Banana Island Hausa NovelHausa Novels

Banana Island 19

Sponsored Links

___________
Yina sakkowa falon ya taradda momynsa da bodyguard ɗin ta yasha baƙaƙen suit da baƙar tabarau a tsaye a bayanta
Itakuwa taci uwar gayu cikin wata doguwar rigar shadda fari tar an masa aikin phonix da jan xare an daddaɓesa da adon stones tun daga sama har ƙasa ,ta kafa ɗaurin gwaugwaro ,ta haɗa ma jikinta mahadin kayan jajaye,kama daga ,takalmi da jakar kayan duk jajaye ,bakinta ɗau yasha jan janbaki sai ta rataya kyakyawar Mayafi mai ruwan golden ,sai walwali takeyi cikin gwala-gwalai kunne da wuya zuwa hannaye.
Daddana wayarta take ƙirar Samsung tana lalubo numbersa tana ɗan magana a hankali ƙasa²
“Can he harbour? Yanzu fa sassafe ne anya ya tashi barci?”

Tanayi tana kallon agogon wayarta sai gashi ya fito da sauri hannunsa riƙe da rigarsa ta gaba

Washe baki tayi cikin murnar ganin yaronta “Ɗan jariri na oyoyo”ta buɗe mashi hannu yazo ya rungumeta

Zuwa yayi gabanta ya rungumeta kaɗan ya doɓana kumatunsa a saman kumatunta na dama sannan ya cire ya sake haɗe kumatunshi da kumatunta na hagu “welcome my apple”

Guards ɗin mamansan ne yace “Good morning sir” bai kallesa ba ya kama hannun maman tasa ,suka fara tafiya ,har ya cire ran zai amsashi sai kuma yaji yace “How Are You doing?”

Kafin ya bashi amsa sai ga Ifty ta kwaso da gudu tana gyara zaman rigarshi da yayi mata yawa .

“Hiii welcome momy” waigowa tayi da sauri jin Muryar mace tana gaisheta da turanci ,kallon Ifty tayi sannan ta kalli Adana ,da alamar tambaya irin “Itaɗin wacece wannan?”
Sororo ifty tayi ,da sauri Adnan ya amshe da

“Momy mah wife Iftyhal khair ” miƙa mata hannu tayi irin su gaisa ɗin nan ,tana tsatsare ta da ido taga level of awareness ɗinta (ƙarfin wayewanta)
Ɗan rausayar dakai Ifty tayi tana mommotsa hannuwanta “Ina kwana momy”

Broad smile ne ya rufe kyakyawar fuskar baturiyar uwar tashi ,cikin tsokana tace “I’ve no idea than to accept you as my in_law….kinaso in zama surukuwarki?” Dariya ifty tayi tana mamakin yanda baturiyar taji turanci ,bata iya magana ba sai jinjina mata kai da tayi cikin jin kunya

“Ki kula mun da yarona sosai and you’ll enjoy my company” sake murmushi tayi

“I’ll thnk you mah” cigaba da tafiya sukayi ta maida attention ɗin ta wajen yaronta

“Ɗan jaririna ina can duk na damu nace bari inzo in ma yarona girki nayi sati bamu hadu ba ,nasan kanacan kana fama da kayan gwangwani sai nazo na tarar da mace a gidan kuma”

“Yes mom kuma ta iya girki muje ma ki gani ” ya wani ja hannunta kamar small pikin ba wannan mai ladaftar macen a bed ba.
Ifty da take biye da su a baya lili ce ta kafa damunta da kira da sauri ta ɗaga masu hannu ,waigowa momyn tayi “Uhm jeki amsa wayarki ƴan nan nagode da kulamun da boy da kikayi”

“Nice meeting you too” tayi maza ta haye stairs da zai kaita next floor matar tayi mata kama da boss amma me yasa ta sakin mata jiki haka?

 

“Matarka kyakyawace ,gashi ta iya girki , me yasa kayi aure baka sanar damu ba?”

Shafa kai yayi yina ɗan sosa ƙeya “You know ,mom you know my condition banason a kirani da auri_saki…”

Jinjina kai tayi da sauri “Yes…Yes …to amma yanzu how far? Wannan tayi ?”

“Momy kamr zatayi ,amma ban gama gwada ta ba”

“Shikenan ,bazan katse maku amarcinku ba…kawai dai da zarar komai ya daidaita ka sanar dani da wuri don in shirya maku shagali na musamman Hajiya Turai ta fara mun gori kasan last month matar ɗansa ta samu ciki wai an gayyaceni baby shower ,cikin yakai 2months ,so inasone matarka tayi tai ciki in ma maƙiyata barazana…”

“momy You started again?”

Ɗaukar jakarta tayi “Eh mana inason in ga grandchild ɗina kuma naga ƙugun yarinyar kamar za tayi ƙwazo” miƙewa Adnan yayi ya rungumeta suka wuce ya mata rakiya har bakin ƙofa ,Jirginsu ta tashi ,sannan ya dawo inda ya bar ifty.

***
Lili cikin masifa tace “Ifty bazaki dawo school ba yau fa anyi test”

Cikin raɗa ta kanga hannunta a baki kusa da wayar tace “Ke surukata ce fa tazo gidanmu zan kiraki anjima”

Tayi maza ta kashe wayar ,ta koma ta kwanta akan gadon tana gyara zaman gashinta tayi crossing ƙafarta ɗaya kan ɗaya .

Cikin sanɗa sanɗa ya shigo ɗakin ,ɗan sansanyan ajiyar zuciya tayi ,wanda ya sashi waro ido

“Akwai matsala ne?” murmushin yaƙe tayi “Uhm uhm ina momyn?”

“Ta tafi da tsananin farinciki ,kinsan bata taɓa ganina da mace ba sai yau ,yau ta yarda da kuzarin mazakutan ɗanta duk macen da tazo kafin su haɗu na kaɗa ta”

Ɗan kishine taji ya taso ma Ifty ,shi wai baya sakaya wasu maganar ne ?

“ammm…mata nawa suka zauna anan?”

Bai tsaya wani ja da tsayi ba yace “Sha biyar”

“Ha’ennn” she sighs

Kafeta da ido yayi sam ba alamar damuwa a ransa,na wai ɓata rayuwar ƴan mata sha biyar da yayi ya karbe budurcin wasu ya maishesu ƙananun zawarawa.

“Me ya dinga faruwa ka rabu dasu”

“Na faɗa maki a baya Ni Harijine so basa iya accommodating sex style ɗina shiyasa muke rabuwa”

“me kace ma momy game dani?”

“Nace mata You Are yet to be my bride idan kin cancanta zan fada mata sai a fara shirye-shiryen aure”

Dukan gadon tayi cikin ɗan fushi “Eh Ni kowa yasan ka aureni dangina .. ƙawayena da kowa ,amma kai kaki barin kowa yasan Ni matarka ne ,anya baka da ɓoyayyen manufa a kaina?”

“Bana ƙarya…ki cinye jarabawarki mana kiga in baki zama full Mrs Adnan ba?”

“Na gaji tests Suna jirana a makaranta ,kwana nawa muna having sex atleast zaka Gane in zan iya daukar ka or not,gaskiya duk wani assignment din da kake jin zaka bani kayi gaggawar bani Inyi in naci in koma makaranta a full house wife in banciba ,ka rabu dani ka daina ƙarar mun da ƙuruciyata kana shanye mun dararen karatuna wajen making fun da gangar jikina da sunan gwaji”

“I’m sorry luv kinsan Ina sonki”

Caɓe baki tayi “Prove it”

“I’ll today ” yayi magana yina ƙoƙarin kamo mata jaw.

Ture hannunsa tayi “Zan juya school gaskiya inada test”

Kissing ɗin goshinta yayi “Ohk dont be offended” ya fice ɗakin ya barta tana saƙe saƙen zuci ,kodai yayi fushine ya haƙura dani?

Ya kwashe kusan 2hrs har tayi barci ma abunta sai gashi ya dawo hannunsa da wani jaka na kwali ya ajiye mata a gefen gado
Ya hauro gadon yina shafa mata bombom cikin tafiyar tsotsa

Firgigit ta buɗe ido ,murmushi ya mata “Zo ki sa kaya ko?”

Gyada masa kai tayi idonta ya ciko da ƙwalla “Bayan ka yaga mun rigan”

Janyo jakan yayi ya miƙa mata ,ready made ɗin kayane a ciki da takalmi da under ‘s’

“Thnk you” ta faɗi tana lumshe ido ,da kansa ya zare mata jallabiyar ,ya kamo masagalin Brazier ɗin ya kulle mata ta baya ya saka mata hannun ta saka pant ,sannan ne yayi kissing saman Nonon ta na dama

“Ina sonki a haka naked ” tsikar jikinta ne ya tashi yarrrr

Da sauri ya ɗaura mata kaya ta zura takalmi ya kamo hannunta suka fito .

Wawakeken gidan da suka fito saida taso firgita ga zafafan motoci nan ga jirage helicopters har guda uku

Gangarawa ta baya yayi da suka isa gaban wani mota mai buɗaɗɗen sama mai suffan kwale_kwale bangajejen gaske ,irin motocin nan masu cinye kwalta su kaɗai baza su iya jera hanya mota biyu a tare ba saidai wasu su biyo bayansu ,irin motocin nan da idan goslow ya hadu akan titi suke tashi sama su tsallake kan motocin su sauka a gaba ….motane da akwai komai na bukatuwar mutum kama daga Tv,fridge da komai,in mutum yaso zai buɗe saman shi ,in ya gan dama zai rufe ta dawo kamar sauran motoci ….Tunda ifty take bata taɓa ganin mota irinsa ba idan bacin ta gansa da taya huɗu da babu abinda zaisa bazatace jirgin sama bane aka fafe samanshi ba.

A gaban motar suka tsaya yina kallonta yanda jikinta ya ɗànyi sanyi ,ya kamo hannuwarta biyu “ Kin iya mota ko?” girgizaa masa kai tayi kamar wawuya.

“Aah ba na ganki a wata mercedez ba farkon Haɗuwar mu?”

“Eh amma ban iya tuka motoci Masu kamar jirgi ba”

“Iri ɗaya ne just automatic…kinji ” ya kamo hannunta ya maƙala mata key ɗin motar a hannu

“Tukwuicin kyautar budurcinki da kika bani” ware ido tayi

“And so?”

“Ki cigaba da yawonki a ciki ” kewaya motar ta dingayi bayida plate number saidai ansa Mrs D.

“Shikenan ka rabu dani nima?”
“Zamuyi magana daga baya ,in da yiwuwar daɗuwar mu zan sanar dake,ynz dai ki koma Hostel akwai kayan ki da zaki ringa sauyawa a cikin motar ”

Jikinta rawa ya kamayi a ranta tace shikenan. Yayi mun nisa ,na bada kyautar budurci na an bani motar da za’a bugeni a hanya a amsa ,motan da ko shuwagabannin kasa basu hawa ina Ni ina hawanta???

 

***
Tanaji tana gani ta yi ma motar key ta na ɗaga masa hannu yina ɗaga mata har ta fice daga nan ta cigaba da tuƙa motar da yawanci ta wani screen ake daddanawa yina directing Dinka da yatsa inda ta kamata ka taɓa.

Tun a bakin gate ɗin makarantar securities Suka rikice da mata sannu da zuwa sanda ta sauke glass sukaga itace

A bakin Hostel kuwa kasa fitowa a motar tayi saidai ta kira lili a waya kafin nan ta rizgi kukanta ma’ishi ,sannan lili na zuwa ta buɗe Boot suka fara sauke akwatunan ashe kayane kamr na lefe.

Su Sumayya na ganin wannan alibidin sukayi maza sukazo da securityn mata dake gadin Hostel ɗin su suka kama mata akwatunan zuwa daki

Duk abun nan ifty na mota ta kasa fitowa saboda jiri da take gani ga idonta sun kumbura saboda kuka ,lili shigowa motar tayi tana bata baki dukda batasan me ya dameta ba,daƙyar ta hakura ta bata sun shade ta rufe ƙwarar idonta suka fito zuwa Hostel.️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_

Back to top button