Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 2

Sponsored Links

page 2⃣

Yarima suhail saida yayi kusan minti biyar yana a kwance sannan yabud’e idonsa ahankali yamik’e yasafka daga kan gadon, alkyabbarsa yajawo yasa batare da ya kalli shahid ba saida yataka yakusan zuwa k’ofa sannan yace kajirani bari indawo, shahid cike da tsokana yace toh ranka yadad’e

yarima baice komai ba yafita yana tafiyarsa ta k’asaita, dogarawan da suke zaune k’ofar d’akinsane suka zube suna kwasar gaisuwa sannan suka tashi domin sutake masa baya, yarima batare da ya kallesuba yad’aga musu hannu.

ganin haka yasa duk suka tsaya, yawuce yacigaba da tafiyarsa shi kad’ai duk inda yagifta kwasar gaisuwa akeyi, d’aga ma mutane hannu kawai yake idan da sabo sun saba da halin yarima ahaka har yashiga turakar mai martaba da mamakinsa yaga har da iyayensu a zaune,

waje yasamu gefen maimartaba yazauna a k’asa tare da kwasar gaisuwa wajensa da wajen iyayensu nan duk suka amsa masa,

maimartaba gyaran murya yayi yace toh Alhmdllh nasan duk zakuyi mamaki akan dalilin taraku nan da nayi ammah ba abun mamakibane alkhairine muke tafe da shi, ba akan kowaba sai akan yarima suhail,

maimartaba cigaba yayi da cewa domin na riga na yanke hukunci saboda nasan zai kar6i abinda nake tafe dashi na alkhairi, bakomai bane sai akan dubawa da cancantar da naga yayi dan haka naza6a maka matar aure bakowa bace face ‘yar uwarka sumayya.

yarima gabansane yaji ya fad’i dasauri yad’ago kai yakalli maimartaba har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan haka yasunkuyar da kansa k’asa tare da runtse idonsa cike da takaicin za6in da maimartaba yayi masa, nan iyayensu sukaita murna suna tofa albarkacin bakinsu akan maganar.

shidai yarima saurarensu kawai yake,

muryar maimartaba ce yatsinkayo yana cewa toh kai uban gayyar bakace komai ba,

yarima suhail kamar ba zaiyi magana ba sai chan yace ranka yadad’e na amshi za6in da kayi min hannu bibbiyu Allah yak’ara tsawon rai.

cike da Jin dad’i maimartaba yace masha Allah, naji dad’i sosai tabbas nasan daman bazan samu matsala daga garekaba wlh ka faranta min nima Allah yakawo lokacin da zan faranta maka,

gaba d’ayansu sukace Ameen, yarima suhail nan yak’ara kwasar gaisuwa sannan yamik’e yafita

umman sumayya kamar tazuba ruwa k’asa tasha saboda murna domin ko bakomai tasan burinta ya kusan ciki ko da taje ma d’iyarta da labarin sumayya har da rawa tataka saboda murna dagudu tafita taje 6angarensu rahama tashaida mata, nan rahama tatayata murna.

 

yarima suhail yana komawa d’akinsa saman gadonsa yafad’a tare da lumshe idonsa cike da bak’in ciki domin an 6ata masa plan saboda shi baida burin yin aure a yanzu ko ma da zaiyi sumayya bata daga cikin irin tsarin matan da yake da burin aure saidai kawai zai amince ne saboda maimartaba domin baya iya jayayya da shi,

shahid ganin yarima acikin wannan mood d’in yasa bai tambayesa abinda yake damunsaba domin yasan ko da ma ya tambaya toh ba zai samu amsaba saidai idan shi yaso yafad’a masa toh dakansa zai basa labari dan haka yasharesa yacigaba da kallon ball d’insa.

 

yarima ya dad’e a kwance sannan daga baya yatashi yashige toilet.

 

bayan sallar isha’i yarima turakar iyayensa yaje inda yatadda mahaifiyarsa kishingid’e wata baiwarta tana mata tausa inda wasu biyu suke gefenta suna mata hira.

suhail yana shiga yatsaya bakin k’ofa ganinsa yasa duk suka zube suna kwasar gaisuwa sannan daga baya suka tashi suka fita suka basa wuri domin yagana da mahaifiyartasa,

sultana bilkisu tashi tayi daga kishingid’en da take nan suhail yataka yaje inda take yazauna sannan yagaishe da mahaifiyartasa cike da fara’a ta amsa masa.

 

suhail duk’ar da kansa yayi k’asa baice komai ba, ganin haka yasa mahaifiyarsa tace yarima me yake faruwane? kafad’a min damuwarka domin bakada wata uwar da tafini,

suhail d’ago fuskarsa yayi cike da damuwa yace ummi yanzu Sumayya ita zan aura?

murmurshi ummi tayi tace toh menene dan ka aureta ina ce ‘yar uwarkace kuma ta cancanta da hakan,
dan haka kakwantar da hankalinka kakoya ma zuciyarka sonta insha Allahu zakuji dad’in zaman aurenku.

cike da damuwa suhail yace ammah ummi kinsan halin Sumayya ko kad’an halinmu bai zo d’ayaba,

ummi tace injiwa yace maka haka? duk abinda kaga tanayi harda yarinta, nidai burina kakwantar da hankalinka tunda ita kaga bata tada hankalintaba kakoya ma zuciyanka sonta insha Allahu zakuji dad’in zaman aurenku.

yarima suhail yace toh ummi nagode, nabarki lafiya.

ummi tace toh my son dan Allah kar katashi hankalinka tunda kaga an amince da aikinka yanzu haka mahaifinka ya sa afara maka ginin hospital d’inka.

murmurshi yarima yayi yace nagode ummi sannan yafita daga turakar yakoma tasa.

 

Bayan kwana biyu aka tsaida maganar aurensa da sumayya nan da wata biyu masu zuwa, yarima yaso asa lokacin dayawa ammah maimartaba yace a’a, ,sumayya farin ciki tayi sosai agaban kowa take nuna murnarta,

yarima ganin dagaske ake yasa yad’an saki jikinsa har suna d’an ta6a hira da sumayya shima d’in kafin yayi magana d’aya tayi biyar, in ko kaga sunyi waya toh itace takirasa shima daga gaisuwa yake kashe wayarsa.

Bayan wata biyu akasha bikkunsu anyi shagali sosai ak’allah saida akayi events kusan guda biyar ammah dakyar aka samu yarima suhail yaje d’aya daga ciki shima saida ummi tasa baki, ammah sauran duk k’in zuwa yayi k’arshe idan yaga za’a takurasa sai yakashe wayoyinsa yace kar abari kowa yashigo sashensa,

ranar asabar aka d’aura aure, auren da dubban mutane daga nahiya dadama suka hallara,

amarya ta sha kyau har ta gaji, inda amarya tatare a part d’in yarima da aka fitar da shi a cikin gidan sarauta, k’arshen gata an nuna mata babu abinda ba a zuba masu na amfani ba.

kowa yazo sai ya yaba tsarin gidan domin babu wanda zai ce acikin gidan sarautane saboda part d’in yarima antsarasa kamar a turai inda aka fidda ma sumayya 6angarenta sai na yarima sai wani part d’in da aka fara ginawa aka aje sai kuma part na ma’aikata da bayinsu maza da mata.

 

da daddare saida shahid yayi dagaske sannan yasamu yarima suhail yayi wanka yashirya suka fito suka rakasa gidansa.

suna ta tsokanarsa shidai yayi shuru yakyalesu saboda wani irin haushi da yakeji, hatta su kansu haushinsu yakeji tunda su suka matsa masa sai yaje.
saida suka rakasa har part d’in amaryarsa sannan sukayi masa sallama suka tafi.

yarima suhail 6angarensa yabud’e da mamakinsa yaga dogarawansa zaune a k’asa suna ganinsa suka zube suna kwasar gaisuwa, yarima suhail batare da ya amsaba yace kun iya tafiya ,

k’ara kwasar gaisuwa sukayi sukace toh ranka yadad’e sannan sukace atashi lafiya sai suka tashi suka fita

bedroom d’insa yashiga komai na ciki very need da mamaki yakalli yadda aka shimfid’a masa farin bedsheet mai kyau a saman gadonsa d’auke kansa yayi yawuce yashiga toilet yawatsa ruwa , bayan ya fito yayi shirin kwanciyarsa yahaye gadonsa.

 

A 6angaren gimbiya sumayya bayan ta gama shirinta su jakkadiya suka take mata baya zuwa turakar yarima, da sallamarsu suka shiga ganin baya parlour yasa suka kwank’wasa masa bedroom,

yarima da yake kwance yabada izinin ashigo, da mamaki yake kallonsu sumayya da suka shigo, nan su jakkadiya suka zube k’asa suna kwasan gaisuwa, ita dai sumayya zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da son mijinta,

haydar bai damu da kallon da take masaba yace lafiya kukazo man d’aki?

jakadiya da take durk’ushe tace ranka yadad’e yarima mai jiran gado daman dada ce tace mukawo maka amarya,

yarima suhail shuru yayi baice komaina yamaida idonsa yalumshe.
ganin haka yasa su jakadiya sukace mun barku lafiya gimbiya da yarima Allah yaja da ranku atashi lfy.

Gimbiya sumayya tace idan kun fita sai kurufe mana k’ofan,

yarima suhail yana jinta mamakine yakamasa domin bai ta6a ganin amarya hakaba.

 

suna fita sumayya tatako ta iso bakin gadon tazauna gefen da yarima yake kwance, suhail batare da ya bud’e idonsaba yace kije kid’auro alwallah,

sumayya turo baki tayi sannan tatashi tashiga toilet d’insa tad’auro alwallah,

lokacin da tafito yarima yana shimfid’a darduma nan yajasu sallah raka’a biyu sukayi sannan yakama kanta yayi mata addu’a.

bayan ya gama yayi mata tambayoyi akan addininta baiyi mamaki ba da yaga bakomai take iya basa amsaba, wata amsarma ba daidai take basaba nan ya Ida tsurewa da lamarin sumayya ammah kuma sai yashare, mik’ewa yayi yanufi saman gadonsa yabarta nan saida yakwanta sannan yace ga nama nan idan zaki ci.

haushine yakama sumayya ganin yadda takejin labari wajen friends d’inta yadda mazajensu suka nuna musu tattalin so a daren aurensu ammah ita ba hakaba, cikin ranta tace lallai yarima halinsa sai shi.

tashi tayi itama taje saman gadon takwanta bayansa saida sukayi kusan minti goma ahaka ammah sumayya taga yarima bai da alaman nemanta dan haka tarungumesa ta baya,

yarima shareta yayi, ganin haka yasa sumayya tajuyosa tare da kwanciya saman jikinsa, yarima bud’e idanuwansa yayi da suke lumshe yawurga mata harara yace ke bakida kunya?

sumayya turo baki tayi tace yarima yau fa daren amarcinmune ammah shine kake shirin yin bacci kabarni hannu takai tana shafa jikinsa.

yarima da mamaki ya gama cikasa kasa komai yayi, jin hannunta yayi yana yawo cikin jikinsa, dasauri yarik’e hannun yace ke bakida kunya?

sumayya tace ammah ai naga ba abun kunya bane tunda munyi aure,
bakinta takai cikin nasa tana kissing d’insa cikin wani irin salo nan da nan yarima yafita hayyacinsa ya’aje sarautarsa gefe yabiye mata suka sha amarcinsu.

yayi mamaki sosai ganin yadda sumayya take zak’ewa babu alamun tsoro atare da ita,
a yadda yasameta bai kawo ma ransa komai ba gudun kar zargi yashiga tsakaninsu dan haka dayasamu nutsuwa janye jikinsa yayi yaje yayi wanka sannan yadawo yayaye bedsheet d’in yayi yakwanta tare da juya mata baya,

sumayya ma tashi tayi taje tayi wanka sannan tadawo bayansa yakwanta tare da rungumarsa ta baya,

da asuba yarima har yadawo masallaci ammah sumayya bata tashi tayi sallah ba, saida yayi dagaske sannan yasamu sumayya tatashi tayi sallah tana ta k’unk’uninta, komawa yayi yakwanta yana kallonta sallarma shaf-shaf tayita ko addu’a bata tsaya yiba tahaye gadon.

 

dasafe jakkadiya ce tatashesu nan tashigo takwashi gaisuwa sannan tad’auki bedsheet d’in tafita.

turakar dada taje, tun da dada tahangota take fara’a jakkadiya duk’ewa tayi takwashi gaisuwa sannan tace ranki yadad’e ga zanen gadon,

dada tace masha Allah bud’e mugani ko da jakkadiya tabud’e babu komai a jikinsa nan hankalin dada yatashi tace nashiga ukka ya akayi haka kar dai ace yarinyarnan ba budurwa bace.

jakkadiya duk’ar da kanta tayi tace ranki yadad’e ai ita mace budurwa ba dole sai anga jiniba ake gane budurwace wasu basu jinin budulci,

dogon numfashi dada taja tace hakane shikenan yanzu aje awankesa amaidasa ma’ajinsa ammah naso ace kowa ya shaida.

 

kowa na gidan kasa kunne yayi yaji ana gud’a ammah shuru kuma kowa tsoron tambaya yakeyi, kasancewar al’adarsuce duk amaryar da aka kowa idan budurwace da anga jinin ake ganewa nan za’a d’auki zanen gadon ayi ta yawo ana gwadawa daganan sarki zai bada shanuwa da rago ayanka ma amarya.

 

yarima suhail har yagama shirinsa ammah gimbiya sumayya tana kwance tana kwasar baccinta haushi ne yakamasa yaja tsaki yace mutum kamar kasa sai bacci, da mugunta yakai mata bugu, firgit tayi tafarka daga baccin

haushi ne yakamata ganin yarima tsaye, d’aure fuska tayi tace haba yarima ya za’ai katasheni bayan jiya kaine kahana ni bacci, gaskiya kadaina domin idan ina bacci ba’a tashina.
yarima da mamaki yake kallonta jin tace shi yahanata bacci bayan itace takawo kanta,

 

tashi tayi tad’auko alkyabbarta tasaka sannan taficce tabarmasa d’aki,
tsaki yarima yaja sannan yacigaba da abinda yake,

bayan ya gama yafito parlour yatarar da anshirya masa breakfast dogarawansa suna ganinsa suka zube suka kwashi gaisuwa sannan d’aya daga cikinsu yayi serving d’insa,

kad’an yaci sannan yatashi nan suka rufa masa baya sunacewa takawarka lafiya yarima.
tsayawa yayi batare da ya juyoba kamar ba zaiyi maganaba sai kuma yace kuje kawai zan nemeki,
su dukansa sukace angaisheka yarima umurninka muke cikawa Allah yatsare mana kai mun barka lafiya.

daganan yawuce yacigaba da tafiyarsa shi kad’ai duk inda yagifta kwasar gaisuwa ake ahaka har yazo 6angaren gimbiya ko da yashigo parlour saida ma’aikatanta sukayita kwasar gaisuwa ko inda suke bai kallaba yawuce direct bedroom d’inta,

lokacin gimbiya sumayya tana zaune bayinta suna shiryata, bud’e k’ofar da akayine yasa duk suka maida hankalinsu domin suga mai shigowa ganin yarimane yasa suka zube gaba d’ayansu suka kwashi gaisuwa sannan suka mik’e zasu fita

gimbiya sumayya ce tace ina zakuje batare da kun gama shiryaniba,
yarima kallonta yake cike da mamaki sannan yanuna musu k’ofa dasauri dukansu suka fita har suna tuntu6e.

takowa yayi cikin takunsa na k’asaita ya iso bakin gadon, gimbiya sumayya tace haba yarima ya zaka korar minsu alhali basu gama shiryaniba,

zama yarima yayi kusa da ita batare da ya kalletaba yace ke ba zaki iya shiryawaba har sai sun shiryaki?
sumayya ta6e baki tayi tace ammah ai tun ina gaban iyayena su suke min kwalliya, banza yarima yayi yakyaleta dan haka taci gaba da shirinta.
banza yarima yayi yakyaleta.

bayan ta gama kiran jakkadiya tayi tace akawo mata breakfast d’inta a nan, cikin minti biyar ancika mata gabanta da abinci da kayan marmari iri-iri

nan tazauna zata ci kallon yarima tayi tace kaifa ba zakaciba,

yarima batare da ya kalletaba yace no kici kiyi sauri kigama muje mugaishe da su maimartaba,

gimbiya sumayya tace tun yanzu?
yarima bai tanka mataba,
ganin haka yasa tacigaba da breakfast d’inta domin tasan halin mutumin nata magana tsada take masa……

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_
?

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

 

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_*Sak’on gaisuwata agareku My Haleema H.A.S nd mummy Zill*_

 

_Wannan page d’in nakune nabaku shi a kyauta my fan’s_

 

Back to top button