Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 4

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na huɗu_

 

https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc

……..Dafeeq dai shima ɗaya ne daga cikin ɗaliban makarantar su Khadijah. Yaro ne mai ƙwazo da maida hankali a karatu sai dai baya jin magana. Shekara ɗaya ne tsakaninsa da Khadijah a makarantar, dan shi a yayinda ta shiga ss2 shi kuma sune suka shiga ss3. Yana ɗaya daga cikin waɗanda aka bama prefect, yana kuma cikin masu manyan muƙami. Sun haɗu ne a sanadin sayayyar kayan ƙwaɗayi da aka san ƴan makaranta a lokacin break. Tana tsaye gaban mai awara ita da ƙawarta Aminatu Dafeeq ya iso wajen tare da tawagarsa su huɗu shi na biyar. Shine a gaba suna take masa baya tamkar wani saraki ko malami. Hakan ba sabon abu bane, dan Dafeeq suna ɗaya daga cikin tsagerun ɗalibai, sai dai ƙoƙarinsa yasa malamai basa iya masa komai. Tunda ya shigo makarantar kuma da rashin kunyarsa ya shigo, dan baifi sati ɗaya ba wani prefect ya dakesa akan makara a wajen ya riƙe bulalar ya murɗesa ya amshe shi ya shiga zabga masa. Al’amarin ya bama kowa mamaki, dan kowa yasan dai akwai seniority a school ɗin musamman prefect nada ƙarfin iko sosai akan hukunta na ƙasa da su. Abinda yay yasa sauran prefect ɗin dake wajen rufesa da duka har sai da malamai suka fito aka dakatar da su da ƙyar. An hukuntashi akan wannan laifin tare da bashi suspecsion har na sati biyu, bayan yaje yayo babansa da aka buƙaci gani yazo ya bada haƙuri. Tun daga wannan abun da yay ƴan ss3 suka tsanesa, hakama ss2 suna cike da burin sauke masa iskancin kansa. Adalilin hakan yasha wahala sosai a cikin makarantar shima kuma ya wahal da wanda suke wahal da shi ɗin. Dan babu fashi ka dakesa a cikin makaranta kai kuma a waje zai saka a maka duka ko kuma shi ya maka da kansa. Daga baya ma daya haɗa daba sai yazam tare suke aikin su biyar. Wannan tsagerancin nasu da ƙoƙarin ya sakasu yin ƙaurin suna a school ɗin. Sannan kuma a wajen sayen kayan break basa saya, sai dai su saka yara su loda musu kaya su cinye suƙi biyansu. Idan an kai ƙararsu wajen malamai ana gama musu hukunci aka sakasu biya dole ana fita wajen makaranta suma yaro ko yarinya duka su amshe kuɗinsu. Tun suna ss1 suke halayyar nan har zuwa yanzu, su kansu masu tallan har sun gaji da kai ƙarar tasu idan sunzo sai su zuba musu kawai dan a zauna lafiya.
Khadijah bata da yawan hayaniya, ba kuma ta da yawan shiga sabgar mutane. Dan haka ba wani sanin Dafeeq tayi sosai a fuska ba, sai dai takan ji ana labarin rashin jinsu a makarantar. Sai kuma duk sanda za’ai hutu idan an musu taro takan ga fuskar idan zai amshi ƙyauta dan duk tarm kam hakan baya wucesa saboda ƙoƙarinsa. Amma ita dai ALLAH bai taɓa haɗasu face to face ba balle magana ya shiga tsakaninsu sai yau ɗin nan da ya sameta a gaban mai awara ita da Amina. Ta juyo zasu bar wajan shi kuma ya kawo jikinsa duk da kuwa ya ganta sarai kuma ya fahimci ita bata lura da mutum a gabanta ba suka bangaji juna. Ledan hanunta ne ya faɗi, awaran ciki ya watse a ƙasa. Tsabar wulaƙanci Dafeeq yabi takansa ya wuce yana wani busar iska da fesarwa tamkar baiyi komai ba. Khadijah nada haƙuri, amma bata ƙaunar wulaƙanci. Ga shi kuma a yau tana cikin yanayin period sai zuciyarta duk take a ƙuntace kuma a kusa. Ranta a ɓace ta ɗago, sai dai har ya gotata zai wuce hankalinsa kwance. Hakan ya ƙona mata rai, batare datama san mitake ba a ƙufule ta furta, “Kai wane irin wawan daƙiƙin mutum ne mara sanin muhimmanci da kimar ɗan adam balle daraja abinci haka!”.
Cak Dafeeq da yaji abin tamkar daga sama ya tsaya. Yayinda wajen yay tsitt a ƙanƙanin lokaci kasancewar a tsawace Khadijah tai maganar. “Kan babbar u…. can”. Ɗaya daga cikin abokan nashi ya faɗa yana wani kallo da ɗaga hannu zai zabgama Khadijah mari. Caraf ta riƙe hannun nasa tare da hantsilashi tana huci duk da ya fita tsayi sai dai shima babu ƙiba kasancewar dukansu yara ne. Jikin Dafeeq da bai juyoba ya faɗa har kansu na gware. Sai lokacin ya juyo a harzuƙe jin ƙarar da Hadiy ya saki sakamakon murguɗewa da ƙafarsa tai dalilin hankaɗawar da Khadijah ta masa. Tarosa Dafeeq yayi ya miƙar, dai-dai Khadijah na ƙoƙarin barin wajen yay wani kalar fisgota baya. Keeeee!! Kake ji hijjab ɗin jikinta ya yage har zuwa ƙasa jikinta da dogon gashinta suka bayyana kasancewar babu ɗan kwali akan nata sai hula. Fisgarta da yay kuma ya haɗo da hular. Taga-taga tai zata faɗi ciki rawar jiki Aminatu ta riƙeta, tana ɗagowa babu wani lissafi ganin hijjab ɗinta ƙasa wanwar jikinta da gashinta a buɗe ido a rufe ta ɗaga hannu ta sauke ma Dafeeq yatsunta biyar a saman fuska. Bai gama dawowa a hayyacinsa ba ta kuma ɗaukesa da mari na biyu hawaye masu zafi na wanke mata fuska. Dan a duniya babu abinda Khadijah ta tsana sama da aga jikinta. Itafa ko’a gida bata zama babu hijjab balle anan cikin makaranta da ko salla bata yarda tayi ba. Shiyyasa da’an tashi bata zama take ɗaukar hanyar gida dan ta samu damar yin sallarta acan.
Tsitttt wajen yayi baka jin komai sai sautin kukan Khadijah, kowa ya zubama Dafeeq ido yaga wane mataki zai ɗauka akan wannan mari, wanda bai ragama senior ɗinsa ba taya jenior ɗinsa zatai masa wannan al’amari a zauna lafiya. Ganin yanda Dafeeq yay tsaye ƙiƙam tamkar wani soja ko wanda yay sumar wucin gadi yana kallon Khadijah kawai dan koda ta maresa baiyi ko gezau ba sai idanunsa da sukai matuƙar kaɗawa jazur, gaba ɗaya sauran abokansa 3 sukai kan Khadijahn a harzuƙe matuƙa. Sai dai da sauri ya ɗaga musu hannu alamar karsu taɓata. Basu iya ƙin bin umarninsa, sai dai da mamaki suke kallonsa. Ya wani kalar lumshe idanunsa da buɗesu a lokaci guda kan ƙirjinta da gashin kanta yana taune lips nashi na ƙasa. Sai kuma ya juya yana kallon sauran ɗaliban wajen. Cikin sauri suka shiga fashewa dan mugun tsoronsa ake saboda rashin mutuncinsa. A dai-dai nan ma aka kaɗa ƙararrawar komawa aji……

★★★★

Daga shi har doctor ɗin ƙofar suka zubama idanu. Sai dai ba kamar yanda yay tsammani bane da tunanin ganin Alimah. Abbansa ne da yayansa. Doctor ya dubesa yana murmushin. Sai kuma ya ɗauke idanun ya maida kan su Abba dake jerama JJ ɗin sannu da jiki. Kai kawai yake iya ɗaga musu, yana mai jin wani iri a ƙasan zuciyarsa. Bayani Doctor yay musu a taƙaice, tare da tabbatar musu zai iya sallamarsu daga yanzu zuwa kowane lokaci. Idan kuma babu damuwa su bashi matarsa, kar suyi dubi da abinda ya faru, wannan ba komai bane akan ma’aurata sabbin aure. Nasu kawai su musu nasiha ne musamman ita yarinyar. Sosai Abba ya gamsu, yayinda JJ kansa ya sake kullewa gaba ɗaya, sai dai kamar an ɗinke masa baki ya gagara cewa komai har Doctor ɗin ya gama bayaninsa ya fice.
Zama Abba da yayansa sukai kusa da shi suna sake jera masa sannu, yayinda yayansa ke haɗa masa shayi kamar yanda doctor ɗin ya bada umarni. Bayan ya kammala ya kawo masa tasan asibiti ya wanke bakinsa sannan aka bashi tea ɗin. Ya ɗanyi nisa da shan tea ɗin zuciyarsa duk a birkice da tunani kala-kala Abba ya katsesa da faɗin.
“Jazool!”.
A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Abban. Kafin ya ɗaga baki da ƙyar ya amsa da “Na’am Abba”. Nisawa Abba yay da cigaba da faɗin, “Jazool sam banji daɗin abinda ka aikata ba. Banda wauta irin taku ta yaran zamani abu kamar cin rabo. Yarinyar nan fa a gidanka take kuma tazo kenan har abada bawai damar daren shekaranjiyan ne da kai ba kawai. Yanzu da iyayenta fitinannu ne kana ganin maganar nan zata zama mai sauƙi ne kamar haka? Duk da kuwa sun riga sun mallaka maka ita. Auren soyayya fa kayi bana ƙiyayya ba balle kace taƙi amince maka zaka haike mata ta ƙarfi. Ka godema ALLAH daya kasance tai hankalin kiran ƴar uwarka ba wani ɗan gidansu ta kira ba ya ganku a wannan halin. Ina mai baka shawara da kazama namiji a gidanka, dan shi namiji mai dattako aka sanshi ba barahaza ba. Idan ka bita a sannu cikin lalama sai ka kai ga inda kake so batare da ita kanta tama san ta mallaka maka kan nata ba. Ban son na sake jin irin haka ta sake faruwa, in ba haka ba ranka zai ɓaci. Yara baku da hankali sam gaba ɗaya kun koma gina aure akan sha’awa kawai soyayyar ciki ƙalilance…” nan dai yay masa tass da faɗa da nasiha. Ya kuma hanashi cewa komai saboda shi Abba suna kallon komai ne a yanayin da suka fahimta kawai. A ta wani ɓangaren kuma shi kansa JJ ɗin bakinsa yay masa nauyin da ya gagara iya cewa komai batare da yasan dalilin hakan ba. Sai ma zaƙuwa da ɗokantuwar son ganin Alimah kawai yake a ransa….

Zuwa bayan la’asar aka sallamesu. Kamar yanda Doctor ya bada shawara gidansa aka wuce da shi. Sun sami mutane uku da suma suka dawo da Alimah babu jimawa dan tunda abin ya faru bayan an kaisu asibiti doctor ya tabbatar da ita bata buƙatar a kwantar da ita can gidansu JJ aka wuce da ita. Ƙannensa ne guda biyu sai sep mom nasu. Tana zaune a falo Alimah a kusa da ita tana mata nasiha, yayinda Rabi’ah da Sadiya ke tsaftace gidan duk da bawani datti yayi ba. A kusan tare JJ da Alimah suka kalli juna, tai saurin rissinar da nata kan cikin yanayin jin kunya da tsoro, shiko ya kasa yin hakan dan har sai da yayansa ya kamasa ya zaunar. Bayan Alimah ta gaida Abba da yayansa shi ta gaida da masa yaya jiki kamar yanda taji Umma ta faɗa cikin jajantawa. Itama da kai kawai ya amsa mata kamar yanda ya amsawa Umma. A haka su Rabi’ah ma suka fito suna masa sannu da yaya jiki. Suma amsa musu yay da kai.
Nasiha mai ratsa jiki Abba yay musu su duka, itama Umma ta ɗaura da nata. Sun sallami Alimah ta koma cikin bedroom wajen su Sadiya, suka sake rufuwa akan JJ a matsayinsa na miji babba da ya fita shekaru. Shi dai saurarensu kawai yake dan baima san yaya zai fassara al’amarin ba. Zuciyarsa gaba ɗaya a rufe take ruff, babu wani abu a jikinsa dake aiki a sashen tunani irin na masu hankali. Abinda kawai ya sani yana jinsu yana kuma ganinsu da idanunsa. Rabi’ah Umma ta ƙwalama kira, ta fito aɗan gaggauce tana amsa mata.
“Ki faɗama Alimah ta haɗa masa ruwan wanka ko? Dan ya kamata ya ɗan watsa ruwa ko jikinsa zai saki.” da to Rabi’ah ta amsa tana juyawa ciki, kusan mintuna shidda tsakani ta dawo ta sanar da an haɗa. Da taimakon yayansa JJ ya miƙe, yay masa rakkiya har bakin ƙofar sannan ya dawo. Daga haka suka miƙe su duka bayan an sake umartar su Sadiya akan su fito. Sosai Alimah ke hawaye dan bata son su wuce ita dai. Su dukansu sun fahimci tsorone a ranta, dan haka Umma ta sake lallashinta da tabbatar mata in sha ALLAH gobe su Rabi’ahn zasu dawo su yini mata. Kanta a ƙasa ta amsa da ta gode. Har tsakar gida tai musu rakkiya, suka wuce ransu fal tausayinta musamman ma Ummah da Abba da Yaya Mujee. Jiki a saɓule ta koma ciki, sai taji gaba ɗaya ma gidan ya fita mata a rai. Bata bi takan JJ ba ta wuce ɗakinta tana hawaye……✍️

_Ina fatan yau dai Yaya JJ zaisha amarcinsa da amarya Alimah _

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button