Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 46

Sponsored Links

PAGE* 4⃣6⃣

Kallonsu yayi d’aya bayan d’aya sannan yace jiya bayan na fita zarah ta shigo part d’ina?

Gaba d’aya shuru sukayi suna tunani sai chan d’aya daga cikinsu yace gaskiya bata shigoba,

Yarima ido yazuba mai sannan chan yace toh ko akwai wanda yashigo?
Nan ma shuru sukayi, Yarima yace kuyi tunani dai.

Chan sai suka kalli juna sai suka eh toh ranka yadad’e gimbiya sumayya ta shigo bayan magrib, gaskiya inba itaba babu wanda yashigo.

Yarima jinjina kai yayi yace kun tabbata? Gabad’ayansu sukace eh ranka yadad’e.
Yarima baice komai ba yawuce yashige,
Koda yashiga parlour saman kujera yazauna tare da dafe kansa mamakin sumayya duk yacikasa ahankali yace idan na fahimta toh duk wani abu da yake faruwa toh dasa hannun sumayya a ciki, toh meyasa sumayya take yin haka? Meyasa takeso taga ta yi silar mutuwar auren zarah? Anya ba da sa hannunta aka zuba poison a abincinba? Wani huci yafitar mai zafi sannan yace koma me kenan da sannu gaskiya zatayi halinta ba zan zargetaba, yana nan zaune a wajen wayarsa tafara ringing ganin mai kiransa yasa yai picking tare da cewa Doctor kin iso?
Daga chan 6angaren tace eh ranka yadad’e gani a waje dogarawa sun hanani shigowa.
Yarima yace ohk, ba d’aya daga cikinsu wayar.
Toh ranka yadad’e, cewar doctor feedoh, nan tamik’a ma dogari d’aya waya, yana d’auka Yarima yace kubarta tashigo.
Jin muryar Yarima yasa yarissina kamar yana gabansa sannan cikin girmamawa yace toh ranka yadad’e angama.
Yarima kashe wayarsa yayi tare da mik’ewa yashiga bedroom d’in tsaye yayi bakin gadon yana k’are ma zarah kallo da gabad’aya ta galabaita, ahankali yazauna gefenta tare da dafa kanta yace ya jikin?
Gyad’amai kai kawai tayi,

Mik’ewa yayi yafito waje yasa d’aya daga cikin guards d’insa yaje yazo mai da doctor feedoh, cikin sauri yatafi.

Nan Yarima yadawo parlour yazauna yana jiransu, bayan minti biyar sai ga guard d’in tare da doctor feedoh sun shigo, duk’awa guards d’in yayi yace gata ranka yadad’e,
‘Daga masa hannu yarima yayi,
Fuskarsa d’auke da murmushi yace u ar wlcm Dr.
Dr feedoh saida tazauna sannan tace thanks Dr, ya mai jikin.
Alhmdllh yace tare da mik’ewa yace bismillah mushiga daga ciki kidubata,
Ohk sir, cewar dr feedoh nan yarima yawuce gaba tana biye da shi har cikin bedroom d’insa, daga gefen da zarah take kwance yazauna, kallonta yayi da tazuba ma Dr feedoh ido, ahankali yace ga doctor nan zata dubaki.
Fuskar Dr feedoh d’auke da murmushi tace sannu gimbiya, ya k’arfin jikin naki?
Zarah ma d’an guntun murmushi tayi cikin k’arfin hali tace Alhmdllh.
Dr matsowa tayi tana fiddo kayan aikinta daga cikin jakka tace ranki yadad’e ko zaki iya fad’amin abinda yake damunki?
Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido, shafa kanta yayi sannan yace kidaure kiyi mata bayani kinji? d’aga mai kai tayi alamun toh, yana fad’in haka yamik’e yace doctor bari inbaku waje.
Doctor feedoh murmushi tayi cikin girmamawa tace a’a ranka yadad’e kayi zamanka ka ga inda na6ace sai kataimaka min.
Murmushi yayi yace kar kidamu ai nasan aikinki, bakida matsala, yana fad’in haka yafita yakoma parlour

Yana fita doctor feedoh gefen gadon tazauna, fuskarta d’auke da murmushi tace ranki yadad’e kamar da me dame kike ji?
Ahankali zarah tabud’e baki tace zazza6i da ciwon kai.
Dr rubutawa tayi tace bayansu babu abinda kuma kikeji?
Zarah shuru tayi kamar tana tunani sai chan tace sai kuma yawan kasala da bacci, jinjina kai Dr tayi tace bayansu bakya tashin zuciya?
Girgiza kai zarah tayi.
Nan Dr tarubuta sannan tace toh kina cin abinci?
Ba sosai ba, cewar zarah.
Dr idon zarah d’aya taduba sannan tad’auko wata roba tamik’a mata tace ko zaki taimaka kiyo fitsari nan ciki, saboda akwai awon da nakeso inje yanzu inyo.

Zarah kar6a tayi tamik’e dak’yar, ahankali take tafiya har taje toilet d’in yarima, nan tayo fitsarin tafito tamik’a ma doctor, kar6a Dr tayi ta aje sannan tace ranki yadad’e kiyi hak’uri munason mud’an d’ibi jininki kad’an.

Zarah bata musaba tamik’a hannunta tare da runtse idonta nan Dr feedoh tad’ibi jinin sannan tamik’e tace bari inje inhad’o miki result d’in.
Gyad’a kai kawai zarah tayi.
Dr ko da tafito a parlour tasamu yarima kallonsa tayi fuskarta d’auke da murmushi tace ranka yadad’e munyi duk abinda yadace yanzu zanje inyi mata test zuwa anjima kad’an insha Allahu zan dawo da result,

Jinjina kai yarima yayi sannan yace toh bakomai Dr Allah yamaidoki lafiya.
Ameen tace sannan tawuce tafita.

Bayan ta fita yarima mik’ewa yayi yashiga bedroom d’in, kallon zarah yayi da take lumshe ido alamun bacci zatayi hannunta yaduba sannan yace baby bari ind’an sa miki drip,
Zarah batace komai ba, kalman babyn da yakirata da shi takemata yawo a cikin kunnenta dan wannan ne karo nafarko da yakirata da hakan,
Shima kansa yarima saida yaji wani iri ammah yashare nan yahad’a drip d’in yasa mata, sannan yawuce yashiga bathroom dan yayi wanka.

Lokacin da yafito zarah har tayi bacci dan haka yashirya sannan yakomo gefenta yazauna yana ganin yanayin yadda ruwan yake shiga jikinta.

Bayan awa d’aya sai ga Dr feedoh tadawo, nan yarima yabada izini abarta tashigo bayan ta shigo fuskarta d’auke da murmushi tace ranka yadad’e albishir nazo maka da shi kuma ina fatan samun goro daga wajenka.
Kallonta yarima yayi cikin rashin fahimta sannan yace albishir kuma?
Har a Lokacin fuskarta d’auke da fara’a tace eh ranka yadad’e.
Yarima yace ohk, ina jinki.
Dr feedoh kallon zarah tayi da tad’an bud’e idonta alamun ta farka tasakar mata murmushi sannan tace madam tana d’auke da juna biyu.
Yarima kalmarce yaji tana yawo acikin kunnensakamar a mafarki, Kallonta yake yace me kikace?
Murmushi Dr tayi sannan tace tana d’auke da ciki na tsawon wata ukku da rabi (14wks) kenan, nan tamik’a masa result d’in tare da takardar magani.
Yarima kar6a yayi ya duba sannan ya jingine kansa a jikin gadon tare da lumshe idonsa yana jin wani irin nishad’i a cikin ransa ahankali yace Alhmdllh, Allah nagode ma, nan yabud’e idonsa yasafkesu akan zarah da take kallonsa ammah bata gane abinda ake nufiba.

Kallon Dr yayi fuskarsa d’auke da murmushi yace nagode doctor tabbas kinmin babban albishir kuma dole inbada tuk’uici, ammah abun mamaki ya akayi har yakai tsawon wannan lokacin ammah ban ganeba?

Murmushi Dr tayi sannan tace kuma doctor kana saurin fahimtar na wasu matan ammah kai naka sai gashi cikin ikon Allah, Allah ya 6oye abunsa har tsawon sati goma sha hud’u (14 wks) sannan yabayyana kuma har da k’arin ba wani laulayi takeyi ba.

Jinjina kai yarima yayi tare da kallon zarah da idanuwanta suke rufe yace hakane, Allah shi yake ajiyarsa kuma sai ya so yake bayyanata, yana fad’in haka yamik’e yaje yabud’e wardrobe d’insa yad’auko cheque yacike sannan yazo yaba Dr feedoh yace ga goron albishir d’inki.
Dr feedoh d’an rissinawa tayi takar6a cikin jin dad’i tace nagode sosai Dr, Allah yasafketa lafiya, nan tacigaba da yin addu’a.

Fuskar yarima d’auke da murmushi yace Ameen mungode.
Dr feedoh jakkarta tad’auka sannan takalli zarah tace toh ranki yadad’e Allah yasafke mana ke lafiya, sai anjima.

Yarima ne kawai yace Ameen tare da mik’ewa yarakata har bakin k’ofa nan tak’ara yi masa godia sannan tatafi.

Yarima dawowa yayi bedroom d’in inda yatarar da zarah har a lokacin idanuwanta a lumshe suke, tunda taji an ambaci ciki gabanta yashiga dukan ukku-ukku dan ita ta ma rasa shin murna take ko bak’in ciki, a chan 6angare guda kuma murna take, bata ankaraba sai jin Yarima tayi ya d’age mata riga yana shafar cikinta, sharesa tayi tak’i bud’e idon nata, ya dad’e ahaka sannan yamik’e yace kitashi kiyi breakfast,
Zarah shuru tayi ta k’yalesa da mamakinsa sai ganin hawaye yayi sun gangaro daga idonta, da mamaki yake kallonta cikin ransa yace kar dai ace cikin ne bata so? Haushi ne yakamashi dan haka yashareta yawuce yafita daga d’akin.

Zarah tana jin fitarsa tabud’e idonta tare da bin k’ofar da kallo cike da tausayin kanta tace taya zan haihu da mutumin da baya sona, chan kuma gefe d’aya na zuciyanta tace ammah kuma yanason abinda yake cikin cikinki, hannu takai tashafi cikin cike da mamaki tace taya ciki yazauna min tsawon wannan watannin ban saniba? Toh wai ma duka yaushe akayi aurenmu?
Tunani tashiga yi sai kuma chan tace idan ban mantaba wata ukku da sati ukku kenan ya kama sati (15) kenan, gabantane yafad’i tace na shiga ukku yanzu cikin satina na biyu ciki yashigeni? K’wallah ce tacigaba da fita daga idonta, batasan lokacin da Yarima yashigoba sai ji tayi ya ce kitashi kiyi breakfast.

Zarah kallon yadda yahad’e rai tayi sannan tamik’e dak’yar, Yarima yataimaka mata yasa mata pillow a bayanta ta jingine sannan yahad’a mata tea mai kauri yamik’a mata, kar6a zarah tayi tafara kur6a jikinta yana rawa saboda wata irin yunwa da takeji.

saida tasha kusan rabin cup d’in sannan tamik’a ma Yarima ya amsa ya aje sannan yazubo mata chips, cikin sauri zarah tajanye kanta ahankali tace na k’oshi.

Yarima ido yazuba mata sannan yace ammah yanzu ba ke kad’ai bace kuma bakiga yadda duk kika rameba ya kamata kidinga daurewa kina d’an cin abinci.

Zarah rik’o hannunsa tayi tare da marairaicewa tace dan Allah kar kafad’a ma kowa ina da ciki.

kallonta yayi cike da mamaki yace saboda mi?
Rau-rau tayi da ido sannan tace kawai hakanan.
Yarima har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa nan yakwashi kayan breakfast d’in yafita da su parlour, zarah da kallo tarakasa har yaficce sannan takoma takwanta tare da maida idonta talumshe tana tunanin wai itace da ciki, hannunta tad’aura saman cikin, tana nan kwance haka sai ga Yarima ya shigo hannunsa d’auke da ledar drugs da injection da yabayar asiyo.

Ajewa yayi saman bedside tare da d’auko ruwa sannan yace kitashi kisha maganin,
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace idan nasha amai zanyi.

Yarima zama yayi gefenta tare rik’o hannunta yace kar kidamu bazakiyi amai ba,
Toh kawai tace, nan yataimaka mata tatashi zaune sannan yabata maganin saida ta runtse idonta sannan takar6a takai baki cikin sauri takora da ruwa, sannan tabud’e ido,
Nan yafara k’ok’arin had’a injection, kallonsa take a tsorace ahankali tace kuma harda ita za’ayi min?
Shuru Yarima yayi saida yagama had’awa sannan yakalleta har da d’an guntun k’wallarta taso tabashi dariya ammah yadake yace kigyara sai inyi miki.

Zarah komawa tayi takwanta tana kuka ciki-ciki, kallonta yayi yace kar kimotsa fa.
Batace komai ba jin zai shigar da allurar yasa tarik’esa gam, tare da runtse idonta.

Murmushi Yarima yayi sannan yatsira mata ahankali, bata ma san lokacin da yazare inj d’inba dan kwata-kwata bataji zafintaba, sai ji tayi yana cewa toh shikenan angama, zarah k’in sakinsa tayi saidai ji yayi tana fitar da sautin kuka k’asa-k’asa.
Ahankali yajanye daga rik’on da tayi mai tare da zuba mata ido sai chan yace kukan fa?
Turo baki tayi cikin shagwa6a tace ba kaine ba kayimin injection ba.
Murmushi yayi tare da jan d’an k’aramin bakinta sannan yace toh ai banyi miki da zafiba ko ak’ara wata?
Cikin sauri tagirgiza kai tare da cewa a’a.
Ido yazuba mata itama shi take kallo, ahankali tace kaida ma kake fushi da ni,
Murmushi yayi yace ni ba fushi nake da keba, kidaina maganar ta wuce kinji ko?
Murmushi zarah tayi tare da d’aga mai kai, hannunsa tarik’o tad’aura saman cikinta tace kana son babynmu?
Yarima ido yazuba mata sai chan yace ke kina sonsa?
Cikin sauri tace eh,
Mik’ewa yayi yace bari inje inhad’a miki ruwa kid’an gasa jikinki.
Murmushi kawai zarah tayi tare da komawa takwanta.

Toilet d’insa yashiga yahad’a mata ruwan wanka, bayan ya had’a fitowa yayi d’auke da towel yamik’a mata, kar6a tayi tare da mik’ewa dak’yar tacire rigar jikinta sannan tad’aura, yarima kamata yayi yarakata har toilet sannan yajanyo mata k’ofar.

Kwance tayi cikin ruwan tana jin wani irin nishad’i a cikin ranta, tunowa tayi da sumayya saida gabanta yafad’i, tsintar kanta tayi cikin zuciyanta tana addu’an neman kariya daga sharrinta.

Nan tafara wanka duk jikinta ya yi sanyi ahaka tagama sannan tafito, lokacin yarima baya d’akin, gaban dressing mirror tazauna tashafa mai sannan tamik’e taje tagyara gadon, bayan ta gama parlour tafito tasami yarima da yake zaune yana jin wani irin dad’i a cikin ransa, kallonsa tayi da shima yakalleta, turo baki tayi sannan tace ni banda kayan da zansa.

Janye idonsa yarima yayi sannan yamik’e yafita yaje ya aiki d’aya daga cikin guards d’insa part d’in zarah dan yakar6o mata kaya.

 

Lokacin da yadawo zarah tana bedroom nan yarima yakar6a yaje yakaimata sannan yadawo parlour yayi Kwanciyarsa saman 3 seater.

Bayan ta gama kwanciyarta tayi saman gadonsa nan bacci yayi awon gaba da ita,

Saida aka kira azuhur sannan yarima yamik’e yashiga bedroom, kallon zarah yayi da take baccinta hankali kwance, takowa yayi yazo yazauna gefenta tare da yaye blanket d’in da tayi rufa da shi gani yayi tana zufa alamun zazza6in ya safka, hannu yakai yad’age mata riga tare da shafa cikin nata, ido yatsura ma fuskarta duk tayi fayau da ita, murmushi yayi sannan yamik’e yaje yacire kayansa yashiga bathroom,

 

Bayan ya fito wanka shiryawa yayi sannan yaficce yatafi masallaci, rufe k’ofan da yayine yasa zarah tafarka, ji tayi zazza6in ya safka, ahankali tasafka daga saman gadon saida tagyara mai sannan tafito takoma part d’inta.

Koda tashiga saida tak’ara wanka sannan tad’auro alwallah.

Bayan ta yi sallah sawa tayi akayi mata faten tsaki taci saboda shi taji tana buk’ata.
tana cikin ci saiga yarima ya shigo, ido yazuba mata tare da yamitsa fuska,
Ganin haka yasa zarah tayi murmushi tace bismillah.

menene wannan? Cewar yarima.
Faten tsakine kazo kad’and’ana kaji akwai dad’i.
no, aci lafiya, ya jikin naki?
Dasauki, cewar zarah.
Ohk, Allah yak’ara sauk’i, idan kin gama kisha drugs d’inki.
Ahankali tace toh,
Juyawa yayi yafita yabar d’akin nan zarah tacigaba da cin faten.

 

A chan 6angaren gimbiya sumayya tun tana sa ido dan taga yarima ya kori zarah ammah shuru a k’arshema a gaban idonta yaje d’akin zarah sannan agaban idonta yafito.
Ahankali tafurta da alama aiki ya 6aci, takaici ne yacikata batasan lokacin da tace anya waccan munafukar bata asirce yarima ba? Tsaki taja cikin jin haushi tace akwai alamar tambaya a cikin lamarin nan, dan babu yadda za’ayi ace kullum itace da nasara, wlh duk sihirinta sai nayi silar barinta gidan nan

 

A haka zarah tacigaba da kula da cikinta, yanzu ta samu sauk’in zazza6in da takeyi saidai yawan amai idan taji k’amshin abinda bata so, abinci ko sai ta za6i irin wanda takejin zata iya ci, ta d’an rame ammah ta k’ara haske da kyau fatar jikinta ta k’ara laushi.

A 6angaren yarima yana zuwa yaduba lafiyarta, sannan yana kiranta a waya koda ace bai jeba, itama tana k’ok’arin ganin ta je part d’insa koda sau d’ayane a cikin kwana biyun, har lokacin ba wanda tabari yagane tana da ciki.

 

*BAYAN SATI BIYU*

A ranar da cikinta yacika wata hud’u, bayan sallar la’asar ji tayi kwanciyar ta isheta, mik’ewa tayi tanufi part d’in yarima lokacin da tashiga a parlour tasamesa yana sa agogo a hannunsa da alama fita zaiyi. kallonta yayi ganin ta zuba mai ido yace ya dai?
Murmushi zarah tayi tare da marairaicewa tace dan Allah inaso inje ingaishe da su dada.
Keda bakida lafiya kuma zaki fita? Cewar yarima.
Zarah shuru tayi sai chan tace na fa samu sauk’i kuma ni zaman ne ya isheni saisa nakeson ind’an mik’e k’afar.
‘Daukan hularsa yayi yasaka sannan yace ohk, muje nima yanzu fada zanje.
Cikin jin dad’i zarah tafad’a jikinsa tare da cewa nagode,
yarima janyeta yayi daga jikinta tare da kallon cikinta yace kar kiji ma baby ciwo.

Murmushi zarah tayi tare da jawo hannunsa tad’aura saman cikinta tace kar kadamu babynka yana lafiya,
Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace muje memartaba yana jirana, zarah wucewa tayi gaba yarima yabi bayanta suna fitowa a jere suke tafiya, saida suka zo wajen turakar dada sannan zarah tashiga yarima yawuce fada.

koda tashiga a parlour ta tarar da dada da kuyanginta ana mata tausa a k’afarta, nan kuyangin dada suka dinga duk’awa suna gaisheta, zarah tadinga amsa musu cikin sakin fuska sannan tasamu waje a k’asa saman carpet tazauna gefen dada da take saman cushin, fuskar dada d’auke da murmushi tace a’ah yau amarya ce dakanta?

Murmushi zarah tayi tare da duk’ar da kai cikin girmamawa tagaishe da dada.
dada amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta ya suke.

Alhmdllh duk muna lafiya, cewar zarah cike day kunya.
Ina wannan miskilin mijin naki? Kwana biyu ban gansaba, ko kuma kun min k’wace yanzu ku kad’ai yasani, dada tafad’i maganar cikin tsokana.

Murmushi zarah tayi sannan tace taya zai mance da ke uwar gida? Ai mu bamu isa mushiga tsakaninku ba, aikine kawai ya6oyesa.
Gidanku ja’irar yarinya kawai, ammah shi aikin bai 6oye muku shi ba sai ni dan rashin adalci.

Dariya zarah tayi sannan tace ranki yadad’e taya zai mance da mu sabon jini?.

Knocking d’in k’ofan da akayine yasa dada tabada izini a shigo, d’aya daga cikin kuyangartace d’auke da wani tray, nan tazube takwashi gaisuwa wajensu sannan tacema dada ranki yadad’e gashi angama.
Murmushi dada tayi tace toh mik’omin shi nan itama kishiyata taci, cikin sauri kuyangar takai gaban dada ta aje.
dada kallon zarah tayi da take wasa da yatsun hannunta tace ga fa dambun kifi kici dada tafad’i haka tare da bud’e murfin da aka rufe shi da shi.
zarah k’amshin yadaki hancinta daurewa taso tayi nan zuciyanta yafara tashi, wani irin tuk’a taji yana taso mata cikin sauri tamik’e dagudu tanufi k’ofa, dada cike da mamaki tace lafiya me yake faruwa?
Batama san dada tanayi ba kafin tafita daga k’ofan sai aman yakubce mata nan tafara kwararashi..

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Jinjinar bangirma agareki mummyna chubad’o muhammad, nagode sosai da dedicated d’in book da nasamu saidai ince Allah yabarmu tare 4ever_

 

Back to top button