Yarima Suhail 5
page 5⃣
yarima duka wayoyinsa yakashe dan kar adamesa da kira dan yasan confirm ne sai maimartaba ya nemesa,
bayan sallar isha’i suka bar gidan gonar, shahid ne yakar6i key d’in motar yayi driving d’insu domin cewa yayi ba zai yarda yarima yatuk’asuba gudun kar yak’ara irin driving d’in da yayi d’azun shidai yarima baice komai ba yamik’a masa key d’in.
ko da suka isa yarima cema shahid yayi yazo sufara shiga fada sugaishe da sarki, shahid bai musaba yabi bayansa a jere suka shiga fad’a nan duk mutane suka zube suna kwasar gaisuwa ahaka har suka iso gaban sarki,
dasauri wani dogari yad’auko wani had’ad’en carpet yashimfid’a musu nan sauran dogarawa suka zo suka baza manyan rigunansu suka kare su yarima daga ganin mutane suna cewa azauna lafiya yarima, saida suka tabbatar da sun zauna sannan suka matsa nan su yarima suka gaishe da sarki, sarki fuskarsa d’auke da fara’a ya amsa nan fadawa suka d’auka angaisheku yarima mai jiran gado sarki ya amsa gaisuwarku Allah yaja da ranka.
sannan yarima suka gaishe da su daddy da abban sumayya, nan ma fadawa suka d’auka da angaisheku kuma,
maimartaba kallon yarima yayi da yake durk’ushe k’asa yace yarima tun d’azun nake aikawa akira min kai ammah sai adawo acemin tunda kafita baka dawoba.
yarima suhail murmushi kawai yayi.
ganin bashida niyar yin magana yasa shahid cewa ranka yadad’e munje gidan gona ne tun d’azun muna chan.
maimartaba murmushi yayi irin nasu na sarakai sannan yace Alhmdllh gaskiya ina jin dad’in hakan kuma duk ayyukan alkhairi da kukeyi a gari yana dawo min a kunnena tabbas nasan ko bayan raina nabar magajin da zai gadeni Wanda zai so kuma yatausaya ma jama’arsa tabbas kaine yafi cancanta da kakasance *Sarkin sarakai*
yarima dasauri yad’ago kai yakalli mai martaba har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa,
gaba d’aya fadawa suka d’auka angaishe da yarima mai jiran gado, angaishe da kwarzon namiji, angaishe da namijin zaki sarki ya gaisheka.
yarima da shahid k’ara gaishe da sarki sukayi sannan suka mik’e dasauri sauran jama’a da fadawa suma suka mik’e nan suka shiga yi ma yarima kirari har saida yafita daga fadar sannan suka zauna.
shahid saida yaraka yarima har wajen turakarsa sannan yayi masa sallama yatafi gida.
yarima yana shigowa dasauri dogarawa suka zube suna kwasar gaisuwa sannan suka mik’e suka take masa baya suna masa kira, takawarka lafiya yarima, Takawarka lafiya babban dodo mai rikita ‘yan maza, takawarka lafiya sarkin sarakai, nan bayi da ma’aikata sukaita fitowa suna gaishesa tun yana amsawa har yagaji yakoma d’aga musu hannu ahaka har ya isa part d’insa dasauri wani dogari yabud’e masa d’akin,nan suka d’auka ashiga lafiya yarima, batare da yarima ya juyoba yad’aga musu hannu nan duk suka duk’a sukace munbarka lafiya yarima akwana lafiya, nan suka tashi duk suka watse, sai guards d’insa kawai suka rage yarima yana shiga bedroom d’insa kawai yawuce.
wanka yayi sannan yakwanta.
tun daga ranar suka rage had’uwa da gimbiya sumayya saidai idan tana son wani abu wajensa sannan take zuwa d’akinsa, yarima bai damuwa da rashin zuwanta hidimar gabansa kawai yake sai inyaji yana buk’atarta sannan yake zuwa d’akinta idan ma yaje sai yayi da gaske yake samu tana amince masa cikin 6acin rai suke rabuwa.
A sibitinsa da aka gina masa yana bada gudunmawa sosai baya bari ana wulak’anta masa patients kamar yarda baya bari awulak’anta masa staffs, hatta talakka idan yazo asibitin ana kar6arsa sannan kud’in magani rabi ake kar6a ana yafe musu rabi nan da nan asibitin yayi suna a garin da wajen garin.
Gimbiya sumayya business d’insu suke kud’i suna shigo mata sosai ammah har lokacin bataje tagano boutique d’in nasuba da yake a garin Abuja inda zinat tazuba ma’aikatan da suke kular musu da kayan kullum tsegumi take ma gimbiya akan rashin zuwanta tagano boutique d’in,
yau ma dai kiran gimbiya tayi a waya, gimbiya sumayya da take kishingid’e bayinta zagaye da ita tuface ake bata a baki tana ci ahankali inda gefenta baiwace take karanta mata labarai anutse, wayarta da tahau rurine yasa kowa yanutsu wadda take rik’e da wayar tatsugunna tace ranki yadad’e gashi ana kira,
gimbiya sumayya yamutsa fuska tayi tace wake kirana?
jikin haule yana kyarma tace bestie naga ansa, harararta gimbiya tayi tace ashe ke kin d’anyi karatu ba laifi ai na d’auka jahilace irinsu indo, indo da take tsaye tana ma gimbiya fiffita murmushi kawai tayi batace komai ba,
gimbiya sumayya d’aukar wayar tayi tare da cewa my zinat dafatan kina lfy?
daga chan 6angaren zinat ta amsa da lfy lou kema dafatan haka sarauniya mai jiran gado
‘yar dariya sumayya tayi tare da cewa ke ni har na hangoni ko nazama sarauniyar, Allah dai yakaimu lokacin
zinat tace am wai yaushe zakizo yau fa kusan 5 months ammah shuru bakizo kikaga yadda komai yake tafiya ba? saidai kawai kiji alert d’in kud’i.
gimbiya k’ara gyara kishingid’ar tayi tare da cewa zinat wlh nima inso inzo kawai ina tsoron wulak’ancin yarima.
tsaki zinat taja tace ke wlh kina bani mamaki sai kace ba big gurl ba? yanzu saboda Allah duk class d’inki ammah kizauna wai sai yadda miji yayi dake, ke ya dai kamata kizo munfayi customers sosai kuma akwai kayan da nakeso ink’ara d’auko mana saboda haka kifitar da rana kizo,
gimbiya sumayya dogon numfashi taja sannan tace toh shikenan baby kar kidamu zanzo nima ai daman nayi missing d’inki,
dariya zinat tayi tace koma dai mekenan saidai kinzo, kinga sai kimin ko 2 weeks ne,
gimbiya sumayya tace ina ma dai laifi kice 1 week, shima sai munyi daga da yarima sannan zan samu yayarda, koma dai mekenan zamuyi waya.
nan sukayi bankwana, gimbiya sumayya tunani tashiga yi yarda zata samu tatunkari yarima da maganar batare da yak’i amincewaba.
chan kuma sai taja tsaki cikin ranta tace dolema ya amince dan babu yadda za’ayi yak’unsheni cikin gida shi yana yawon gararanbarsa a gari. bari ma yadawo.
gimbiya sumayya kallon haule tayi tace yau inaso kisamin ido ga yarima idan ya shigo kiyi min magana?
haule cike da ladabi tace tau ranki yadad’e umurninki shine abun cikawata.
wajen k’arfe tara gimbiya tagama shirinta cikin kayan baccinta sannan tad’aura alkyabba daga sama tafeshe jikinta da turare mai k’amshi sannan tafito dasauri ma’aikata da bayi suka hau gaisheta tare da yi mata kirari,
gimbiya sumayya sai yatsina take tana ji suna k’ara mata girman kai, baiwarta haule kawai tace tazo tarakata nan haule cikin sauri tataso tatake mata baya har sukaje 6angaren yarima nan ma dogarawa suka shiga gaisheta sannan suka bud’e mata k’ofa, kallon haule tayi fuskarta ba yabo tace zaki iya tafiya.
haule durk’usawa tayi k’asa tace toh ranki yadad’e atashi lafiya,
sumayya tana shiga ganin yarima baya parlour yasa dan haka tashiga bedroom tana bud’ewa yarima da yake tsaye yana sanya kaya da alama daga wanka yafito yakallota, kallo d’aya yayi mata yad’auke kai gimbiya sumayya cire alkyabtarta tayi ta aje gefe tare da takawa inda yarima yake tsaye tace my sweetheart ko intaimaka maka?
yarima bud’ar bakinsa sai cewa yayi a yau kuma? kedai kawai kifad’amin me kikeso?
gimbiya tace haba yarima daga nace zan taimaka maka shine harda tambayar me nakeso?
kenan banda ikon yi maka komai sai idan ina buk’atar wani abu.
yarima a wulak’ance yace ai hakan halinki yake, kema kuma kinsan hakan kike, yana gama fad’in haka yazagayeta yawuce yaje yahaye gadonsa yakwanta.
gimbiya sumayya tsaye tayi tana mamakin halin yarima cikin ranta tace nasan ta yadda zan 6ullo maka, itama takawa tayi tanufi gadon tahau
takwanta tare da rungume yarima tace sweetheart ni bana buk’atar komai sai kai mijina.
yarima murmushi yayi yace ashe anyi miki karatun ta nutsu gaskiya natayaki murna idan har dagaske kin gyaru.
cike da k’ulewa gimbiya tace haba yarima wai meyasa kakeson kaga ka cimun fuska wani fa lokacin har a gaban bayina da kuyangina kake yada min magana.
yarima shuru yayi baice mata komai ba, ganin haka yasa tad’ago kanta takallesa sai ganin idanuwansa a lumshe, shafa sajen fuskarsa tayi tare da yin murmushi tace my dear ba dai bacci zakayi ba,
yarima batare da ya bud’e idonsaba yace ya dai?
gimbiya sumayya bakinta takai cikin nasa nan da nan yarima yacafke suka shiga faranta ma junansu.
saida yarima yadirjeta son ransa sannan yabarka atare sukayi wanka sannan suka kwanta tana rungume a jikinsa, yarima yana mamakin sauyawar da sumayya tayi ahaka bacci yayi awon gaba da su.
da asuba ko da sukayi sallah komawa sukayi bacci sai wajen k’arfe tara sannan suka farka a tare sukayi wanka sukayi breakfast bayan sun gama gimbiya jerawa sukayi da yarima suna tafiya inda dogarawa da kuyangi suka take musu baya har saida yarima yazo wajen motar da zai je wajen aiki da ita sannan sukayi sallama dasauri wani bawa yabud’e masa motar yashiga, saida sukaga tafiyarsa sannan gimbiya tajuya suka koma gida, cikin ranta tana ayyana yadda zata biyo ma yarima ya amince batare da tashin hankali ba.
ko da yarima yadawo wajen k’arfe biyu ita taje tataresa cikin shigarta ta alfarma tafito a sarauniyarta ta asali sannan tarakasa har d’akinsa shidai yarima kansa yad’aure sosai ganin wata irin kulawa da yake samu a wajen gimbiya wadda tun satin aurensu rabon da yasameta,
ita tataimaka masa yayi wanka yashirya duk k’uiyarta ajeta tayi gefe tatattali mijinta
bayan kwana biyu yarima ne kwance da gimbiya manne da juna suna ta wasanninsu, gimbiya ganin yarima yana shirin nemanta yasa tadakatar dashi, yarima kallonta yake da mamaki idanuwansa duk sun canza kala, yarima dakyar yabud’e baki yace ya dai?
Gimbiya turo baki tayi cikin shagwa6a tace sweetheart Please wani taimako nakeso kayi min, yarima zuba mata ido yayi baice komai.
ganin haka yasa gimbiya sumayya yin murmushi tana wasa da gashin da yake kwance a k’irjinsa tace dan Allah so nake kabarni inje Abuja.
yarima da mamaki yake kallonta yace me zakiyi kuma a abuja? Sumayya d’ago kai tayi tana kallonsa tace so nake inje inga boutique d’in da muka bud’e kaga tunda aka bud’e banjeba kuma badad’i ace har tsawon wannan lokacin ban lek’aba,
yarima d’auke kai yayi tare da cewa ba zakije ba, gimbiya a firgice takallesa tace yarima meyasa? dan Allah kar kahana ni.
yarima suhail wani mugun kallo yawurga mata tare da cewa idan ke bakida hankali to ni ba mahaukaci bane, babu yadda za’ayi insaki matata tayi irin wannan tafiyar mai nisa kuma ya kike tunani mutane zasu d’aukeni? kawai akan kasuwanci?
gimbiya sumayya tashi tayi daga jikinsa cikin fushi tace wlh ban ta6a sanin kai butulu bane sai yau duk hallacin da nayi maka kwana biyu ammah baka ganiba? toh bari kaji akan *KUSUWANCI NA* zan iya yin komai dan haka muzuba mugani kuma tafiya tana nan daram ko da baka. ….
wani gigitaccen mari da yarima yad’auketa dashine yasa takasa k’arasa maganar, kallonsa take da mamaki saida ‘yan cikinta sukaso sukad’a ganin yadda yake huci,
yarima dakyar ya iya bud’e baki yace ke har kin isa kidinga min shouting haka? ko dan kinga ina lalka6aki? toh bari kiji albarkacin iyayena kawai kikeci kuma babu inda zakije sannan daga yanzu kidinga ladafta maganarki idan kina a gaban *yarima suhail*, yana gama fad’in haka yad’auko rigarsa yasaka yaficce daga d’akin fuskarsa babu alamun annuri a tattare da shi ahaka yawuce yatafi part d’insa.
gimbiya tana ganin ya fita tafad’a saman gadon tacigaba da rizgar kuka takaicinta marin da yarima yayi mata tun da take iyayenta basu ta6a sa hannu suka daketaba sai yau wani yadaketa kuma wai miji.
tashi tayi tajanyo alkyabtarta tasaka tafito fuuuu dasauri kuyanginta suka mik’e zasu take mata baya cikin fushi gimbiya tadaka musu tsawa tace duk wacce takuskura tabiyoni abakin aikinta.
dasauri duk suka koma suka zauna domin sunsan abinda gimbiya tafad’a zata iya zartar da shi.
cikin sauri take tafiya kamar ta6a66a har ta isa 6angaren ummanta duk mutanen da suke gaisheta bata luraba saboda hankalinta baya a tare da ita tana cikin matsanancin bak’in ciki,
ummah da take zaune bayinta suna ta mata hidima saidai ganin gimbiya tayi kamar an jefota, a firgice ummah tatashi daga kishingid’en da take tace sumayya lafiya?
sumayya dasauri tazo tafad’a jikin ummah tare da fashewa da wani sabon kukan nan hankalin ummah ya ida tashi, cewa take sumayya kifad’a min abinda yake damunki mana,
ummah cikin 6acin rai takori ma’aitanta duk suka fita suka bar d’akin, sannan tad’ago kan sumayya cike da damuwa tace shalele wa yata6a min ke?
gimbiya share hawayen fuskarta tayi nan takwashe dukkan abinda yafaru tsakaninta da yarima tafad’a ma sultana sadiya
sultana sadiya ranta ya 6aci sosai musamman ma da taji wai ya mari sumayya, cikin 6acin rai taharzuk’a tamik’e dasauri sumayya tarik”ota tace ummah ina zakije? ummah tace sakarni inje inci mutuncinsa sai yafad’amin dalilin da yasa yamareki ko mu da muka haifeki hannunmu bai ta6a kaiwa ga fuskarkiba da sunan mari sai wani banza zai mareki.
sumayya tace ummana kibarsa kawai ai sai na rama marin da yayi min dan ba zai ta6a ta6aniba azauna lfy, nidai yanzu kisamo min mafita saboda ina da burin tafiyar nan cikin satin nan.
ummah komawa tayi tazauna tare da cewa ai dole ma ne kitafi dan haka taso muje wajen dada nasan yadda zan 6ullo ma lamarin
cike da jin dad’i sumayya tace nagode ummana wlh saisa nake k’ara sonki, murmushi sultana sadiya tayi tace ai dole inso duk abinda kikeso shalelena. nan suka tashi suka d’unguma turakar su dada. ………
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja’art✍_
_*YARIMA SUHAIL*_
_*Written By~Sis Nerja’art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔