Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 59

Sponsored Links

PAGE* 5⃣9⃣

Wajen k’arfe biyu su yarima suka dawo lokacin zarah tana a room d’insu tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya yarima yaturo k’ofan yashigo,

Dagudu zarah taje tafad’a jikinsa cikin wata irin siririyar murya tace sannu da zuwa my prince.

Rungumeta yayi sannan cikin kasalalliyar murya yace yauwa ya gidan?

‘Dago kai zarah tayi suka had’a ido tace gida ba dad’i saboda baka nan ammah yanzu da kadawo yayi dad’i.

Yarima baisan lokacin da murmushi yasu6uce masaba yace tsokana ko?

Marairaicewa tayi tace dagaske fa.

Rik’o hannunta yayi yace muje parlour kiga abinda nasiyo miki,
Zarah bata musaba tabisa suka fito parlour.

Babban trolly ne tagani aje koda yarima yabud’e cike yake taf da kaya, saman kujera yazauna yace duba kiga.

Zarah bin kayan tayi da kallo sannan tafara d’agawa d’aya bayan d’aya daga gowns ne sai English wears jibgi d’aya da sleeping dress, rigunan tafara d’agawa daga mai budad’en k’irji sai ‘yar firit wadda bama zata rufe cibi ba, wasu ma sharashara ne, sai mini skirt da wando atak’aice dai dukkan kayan ba wanda zaka iya zama da su cikin gida bane, saidai in daga kai sai mijinkane.

‘Dago kai tayi takalli yarima murmushi yasakar mata yace ya sunyi?

Itama zarah murmushi tayi tace sunmin kyau sosai.

Cikin jin dad’i yarima yace toh kije kigwada, zarah kallonsa tayi tace toh ammah ai kayan bazasu sanyuba cikin gidannan tunda bamu kad’ai bane.

Yarima jingine kansa yayi da kujera sannan yace zasu sanyu man in zaki fita ba sai kidinga d’aura zaneba.

Shuru zarah tayi nan taja trollyn tashiga bedroom da shi, d’auko kayan tayi tafara dubawa tana gwadawa a jikinta daga ‘yar riga iya cinya, sai wacce bata rufe cibiba sai marar hannu, gunguni tafara tace inbanda abin Yarima ya za’ayi yasiyo min wad’annan kayan sai kace wata arniya,,,daidai ta d’auko wata zata saka sai gashi ya shigo.

Juyowa tayi takallesa yana tsaye bakin k’ofa ya hard’e hannuwa, murmushi suka sakar ma juna sannan tajuya tasaka rigar,

Kallon kanta tayi ta mirror rigar shara-shara komai na jikinta a waje yake ga iyakar tsawonta iya cinya.

Tana shirin cirewa sai jin yarima tayi ya rungumeta ta baya, lumshe idanuwanta tayi tana murmushi, yarima ta cikin mirror d’in yake k’are mata kallo, ahankali cikin kunnenta yace kinyi kyau baby.

Zarah bud’e idanunta tayi ta mirror suka had’a ido nan tasakar mai murmushi sannan tace nagode,

Gyad’amata kai kawai yayi sannan yajanye jikinsa daga nata, Zarah tana shirin cire rigar yace please kibarta.

Juyowa tayi takallesa sannan tace lunch fa zamuje kayi,

Duba agogon hannunsa yayi sannan yace no zan fara wanka before inyi lunch.

Ohk, bara inje inhad’a maka ruwan,

Yarima baice komai ba yawuce yad’auko towel,
zarah toilet tawuce tahad’a mai ruwan wanka lokacin da tafito ganin yana cire kaya yasa tafito takoma parlour.

 

Zarah tana zaune yafito sanye cikin k’ananun kaya sunyi mai gwanin kyau.
Tsaresa tayi da ido tana kallonsa.
Ganin batada niyar daina kallonsa yasa yarima yace ya dai?

Janye idonta tayi cike da jin kunya tare da mik’ewa tace bari incanza kaya muje kayi lunch, ta gefensa tatafo zata ratsa tawuce, jawota yarima yayi tafad’o jikinsa, wani irin kallo yake aika mata da manyan idanunsa kallon da yake kashe mata jiki sannan yace ba sai kin canza kayaba kisaka hijab da zane kawai sai muje.

Cikin kasalalliyar murya tace toh, ba yadda ta iya haka tawuce bedroom tad’auko zane, cikin ranta tana cewa ina ma ace guy d’innan sona yake da naji dad’i.

Hijab d’inta har k’asa tad’auko tazura sannan tafito tasamesa a parlour yana jiranta, tsaye tayi tana kallonsa ganin yadda ya jingine kansa da kujerar da yake zaune samanta, cike da tausayi tabisa da kallo dan ko ba’a fad’aba tasan tunani yakeyi.

Gyaran murya zarah tayi nan yarima yad’ago kai yakalleta yace kin fito?

d’aga masa kai zarah tayi batare da tayi magana ba, nan yamik’e yana gaba tana biye da shi suka fito main parlour basu tarar da kowaba cikinsa nan suka wuce dining, zarah kujera tajawo masa yazauna sannan tazauna gefensa nan tayi serving d’insa, ganin bata da niyar zuba nata yasa yarima yace ke ina naki?

Yamitsa fuska zarah tayi sannan tace ni na k’oshi.

Kallonta yarima yayi yace me kikaci da zaki k’oshi? Turo baki zarah tayi tace ban iya ci.

Yarima batare da yayi magana ba yad’ebo yace bud’e bakin.

Zarah ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa tabud’e bakinta yasaka mata, tana yatsine fuska tana tauna ahaka yakeci yana feeding d’inta itama, har saida yatabbatar da ta k’oshi sannan yabarta nan suka tashi suka koma part d’insu.

Suna shiga zarah tacire hijab d’in tashiga bedroom takai cikin wardrobe ta aje sannan tafito tasami yarima a parlour zaune ya tsura ma waje guda ido, wajen da yake tanufa bai ankaraba sai jinta yayi a jikinsa, kallonta yayi nan tasakar mashi k’yataccen murmushinta, shima maida mata yayi tare da d’aura hannunsa saman cikinta yana shafa yace kinga babyna shima ya samu wadataccen abinci ammah da sai kizauna da yunwa kina k’wararman shi.

Zarah kamar zatayi kuka tace toh ai shine yake wahalar da ni, kuma baka ganin laifinsa sai nawa shi dayake ana sonsa ammah ni ba a sona.

Yarima kallonta yayi yace zarah wanene baya sonki?

K’wallah ce tacika mata ido tace kai man, kawai dai kana zaune da ni ne ba dan kana sonaba,,,tak’arashe maganar tare da fashewa da kuka.

Cike da mamaki yarima yake kallonta ganin batada niyar daina kukan yasa yace, kukan ya isa haka zarah toh ke tsakaninki ga Allah kina sona?

Tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace akwai macen da zata ganka tace bata sonka?
Tsareta yayi da ido yace tambayarki nayi kiban amsa
Kwantar da murya tayi tace ina sonka sosai,,,cikin sauri tafad’a k’irjinsa tare da rufe idonta alamun kunya.

Murmushi me sauti yarima yayi sannan yace yau kika fara sona ko?

Girgiza kai zarah tayi cikin sauri sannan tace ni tun tuni nake sonka.

Shafa bayanta yarima yayi yace toh nagode.

‘Dago kai tayi takallesa tayi kalar tausayi sannan tace toh kai baka sona ni ba ajin aurenka bace ko?

Yanayin yadda tayi maganar yaso yaba yarima dariya, murmushi yayi sannan yace ni ban ce ba.

Langwa6e kai tayi tai kalar tausayi tace toh kana sona?

Jan hancinta yayi yace ko ban furtaba jikina ai ya isa yanuna miki amsar tambayarki.

Girgiza kai tayi tace babu abinda zan iya ganewa ta haka nafiso kafurta min da bakinka, in ma bakasona toh ya zanyi dole in hak’ura k’ila wani lokacin zaka soni nidai fatana kar inhaihu babyna yataso yaga daddynsa baya son mahaifiyarsa.

Tausayinta yakama yarima goge mata hawayen fuskarta yayi sannan yace kikwantar da hankalinki zarah domin duk kin mallaki abinda kowane namiji zaiso mace dan shi, kuma da ace bana sonki kina tunani zan amince inrabu da kowa nawa inza6eki?

Girgiza kai zarah tayi tare da maida kanta takwantar a k’irjinsa tana jin wani irin dad’i a ranta son mijinta yana fizgarta ga tausayinsa da yadabaibaye mata zuciya, hawaye yana zuba daga idonta tace nagode sosai my soulmate insha Allahu bazan ta6a yin abinda zai 6ata maka raiba, nayi ma alk’awali zan kasance da kai a kowane hali, fashewa tayi da kuka tace ina sonka sosai zan iya rasa komai saboda kai, ina fata kaima zaka kasance da ni duk rintsi duk wuya.

Wani irin sonta yaji yana zagaye duk illahirin jikinsa shI kansa mamakine yakamasa ganin a lokaci guda ya ji kamar an dasa masa sonta a k’irjinsa, matseta yayi jikinsa tare da runtse idanunsa yace baby nima ina sonki insha Allahu nima babu abinda zaisa inrabu da ke indai zaki cigaba da sona toh nima zan cigaba da nuna miki *K’AUNA* har k’arshen rayuwata.

Zarah dasauri tad’ago kai takallesa dan jin maganar tayi kamar a mafarki yarima ya furta mata kalmar so.
‘Daga mata kai yayi, alamun eh.
cikin jin dad’i tarungumesa tace nagode sosai insha Allahu nikuma zan cigaba da nuna maka k’auna zallah.

Ringing d’in da wayar yarima tafara yasa yajanye Zarah daga jikinsa yamik’e yaje yad’auko dan yasan mu’az ne kawai yake da new number d’in da yacanza.

Picking yayi tare da yin sallama
Daga chan 6angaren mu’az amsa masa yayi tare da cewa sorry prince kun fito lokacin mun shiga ciki da madam.

Murmushi yarima yayi yace kar kadamu ai nayi muku uzuri.

Dr mu’az dariya yayi Sannan yace godia muke ranka yadad’e, ina fata princess zata aramin kai mud’an fita.

Yarima kallon Zarah yayi da tatsaresa da ido sannan yace toh zan dai tambayeta inji idan zata amince.

toh kodai inzo da kaina intambaya?,,cewar mu’az.

Murmushi yarima yayi yace kar kadamu ganinan zuwa.

Bayan sun gama wayar kallon Zarah yayi yace princess bari inje indawo.

6ata fuska Zarah tayi tace yanzu saboda Allah ba zaya barka kazauna da matarkaba duka yaushe kuka dawo?

Matsowa yarima yayi yazauna gefenta tare da shafar fuskarta yace kar kidamu baby bazamu dad’eba.

Zarah turo baki tayi tace nidai uhm-umh.
Tallabo fuskarta yayi yakai bakinsa cikin nata yafara aika mata da wani mayen kiss, gabad’aya yarikita zarah jikinta yamutu, ahankali yazare bakinsa daga nata yace baby sai nadawo.

Kasa magana zarah tayi saidai kai kawai tad’aga mashi dan gabad’aya jikinta yai sanyi.
murmushi yayi sannan yamik’e yafita.
Da kallo tabisa har yaficce sannan tajingine kanta da kujerar da take zaune sama, nan tashiga maida numfashi, ita kanta tana jinjina ma yarima dan duk hanyar da zaibi yarikita mace ya santa, hannu takai tashafa le6enta tana murmushi.

Tana zaune taji ana knocking d’in k’ofa cikin sauri tamik’e tashiga bedroom tad’auko hijab tasaka sannan tadawo tabada izinin ashigo.

Jamila ce taturo k’ofan tashigo had’e da yin sallama.

Zarah kallonta tayi tana murmushi tace oyoyoo Aunty jamila.

Zama jamila tayi kusa da Zarah sannan tace najiki shuru tun d’azun baki fitoba,
Murmushi zarah tayi tace wlh kau Aunty jamila nima inata so infito sai gashi kin rigani.

Hmm kedai ko prince ne yarik’e ki dan da alama prince d’an love ne.

Dariya zarah tayi tace kai Aunty kin bani dariya wlh, ku ma fa damukaje yin lunch kuna chan.

Dariya tayi tace au kin rama kenan.

Nan suka cigaba da hira sai gab da magrib sannan jamila takoma part d’inta.

Bayan sallar isha’i zarah wanka tayi tashirya cikin d’aya daga cikin sleeping dress d’in da yarima yasiyo mata, riga da wando iya cinya, tufke gashin kanta tayi tadawo parlour tazauna tana jiran yarima, kad’an kad’an ta kalli agogon bango dan a k’agare take yadawo.

Sai wajen k’arfe tara sannan yaturo k’ofan yashigo, juyowa tayi dasauri takallesa,
tsaye yayi yahard’e hannuwansa shima yana kallonta , mik’ewa tayi dagudu tanufi inda yake tafad’a jikinsa,

Rungumeta yarima yayi, zarah cikin shagwa6a tace shine kaje kayi zamanka kabarni ko?

Yarima shafa kanta yayi yace sorry baby yanzu gani ai nadawo inkuma ba’a murna da dawowar tawa sai inkoma.

‘Dago kai tayi takallesa idanuwanta sukayi rau-rau da hawaye tace kuma zaka iya komawa?

Murmushi yarima yayi tare da janyeta daga jikinsa yace toh sarkin kuka yanzu dai muje kitaimaka min inyi wanka dan agajiye nake.

Rik’o hannunsa zarah tayi suka shiga bedroom towel tad’auko tamik’a mashi sannan tawuce bathroom tahad’a mashi ruwan wanka,
koda tafito yana tsaye inda tabarsa, kallonsa tayi tace na ma d’auka ka cire kayan?

Wani irin kalloh yayi mata wanda yake sakar mata da kasala sannan yace baby ke fa nake jira kizo kitayani cirewa.

Zaro ido zarah tayi tace karufan asiri wlh ba zan iyaba.

Murmushi yarima yayi tare da tunkaro inda take yace zaki iya man, ai lada zaki samu.
kallonsa tayi nan yad’aga mata gira.

cikin sauri tajuya zata bar wajen, janyota yarima yayi yace dole fa sai kinyi min abinda nakeso kinsan ban ta6a neman komai narasaba a rayuwata kuma umurni nabaki indai kinaso mushirya dole kiyi abinda nakeso.

Zarah kallonsa tayi ganin dagaske yake yasa tafara cire masa button d’in rigarsa, ahankali tacire rigar nan tasafke idanunta akan lallausan gashin da yake kwance saman k’irjinsa, d’ago kai tayi takallesa nan yad’aga mata gira.

Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace please kataimaka kacire wandon da kanka,,,tafad’i hakan tare da mik’a mashi towel.

Ganin yadda tamarairaice yasa yarima yayi Murmushi sannan yakar6i towel d’in.
Dasauri tajuya masa baya dan yacire.

Yarima koda yacire, saidai ji zarah tayi ya sungumeta ya nufi toilet d’in da ita bai zarce ko’ina ba sai cikin ruwan da tahad’a mashi nan shima yashiga,

Zarah kunyace takamata cikin sauri tarufe fuskarta da hannunta tare da sa kukan shagwa6a.

Yarima bai damuba nan yazage zip d’in rigarta yacire rigar sannan yarabata da wandonta,

Daga gefe yakoma yana wankansa ammah idanuwansa suna a kan zarah.

Jin ya kyaleta yasa tajanye hannuwanta daga fuskarta, karaf suka had’a ido da yarima da yake wankansa, cikin sauri tamaida idanunta tarufe tana jinsa yagama wankan yafita yabarta cikin ruwan.

Saida taji fitarsa sannan tabud’e idanunta nan tayi wankan sannan tad’auro towel d’inta tafito.

Tsakiyan gado tahangosa kwance ya yi matashin kai da hannuwansa, ganinsa a wannan yanayin yasa taji ba dad’i a ranta takowa tayi tazo tahau gadon tare da kwanciya saman k’irjinsa, cikin ‘yar siririyar muryata tace meyake damunka?
Batare da ya kalletaba yace ba matsalarki bace kikyaleni.
Zarah kamar zatayi kuka tace wlh matsalarka tawace indai kana cikin yanayinnan toh nima damuwa nake shiga.

Wani irin kallo yarima yayi mata sannan yace wai har zan nemi abu wajenki kik’i yimin, hakan ya nuna min son da kike ik’irarin kina min toh ba gaskiya bane.

Zarah jikintane yayi sanyi tace kayi hak’uri wlh kunyarka ne nakeji ammah bazan k’ara sa6ama umurninkaba.

Shuru yarima yayi yakyaleta.
Tallabo fuskarsa tayi tace please my soulmate *KAYARDA DA NI*

sai a lokacin yarima yakalleta yace shikenan na yarda da ke baby, atare suka sakar ma juna murmushi nan yarima yakai hannu yacire towel d’in da take d’aure da shi.
kafin tayi magana har ya birkiceta takoma saman katifar nan yadawo kanta.
Zarah ga jikinta bata jin dad’insa ammah haka tadaure taba yarima kanta yayi yadda yakeso,
Saida yagaji dan kansa sannan yabarta.
Shi kansa yana jinjina ma dauriyarta dan ya san ya bata wahala sosai.

daga k’arshe d’aukanta yayi yanufi toilet da ita dakansa yayi mata wankan tsarki, shima yatsarkake jikinsa sannan yad’aukota suka fito.

Saman bed d’in yahau da ita nan suka kwanta tana manne a jikinsa yana shafa gashin kanta, cikin kunnenta yake rad’a mata cewa nagode sosai zarah, hak’ik’a kina sani cikin farin ciki Allah yaimiki albarka yadda kike faranta min kema Allah yabaki masu faranta miki.

Zarah k’ara shigewa tayi jikinsa cike da jin kunya,,ahaka bacci medad’i yayi awon gaba da su.

________________

A chan masarautarsu yarima ko bayan yarima yabar gidan, memartaba kallon family d’in nasa yayi da gabad’aya kowa yake cikin yanayi, saida yak’are musu kallo d’aya bayan d’aya sannan yace toh kunga dai abinda yafaru, yarima ya ci amanata ya nuna min ban isa da shi ba dan haka tunda ya za6i matarsa a kanmu shikenan yaje na sallama mata shi yaje yaga idan za’a iya rayuwa ba dangi ko dashi ko babu shi gidana ba zai k’i cigaba da tafiya daidai ba,

sannan yakalli sumayya da take ta kuka yace kekuma sai kiyi hak’uri da k’addararki dan dama chan Allah ya k’addara yarima ba mijinki bane na da’iman, dan haka daga yanzu zakije kifara iddah kafin muga yarda Allah zai tafiyar da al’amarinsa, saidai muce Allah yamusanya miki wani mijin da zaifi zama alkhairi agareki.

Yanzu kai Ahmad kaine yakamata kakasance magajin garina a yanzu.

Sultan Ahmad k’ara duk’ar da kansa yayi cike da biyayya yace ranka yadad’e ka gafarceni ba nak’iba ammah da d’an uwana aka nad’a magajin garin.

Girgiza kai memartaba yayi yace na riga na gama magana, dan haka idan da mai magana zai iyayi.

Kowa shuru yayi, ganin ba mai niyar yin magana yasa memartaba yasallamesu nan duk suka duk’a suka kwashi gaisuwa sannan suka tashi kowa yawatse cike da damuwa a ransu.

 

Ummi koda takoma part d’inta a parlour saman kujera tazauna tarushe da kuka, rahma da husna da suke bayanta tsaye sukayi suna kallon mahaifiyar tasu cike da tausayinta suma hawayen yana fita daga idanunsu.

Wajen da take suka nufa cikin sauri suka fad’a jikinta suna kuka, rahma ce tayi k’arfin halin cewa ummi kikira bro a waya please kice yarabu da matarsa yadawo gida wlh muna sonsa bamu iya zama babu shi, meyasa yaza6eta akan mu, dan Allah kice yadawo

Ummi cigaba tayi da kukanta cike da tausayin d’an nata, ahankali tace rahama na yarda da yarima nasan abinda zai iyayi da wanda bai iyawa kuma na tabbata akwai abinda sumayya tayi masa wanda yaja har yasaketa dan ban yarda da maganar da tayiba a gaban memartaba.

Rahama tsagaitawa tayi daga kukan da take sannan tace ummi bakya tunanin ko wacchan matar tasace tashiga tsakaninsu har hakan yakasance?

Girgiza kai sultana bilkisu tayi tace bana tunanin haka daga wajen zarah dan zarah mutuniyar kirkice.

Kidaina cewa haka ummi kinsan fa ita za6insa ce sumayya kuma za6in iyayenmu ne kinga daman bason sumayya yakeba,,,,cewar Aunty husna.

Murmushi ummi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace zarah ba za6in suhail bace kamar yarda yake zaune da sumayya toh itama biyayyace kawai tasa ya aureta.

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Sak’on gaisuwa da jinjina agareki my besty *Sadiya Sidi Sa’id* ina tayaki murnar kammala novel d’inki mai suna *RAYUWAR MATA* hak’ik’a kin zuba darasi da fad’akarwa acikinsa gaskiya dole inyaba miki, Allah yak’ara basira da zak’in hannu, Allah yabarmu tare_

 

Back to top button