Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 59

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*59*

Inna tayi fada sosai akan Ayman Yana barinta tana abunda take so Kuma ta hana yawo tace ya daina barinta tana fita daga nan suka mata sallama suka wuce school nasu ya sauketa akan zai dawo ya dauketa by 3 idan ta gama classes, tana zuwa ta fara Neman layin Ummeey da Salima sun fito a guje suka rungumeta suna oyoyo amarya nan Yan department nasu suka taru suna tayata murna suna mata fatan class suka shiga na 10-12 bayan sun fito ne suka zauna hira shawarwari suka Bata akan zaman da zatayi da kishiyar tata tana Basu labarin yadda sukayi da safe akan breakfast, Salima tace ” ke kiyi hankali da ita wallahi wasu fa cikin abinci zasu gama dake su rabaki da miji kina ji kina gani ki koma y’ar kallo ” dariya Ummeey tayi tace ” toh ya zatayi idan ba tare zasu na cin abincin ba Allah dai ya kare ” sauke numfashi hajjo tayi tana hango abubuwa da dama game da auren nata , a duk lokacin da ta tuna kalaman kawu Bakura sai gabanta ya Fadi tayi saurin kauda tunanin tana dauko Wani hira daban har 1 yayi suka shiga sallah.

Bayan azahar Yan uwan Failuzaa sukayi sallama da Ayman akan zasu tafi gidan Ammi su kwana washe gari zasu koma Sudan , godiya ya musu bayan ya cikasu da kudade masu tarin yawa driver ya daukesu zuwa gidan Ammi saboda Fauzan na office, gidan ya rage Failuzaa da meenal saboda Ayman yaki bari a kawo y’ar aiki yace baya bukata . Karfe 3 ya sake wanka cikin half jumpa sky blue sai zuba qamshi yake ya tafi school daukar hajjo, suna fitowa ta hango motarsa inda ya sauketa da safe tayi sallama da kawayen nata ta tafi.
ta Bude front seat ta shiga bakinta dauke da sallama ya amsa cikin sakin fuska haka suka dau hanyar gida Babu Wanda yayi magana tsakaninsu har ya shiga gidan yayi parking ta fito tare da cewa “thanks”
Part nata ta wuce ta saka key tana budewa Failuzaa ta fito
“Barka da dawowa Yan makaranta” murmushin karfin Hali tayi ” yawwa nagode ya gida ”
“Alhamdulillah ya school Kai Boko akwai wahala haka lokacin da nake BSc dina Nasha wahala bare a ce kana da aure ai sai a hankali” haushinsa taji wato sai da ya fada mata inda taje kenan ,
“Allah Sarki dayake Ina final year ne ai nan da nan zaki ga na gama ”
“Hakane Allah ya taimaka, meenal ga anty Baki gaisheta ba” murmushi yarinyar tayi hajjo ta mayar mata tana Mika mata hannu
“Zo y’ar Dady ne ko y’ar momy ”
“A’a y’ar dady ce saboda idan babanta na kusa Bata kulani haka nan Shima yake jida ita ”
Murmushi hajjo tayi ” ba dole ba irin wannan kamanni haka no wonder take kama dashi ”

Cike da jindadi Failuzaa ta gyara tsayuwa ” haka dai kowa ke cewa ni Kuma dai bana ganin kamannin ”
“Uhmm saboda Kuna tare ne ai..bari na shiga na dan huta ”
“Ok bari a kawo Miki abinci ” Bata Jira amsa ba ta wuce kitchen meenal kuwa ta tsaya tana kallon hajjo, ” taho y’ar Dady ” make kafada tayi tana tsaye uban ya shigo tana ganinsa ta ruga zuwa wajensa hajjo ta Bude kofa ta shige Ayman ya manna mata peck Yana kallon fuskarta yace ” have you greeted your aunty ” make kafada tayi tana zumbura Baki ya lakuci hancinta yace ” idan kina gaisheta zata na Baki sweets n ice cream fah ”
“Really! ta furta Yana dariya yace” yeah..sosai ai Nima kullum tana bani ” Failuzaa ce ta fito dauke da food flask tana ganinsa ta fara murmushi ” welcome Qalbee ” tanx ummu ”
“Nifa banson wannan sunan meenal da take kira na dashi na fada mata ta daina amma taki Kai Kuma kana son kama sunan ”
“Where are you heading to?” tayi fari da Ido
“Abincin Antin meenal ne zan Kai mata ”
“Da kin bari a part naki tazo taci a can dama Ina son ku Saba da Hakan duk wacce take da girki a part nata zamu ci abincin” ta langabe Kai ” angama yarima amma dai yau kadai a mata afuwa saboda ta dawo a gajiye Kuma kasan amarya ce dole a lallabata kamar kwai ”
Mamaki yake Yana kallonta yadda take haba haba da hajjo Baiyi tunanin zai sameta da sauki haka ba saboda yasan balain kishinta, d’aga kafada yayi yace “well.. duk yadda kika ce”
dadi ya lullubeta wato kissan na aiki gashi har ta hango alamun nasara tun yanzu ai ya zama dole ta kwantar da Kai, kofa ta kwankwasa tare da sallama Ayman ya wuce part nasa tare da meenal hajjo ta Bude kofa Failuzaa ta shige ta nemi waje ta zauna tana karewa falon kallo da wayo ba lallai agane Hakan ba saboda ta sake tana ta zuba hira.
Bayan mintuna ta tashi ta fice hajjo ta tabe baki tace ” zakiyi ki gama y’ar iyayi Ina dai dai da zamanin ki wallahi wai ni zaki nunawa munafunci muje zuwa ”
Abincin ta Bude jollof din shinkafa ne sai qamshin spices ke tashi ta dauki plate don yunwa takeji , kadan ta zuba tayi Bismillah ta fara ci ba laifin ta iya girki amma wannan spices din Bata taba Jin irin dandanon ba maybe daga Sudan din aka kawo mata, haka dai ta cinye Wanda ta zuba a plate ta ajiye sauran bisa dinning table ta shiga d’aki wanka tayi kafin ta fito tayi la’asar, doguwar Egyptian cotton gown ta saka black color batayi makeup ba sai kwalli da lip balm ta shafa da turare sannan ta dawo parlor ta kwanta. Gidan shiru kamar Babu kowa kewar mijinta take amma ta kasa yarda da Hakan tana Jin zuciyarta Babu dadi TV ta kunna tana kallo Babu Wanda ya sake shigowa har aka kira magariba, zaman ya gundureta bayan tayi salla tana zaune ta dauki wayarta tana game din subway har akayi Isha ta tashi tayi sallah sannan ta dauki Qur’ani tana karatu, bayan minti talatin Failuzaa tayi sallama ta shigo Wani uban qamshi take sai da hajjo ta d’aga Kai idanunta suka sauka kan kwalliyr da Failuzaa tayi cikin Wani leshi Mai uban kyau sai daukan Ido yake ga sarkar diamond Dake kyalli sai daukar Ido yake Yana reflecting da hasken NEPA, murmushi tayi” sorry anty amarya kina karatu ne maigidan ke son magana damu dama Yana falonsa Yana Jira ” “okay Gani nan fitowa” daga haka ta juya ta fita, hajjo ta zauna shiru ta rasa meke damuta dama wannan shine ake kira da kishiya… Ya Allah ka bani iKon cinye wannan jarabawa” rufe littafin tayi ta maidashi bedroom ta fito sanye da jalbab ta Kara fesa turaruka sannan ta nufi part din nasa.
Yana zaune Yana kallon news sanye yake da jallabiya maroon me Karen kyau ga qamshin turarensa ya mamaye falon gaba d’aya, meenal tayi bacci bisa cinyarsa hannunsa rike da remote control fuskarsa sai sheki yake ya amsa mata sallamar da tayi Failuzaa na zaune daf da kafafunsa tamkar wacce ta zauna gaban ubanta, bugun zuciyarta ya dada tsananta saboda jallabiyr ta masa kyau sosai ga hasken fitilun NEPA da suka haska falon fuskasa sai sheki yake gashin Kansa da alama ya shafa Mai sai kyalli yake da sauri ta sunkuyar da Kai ta nemi waje ta zauna can nesa dashi bisa kujera wato saboda matarsa tana nan shiyasa yau Bai shigo part nata ba …
“dama ma taraku a nan saboda na muku y’ar tunatarwa ne , Ina son ku zauna lafiya please ku hada Kai bana son hayaniya am not used to it, ku rike juna tamkar Yan uwa sannan girki kuyi deciding how many days zaku raba, abinci Kuma duk wacce take da girki a part nata za’a ci abinci Kuma tare za’a ci , idan da Mai magana am listening ” Failuzaa tace ” insha Allah Qalbee zaka samemu da hada Kai fiye da yadda kake tsammani sannan batun raba girki anty amarya sai ki fada yadda kike so ya kasance ni bani da matsala ”
Murmushi Hajjo tayi tunda ta shigo Ayman Bai Kalli ko inda take ba abin ya mata ciwo tace ” A’a ai kece babba duk yadda kika gani Babu matsala ”
” Toh shikenan kwana d’aya yayi” Failuzaa ta fada tana kallon hajjo
“Is ok Hakan yayi ”
“Idan Bai Miki ba wallahi kiyi magana sai a Kara ”
“A’a wallahi is ok ” hajjo ta amsa Ayman dai baice komai ba idanunsa na bisa TV, ” toh Qalbee kaji kwana d’aya yayi Allah ya bamu zaman lafiya ”
“Ameen ya amsa , hajjo ta tashi tsaye don bazata jure wannan wulakancin ba ” sai da safe mom meenal ”
“Toh anty amarya har zaki tafi toh mu kwana lafiya” ta juya ta fice zuciyarta na mata Kuna tamkar an zuba garwashin wuta a ciki lallai namiji munafuki ne dubi yadda yake riritata cikin kwanakin baya yanzu daga dawowar matarsa shikenan.
Key ta saka ta kulle part din saboda tasan Babu Mai sake shigowa ,cire jalbab din tayi ta kwanta a falon tana Jin zuciyarta na radadi wayarta ta dauka ta shiga Whatsapp she wants to keep herself busy , number Aman ta shiga Yana online kamar zata masa message ta fasa ta kurawa profile nasa Ido nan da nan hawaye suka cika idanunta tana tuna lokuta da dama na rayuwarsu tare da irin tanadin da sukayiwa juna idan sukayi aure. Ajiye wayar tayi ta kife kanta bisa kujera tana kuka Mai ban tausayi Babu Mai rarrashinta dama haka aure yake no wonder kowa yake cewa Allah ya Baku hakurin zama lallai wannan shine hakurin yanzu ne tagane dalilin dayasa mata suka tsani kishiya Niko nace me kika gani hajjo karatun kishiya na dayawa ko babin farko baa Bude Miki ba .
Bacci ya fara daukar ta can taji ana knocking sama sama cikin bacci ta Bude Ido ta Kalli agogon dake makale jikin bangon falon 10:25 ta tashi taje ta Bude, qamshin turarensa ne ya fara dosar hancinta Yana tsaye ta juya ta koma ciki ya shigo tare da rufe kofar . Kwanciya tayi bisa kujera ta juya masa baya ya taka yazo inda take ya tsaya ” Ayshah!”
ko motsi batayi ba bare ta amsa lumshe Ido yayi shin yaya zaiyi da ita ne da wannan yawan fushin nata ” me Kuma na Miki baby girl” ya furta kamar zaiyi kuka, tabe baki tayi tana rufe idanunta, ya zube guiwowinsa bisa carpet Yana leka fuskarta ” tell me what have I done to you kike fushi dani”
“Ni nace Ina Fushi da Kai ne ?” ” I can sense it Ayshah please kiyi hakuri I have no option ne haka Allah ya tsara min wannan rayuwa ta zama da mata biyu ba yin kaina bane don Allah kiyi hakuri ki daina yawan fushi dani bazan jure Hakan ba”

“Na sani ba da son ra’ayinka bane aka aura Maka ni , kana rayuwa tare da matarka cikin kwanciyar hankali aka….
“Shhhh…bana son sake Jin wannan kalaman don Allah ki daina please” hawaye ne ya cika mata idanu tana kokarin boyewa, ya juyo da ita tare da jawota jikinsa Yana mata rada a kunne
” You know I love you and you are always my favorite, u are not an option u are my priority please baby ki daina yawan Bata rai bana Jin dadin Hakan please…
Narke masa tayi ta fara kukan shagwaba tana fisge jikinta alamar ya saketa nan kuwa ya rikice yahau rarrashi ganin zata bore masa yasa ya hade bakinsu wuri nada ya fara aika mata Wani sakon English kiss Mai rikita brain , tuni jikinta ya fara rawa notunan kanta na Neman kuncewa dakyar ta kwace kanta saboda Jin abin na Neman zarce tunaninta. Numfashi suke saukewa idanunsa sun canza launi Yana lumshesu Yana budesu a hankali shi kadai yasan me yakeji game da ita Amma ta kasa ganewa , rike hannunta yayi ” am going please take good care of yourself for me ok ” Kai ta gyada saboda a tsorace take tana son ya fice ya bar mata d’aki, peck ya mannawa yatsun hannunta ya tashi cikin kasala yace ” kizo ki rufe kofa good night I’ll really miss you today” kauda Kai gefe tayi ya juya ya fita dakyar ta ja jiki ta tashi ta kulle kofar ta koma ta zube bisa kujera tana lumshe Ido tana tuna abubuwan da suka faru tsakaninsu.

Back to top button