Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 14

Sponsored Links

kraam~ By Khaleesat Haiydar 14…… Ammi na isa gidan Yayarta ta xube gabanta tana kuka, yayar tata da ake kira da yakumbo duk ta rikice ganin Ikram ma kukan take, a rude ta shiga tambayarsu lfya, ganin Ammi taki cewa komai sae kukan da take yasa yakumbo ta jawo Ikram ita ma tana hawayen don duk hankalinta ya tashi tace “Rabi’a ki gaya min me ya faru, wani abu ya sami babanki ne” Ikram ta share hawayenta ta girgixa mata kai tace “wae don wata yarinya ta nemi tsokanata na kwabar mata da wara shine Ammi ke ta dukana tana dukana ta kawo ni nn” Ammi ta fixgota a fusace, yakumbo ta kwace ta cikin fada ta fara magana “kan wnn dalilin xaki xo gidana ki daga min hnkli Aisha, hka kawae xata barar da wara ba ayi mata komai ba” Ikram tace “yakumbo wllh ita ta fara tsokanata” Yakumbo ta rungumota tace “yi hkuri Rabi kyale mamarki kinji kawae kiyi xamanki wajena, taje ta tattaro min kayanki ta kawo min nn, kin isheta ne” ikram tace “Yakumbo kuma ban ci abinci ba fa yunwa nke ji” yakumbo ta mike ta xuba mata shinkafa da mai da yajin da tayi Ikram ta dauka ta fita tsakar gida ta ci kayanta ganin ynda Ammi ke ta harararta, yakumbo ma ta mike xata fita Ammi ta ce “wajen ki na xo yakumbo” ta juya tana hararar Ammi tace “to me xan maki duk kin bi kin takura yarinya ki bani ni da Allah bae ba ba kuma kin ki, ae wllh Rabi ta dawo hannuna knn, ki koma gida ki gaya ma Amadun, tunda kun kasa rike guda dayan da Allah ya baku, to ni xan rike maku” cikin kuka Ammi ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya faru, yakumbo ta rude ta shiga salati tana cewa “yau mun shiga uku a ina suka san Ikram din, daga ina suka ce maki suke, wayyo Allahnmu kila ma yan yankan kai ne” yakumbo ta shiga kwada ma Ikram kira da karfi amma shiru, hkn yasa ta fito tsakar gidan da sauri amma sae taga kwanon abincin kadae ne xaune tsakar gidan bayan ta sude shi ta kara gaba, da gudu Yakumbo ta dawo daki a rude tace “Aisha ban ganta tsakar gidan ba” Ammi ta mike da sauri tayi waje ita ma tana salati. Ikram kam tana gama cin abinci ta kama hanyar gida ko xata ga Mami, kila ma Ayaba ta kawo mata Ammi ta dauketa ta kawo ta nn, bbu kowa gidan ta fashe da kuka tana bubbuga kafa, fitowa tayi daga gidan xata koma gidan yakumbo ta tuna yaron Anty dake bata chocolate, tayi gun da suke haduwa da sauri ko xata gansa, ta ko gansa xaune shi kadae yana danna wayarsa, ya mike da sauri ganinta yace “Ikram” ta mika masa hannu tace “xo ka ban wnn abun me ddi” ya kamo hannunta yace “daga ina kike Ikram” tace “gidan yakumbo mana” ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace “Ikram Ammin ki baxata bari ki koma gidanmu ba” Ikram ta gyada masa kai ta marairaice tace “kuma ni ina son in je gidanku” ya dan yi shiru snn yace “babanki ma baxae bari ba ko” ikram tace “eh nasan Ammi xata ce masa baxan je ba, amma kasan me” ya girgixa mata kai, tace “ku je gidan kawu na lado ku gaya masa nasan xae bari in bi ku gidan Anty, kasan Ammi tace min Abba najin mgnrsa ssae” da sauri Aliyu yace “ina ne gidan kawun” tace “can da nisa mana” ya ce “to muje ki nuna min mana kanwata” tace “to” yana rike da hannunta tana ta nuna masa hanya har suka isa anguwar, daga nisa ta nuna masa gidan wae bata son shatu ta ganta. Gidan yakumbo ta kae sa daga nn, suna isa tace “kaga nn gidan yakumbo ne, matar tana so na, ni ma kuma ina sonta daxu da Ammina take so ta dokeni a dakinta tayi ma ammina ihu, sae Ammina ta kyaleni, kuma ta girme Ammina, kuma mijinta ya mutu, kuma bata da yara, kuma ita kadae ke xaune a gidan nn, kuma tsohuwace” murmushi kawae yyi yana kallon karamin bakinta mai bayanin, tace “to bani abun nn in wuce” ya durkusa gabanta ya dafa kafadunta a hankali yana kallon cikin idonta xae yi magana sae kuma ya fasa yyi mata murmushi, ita ma murmushin tayi masa hade da washe hakora ya daura yatsansa kan dimple dinta, ita ma ta daura kan nasa, ya daura kan lip dinta ita ma tayi hkn, mikewa tsaye yyi yana dariya yace “bye na tafi, gobe xan kai Mami wajen kawun naki,” da sauri tace “to baka ban sweet din nn ba ae” bae yi musu ba ya ciro biyu daga aljihunsa ya mika mata, ta karbe tayi cikin gida a guje, ya dde nn tsaye snn yyi murmushi [truncated by WhatsApp]

Back to top button