Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 43

Sponsored Links

*PAGE* 4⃣3⃣

Da asuba saida yayi sallah sannan yatada zarah saida yataimaka mata tayo alwalla sannan tazo tayi sallah.

tana gamawa k’wallah ce cike da idonta takalli yarima da yake zaune ahankali tagaishesa.

Gyad’amata kai kawai yayi alamar ya amsa, janye idonta tayi daga kallonsa sannan tace nasan bazaka ta6a yadda cewa bani nazuba poison d’inba ko? Wlh ko da sau d’aya ban ta6a kawo ma raina incutar da kai ba, juyowa tayi takallesa da shima ita yake kallo sannan tace nasan bazaka ta6a yadda daniba a yanzu ka tsaneni ko?

Har a lokacin kallonta yake baice komai ba, zarah mik’ewa tayi dak’yar taje inda yake zaune tatsugunna tace koda ace zaka yanke min hukunci inaso kataimaka kayi min wanda iyayena bazasuji labariba, ammah dan Allah kataimaka kayi bincike kafin kazartas min da hukuncin,

Sai a lokacin yarima yajanye idonsa agareta sannan yace zarah kinji na ce miki wani abu?

Girgiza kanta tayi cikin sauri har a lokacin k’wallah tana fita daga idonta.

Toh indai banceba kikyaleni kije kikwanta kihuta.

Zarah girgiza kai tayi cikin kuka tace taya kake tunani zan iya kwanciya alhali ina cikin wannan matsalar?
Tausayi tabashi yanayin yadda tayi maganar, d’aura hannunsa yayi a kumatunta sannan yace kar kidamu, yana fad’in haka yatashi yafita daga d’akin,
Zarah kife kanta tayi da gadon tana mai ci gaba da kukan.

Koda yaje magana sukayi da doctor sannan yashigo yace ma zarah tataso sutafi har a lokacin kuka take jikinta ba k’wari dakyar take takawa, har bakin mota doctor yarakasu sannan sukayi sallama.

 

 

lokacin da sumayya tatafi d’akinta takaicine yacikata ganin burinta bai cikaba domin taso ace poison d’in yafara aiki agabansu dada saboda tasan da anga haka k’arshen rabuwar yarima da zarah tazo.

tsaki taitayi daga k’arshe dabara tafad’o mata nan takira kuyangarta zabba’u tace taje tasa mata ido akan duk wani motion d’in zarah

nan zabba’u takwashi gaisuwa sannan tafito tasamu inda ba za’a gantaba tala6e, tun daga fitowar zarah har tafiyar da sukayi da yarima asibiti duk akan idontane,

nan tazo taba sumayya labari dariyar mugunta sumayya tayi tare jinjina kai ahankali tace lallai zarah kinyi jarumta.

tunda asuba tazuba ido domin taga dawowarsu,

lokacin da yarima yayi horn suka shigo gate da mamaki yake kallon dada da umman sumayya da ita kanta sumayya da suke tsaye cikin ransa yace tabbas wannan aikin sumayya ne.

 

zarah kau rikicewa tayi takalli yarima tace shikenan yarima sun gano ni nashiga ukku.

yarima batare da ya kalletaba yace kar kisaki kinuna akwai wani abu indai kika nuna suka gane babu ruwana sai kisan yadda zaki Kare kanki,

daidai lokacin yagama parking d’in motar yabud’a yafita batare da ya kalletaba.

zarah tana ganin haka itama tabud’e tafito cikin zuciyanta tana ta addu’a

 

bayan yarima tabi a tsorace shidai tafiyarsa yake hankali kwance gab da zai isa wajen da su dada suke nan wayarsa tafara ruri tsayawa yayi yad’auko wayar yana dubawa murmushin nasara yayi sannan yayi picking d’in wayan batare da yayi magana ba,

daga chan 6angaren akace ranka yadad’e Dr, Ahmad ne yake magana daman wannan patient d’inne da kayi ma theater toh ya farka.

yarima shuru yayi nad’an lokaci sannan yace idan kun tabbatar da babu abinda yake damunsa toh sai kuyi masa wannan injection d’in da na aje inyaso da anjima idan nashigo sai in rubuta masa drugs.

daga chan 6angaren akace toh ranka yadad’e sai ka shigo, yarima baice komai ba yakashe wayarsa, sannan yamaida kallonsa ga dada da tatsaresa da ido ammah ko inda su umman sumayya suke bai kallaba.

murmushi yasakar ma dada yace ranki yadad’e ya akayi naganki nan a tsaye a wannan lokacin?

fuskar dada a d’aure tace daga ina kuke?

shuru yarima yayi yana murmushi,

dada tace ashe yarinyar nan dagaske guba tazuba maka tunda da taci abincin saida kukaje asibiti, kai wlh bansan samna bane sai yanzu matar da tayi shirin kasheka itace kataimaka mawa toh wlh dole memartaba yaji maganar nan.

 

har a lokacin yarima murmushi yake sai chan yace dada bai dace kice hakaba tunda baki gani da idonki ba, kirana fa akayi daga hospital akan wani emergency case cikin dare shine zarah tace zata bini mukaje tare kuma ma yanzu ai gabanki aka kirani waya.

sumayya tayi karaf tace wlh bahaka bane poison d’in da tacine a cikin abinci kiduba kiga yadda duk tazure,
ummanta tace ai wannan dama daga ganinta poison taci.

 

yarima murmushi yayi sannan yace sumayya gabanki tazuba min poison d’in? gabanki tayi girkin? Lokaci guda yajero mata wad’annan tambayoyin.

sumayya tace toh ai lokacin da takeyi naga ta zuba wani abu.

yarima wani mugun kallo yawurga mata yace toh kina dai nufin la6e kikayi mata.

sumayya hararar zarah tayi da take raku6e bayan yarima tace wannan gajar zan yi ma la6e? tak’aryata mana idan batayiba, kuma naga lokacin da katafi kakaita asibiti.

murmushin mugunta yarima yayi yace toh in ko ta zuba min poison toh tare da ke aka zuba kokuma ke d’in kika Zuba.

zaro ido sumayya tayi tace ni ya za’ayi inzuba maka poison?

yarima kallon dada yayi yace ranki yadad’e kiduba kiga inda ace yarinyar nan ta zuba poison kina tunanin zata amince taci abincin alhali tasan zata iya mutuwa?

dada jinjina kai tayi batare da tace komai ba.

yarima suhail rik’o hannun zarah yayi yace bari mushiga daga ciki.

kallon ummah yayi da tacika tayi fam yayi murmushi yace ummah gaskiya ya kamata kija ma d’iyarki kunne tadaina la6e, na barku lafiya.
jan zarah yayi suka shige sukabar su dada a tsaye, sultana sadiya da harara tabi yarima ji take kamar tashak’esa yamutu kowa yahuta,

dada kallon sumayya tayi tace sumayya yakamata ki iya bakinki yanzu gashinan kinja naji kunya, tana gama fad’in haka tawuce tanufi turakarta.

sultana sadiya kallon sumayya tayi da duk tasusuce tace ai ga irinta nan gashinan kinja yaro k’arami yana nema yarainani,

sumayya turo baki tayi tace ammah ai ummah bak’arya nayiba.

ummah tace ko da ace ba gaskiya bane ai bakida k’wak’warar hujja, wlh matsalata da ke bakida isashen wayau, duk yadda zakiyi abu bakisan yadda zaki fitar da kankiba.

sumayya cikin fushi tace haba ummah dame zan ji? da rashin cin nasara ko da surutun da kikeyi min?

sultana sadiya ganin d’iyartata tayi fushi yasa tafara lallashinta har saida taga ta hak’ura sannan tace tafi kiyi baccinki kicire komai a ranki ina tare da ke kinji ko d’iyata.

Toh ummana kema kije kihuta, murmushi sultana sadiya tayi sannan tatafi cike da tausayin ‘yartata.

Yarima ko da suka shiga cikin gidan yana rik’e da zarah har part d’insa umurni yaba guards d’insa yace kar subar kowa yashigo koda ace sumayya ce, gaba d’ayansu sukace to ranka yadad’e angama.

 

Back to top button