Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 39

Sponsored Links

39*

 

Kwanaki sunata tafiya cikin rikici da chakwakiyar rayuwa soyayyar Mainah Abdu kacokan ta koma kan yayansa da matarsa gefe guda yanata binciken sirri ta qarqashin qasa duk wani sirri da Hajiya Lubabatu da fulani Hadiza suke qullawa akanshi da Dad da kuma matarsa da yayansa akan idonsa duk wani motsinsu yana ankare dashi yana bin takunsu duk inda suka sanya qafarsu nan yake tsoma tasa.
Zamansu da Mama Mairoh gwanin sha’awa sosai Samha take girmamata ita kuma take kula da yan uku ko yaushe suna gurinta ita da Dr Hasina ranar da suka cika kwanaki arba’in sabon bikine ya tashi a gidan na arba’in din sai dare sannan suka samu kansu nan fah wata sabuwar bidi’a ce ta balle duk da irin gyaran da Dr Hasina da Fulani Amina sukayi mawa Samha amma ranar arba’in din cewa sukayi Saida ta koma bangaren Fulani Amina ta zauna shi Abdul baisan rikicin da akeyi ba saida ya dawo da dare ya shiga part dinsa ya tarar babu kowa a mamakance ya kira wayar Samha yace.

 

 

“Wai Ina kuka shigane My Aysha?”ajiyar zuciya tayi tace “Fulani ce tace mu dawo nan….” “what kamarya me kenan?” Qasa tayi da kanta tace “nima bansani ba naji dai mama Mairoh tace wai dama anayin bikin shan kunu idan yara sunyi wata biyu” numfashi ya ajiye yace “nidai ko bikin shan koko ne wlh yau saina ratsaki haba don Allah kasheni kukeso kuyi ne ai nayi na qa’ida” kashe wayar yayi tabi wayar da kallo ta koma ta kwanta ta jima a kwance Yasmin ta shigo da gudu tace “kizo inji Dad aunty Aysha mijinki yana nemanki” gyara kwanciyarta tayi tace “kice masu nayi bacci”juyawa tayi ta fita ita kuma ta sake gyara kwanciyarta taja bargo ta rufe jikinta bataji shigowarsa ba saijinshi tayi ya kwanta a jikinta tayi luf taqi mgn miqewa yayi ya budeta sukayi ido biyu ta lumshe idonta tare da cewa “nidai don Allah ka kyaleni kaje ka kwanta…”

 

 

Hanunsa ya dora a bakinta yace “shine na turo a kiraki kikace kinyi bacci Allah yau kodai subani matata ko Yasmin ta nemi wani dakin ta kwana amma bazan kwana nikadai ba bayan inada ke haba kadaici ai saiya kasheni” yana fadin haka ya hade bakinsa da nata yana tsotsa lumshe idonsa yayi yana dora hanunsa a saman qirjinta bude qofar Yasmin tayi da niyyar shigowa tayi saurin juyawa tare da jan qofar da sauri tureshi ta farayi tana roqonsa ya bari amma yayi banza da ita yana qoqarin janye rigarta ta qanqame qirjinta tana shirin sanya masa kuka ya rufe mata baki tare da dagata yace “Idan kika bari raina ya baci zakisha mamaki ne Fulani tace nazo na tafi dake ke kina nunamin bazaki bini ba damuwata bata dameki ba to naji kuma na gde amma zan baki mamaki My Aysha ki shekara anan bazan qara nemanki ba tunda abin naki rainin hankali ne”

 

Miqewa yayi ya fice a fusace ta bishi da kallo ta rasa irin mijin nata da abin fushi bashi da wuya a gurinsa tananan kwance cikin rashin tunanin mafita Dr Hasina ta shigo ta zauna a gefenta ta dafa kanta tace “me kikayiwa Mainah ne yake shirin barin qasar?” Miqewa tayi zaune a hankali tace “bansan abinda nayi masa ba ki qyaleshi ya tafi kawai Aunty laifi nane ko nice nace zanzo nan na zauna naga al’adar masarautarsu ne shikenan saboda shine yafi kowa zane saiyace bazaayi akansa ba nifa gsky wannan saurin fushin nasa ya isheni yamayi duk abinda yake tunanin zaiyi ina ruwana mutum sai dacin rai kamar wanda akayiwa wankan farko da madaci”

 

Murmushi Dr Hasina tayi tace “yaro yarone Samha sonki yake shiyasa yake son kasancewa dake ya zamuyi hqr shine ya kamaki tunda Allah yayiki mace kuma ta bakin nasa ai yayi qoqari banyi zaton ma zai barki kiyi arba’in din ba yanda naga kansa na rawa gsky ki tashi kije kiji matsalar mijinki indai zaki iya kiyi masa maganinta yana da lfy dole zaiyi burin kasancewa dake a yau dinnan da kowanne namiji yakeson yajishi a saman matarsa” Fulani Amina ce ta shigo tace “ki kyaleshi Hasina bazata bishi dinba shi wanne irin mutum ne mara Lissafi haba ai yarinyar nan ko baa fada masa ba yasan tana buqatar hutu yaya uku haihuwar fari aita zazzagu ya bari gurin da aka farka ma ya gama hadewa mana” haka sukayita yi tsakaninsu daga qarshe dai dole Dr Hasina ta hqr ta qyale Fulani Amina saboda ta kafe kan sai yaran sunyi wata uku zata koma.

 

 

Ranar saboda haushi Abdullahi bai iya bacci ba saboda haushi washe gari kuwa tun asuba yabar gdan ya koma England fushi yakeyi sosai da Samha danko waya idan ya kirata lfyr yaransa kawai zai tambaya ya kashe a haka har suka dauki sati uku tun abin baya damunta harya fara damunta amma ta dake ta shareshi itama a wannan tsakanin ne mamy ta samu damar shigowa taga yaran sunyi bulbul dasu baqin ciki kamar ya kasheta daqyar ta iya jan qafarta ta koma bangarenta ta kwanta tana juyi bata jima da kwanciya ba wayarta tayi ring ta daga ta kara a kunnenta yayi murmushi yace “kin shiga kingano yara kyawawa kyautar Allah wadanda kikayita qoqarin hana zuwansu duniya Allah ya nuna miki iyawarsa amma har yanzu baki saduda ba kinaci gaba da neman hanyar kashemin yayana da matata harma da suruki na kai ashema hardani nine target dinki na farko fah ko? Hmn to kafinnan Ina mai farin cikin yimiki albishir din cewa qawarki aminiyarki Barirah tana hanun Force C.I.D zatayi bayanin yanda kukayi kuka qulla komai sannan kema ki shirya yin bayanin yanda komai ya wakana tsakaninki da mijinki harma da yanda akayi kika kashe iyayensa da hanyar da kikabi kika raba uwa da yarta a gabar haihuwa karkice na cikaki da surutu na barki lfy surukata”…………

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/20, 9:14 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Back to top button