kawali Ne 15
*KAWALINE*
*Zahra Surbajo*
*Bissimillahirrahmanirrahim*
*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*
https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv
*15*
A razane siyama ta miƙe zaune jikinta na ɓari bakinta na kakkarwa tace”jamcy hiv kuma nufinki mu yanzu hiv muke da ita?”
“Kwarai ma kuwa inbaki yarda ba zaki iya zuwa asibiti”ta bata amsa tana fari da ido.
Da sauri ta sakko ta zura doguwar riga,ta ɗauki key da mayafin rigar ta fice da gudu,jamcy cool ko tuntsirewa tayi da dariya ta faɗa kan gado,
Tuƙi take hankalinta atashe ko gabanta bata gani sosai,batai auneba taji ta bugi abu,koda ta kai dubanta da sauri ta taka burki dan motar dake gabanta ta fashewa fitilun baya.
Buɗe ƙofar tayi ta fita dan taje taba mutumin haƙuri danshi yarigata ma fitowa,yana kallon ɓarnar datai masa.
“dan Allah kayi haƙuri wlh ina cikin saurin zuwa asibitine na bugeka kayi haƙuri”ta faɗi cikin harshen turanci dan zatonta balarabe ne.
Da sauri ya waigo dan yaji muryar dayakeji ta gaskence koko gizon data saba masa ne”
.”Siyama”ya furta ahankali.
“Rayhan”ta faɗi baki buɗe.
Kasa cewa komai yayi yana kallon kamannin ƴar uwarta ajikinta sosai.
Horn da motocin bayansu suke musu ne yasa kowa yakoma motarshi suka gyara parking.
Fitowa tayi da sauri ta iskeshi a motarshi,shide gaba ɗaya tausayi ma take bashi,itako tuni ta mance tashin hankalin datake ciki tace tana kamo hannunsa.
“rayhan kwana da yawa?ka ɓuya ashe rai kanga rai”ta faɗi tana murmushi.
Murmushi yayi yace”to siyama kin saci maƙudan kuɗaɗe irin haka kin jefamu cikin masifa,ba dole muyiwa juna wiyar ganiba.”
A zabure ta saki hannunsa tace bakinta na rawa”habu buƙata kai ya kama amadadina?”
“Kwarai siyama kuma yasa muka biyashi kuɗinshi,wanda last week jabeer ya biyasa sauran”
Rau rau tayi da ido hawaye na biyo fuskarta tace”kayi haƙuri don Allah wallahi dana san kuze kama ko kusa bazan aykata hakan ba.”ta faɗi tana hawaye.
“baki da damuwa siyama,to amma me kike adubai?”
“Nan na gudo da kuɗin”ta bashi amsa a sanyaye.
“good to ya nigeria ƴan uwankifa,sun san kina nan,koko ke kawai tunda duniya tasamu sekika mance da kowa?”
Kuka ta fashe dashi tace”rayhan mahaifiyata na gida ba isasshiyar lafiya,ƙanwata rayhana wacce muke ƴanbiyune nida ita,suna tare tana sona sosai kuma nasamu labarin nemana da sukeyi,amma ban iya tunawa dasuba in banda yanzu dakai maganar”taƙarasa maganar cikin kuka.
Ga mamakinta shima kukan yake yace bakinsa na harɗewa”kinyi kuskure siyama a rayuwarki me girma,wanda sanadin munanan ɗabiunki kin jawa ƙanwarki rasa budurcinta siyama baki kyautaba”ya ƙarasa maganar cikin kuka.
“rayhan kasan rayhana ne meya sameta sisterna ba irina bace ko hannu namiji be taɓa riƙe mata ba taya zata rasa budurcinta”ta faɗi agigice.
“siyama sanda buƙata yazo yasa akai mana wulaƙanci muka baza komar nemanki,anan ne Allah ya haɗani da siyama,koda naganta zatona kece tunda baki taɓa shaidamin ku tagwayene ba,ni nan da kaina naiwa rayhana fyaɗe azatona kece siyama kin cutar dani da yawa nima,tundaga lokacin natubarwa Allah nadena duk abinda nake”ya ƙarasa maganar cikin kuka.
Itama kuka take kamar zata shiɗe tace”nasan tunda wannan abu ya faru gidanmu sun rasa kwanciyar hankalinsu,rayhan ni kaina baason ransu nake runs ba”
Kwashe duk abinda yafaru yayi ya sanar da ita,ya ƙara da cewa”nide na barosu a asibitin amma ban sake komawa ba.”
“dole zani nigeria cikin satin nan,hankalina yayi gida rayhan”
”
Dade yafiye miki kam dan bariki ba komai cikinta se danasani ki tuba kan lokaci ya ƙure”ya faɗi yana duban agogon hannunsa.
“Rayhan me kakeyi anan kai?”
“Business,yanzu haka meeting zani nama yi latti”
Wayarta ta ciro ta miƙa masa tace”samin numbarka”
“No need siyama nasan gidanku a nigeria inkin dawo wataran zaki ganni amma bana buƙatarr muamala ta waya atsakanina dake”ya faɗi yana murmushi.
Ji tayi duk ta muzanta,daurewa tayi tai murmushin ƙarfin hali tace” to nagode semun haɗun”tana kaiwa nan ta buɗe motar ta fice ta koma tata.
Shiko ja yayi da mahaukacin gudu yabar gurin dan ganinta yanzu ya fama masa mikin dake cikin zuciyarshi gameda ƴar uwarta.
Saida ta dena hangoshine ta tuno balain daya tunkarota,da gudu taja motar zuiwa asibitin,koda taje akai mata test ɗin de d results is positive.
Ranar tayi kuka kamar ranta ze fita,da ƙyar ta ita dawowa gida,sede tundaga falo hankalinta ya ƙara sabon tashi,dan bataga alamun jamcy cool ba.
Da gudu ta ƙarasa cikin ɗakunan ta duba bata ba kayanta,sai kuɗi da takarda datai mata short note ta ɗora mata akan kuɗin.
“hey babe na ɗauki rabona na ƙara gaba,5m ne wannan nasan zata kaiki gida,sabida banaso kiyi ƙarƙon da karuwai suke na saida goro da sigari yasa na bakisu,
Karki manta zan dawo komai daɗewa”
Faɗuwa tayi gurin tana kuka kamar ranta ze futa,tabbas ta cuci kanta.
*Ku hanzarta siya 500 ne kawai dan vama ayi komaiba awannan labari*
COMPLETE ƊINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.
*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*
Surbajo for life.