Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 24

Sponsored Links

 

 

Part din Abba bakin suka shiga suka zauna suna jiran fitowarshi babban part ne dan yafi duka part din gidan girma gashi yasha kayan dukiya kam kamar zasuyi magana.
Zaune suke a babban falon kasa sunata hira yaran anty amina aslam da islam se wasan su sukeyi mikewa ummi tayi tahaura upstairs direct dakinta tawuce taje toilet dan tahadawa abba ruwan wanka jin motsi tayi a dakin nata fitowa tayi taga Abba atsaye atsakiyar dakin fuskanshi dauke da murmushin so da kauna yabude mata hannu ahankali taje tayi hugging dinsa dagowa tayi tana kallon fuskansa cike da kaunar mijin nata magana Abba yafara yana fadin” i really miss you my zaujat ” ” I missed you too” ummi tafadi haka fuskanta yana canzawa ganin kamar ranta adan bace ne yasa Abba tambayarta ” meyafaru kuma naga ranki abaci ko bakiyi farin ciki da dawowata bane!?” Jan hannunsa tayi suka zauna abakin gado tana fuskantar shi tace ” bahaka bane nafi kowa murna da dawuwarka saboda nayi missing dinka sosai, kawai de abinda kakeyine banajin dadinsa domin baka kyautawa banason ran tashin al’qiyama mijina yatashi da shanyeyen barin jiki dukda nasan iya kokarinka kana kwatanta adalci a tsakanina da mommynsu amma dan Allah kadinga adalci kaga itace uwargidanka uwar manyan yayanka abangarenta yakamata kasauka ba anan ba kokuma kasauka apart dinka nasan yanzu dole zataji badadi kuma tana da gaskiya ko nice zanji badadin hakan mijina kayi hakuri in akwai abinda nafada daya bata maka rai bazan iya zuwa ido inga kana irin haka a tsakaninmu ba ” tagama maganarta kanta akasa ( gareku mata masu kishiyoyi karkiyi murna dan wai mijinku yafi fifitaki akan yar uwarki kita farin ciki, zakiga wani namijin Yana fifita daya akan daya Kuma baya iya boyewa wannan rashin Adalci ne zakiga in ranar Kwanan dayan ce zeshiga dakin yar uwarta yaki fitowa dawuri kokuma yaje ya yini agunta , kekuma a maimakon kimishi magana akan hakan badacewa bane sekiyita farin ciki harma yazama kina mata gori tom karkiyi tunanin wai shikadai ne da hakkin rashin Adalci kema harda nake komishon din kema kin bada naki gudunmawan Dan dabaki sakar mishi fuska ba babu yanda haka zefaru kokuma kimishi nasiha akan hakan be kyautu ba zakiga jikinshi yayi sanyi nan gaba dole zeji nauyin sakewa, Amma maimakon hakan se mata suka maidashi ado suna tutiya da miji nasonsu yana banzatar da kishiyarta bazakiyi tunanin namijine fah abinda yawa yar uwata nima inbanyi wasa ba wata rana dole zejuyo kaina saboda zaman aure zamane nahar abada ba kullum bane ake cikin jindadi ba zamane na yar hakuri , tom tunasar da mazajenku akan hakan zesa arage wani rashin Adalcin Allah yakyauta). Tunda ummi tafara magana Abba kebinta da ido wutan sonta nakara ruruwa acikin zuciyarshi tabbas yayi dacen mata aysha macece da har kullum yake alfahari da ita macen kwarai datasan yakamata wani irin tausayinta ne yakamashi aranshi yana fadin “baiwar Allah datasan wacece hafsat dabata tsaya tana cewa bana mata adalci ba datasan irin mugun nufinta akansu da setaji ta tsaneta amma banga laifinki ba dan nasan bakisan ba aure a tsakanina da itaba ” ajiyar zuciya yayi yariko hannunta yace ” bakomai my wife in sha Allah zangyara karki damu ” murmushi tayi tace” yauwwa shukhuran ya Habibi” mikewa yayi yashiga toilet din yasamu yayi wanka ta fito masa da kayan sawansa sannan ta koma kasa. Suna zaune afalon yafito suka je dinning area akayi saving din kowa abinci, kallon Abu tayi tace ” ankaiwa bakin dake part din abbansu abinci !? Eh hajiya nakai musu” okay ankaiwa son nashi ne?” girgiza Kai Abu tayi tace ” ah ah yanzu aka gama shirya mishi nashi zaakai mai” gyada kai ummi tayi kafin suka faracin abinci shuru sukayi bakajin karan komai se cokula bayan sun kammala ne Abba yamike Yana fadin ” bari inleka jamaata ” to sukace mai.

 

” Sir wannan sune list din kayan da muka fitar awannan shekaran Kuma alhamdulillah duk sun kare komai yatafi smoothly, a motoci kwaya Dari shida na company duka sun kare saura guda gomane suka rage range Rovers , sekuma company shinkafa nanma abuhu million biyar da aka fitar duk sun kare,haka company sauran kayan abincin Suma komai yatafi yanda yakamata kuma ansayar da komai akan farashin daka fada, sekuma azaad unlimited company (inda ake sarrafa kowani irin nau in kayan sawa) nanma duk kayan ciki sun kare anzuba wasu, se manyan super market dinka dakuma manyan shagunanka na furniture Suma haka komai na wannan shekaran yakare anzuba wasu , se gidajen da akeyin renting ( gidan haya) Suma kowa yabada payment dinsa, masu napep masu taxi kowa yakawo nashi balance din, se gidan gona Shima anzuba wasu kayan aciki , shopping mall dinkama haka, bayan hakama Muna bukatar sabbin ma aikata akalla guda dari ko sama da hakan wannan shine list din wannan shekaran sir” Faisal yagama magana yana juyawa azaad dake kwance akan lallausan gadonshi laptop din dan yagani , mikewa yayi yace ” good job faisal karka damu base kanuna min ba kamanta komai inde abinda yashafi system dinka dana duk sauran ma aikatana ninake juyashi bane, you did a great job, yanzu abu nagaba shine kafadawa marketing manager yakaro sabbin ma aikata sannan kuma kaje kasamu accounter kowani employee dina akara masa salary akalla 50k each employee, sannan kayi arranging din ziyaran daza mukai gidajen marayu in this week” yana magana yana bata fuska kamar wanda akawa dole seyayi maganar, faisal kam ko ajikinshi inda sabo yasaba da halin ogan nashi shekara 10 bawasa ba , cigaba da magana faisal yayi ” sir kanada meeting jibi misalin karfe biyu da kautal Jude company, sekuma jiri brothers and son’s sunyi request din appointment dakai zaayi accepting dinsu neko Kuma!?” dan daga kai sama yayi kamar wani me tunani can kuma yace “okay I will think about it” okay sir suna cikin haka me aiki takawo musu abincin ta ajiye a dinning area na falonshi kafin tadan daga murya tace” sir your food is ready” tana gama fadin haka ta tafi ko motsawa azaad beyiba ,tashi Faisal yayi yaje dinning din yaga food flask sunkai takwas ajere bude nafarkon yayi yaga fried rice taji nama zuku_zuku plate yadauka yayi serving kanshi yazauna yafaracin abinci yaci yakoshi yasha drinks dinshi tukun yakoma gun azaad yace ” sir cikina yadauka nizan wuce se anjuma” yadauki system dinshi dan dama beyi tsammanin amsa ba yatafi.

Safa da marwa mommy takeyi afalonta fuskanta ahade kamar anmata sako da mutuwa ita kadai se sambatu takeyi ” ni Muhammad zeyi kokarin tozartawa wlh be isaba karyanshi yasha karya itakuma aysha senayi maganinta munafukar banza da wofi mtsssw” gaba Daya yaranta tagumi sukayi suka zuba mata ido ganin yanda take maganganu kamar wacce ta zauce anty shayida ce tace ” please calm down mommy meyasa kike yawan tayar da hankalinki akan abinda betaka kara yakarya ba wannan aibawani abu bane nide nasan wallahi ummi nasonki tsakani da Allah ” wani irin uwar harara mommy ta wurga mata ” nide kam banji dadin rayuwata ba Allah yaban yara marasa kishin uwarsu Yan iska marasa zuciya,barinma ke tanuna anty shayida da yatsa nayi dana sanin haihuwarki saboda bazeyu ace nahaifi yarda bata kaunata ba banza laa’nanniya shisa kika kasa samun ci gaba arayuwa keda yara Kuma sede kiga ana haihuwa ” ( iyaye yakamata musan irin kalman da zamu dinga furtawa yayanmu domin bakin uwa nada matukar kaifi akan danta walau adduah’ta walau mumunar Baki, Koda yakasance dah namaka laifi duk muninsa karkiwa danki baki domin rayuwarsa ne zetabbare Kuma daga karshe kema kizo kina danasani to miye riban haka, yaro tun Yana dan karami dashi Zaki tankwarashi takan farki mekyau yanda kinsan nan gaba inya girma baza kisha wahala ba, in laifi yayi kimishi fada sosai sannan kijashi ajiki kimai fada yanda nan gaba bazeyi shaawar Kara aikata hakan ba , sannan duka wasu iyayen suna ganin idan yaro yayi laifi akamashi amishi dan bazan duka shine dede to nanma bako wani laifi bane ake bugun yaro, saboda idan jikin yaro yasaba da duka nan gaba koya ganki da bulala wallahi baze gudu ba kokuma kiga alamar tsoro akan fuskanshi ba saboda yariga daya saba da dukan ahakane zakiga yaro yataso marajin magana da rashin ji,.)
Jin irin mugayen kalaman da mommy take binta dasune yasa kukanta da take dannewa yafito Fili, tashi tayi tahaura upstairs dakinsu dasuke ciki time din yanmatancin su ta cigaba da kukanta bin bayanta anty Zainab tayi tana rarrashinta “kiyi hakuri shayida komai lokacine wata rana se lbr yakamata yanzu inda sabo kisaba da halin mommy Kuma kidinga sata a adduah Allah yasa tagane gaskiya ” cikin muryan kuka anty shayida tace” anty Zainab irin abinda mommy take mana kamar ba ita tahaifemu ba narasa dalilin dayasa bata kaunar mu tadauki Karan tsana tadaura mana barinma ni tafi tsanata shisa yanzu inbadan Abba da ummi ba wlh se infi watan ni banzo gidan nan ba, anty Zainab ninasan bakin cikine ze kasheni acikin Wanda sukemin gorin haihuwa ace harda uwata wacce yakamata itace zatana rarrashina amma harda baki take
min wai bazan taba haihuwa ba innalillahi wainna ilaijiraji unnn ya Allah kakawomin mafita ” tagama magana tana Kara rushewa da marayan kuka rungumeta anty Zainab tayi tana bubbuga bayanta “is okay kinji kokin manta haihuwa na Allah ne shiyake bayarwa alokacin da yagadama in lokacin dazaki samu ciki yayi babu wani mahalukin daze hanaki samu kuma kici gaba da kai kukanki wajan Allah , kidena sawa kanki damuwa kokin manta munada ummi da abba ne ga kannanmu duk suna sonmu ga Amina ma ” haka taci gaba da kwantar mata da hankali hartasamu tayi shuru.

 

 

Back to top button