Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 47

Sponsored Links

PAGE* 4⃣7⃣

Dada da take zaune ido tazuba mata tana kallon ikon Allah ganin tana ta aman kamar zata amayen ‘yancikinta yasa tafara yi mata sannu nan tasa kuyangarta d’aya tad’auke dambun kifin daga wajen.

Bayan zarah ta gama aman a galabaice alkyabbarta kawai tacire saboda ita kad’ai ta6aci.
dada kuyangi tasa sugyara wajen nan tacigaba da jera ma zarah sannu sannan tace tashiga ciki tagyara jikinta,

A kunyace tace toh sannan tawuce toilet da yake cikin bedroom d’in dada batare da ta kalli dada ba,

Dada ido tazuba mata tana kallonta har tashige sannan tayi murmushin jin dad’i tace Alhmdllh da alama mun samu rabo.

Zarah jiki ba k’wari tahad’a ruwan d’umi tayi wanka bayan ta fito kayan jikinta tamaida tunda su basu 6aciba, zaune tayi takasa fitowa saboda wata irin kunyar dada da takeji na amai da tayi mata a parlour.

Ta dad’e a zaune sannan daga baya tamik’e lokacin da tafito parlour da mamakinta taga angyara wajen tes d’akin sai k’amshin turaren wuta yake, kallonta dada tayi har tazauna sannan tace sannu ‘yar nan ai da kin fad’i bakison k’arnin kifin da ban bud’eba, kuma bakida lafiya baku fad’amin ba ai da nazo na dubaki, kokuma wannan miskilin mijin naki taya zai fad’a, abinda ma yashafesa bai fad’aba barema ayi tunanin fad’an na wani.

K’ara duk’ar da kanta tayi k’asa cike da jin kunya.

Ganin haka yasa dada tace yanzu me kikeson ci? Naga kin amaye duk abinda kikaci.

Cikin jin kunya tace na k’oshi.

A’a wane irin kin k’oshi keda ba komai cikin cikinki, k’walah ma kuyangarta kira dada tayi tace aje akawo ma zarah tuwo, cikin sauri kunyarta tace angama ranki yadad’e sannan tafita tabar d’akin.

Dada tace ai nasan shi tuwo zaki so shi, murmushi kawai zarah tayi.

Bayan ‘yan mintuna sai ga kuyangar nan ta shigo d’auke da kular tuwo, wata kuma tana rik’e da na miya da plate nan suka aje gaban zarah.

Dada tace suzuba mata taci, nan suka zuba sannan suka bud’e miya kala biyu ce sukace ranki yadad’e wace za’a zuba miki?

Zarah kallon miyan tayi ganin miyan ku6ewa d’anya da ta ganye ce yasa tace azuba mata ta ku6ewa nan suka zuba mata sukace ranki yadad’e man shanu fa?
Cikin sauri tagirgiza kai tace kar kuzuba min.
Cikin sauri sukace angama ranki yadad’e sannan suka tashi suka fita daga d’akin.

Dada kallon zarah tayi fuskarta d’auke da murmushi tace kici man.

Murmushi zarah tayi sannan tafara d’iba taci, ta ji dad’in miyan sosai ga tuwon mai laushi irin mai wucewa silif wanda take so nan tacigaba da ci ahankali cike da jin nauyin Dada.

Ganin haka yasa Dada ta tattara hankalinta ga news d’in datake kallo dan zarah tasamu taci sosai.

Haka zarah tad’anci sannan tature plate d’in, kallonta dada tayi tace ba dai har kin k’oshiba?

Zarah ahankali tace eh dada na k’oshi.
Kidaure kid’an k’ara ko kad’anne, cewar dada.
Zarah cikin jin kunya tace na k’oshi.

Dada tace toh shikenan, nan tamaida hankalinta ga TV.

Zarah samu tayi tamik’e dan tawanko hannu.

Da kallo dada tabita cike da farin ciki dan ko ba’a fad’a mataba yanayin zarah da tagani yasa ta gane cikine gareta, ahankali tace Allah sarki sumayya naso inga jininki ammah da rabon na zarah zan fara gani….tana chan tana tunani batasan lokacin da zarah tadawo ba sai da tafara tattara kwanukan sannan hankalin dada yakai wajen, zaro ido dada tayi da cewa miye haka zakiyi?
Zarah batare da ta kalli dadaba tace ranki yadad’e zan d’an rage kayanne.

Dada tace a’a aje bari ma’aikatan suzo sukwashe keda bakya jin dad’in jikinki, kawai kizauna kihuta.

Dada ai zan iya, cewar zarah.

A’a kibari suzo sukwashe.

Zarah ajewa tayi sannan takoma tazauna,
Dada tace da kin shiga ciki kin d’an kwanta kihuta.

Murmushi Zarah tayi sannan tace dada ai yanzu ma nakeso inwuce gida.

Jinjina kai dada tayi tace kar kikwanta nan musaceki ko?
Yanayin yadda dada tayi maganar saida yaba Zarah dariya tace a’a dada kawai dai akwai abinda zanje inyine.

Cikin gamsuwa da maganar dada tace toh ai shikenan hakan ma mungode Allah yabada ladan zumunci, Allah yayi muku Albarka.

Ameen ranki yadad’e, nan Zarah tayi ma dada sallama tafita.

Dada binta tayi da kallo cike da sha’awa tace Allah sarki sumayya kema Allah yasa ina da rabon ganin naki d’an,
Ita kanta dada tana mamakin yadda cikin jikokinta ta fi son sumayya, hakan ya samo asaline ta dalilin duk cikinsu ita sumayya tun tana k’arama daman itace ta wajen dada inbata wajen ummanta to tana wajen dada, dan a k’arshema dada ce tayi yayenta.

 

Zarah tana cikin tafiya har zata shiga 6angarensu sai ga sumayya ta fito, saida gaban Zarah yafad’i dan rabon da taga sumayya Ita kanta ta mance dan zata iya cewa tayi kusan 2 weeks.

Tsaya sumayya tayi tana kallon zarah cike da mamaki ganin yadda tacanza tak’ara fresh da kyau, chan sai taja tsaki sannan cikin fad’a tace ke dabbar ina ce kina ganin mutane zasu wuce ammah kikasa basu hanya suwuce.

Zarah murmushi tayi cikin rashin damuwa tare da dakewa tace kar kidamu ke ai naga ko cikin dangin namu na dabbobi kamar makauniyace tunda duk fad’in hanyarnan kirasa ta inda zakibi sai ta wajena.

Cike da mamaki sumayya takalli Zarah dan bata d’auka zata iya yada mata magana irin hakaba, ran sumayya in yayi dubu toh ya 6aci cikin d’aga murya tace eh dole kice haka dan a yanzu kinsha jan miya kin waye kina gani kamar daidai kike da ni, toh wlh bari kiji ni nan da kike gani bani ta6uwa kuma duk ubanda yace zai ta6ani toh aikam zai ta6o ma kansa masifa da bala’i ke sai kinyi kuskuren abinda kika aikata agareni.

Zarah dafe kanta tayi cikin kwantar da murya tace please malama kiban waje inwuce idan ke kinsaba hargagi toh ni ban sababa dan har kin fara haddasa min ciwon kai.

Sumayya a harzuk’e tace ke ko ubanki bai isa yafad’amin maganaba bare ke jakkah,

Zarah murmushin takaici tayi sannan tace Allah sarki kar kidamu nasan jahilcine yayi miki yawa ammah dan Allah ya kamata kikoma islamiyya gimbiya, tana fad’in haka tacanza hanya tawuce tabar sumayya tsaye tana ta balbalin bala’i.

 

Sumayya cikin 6acin rai tawuce tanufi turakar iyayenta, a parlour ta tarar da sultan Abbas da mahaifiyarta, ganin Abbanta yasa tad’an saki fuska gefensa tazauna cikin sakin fuska tagaishesa.
Murmushi sultan Abbas yayi sannan ya amsa mata tare da tambayarta mijinta.
Sumayya cikin shagwa6a tace Abbah yana lafiya.
Toh ya ‘yar uwartaki dafatan kuna zaman lafiya?
Sumayya ji tayi kamar ya da6a mata wuk’a a mak’ogwaro jin ya kira wadda tafi tsana a rayuwarta a matsayin ‘yar uwarta, murmushin yak’e tayi sannan tace abbah tana nan lafiya.

Toh masha Allah adaicigaba da hak’uri sumayya kizauna da ita lafiya banason fad’a ko tashin hankali.

Toh Abbah daman muna zaman lafiya.
Cikin jin dad’i sultan abbas yace yauwa ‘yar abbah Allah yaimiki abarka.
Ameen abbana, cewar sumayya sannan takalli sultana sadiya da tazuba musu ido tana murmushi, itama sumayya murmushin tayi sannan tace ummana ina wuni?
Lafiya lou daughter ya gidan?
Alhmdllh ummah,
Toh masha Allah ina fatan mijinki da ‘yar uwartaki suna lafiya.
Sumayya cike da mamaki take kallon ummah ganin yadda ummanta take Magana a gaban abbah.

sumayya murmushi tayi mai fassara sannan tace duk lafiya lou ummah.

Sultan Abbas mik’ewa yayi yace bari inje fada nasan yayana yana chan yana jirana dan akwai wata jana’iza da zamuje ta abokinsa.

Sultana da sumayya nan sukayi mai adawo lafiya dan sultana sadiya har bakin k’ofa tarakasa sannan tadawo.

Da mamaki take kallon sumayya da lokaci guda tacanza fuska, sultana sadiya cike da damuwa tace sumayya lafiyarki?

Sumayya k’wallah ce tafara fita daga idonta cikin muryar kuka tace ummah na tsani yarinyar chan natsani inbud’e idona inganta cikin gidannan.

Sultana sadiya cike da damuwa tazauna gefen sumayya tare da rungumota jikinta cikin rarrashi tace sumayya kema kin sani nima hankalina ba zai ta6a kwanciyaba in ina ganinki cikin damuwa, kicigaba da hak’uri insha Allahu zarah ta kusan fita tabar miki gidanki.

Sumayya cikin sauri tad’ago kai takalleta tace ummana taya hakan zata kasance, wlh yarinyar chan yadda kikasan ta asirce yarima, kiduba kiga duk makircin da ake k’ullah mata ammah bai ta6a d’aga kai yakalletaba, ni wlh har na fara gajiya ina tunani akwai abinda tak’ullah.

Murmushi sultana sadiya tayi sannan tace kidaina damuwa daughter kibarni da ita in ta san wata toh batasan wataba ni nasan yadda zanyi da ita dan suhail na sumayya ne ita kad’ai.

Cike da jin dad’i sumayya tak’ara ruk’unk’ume ummanta tace nagode sosai ummana Allah yabar min ke.

Sultana sumayya cike da son d’iyartata tace Ameen daughterna.

 

A chan 6angaren zarah lokacin da tashiga part d’inta a parlour ta yada zango saman 3 seater tare da jingine kanta da kujerar tana maida numfashi ahankali, chan taji wani irin tuk’a ta taso mata, cikin sauri tamik’e tanufi toilet,
Saida ta amaye dukkan tuwon da taci duk ta galabaita, dak’yar tasamu tawanke fuskarta tafito tahau saman gadonta tayi kwanciyarta,
Tana mamakin yadda yau daga safe zuwa yanzu ta yi amai ya kai biyar.

Juyi kawai take saman gadon har aka kira sallar magrib tayi sallah tana zaune saman darduma tana lazumi aka kira isha’i.

Bayan ta gama sallah wanka tashiga tayi sannan tayi shirin bacci, yunwa taji tana ji ammah gudun kar tayi amai yasa tayi kwanciyarta haka.

Wajen 8:30pm kwance take saman gadonta ga yunwa duk ta addabeta, kawai ji tayi tanason shan ice cream,

Sharewa tayi tai kwanciyarta tana ta juyi daga k’arshe ji tayi bata iya daurewa indai batasha ice cream d’inba toh akwai matsala, dan haka tamik’e cikin sauri tad’auko hijab tazumbula tafito tanufi part d’in yarima har tana tuntu6e.

Tana shiga tasamesa zaune a parlournsa yana kallon ball gabad’aya ya tattara hankalinsa a TV d’in kasancewar yana son wasan, bai ankaraba sai jinta yayi ta fad’o jikinsa,

Kallonta yayi cike da mamaki yace ke lafiya? Zarah k’irjinsa tashige tare da fashewa da kuka.

Yarima gigicewa yayi yace lafiya zarah? Meyake faruwa?
Cikin sheshek’an kuka tace ni ice cream nakeson sha, bana iya cin abinci da naci amai nake, d’azun ma saida nayi wajen dada.

Yarima ajiyar zuciya yasafke sannan yace yanzu saboda ice cream kike kuka?

Turo baki tayi cikin shagwa6a tace uhm.

Wayarsa kawai yajanyo batare da yayi magana ba yakira wani guard d’insa yace yaje yasamo masa ice cream yanzu, daga chan 6angaren guard d’in cike da girmamawa yace toh ranka yadad’e angama.

Kashe wayar yarima yayi tare da kallon zarah da tatsaresa da ido har a lokacin k’wallah tana fita daga idonta, sannan yace bari akawo miki.

Gyad’a kai kwai tayi sannan tacire hijab d’inta takoma ta lafe a k’irjinsa wani irin numfashi taja dan har cikin ranta taji dad’in hakan,

Yarima maida idanuwansa yayi yalumshe yanajin yanayin d’umin jikinta.

Haka suka kasance babu wanda yak’ara magana sai chan wayarsa tafara ringing, d’aukota yayi ganin mai kiransa yasa yayi picking batare da yayi magana ba,
Daga chan 6angaren akace ranka yadad’e ansamo,

Kallon zarah yayi da tazuba mai ido sannan yace ohk ina zuwa.

Jin haka yasa zarah tasafka daga jikinsa nan yamik’e yanufi k’ofa yakar6o yadawo saida yazauna sannan yamik’a ma zarah k’atuwar ledar.

Cikin sauri tak’ar6a fuskarta d’auke da murmushi tace nagode sannan tabud’e robabin ice cream ne manya kusan guda biyar nan tafito da guda, kallon yarima tayi da yake kallonta tace zakasha?
Girgiza mata kai kawai yayi.
Mik’a mai d’ayan tayi cikin shagwa6a tace karik’e min insaka sauran cikin freezer kar yanarke.

Yarima zuba mata ido yayi batare da ya yi magana ba kamar ba zai kar6aba sai kuma chan yakar6a.

Mik’ewa tayi tanufi freezer d’insa tasaka sannan tadawo tazauna saman cinyarsa tare da kar6a tabud’e robar, jikinta har rawa yake nan tafara sha.

yarima ido yazuba mata yana kallon yadda take sha saikace wadda akace za’a k’wacemawa, hannu baka hannu k’warya takeyi.

Har saida takusan shanyewa sannan ta aje takalli yarima tayi murmushi ahankali tace nagode nan takwanta k’irjinsa tayi lamo,

Ahankali taji yarima yana neman tura hannuwansa cikin rigarta, maida idanuwanta tayi talumshe fuskarta d’auke da murmushi.

Cikinta yashiga shafawa, yanayin yadda yake shafarsa wani irin shock takeji a jikinsa, nan tak’ara lafewa,

Ahankali yamaida hannuwansa a k’irjinta yana shafa cikin wani irin salo, zarah nema tayi tarikice mashi nan taruk’unk’umesa.

Cigaba yayi da abinda yake saida yayi kusan 5 minutes sannan yafitar da hannunsa daga cikin rigarta, ahankali yabud’e idanuwansa da suke lumshe tare da lek’a fuskar zarah da tatura cikin k’irjinsa kamar zata shige ciki sai maida numfashi take kad’an kad’an, murmushi yad’anyi kad’an sannan yad’auketa cak yanufi bedroom d’insa bai zameta a ko’inaba sai saman bed d’insa.

Zarah na ji ya safketa cikin sauri tajuya mai baya, murmushi yayi sannan yawuce yakoma parlour yakashe kayan kallon sannan yadawo bedroom d’in, kashe gloves yayi nan yahau gadon yakwanta daga bayan zarah.

Hannunsa taji yad’auro saman cikinta, murmushi tayi sannan ahankali itama tad’aura hannunta saman nashi tana shafawa juyowa tayi takallesa cikin d’an hasken da yake d’akin har a lokacin hannunta yana cikin nasa ganin shima idanuwansa suna a kanta yasa tamaida kanta a k’irjinsa takwanta.

Lumshe idonsa yayi yana shak’ar k’amshin gashin kanta, sai chan yace meyasa bakison cin abinci?
Zarah d’ago kai tayi takallesa ganin idanuwansa a rufe yasa kamar zatayi kuka tace amai yake sanyani.

Bud’e idonsa yayi yakalleta, sannan yace kidinga ci kokad’anne.

Umhum kawai zarah tace.

Hannu yakai yajanye mata gashinta da yabazu har gefen idonta, ido suka zuba ma juna suna ma junansu wani irin kallon da su kansu basusan ma’anarsaba, yarima ne cikin sauri yafara janye idonsa daga cikin nata.

Zarah ma cikin jin kunya tamaida kanta takwantar a k’irjinsa,
Ahankali taji ya kai hannunsa yana neman rabata da ‘yar rigarta.

Yana cirewa tazame jikinta daga nasa.
Da mamakinta sai ganin yarima tayi ya dawo bisa ita, zaro ido tayi kafin tayi magana sai jin bakinsa tayi cikin nata, sun dad’e a haka sannan yagangaro wuyanta zuwa k’irjinta.

Zarah bada kai tayi dan ita kanta tasan abuk’ace take da mijin nata.

Bayan komai ya lafa Zarah kukan shagwa6a tasaka mai, yarima rungumota yayi jikinsa yana d’an bubbuga bayanta ahankali alamun lallashi.

Zarah cigaba tayi da kukan, ahankali yabud’e idanuwansa da suke lumshe cikin muryarsa da tadashe yace kukan fa?

Turo baki Zarah tayi cikin kuka tace toh bakaibane kaban wahala, kuma wanka nakeso kayi min.

Ido yazuba mata sai chan yace na ji.
Janyeta yayi daga jikinsa yamik’e yanufi toilet, saida yatsarkake jikinsa sannan yahad’a mata ruwan d’umi.

Bayan ya fito kallonta yayi yace muje.

Hannu Zarah tamik’a mai alamun yad’auketa.
Yarima babu yadda ya iya haka yaduk’a yad’auketa yanufi toilet da ita, cikin komin yasakata.

Har ya juya zaya tafi Zarah cikin sauri tarik’o hannunsa tare da fashewa da kuka tace kayi min wankan.

Yarima haka yatsaya yana mata wanka ita kuma tana zuba mai shagwa6a, har yagama sannan yahad’a mata wasu ruwan yace tayi wankan tsarki.
Ganin ya juya zai tafi yasa zarah tace bana fa iyayi please kataimaka kayi min.

tsaye yarima yayi cikin ransa yace yarinyar nan ta raina min wayau, kamar yace bazaiyiba sai kuma chan yafara yi mata.

Zarah kallonsa tayi ganin yadda yahad’e rai yaso yabata dariya, nan tafara yin dariya ciki-ciki, tanak’unshe dariyar karaf suka had’a ido da yarima.

Wata uwar harara yawurga mata sannan yasaketa yafita yabar toilet d’in.

Zarah dariyarta tacigaba dayi ahankali sai daga baya da tatuna a inda take yasa tatsagaita yin dariyar sannan tayi wankanta.

Bayan ta gama fitowa tayi tatarar yarima lokacin har ya kwanta, dan haka itama rigarta tamaida sannan taje bayansa takwanta.

_*BAYAN KWANA UKKU*_

Sultana bilkisu ce zaune parlourn dada bayan sun gaisa nan suka shiga yin hira suna cikin hirar ne dada tace ummin suhail ashe da rabon zanga jinin yarima.

Ummi cikin rashin fahimta tace dada ban ganeba.

dada har ta bud’e baki zatayi magana sai ga sultana sadiya ta shigo da sallamarta.

Gabad’ayansu suka amsa mata nan tazauna saman d’aya daga cikin cushin d’in, cike da girmamawa tagaishe da dada.
nan dada ta amsa mata tare da tambayarta gida.
Alhmdllh cewar sultana sadiya fuskarta d’auke da murmushi tace ina fatan kina cikin k’oshin lafiya?
Dada tace Alhmdllh saidai abinda ba’a rasaba kinsan yanayin tsufa.

Gabad’ayansu sukace Allah yak’ara lafiya.
dada tace Ameen.

Sultana bilkisu fuskarta d’auke da murmushi tace sultana anwuni lafiya?
Kallonta sultana sadiya tayi tare da yin d’an guntun murmushi sannan tace lafiya lou sultana dafatan kina lfy?
Alhmdllh, cewar ummi.

Sultana sadiya tace wai ni ina yarima ne naga kwana biyu bansashi idonaba ko baya garin?

Mamakine yakama sultana bilkisu ganin yadda tayi tambayar, bayan jiya-jiyannan yarima da yaje gaisheta yace mata daga turakar umman sumayya yake ya je sun gaisa.
Sultana bilkisu d’an murmushi tayi sannan tace yana nan man, ashe baya zuwa yagaisheki, gaskiya yarima halinsa sai shi ya kamata kuyi mashi fad’a yagyara.

Rik’e baki sultana sadiya tayi tace taya zanyi mai fad’a? Rufamin asiri wa zai iya da halin wannan miskilin yaron.

Dada murmushi tayi tace ina ruwan yarima, ni har mamakin halinsa nake wani lokacin ma cewa nake anya shi kad’ai ne?

Ta6e baki sultana sadiya tayi tace ranki yadad’e shi kad’aine kawai dai iskancine yayi masa yawa dan ko mahaifiyartasa kamar bata isa da shi ba.

Sultana bilkisu murmushi tayi tace haba sultana kema shedace tsaye nake kan suhail, kuma ina masa fad’a akan wannan hali nasa ammah ya k’i canzawa.

Ta6e baki sultana sadiya tayi tace duk dai lokacin da yafara aje ‘ya’ya ai dole ya aje wannan iskancin nasa.

Dada murmushi tayi sannan cikin jin dad’i tace ai insha Allahu nan ba da dad’ewaba zamu sha suna.

Gabad’ayansu kallon Dada sukayi cike da mamaki sukace suna kuma?

Murmushi dada tayi tace ashe ku ma baku saniba, ai matarsa cikine da ita.

Murmushi sultana sadiya itama tayi sannan tace ranki yadad’e batada komai ai sumayya har yanzu Allah bai kawoba.

Dada kallonta tayi tace kekuma kinji ki da wata magana ai amaryarsa ce keda ciki.

Sultana sadiya jin maganar tayi kamar an jefota cikin kunnenta, nan gabanta yayi wani irin mugun fad’uwa, cikin k’ani’anin lokaci fara’ar fuskarta tagushe,

akasin sultana bilkisu da taji abun kamar a mafarki farin ciki nan yadabaibaye zuciyanta cikin ranta Alhmdllh kawai take cewa, dan batada buri a duniya da yawuce taga jinin yarimanta………

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*Yau page d’in nakune my fan’s mutanen saudiya, sak’onku yana zuwa a gareni nagode sosai da soyayyar da kuke nunamin saidai ince Allah yabarmu tare, jinjinar bangirma agareku Sis Aisha*_

Back to top button