka ya taho mata tana son Baso matuka a duniya bata taba son wani ba face Baso,Auta shi dai Halin da ya gansu yaji Kuma Salma ba muharramarsa bace gata kyakyawa ta karshen karshe gata katuwa me shape komai ya fita a jikinta son kowa kin Wanda ya rasa fara da ita amma ba fara can ba normal normal dai sai kyawun tsiya kamar me,shi Kuma Auta bata dame shi ba Sam Sahar ce a ransa.
Tambayar Salma yayi yace baku da Iyaye ne?Salma idonta ya kawo ruwa tana kallon Baso tana jin tsoro tace ae bamu da su,Yaya na bashi labari? Baso yace cikin dabanci ku kuka sani ko ki bashi ko kar ki bashi duk daya.

Salma ta Kalli Nawaf tace mu yan asalin Ringim ne da babana da baban Baso uwarsu daya ubansu daya,su biyu iyayensu suka Haifa,tun suna Yara iyayensu suka rasu sai yan uwa Kuma suna can kauye,cikin maraici suka taso ba irin wahalar da basu sha ba a rayuwa har suka dawo Kano suna Sana’a suka samu gidan haya suka yi aure a cikin gida daya kowanne da matarsa suna zamansu lafiya kuma matan nasu duk Yan Ringim ne dangi ne,lokacin baban Baso shine Babban Haladu matarsa ta haife shi yaci suna Umar ana ce masa Baso,ni kuwa ko cikina Babu lokacin suna zaune har sai da ya shekara goma sha biyar sannan aka samu cikina,lokacin Kuma Maman Umar Baso ta rasu sai Babansa,ranar da Mamata ta haife ni anyi murna naci suna Salma,muna zaune lafiya har Baso ya cika shekara 32ni Kuma ina shekara 18, watarana Mamana Aisha tayi girki shinkafa da wake lokacin ina Makaranta, Baso kuma ya gama iya secondary an turashi almajiranta har ma yana Shirin dawowa ya zama saurayi sai aure,ni Kuma ina Ss3,Mama ta zubawa Haladu Baban Baso abinci itama ta zuba nata taci ta koshi,Sallar azahar tayi da kyar lokacin cikinta ya fara ciwo tana idarwa ta kwanta daga nan ko tashi batayi ba ta rasu,Ranar Kuma Baso ya dawo ganin gida ya zama saurayi ashe ba karatun yake ba kawaii Shaye Shaye ya koya a almajirantar shi,tun yana yaro a boye yake sha Idan baya gida yana can duk an zaci mutumin kirki ne ashe ya lalace illar tura yaro wata uwa duniya da sunan Almajiranta wasu dai ba karatun suke ba,sabo da Babu me daukan nauyinsu yunwa masifa ce ace yaro bara zaiyi yaci ya koshi,Babu tarbiyya Babu me lura da shi bare lafiyarsa duk sai abinda yaga dama.
Baso yana zuwa ya samu Haladu Babansa yana Shure Shuren mutuwa ina shigowa Nima da Uniform Dina na iske Mamata ta rasu bata motsi na fito da gudu na samu Baso gaban Haladu yana Shirin tafiya lahira.

Haladu Hannuna ya kama ya kama Hannun Baso ya hada waje daya yace Baso gata nan ban muku dole ba amma zanso ace ka auri Salma,ka daure ka auri Salma Kaine kadai zaka rike min marainiya yar Dan uwana da Amana,Karka bari tayi kuka ka aureta ku zauna lafiya ka kula da ita,Karka sake komawa Makaranta ka zauna ka nemi Sana’a kuje danginmu su daura muku aure Karka Kaci Aman….kafin ya karasa rai yayi halinsa, ranar munyi kuka na fitar hankali ni da Yaya Umar Baso, bayan anyi bincike aka gano ashe waken da Umma tayi amfanin da shi ta dafa shinkafa da wake maganin kwarin da aka Saka masa guba ce wacce su dai tafi karfin jininsu tunda wasu sun dafa Kuma basu mutu ba amma su ta musu illa.

Salma taci gaba da cewa abinda iyayenmu suka mutu suka bari shi muka tattara muka siyi wannan Dan gidan muna zaune,tace Yaya Baso kayi hakuri zan fadi halinka,yace to yar iska sai kinci ubanki karasa ina ji,Salma tace ni da ka ganni bana jin magana ina da tsokana,shi Kuma Baso kullum Shaye shayensa yawa yake gashi ya iya gyaran machine sana’arsa kenan gyaran machine yana Shaye shayensa amma Kuma ba laifi kullum muna ci mu koshi ko ba Dadi,yana masifa yaki cikawa Mahaifinsa burinsa yace baya so na,ba wacce ya tsana Irina,kullum sai ya dake ni ya zageni ya tsine min ba muguntar da baya min…kafin ta rufe baki a labarinta Baso yace to bana sonki ko dole ne nace bana so, Salma taci gaba tace duk duniya ni ba Wanda nake so Irin Baso ina sonsa a duniya amma yaki aurena,ni ke masa wanki da guga,girki,ebo ruwa,komai da ka sani macen aure tana yi ina masa burina ya aureni,rannan daga tambayarsa yaushe zai kai Sadakina wallahi har targade ya ji min,gashi a haka yana da addini ga taimako,Kaga wancen mahaukacin tun muna Yara kowa ya sanshi a bola yana tsince tsince sai dai baya duka sannan haka zaka Ganshi a unguwa yana bin gidaje da kwanon barar abinci ana bashi sadaka yana ci,Kuma baka Isa ka wanke masa kwanon ba,sannan ko an masa wanka ya dinga ihu yana zubawa jikinsa kasa da bola,sannan baya magana,bashi da inda yake kwana haka zaka ga ruwan sama ya masa dukan tsiya a bola,sauro,sanyi rana duk a Kansa,amma Baso Baba yana rasuwa kaga wancen dakin zaka Ganshi kamar kango to dakine Baso ne ya dakko mahaukacin ya kawo shi,wallahi duk sati sai ya masa wanka,Idan bashi da lafiya shine yake Kiran mutane suna tayashi ya kaishi asibiti ayi masa Allurai,abinci Kuma kullum da kwanonsa ina dafawa zai fito har ya Saba ma.
Dakinsa ne leka ka gani har net ya Saka masa amma dake mahaukaci ne sai ya fincike net din ya kwanta haka sauro yayi ta cizonsa, Dan Allah ai ya cancanci a so shi ko?

Nawaf yana gama ji yace ya cancanta gaskiya ta wani bangaren ma sai wannan ya zama silar shigarsa Aljanna wannan ba karamun jahadi yayi ba,Baso yana ciccijewa yace ke zan tattaka ki wallahi Allah bana sonta ni bana son kyakyawa,Auta dariya yayi ana Neman me kyau shi baya so,yace kai to sai mummuna? Yace ae ni mummuna zan samu na taimakawa,Nawwar yace lallai Shaye Shaye ya maka illa baka ganewa ka haukace ai wannan tayi gata da hankali kalleta fa chaschas chas da ita,Baso matashi son kowa kin wacce ta rasa da shi Shima yana nunawa da hannu yana magana bana so wallahi,Salma ta fashe da kuka tana cewa Idan baka aureni ba mutuwa zanyi Dan Allah ka cikawa Baba burinsa ka biya Sadaki na,a fusace Baso ya mike ya zare belt dinsa ya fara tafkar Salma,Auta ne ya kwaceta da kyar akan kawai tace ya biya Sadaki ta har da fasa mata gefen Ido tana kuka wiwi,Nawaf a ransa yace ya kamata a taimaki yarinyar nan gaskiya zai iya kasheta watarana gasu su biyu a gida Kuma ba muharramai ba wani abu zai iya faruwa gashi shi Umar din Dan kwaya ya fara haukacewa,Nawaf tashi yayi yace zai tafi Salma ta biyo shi tana kuka tana cewa Dan Allah duk da cewa baka da wasu shekaru kamar Yaya ka sa baki ya aureni,Auta yace karki damu zan taimakeki,ta fara murna ta goge hawayenta kamar ba ita aka gama zanewa ba, tace yau kawata Sumayya sai ta ji labarin nan Umar zai aureni tana tsallen murna,Nawaf yayi dariya suka fito har Baso.

Suna fitowa kofar gida Salma taga me siyar da madarar turare da yawa zai wuce da abinsa a Kansa,Salma tace tsaya me turare,ya kawo ya sauke kwandonsa na turare,Salma sai da ta samu Wanda zai wahala a samu a wajensa dama haka takeyi Idan taga me turare wai Dan ta samu na banza,sai ta Kira Wanda babu ma sunan turare haka wai malam kana Umarsal? Sunanta ta hada Dana Baso Umar ita Kuma Salma shine Umarsal,Bai taba jin sunan turare haka ba bashi da shi yace Hajiya Babu,tace a’a dole kana da shi Muji na wajenka,Me turare ya dinga Bude turarukansa tana dangwalawa a hannunta kala yafi talatin tace gaskiya Babu kayi hakuri jeka,shi me turare sana’arsu ce haka dole sai an dangwala kaji irinsa,yace to ya tattara tarkacensa ya tafi,yana tafiya ta murje a hannunta ta shafe hijab dinta da kayan jikinta har wuyanta ta shafe tace Alhmdllh naci banza ina fita za a ce na Faso gari,Auta yana tsaye yana kallon ikon Allah dariya ta bashi da son banza yace ke turare 500 baza ki iya siya ba? Salma tace rufa min asiri ban iya almubazzaranci ba shinkafa bata ishe ni ba ina naga ta kamshi ta wuce tayi tafiyarta ta bar Baso da Auta.

Baso yace yawwa ta tafi yanzu kai Dan inane? da Alama ku masu kudi ne Kalli shaddarka Kalli ma fatarka wallahi kayi hankali yan Hisba suna ganinka a Kano sai sun aske maka wannan gashin na kanka da ka masa wani aski mu a nan easy dai easy dai abokina Allah wallahi,Auta yayi dariya yace Sabreen tazo ga Dan uwanta wannan ya girmi kanta,Umar Baso yace yawwa wani Deal zamu yi,kai kaga da Alama kana da kudi,ni so nake na samu kudi na alkinta rayuwata gashi gyaran machine nake yi,Dan Allah Oga ko zaka lallaba ka rufa min asiri? Zabura yayi ya sake ja da baya yana gwadawa da hannu yace kaga master asiri zaka rufa min ya sake kankame hannayensa kamar me jin sanyi ya makale a jikin Katanga yace wani taimako zaka min kaga kullum sai na roki kudi wajen me duka kaga na roki trillion dari,billion bakwai,na dawo million talatin, na sauke farashin zuwa dubu dari biyar,dubu dari,dubu hansim har na dawo dubu biyar to abin sai godiya kudin sunki zuwa,jari nake nema Dan Allah ko zaka siyi Salma ni ka siyeta duk yanda zaka yi kayi da ita,Idan ma za a iya maka aure kazo na baka ita ka bani million daya gata nan.

Auta yace ba ruwana ya juya zai tafi abinsa amma Umar ya tare masa gaba yana karkace baki yace ya haka yawa kake Oga haba abokina,haba Yayana to ka aureta ka bani dubu dari biyar,kai dubu dari uku ma ya Isa ai baza tayi tsada ba tunda ba a gidan masu kudi ta taso ba,Nawaf yace to naji kawai ya furta sabo da ya kyale shi ya tafi,yace Yayana bani number ka zamuyi Business din ko baka gane bane ey kar ka Yi mini ae yane ka gane,Nawaf ya bashi number dinsa suka rabu Umar Baso yana ta uban murna zai rabu da kaya ya huta ga kudi zai samu,Nawaf Kam Airport ya wuce yana tunanin lamarin Baso shi Kam ba ruwansa bazai iya ba zai Jira dai Sahar dinsa.
Bayan ya koma gida da kwana daya Baso ya addabi Nawaf da Kira a waya Nawaf kuwa yaki dagawa abinsa ya share Kiran yaki dagawa Sam.

Yana dakinsa a kwance Mami ta shugo tace gobe dai kasan zaka fara zuwa University an gama komai ko? Yace ae na sani Mami,kallonsa tayi tace ko tunanin Sahar dinne? Kai ya daga mata wai ae ya furta please Mami kije ki ji min ko zasu yarda ni nafi sonta,hmm amma Idan naje suka ce a’a shike nan ka hakura? Yace ae na hakura amma kije,to shike nan cewar Mami.
Bayan kwana hudu Mami ta shirya tare da Nasira da Sultana suka siyi kayan kwalliya masu kyau da turaruka driver ya tafi kaisu da yardar Baffa.
Mami suka ga gidan su Sahar masu kudi suma,iso aka yi musu,Sahar dince ma ta tarbe su tana Palo tana kallo dama Nawaf ya fada mata sun taho,taci kwalliyarta sosai ta sha Atamfa me tsada,har kasa ta durkusa ta gaishe da su Mami tace bari na Kira Hajiyanmu ta haura sama da sauri,tana uban murna Hajiyansu tace sun zo kenan? Sahar tace ae,shi yasa naga kina murna kamar Zaki tashi ki sani wallahi baza ki auri wannan yaron ba yaro karami wani aure zai iya rikewa,ga saurayi na kirki babban mutum me hankali me kudi na Kansa ba Wanda ya dogara da kudin Iyaye ba,wallahi Idris Zaki aura nutsatsen yaro ni da mahaifinki ma ki sani baza mu yarda da wannan yaron ba karki ce ban fada Miki ba.
Hajiya fitowa tayi wajen su Mami da fara’a suka gaisa sosai,sunyi hira Mami tace dama akan maganar Nawaf ne da Sahar…kafin ma Mami ta rufe baki tace ai an Riga anyiwa Sahar Miji Idris shi zata aure,ina Sahar ina Nawaf wannan ai yayi kankanta sai dai karatun ai,ya tafi Makaranta wannan ai Gigi ne na Yara haba Kuma sai ku biye masa shirme ne wannan,Baban Sahar ne ya fito zai fita Hajiya tace Mamin Nawaf ce yaron nan da aka dinga rikici da shi yana hurewa Sahar kunne,to…to.to Allah sarki ai kin fada musu anyi mata Miji Ina Sahar ina wannan,Sahar tana gefe ta labe tana kuka wiwi bata da bakin magana face kawai ta kyale Nawaf yayi kokari yayi iya yinsa,Mami ta gama jinsu irin rashin iya magana ta iyayen Sahar tace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa suka ce Ameen suka watse suka bar su Mami su kadai a Palo da ruwa da lemo a gabansu,Sahar ce ta fito tana cewa Dan Allah kuyi hakuri,ba komai wlh baki da laifi ke amma kinji abinda suka ce kiyi hakuri kiyiwa Iyayenki biyayya Dan Allah karki sake Kiran Nawaf ku hakura da juna Allah bai so ba.
Sahar tana goge Kwalla ta raka su Mami har mota suka bata abinda suka kawo mata tayi godiya ta koma ciki bata da bakin magana iyayenta sun gama da ita.

Mami tana komawa Nawaf ya tareta a Palo yana tambaya Yaya? Mami ta Mika masa waya tace ji da kunnenka shi yasa na maka recording sabo da Karka dameni,Nawaf ya kunna ya gama jin komai a kunnensa Sultana tace sai kaga ma irin wulakanci da suka mana wallahi Auta amma Sahar bata da laifi,Nawaf yace sai na Riga yar tasu aure inshallah auren huce takaici zanyi,Mami tace ko kai fa kayi hakuri ka nemi wata amma tare da bikin su Sultana za a hada da naka tun wuri ka nemo mace wlh ko mu zabo maka ni da Baffanka,Auta yace yanzu Mami ai dai sai ku bari na huce ko ku sanda na hadaku kuka shirya haka nayi muku? Auta zaiyi hawaye yace Mami daga cewa ina son aure shike nan sai kuce ko ban samu wacce nake so ba zaku zabo min Hakan yayi kenan? Baffa Shima ai ba haka mukayi da shi amma Yaya Nawwar shi kuka kyaleshi ya zaba ya darje ni sabo da bani da kudi kune zaku min komai shine ni za a min auren dole,Shut up Baffa ya furta da shigowarsa kenan yana murmushi yace Auta kana bukatar aure bama so ka fada wani Hali ka nemo to mun baka zabi kafin bikin Su Sultana Idan ba haka ba mu munyi maka mata ma,Auta bedroom ya shige kawai abinsa ya bar Mami da Baffa baki Bude

Cele tunda ta sauka take garari tana zaga unguwar ta rasa ina zata shiga har gari ya waye inda taji Kiran Sallah nan ta nufa,masallacin bangaren mata tayi tayi fitsari ta fito tayi Alwala tare da Sallah sannan ta fito taci gaba da tafiya har rana ta fito mutane ana ta hada hada,Cele yunwa ce ta ciyota ta shiga wani Dan waje inda ake soya kwai da tea,tana shiga tace da me Kwan a soya mata guda biyar,shi dai yayi mamaki mutum shi kadai haka ya soya biyar ya cinye,tace a hada da dankalin turawa sai bread da tea aka zuba mata komai,inda aka tanada na cin abinci ga me ci a wajen, nan ta zauna taci ta koshi tayi tafiyarta,balaraben yana ta Kiranta da larabci Hajja amma ina tayi tafiyarta sai da ya fito da gudu ya riketa Cele tana juyowa ta mareshi gauuu ta fara masifa da Hausa aikin banza na zaci ma a kawo Kaduna nake,jiya ai ta malali na wuce na shugo ta unguwar sarki ashe nan a unguwar Rimi nake ma Dan wulakanci zaka rike ni Abuja zan tafi,ta kwaso kudi da yawa ta watsawa balaraben tana masifa tace ku dama yan kantin Kwari baku da mutunci indai aka zo sarin kaya sai kunyi wulakanci aikin banza kano dinma zan bari gaba daya tayi gaba,tana tafiya taga masu gasa kaji ta karasa wajen tace akwai kifi na sukunbiya? Ko yan gezu ba Wanda ya kulata,ta dauki hanyar harami tana Maheerah Kiji tsoron Allah,Kaka ya dawo daga masallacin kaabah ya kwana yana addua a hanya yaci karo da mutane sun rufe wani waje wai wata ce a Nigeria ta bata sannan bata da hankali mahaukaciya ce,Bai San Cele bace yayi tafiyarta yace su karanta sai naje askarawa suyi ram Dani yanda nayi kiba nayi jajir Dadi haka nada ni ba.
Mutane suna ta zuwa inda Cele ta fadi tana birgima da Shure Shure tace cewa wlh sai na soya Awara.
Haka ba Wanda ya saurari Cele sai wata mace wacce ta Dade a kasar ta dauki Cele tana zagawa da ita gidajen takari mata da maza ko an Santa har ta zo laying su Kaka,lokacin Kaka juya baya a layin yana siyen kwai dafaffe wajen takari suka ga Cele ta kwace da gudu ta nufi wajen Kaka ta rukunkume shi ta baya tana murna tana cewa Kaka, Cele da karfi Kaka sabo da bai shirya ba ya fadi a kasa wanwar sabo da karfin Cele gashi ta wani yi tsalle a jikinsa,kaka ya juyo yaga Cele dinsa, ya fara cewa a’a a’a Cele ta ya rungumeta suna murna,lokacin Cele ta dawo hankalinta kanta ya Bude kwakwalwarta ta dawo dai dai,tsalle take tana murna Kaka ma haka ta saki kuka Kuma daga baya da ta tuna da Ahsan.

Tace Kaka yace Cele kyale labarin nan mu koma ciki kawai ya rike hannunta suka shiga lifter zuwa bangaren kaka har dakinsa,Zama sukayi a gefen gadon kaka Cele tace Kaka ji yanda ka sake yin wani kyau da kiba kayi jajir, kafar Kaka ta kalla tace ina kaushinka kaka? Yace ya gudu Cele dole kiga nayi ja ga Zaki ga maiko kullum a cikinsa nake Cele ta,Kaka mu sake rungumewa suka sake rungumewa da kaka karo na biyu sannan Cele tace Kaka Ina yini tana washe baki murna ta isheta Kaka ya amsa yace lafiya kalau ‘yata ta kaina,kaka Nawa Cele ta furta,kaka ya saki shewa kamar mace heeeeeeey wuuuuuu ya Mika mata hannu suka tafa,Cele tace Kaka na bayan hannu mu tafa dukkansu suka juyo da bayan hannu suka tafa,Kaka yace Cele ni sai naga kamar kin kunkunbura wallahi kamar baki da jini inda kisan haihuwa kika yi Cele kalau kuwa? Cele ta tuna dake kwakwalwa ta dawo tace Kaka labarin dogo ne Kaka bakin Abba ne ya bini da yace sai nayi ciki,Kaka kirji ya dafe yace Dan ubanki ba dai kafa kika budewa wani ba.

Cele tace to ka tsaya mana kaji labarin, ta kwashe labarin komai da komai tun sacewarta har zuwa yanzu data gudo karshe tace Kaka makuwa nayi kaina sai naga ya juye na rasa a Ina nake,gashi nasan kowa amma abinda nake gani daban sai na ganni a garin Kaduna,anjima na ganni a Kano jiya ni a cikin dajin falgore na ganni,dazu fa sai na ganni kamar a sambisa Allah Kaka amma yanzu sai naji Ina ganinka na dawo dai dai kaka za ayi burar….Dani,sai Kuma ta tuna Ahsan tace Kaka yau dai jikarka tana son wani a duniya,Kaka yace Allah jikalleta waye me sa’a haka? Ahsan mana yanzu Allah sarki na taho na barshi bai sani ba,Kaka yace Idan ma Bai nemeki ba sai mu koma,ita kuwa Maheerah matarsa Allah yayi mana maganinta ta cuceki jikata,Cele tace ba komai Kaka kaddara ce sannan bakin Abba ya bini yayi min ma da kyau da cikin ya zube,Kaka yace ai ni yanzu farin ciki ya samu jikata ta dawo,Cele tace kaka ka bani labarinka bayan mun rabu,Kaka ya furta Allah ya takaita ni da aka so ayi farfesu na sau biyu ana siyar Dani kaka ya bawa Cele labarin taji tausayinsa tace wallahi kuwa da sun samu nam me auki kanka kadai kaka ya Isa ya cika musu tukun ya,Kaka yace to abu ne kamar fanteka,Kaka yace yanzu akwai kudi ki huta sosai kafin ki fara sana’a,Cele ta zumburi baki tace gaskiya mu koma Nigeria zama a nan baida amfanin face wahala da zubar da mutunci kadan ne suke dacewa gaskiya.
Hakane Cele amma saurayin naki fa a Ina zai ganki mu Jira mu gani,tace to Kaka ba sai in yana so na ba,bafa cewa yayi yana so na ba nice kawai nake sonshi kadan,ni ko bai zo ba kawai muci gaba da rayuwar mu a kyale shi,yace to Allah ya zaba na gari,Cele duk ta kumbura bata da jinin kirki.

Ahsan bai Farka ba sai washe gari sai da ya gama Shiri fes ya fesa uban wanka ya fito ya zauna a Palo yana jiran Cele shuru,shuru har rana tayi nisa 12pm tashi yayi ya leka dakinta wayam,ya fito ya Bude daya dakunan amma shuru,gidan ya duba ko Ina wayam ba kowa,hankalinsa tashi yayi gaba daya mussamman da ya tuna fa a rude take bata da lafiya ga rashin jini a jikinta ga magungunanta ta barsu,hankalinsa yayi mugun tashi ya fito cikin sauri ya shiga bakar motarsa yana bin layi layi yana dubawa amma Babu alamarta,rasa inda zai sa Kansa yayi gaba daya,parking yayi a gefen hanya ya kifa Kansa a saman sitiyari ji yake kamar yayi hauka,Innalillahi wa Innayhirajun yake furtawa kawai kafin daga bisani hawaye suka fara sintiri a kumayunsa,hankali ya tashi a fili ya furta da larabci bazan iya rayuwar ba sai da ita, directly ya wuce gidan su Maheerah yana zuwa akace Maheerah tana wajen aiki iyayenta sun zaci biko Yazo sai kawai ya Mika musu takardar sakin da ya Dade da rubutawa bayarwa ne baiyi ba sai yau ya mikawa mamanta yace Idan tazo a bata,mamaki ya kamasu suna tambaya ko lafiya yace lafiya lau kawai na saketa bana bukatar sake ganinta a rayuwata na tsaneta,dama makantar karya nayi bayan na kamata da idona. Yana gama fadar haka ya juya ya bar unguwar,gidan abokinsa Husam ya nufa ya nemo shi yana bashi labari suka tafi can garin Makkah ko zasu dace.

Cele kuwa akwai kudi a wajen Kaka cewa tayi kawai Kaka mu koma gida Nigeria,Kaka yace a’a an kusa fita aikin hajji ki tsaya Idan muka sauke farali sai mu koma gida lokacin Idan saurayin naki Yazo shike nan,Cele tace ina sonsa amma ni wlh bana son zama a nan Sam ni bazan iya aurenshi ba gaskiya sannan Kaka jikinsa yayi ja da yawa kullum na dinga ganin Jan nama,dariya Kaka yayi yace yanzu akwai kudin da aka bani sadaka muci dadinmu muyi tsaraba ana gama aikin hajji mu gudu kasar mu,Cele tace gobe sai na samu gidan da mata suke na zauna a can ko? Kaka yace kwarai kuwa ai zamana a nan na Saba da mutane da yawa amma yau kwana zamuyi muna hirar haduwa,ai kuwa kwana suka yi suna Hira suyi bacci su Farka Cele tayi shimfida a kasa Kaka yana saman Katifarsa su biyu ne a dakin dama kaka kudin da ya samu daki ya samu shi kadai yana jin dadinsa.
Washe gari da yamma Kaka da Cele suka yi wanka suka fito gari Cele murna ta kamata yau gata ga kaka ta rike Hannun Kaka suna tafiya harda cewa Kaka ba’a wakar soyayya a Makkah ne? Kaka yace Ina fa akeyin soyayya kina kusa da dakin Allah sai dai wakar yabon manzo, Kai zan yiwa Kaka masoyina,wajen Taron askarawa suka karaso wajen da motarsu suna tsokanar Kaka da larabci sabo da kaka ba laifi ya iya da yawa sabo da yawonsa,tambaya suke yarsa ce? Yace ae,suka dinga cewa suna son Cele,haka da suka je ma kanti Cele zata siyi kayan sawa kowa yace ga kudi Dan Allah yana so a bashi ita zai aura,harda masu alkawarin Sarkokin gold ganin Yan Nigeria mayun kudi da Gold ne,suna hanyar dawowa wasu askarawan sun fito Kame cikin sirri,Kaka ya gane yace Cele gyara kafarki wancen kame sukeyi wlh,ai kuwa sai gasu sun biyo su Cele suka take a million Cele mamaki irin gudun Kaka yake ya fita gudu ita da take sabon jini ma,da mota suka biyo su Cele suka bi ta lunguna ga kaya Kaka ya rungume Wanda suka siyo,wani me shegen gudun tsiya ya kama abayar Cele tana juyowa ta masa wani shegen Elbow da gwiwar hannu ya saketa ba Shiri ya tsuguna a wajen yana Sosa hancinsa ya sake harzuka yace ba komai ai ana gama aikin hajji za ayi kazamin kame har gida gida bakake zasu shugo sai sun koma kasarsu,yace Cele zata ci ubanta Idan ya kamata ai sai an kaisu sijin inda ake cewa kurkuku Idan suka kama mutum sai an fara kaishi can kafin Nigeria to sai ya sa an gana mata azaba tunda ta masa wannan dukan.

Cele gidan su Samira Kaka ya samo mata wajen kwana su uku ne duk daki bai San Yan madigo bane,Cele ta tafi da kayanta gidan wasu manyan mata ne a gidan sunfi shekara ashirin a can suna matukar jin larabci su kansu takari dake gidan basa Hausa sai jefi jefi larabci suke yi,Samira ma zama a ciki yasa nan da nan ta iya larabci sosai, Cele tana zuwa tayi sallama wata Hajiya wacce itace ta samowa Cele wajen kwana ta amsa tace bakuwar alkhairi barka da zuwa ta nuna mata dakinsu da gadonta a gefe, dama sun biya kudin da komai.

Matan gidan sai kallonta suke suna lashe baki sai kace mayu,Cele tace wai Meye haka ne kamar karnuka sai wani lashe lashe kuke ba tsofaffi ba ga yaran kalau? Kafin ta rufe baki taga Samira dakinsu Daya,dama tare suka zo kasar,Samira tace Cele wai kece? Kin ganeni wacce muka zo kasar nan tare,na ganeki Kuma ai naga kin koma fara ne kinyi wata kiba,Samira tayi dariya tace uwar sana’a ke Kuma gani nayi kin Kara budewa kin Dan kumbura Kuma gaki fara kin Kara yin wani jakin fari tas anya kuwa Cele kina da jini? Cele tace naje asibiti suka ce jinina yayi kasa sunce na koma a rubuta min maganin na bar Riyad na dawo nan,Samira tace tab ai jini ba abin wasa bane akwai wata likita tana nan takari ce zan rakaki ta rubuta Miki magunguna ba a wasa da rashin jini,Cele tace na gode.

Tunda Cele tazo sai dai taji suna ta larabci sun San bata ji amma Basu mata Hausa ko ta gane ko kar ta gane sai dai tayi ta tambaya tana cewa me akace sai a fassara mata a haka take koyo,da Samira suka je wajen likitar ta duba Cele tace sai kace wacce ta haihu, Cele tace ko daya ta boye labarinta ta dai rubuta musu maganin suka je suka siya ta dawo tana Shan abinta.
Ahsan ya dira a garin Makkah tare da abokinsa a airport wani driver yaje ya dakko su Dan uwan Ahsan ne babban mutum ne amma shi a Makkah yake zaune, Hotel ya kaisu suka kama dakunan shi da Husam sannan ya kawowa Ahsan mota dalleliya me kyan gaske sabo da zasuyi amfani da mota dole sai da driver Wanda ya fisu sanin garin Makkah, shi yasa aka hada su da wani bakin fata bahaushe ne amma haifaffen garin Makkah ne yana jin both Hausa da larabci,mota suka shiga bayan sun sha Shiri Husam yana gaban mota Ahsan ya kame a baya ya wani harde kafa sanye cikin jallabiya fara Kal me tsadar gaske,takalminsa baki agogonsa baki me tsada sai uban kamshi da sheki yake,gashin ya sha gyara

Baso kuwa Salma ya kwalawa Kira ta fito jikinta yana rawa yace kinga bana son hauka ko baki ga gidan nan ba ruwa bane? tace na sani zan ebo ne,uban me kike yi da baza ki cika gida da ruwa ba,ki tafi tun wuri ki Tara ruwa banza shashasha wa ya sani ma ko tsuntoki akayi za a hadani dake ace na aureki,ke Dalla tafi can uban me zan ci dake bana sonki,Salma ta fara hawaye ta tsani ace Baso baya sonta ko da wasa,ba wulakancin da dukan da baya mata amma indai Baso ne ko a jikinta,baza ki wuce ki tafi ba kin tsaya kina kallonsa bakar yar iska ya kai mata wani duka Allah yasa ta fada daki da gudu ai kuwa ya rufa mata baya ya hau jibgarta yana cewa Dan uwarki ni kike yiwa kallon Soyayya? Salma tana ta ihu tana bashi hakuri tace wallahi bazan sake ba kayi hakuri.
Mahaukacin da suke taimakawa shine ya shugo dakin da rarrafe yana jan kafar Baso alamar ya bari,Baso juyowa yayi yaga mahaukacin ne dama ya Saba Idan yaga suna fada Yazo ya rike kafar Baso,Baso da maganar Yan daba yace na hakura na hakura Uban gidana ka fada mata kar ta sake yawwa bana sonta ni ya juya ya fice,Mahaukacin ma da rarrafe ya fito ya shiga harkarsa aka bar Salma tana kuka har ta gaji ta fito ta tafi ebo ruwanta tana hawaye ta gaji da aiki amma ya ta iya.
Yayan Salma wato Umar Baso kullum sai ya Kira Auta akan Business dinsu,Shi Auta ma karatunsa yake ko bi ta Kansa bai yi sai dai yace zaizo ne.

Cele kuwa tana kwance tana bacci fasikan gidan wata tsagera Meenal dakinsu Daya da Cele da Samira,ta lallabo jikin Cele tana shafa mata gashi ta gangaro Wuyanta,Samira ce ta Farka tace da larabci wallahi Idan ta Farka ta kamaki Zaki ci ubanki yar tijara ce na Santa sosai bata da mutunci Idan ka shiga sabgarta ki kama kanki tun wuri gwara ma ki dawo muyi abun mu yanda muka Saba,Meenal tace ni ita nake sha’awa yanzu Kuma sai na sameta ta juyawa tana shafa gashin Cele ta wani zaro harshe, kirjin Cele ta gangaro tana shafawa Cele ta zaci mafarki takeyi tana cewa Ahsan Dina ya Isa haka,farkawa tayi jin ana kokarin dage mata riga tana bude Ido taga ba mafarki take ba macece yar uwarta take taba mata jiki sabo da asara, Cele tashi tayi zumbur ta dura wata ashar ta mike tace yau za fitar da gawa a gidan nan….

 

 

Kuyi hakuri Fans jiya ban gama nutsuwa bane shi yasa ban baku ba, dole ce ta sa,ayi hakuri.

Duk naga masu tambayar ci gaba,masu tambaya ko lafiya da masu Text da masu Kirana na gode na gode Allah ya bar kauna

Mayyata MRS CHIEF Ina godiya kinji dai ME ASMA da kunnenki

 

 

AsmaBaffa
08061929616[8/15, 9:28 PM] AMINA KABIR CAPS: ‘YAR AIKIN KARUWAI 2
MATAFIYA

Book2

46-50

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN

 

Page naki ne
MAMA GEE

godiya ta mussamman
BINTA UMAR ABBALE

Gingina ga me karanta Audio na books dina
HAUWA S ZARIA

 

*MISKI 3in1 Alfirdaus* Albishirinku original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi yana dauke 1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al’ada inda hali za’a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi bayaga haka sunnah ne amfani da miski
2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi
3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan sosai, kuma ana shafawa a hammata yana kawar da da wari karku bari abaku labari ‍♀️‍♀️

Masu bukata ku ne wannan number
09065959708

 

 

Back to top button