Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 3

Sponsored Links

page 3⃣

 

bayan ta gama d’auko alkyabbarta tayi tasaka sannan suka jera ita da yarima suka fito, a k’asa suke tafiya a jere, kuyangin gimbiya suka take musu baya ahaka har suka isa fada nan mutane suka dinga kwasar gaisuwa, d’aga musu hannu kawai yarima yakeyi har suka isa gaban maimartaba dasauri dogarawa sukazo suka kare su yarima daga ganin mutane suna cewa Allah yataimaki yarima da gimbiya azauna lafiya, har saida suka tabbatar da yarima da gimbiya sun zauna sannan suka matsa nan su yarima suka kwashi gaisuwa wajen sarki nan fadawa suka d’auka, sarki ya amsa muku yarima da gimbiya, sarki yana godia yarima mai jiran gado ku ma angaisheku.

 

sannan yarima yatashi yaje kujerar da take kusa da sarki yazauna, ita dai gimbiya tana tsugunne a k’asa sai yatsina take tana kallon mutane a wulak’ance.

maimartaba ne yad’auko wata alkyabba maikyau da tsada yamik’a ma gimbiya sumayya hannu biyu gimbiya tasa takar6a tare da yin godia sannan tamik’a ma jakkadiya, jakkadiya tazube gaban sarki tace ranka yadad’e gimbiya tana k’ara godia Allah yaja da ran sarki mai adalci sarkin sarakai,

gyad’a kai sarki yayi nan fadawa gaba d’ayansu suka d’auka angaisheki gimbiya sarki ya ji godiar ki.

 

nan sarki yayi musu nasiha tare da yi musu addu’an zaman lafiya, sannan suka k’ara kwasar gaisuwa suka tashi suka fito, cikin gida suka shiga turakar dada,

nan suka gaisheta itama tayi ma gimbiya kyauta sannan suka wuce 6angaren ummi suka gaisheta itama kyauta tayi ma gimbiya sannan daganan sukaje 6angaren umman sumayya suka gaisa daga nan suka koma 6angarensu

suna shiga yarima yanufi hanyar zuwa 6angarensa ganin gimbiya tana niyar binsa yasa yadakata da tafiyar batare da ya kalletaba yace zaki iya tafiya 6angarenki domin yanzu inason inhuta bai jira jin abinda zata ce ba yawuce part d’insa.

Gimbiya sumayya tsaye tayi takaici duk ya cikata ganin yadda yarima yadizgata gaban bayinta, tsawa tadaka musu tace suwuce subata waje dasauri duk suka bar wajen,

nan gimbiya tanufi part d’inta cike da jin haushi.

 

 

haka sukayi sati d’aya suna shan amarcinsu tun yarima bai kulata daga baya sumayya saida tasan yadda tayi yarima suhail yad’an sake mata, ammah idan yana jin ‘yan miskilancin ko sarautar takad’a masa toh ko kallon inda take bata yi.

 

 

 

bayan sati guda gimbiya sumayya ce kishingid’e a parlourn ta inda bayinta suke zagaye da ita wasu suna mata tausa wasu fifita, d’aya tana karanta mata labari, wayartace tashiga ruri baiwar da take rik’e da wayoyintane tamik’a mata, cike da Jin dad’i sumayya tayi picking d’in wayar ko sallama batayiba tace haba zinat ai ni fushi nake da ke wai har ayi aurene bakya garin,

daga chan 6angaren Zinat tace toh sarkin k’orafi yanzu dai gani a k’ofar gidanki dogarawa sun hanani shiga kituro a shigo da ni,

cike da jin dad’i sumayya tace yanzu ko zan aiko, kallon d’aya daga cikin bayinta tayi ta yamitse fuska tace ke jeki waje kishigo min da bak’uwata,

dasauri tamik’e tace angama ranki yadad’e

batafi minti biyar da fitaba sai gasu sun shigo da zinat, sumayya tashi tayi daga kishingid’en da take tace oyoyoo k’awata takaina, nan bayi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen wadda aka kira da zinat sai yamutsa fuska take tana taunar chewing gum tazauna saman kujera, nan gimbiya sumayya takori duka bayin daga d’akin,

gimbiya sumayya kusa da ita takoma tazauna kafin kace mi ancika gaban zinat da kayan ciye-ciye da na shaye-shaye, sumayya cike da farin ciki tace k’awata kenan ai ban d’auka zan ganki a yanzu ba,

zinat kur6an ruwan inibi tayi sannan ta aje cup d’in tace wlh jiya nadawo garin shine nace ba zan fad’a mikiba surprise kawai zan baki yau.
.
murmushi Sumayya tayi tace kin ko kyauta wlh, na ma d’auka sai kin gama hutawa zaki dawo domin na sanki da son tafiya kihuta, zinat tace ai saboda ke nadawo amarya kinsha k’amshi kinga ko yadda kika koma?

murmushin jin dad’i gimbiya sumayya tayi tace ya nakoma dear?

zinat tace ai kin fito a gimbiyarki ta ainahi ke ni bani insha kifad’a min yadda kuke zaune da wannan miskilin mijin naki.

sumayya gyara zamanta tayi tace ai lafiya lou miskilanci kau saidai abinda yayi gaba, zinat tace ke ya batun first night d’inku,

dariya gimbiya sumayya tayi tace ai babu abinda yagane game da hakan kinsan nayi amfani da magungunan da kikasa aka had’a min wlh har tausayi yabani ganin bai gane komai ba.

ta6e baki zinat tayi tace ke inbanda abinki wa yace miki ana tausayin maza indai kina lalla6a miji ai sai yarainaki, shawarace zan baki daga inda miji yafara d’aga miki murya ke kinuna masa kinfi sa hauka,

sannan ba kowane lokaci zaki dinga ba mijinki kankiba saboda idan kika saba masa da haka toh sai kin gunduresa yaji ya gaji da ke daga k’arshema sai kiga kishiya

zaro ido sumayya tayi tace kishiya kuma? zinat gyad’a kai tayi tace eh man ai wlh namiji ba a basa amana ke nifa saboda tsoron halin maza yasa nakasa aure nake cin karena babu babbaka dukiya ce natara bakin gwargwado a lokacin da kuma naji ina buk’atar namiji ga mazanan birjit sai na za6a, inma macen nake buk’ata kema kin sanni.

 

dariya sumayya tayi tace hakane k’awata wlh kin kawo shawara mai kyau, ke nima fa sonake inga natara dukiya dan ban had’a kud’i da komai ba tunda ga mulki ga miji kinga dukiya yarage dan haka business zan fara. saidai anya zamu kwashe lafiya da yarima?

 

harararta zinat tayi tace kefa matsalata da ke wani lokacin baki da ganewa ammah asannu zan ganar da ke yadda zaki fahimta, ammah nagargad’eki da lallashin miji bare ma wannan mijin naki idan yashareki kema kifita harkarsa ke da nice da nasan yadda zan juyasa yakoma a tafin hannuna,

gimbiya sumayya tace hmm ba dai yarima ba anya akwai macen da zata iya juyasa?
zinat tace kefa matsalata da ke kenan bakida ganewa, kedai kigwada kigani dakanki zaki bani labari, yanzu dai taso mushiga daga ciki.

mik’ewa sumayya tayi tana dariya zinat tana binta a baya suka shige bedroom,
a ranar haka zinat tawuni gidan gimbiya sumayya tana k’imsa mata makirci iri-iri har saida taga gimbiya sumayya ta hau ta zauna sannan tabarta.

 

 

Tun daga ranar gimbiya sumayya tadaina shiga sabgar yarima shima shareta yayi yacigaba da hidimar gabansa,

yarima tun bai damuwa har abun yazo yafara damunsa yanzu tsawon wata d’aya da aurensu tun satin farko rabonsa da gimbiya domin ko d’akinsa bata zuwa.

 

yau da dare kasa daurewa yayi dan haka yatashi yasaka alkyabbarsa yafito yanufi 6angaren gimbiya sumayya, da key d’insa yabud’e direct bedroom d’inta yashiga chan tsakiyar gado yahangota ta baje sai baccinta take ahankali yataka yaje yahau saman gadon.

 

gimbiya sumayya da take bacci jin ana shafata yasa tafarka, da mamaki take kallon yarima, chan kuma sai tad’aure fuska tace lafiya?

yarima cigaba yayi da abinda yake kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace sumayya yanzu saboda Allah hakan da kike min kina ganin kin kyauta? hak’k’ina nazo kar6a,

gimbiya sumayya janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tana jin dad’in shawarar da k’awarta tabata ganin yau dakansa ya aje girman kan yazo d’akinta,

ganin yarima suhail yana shirin rikitata yasa tajanye jikinta gefe tace haba dan Allah yarima wai menene haka nifa a gajiye nake.

da mamaki yarima yake kallonta yace haba sumayya saikace wadda tayi wani aiki nidai yanzu kibari inyi inyaso daga baya sai kiyita baccinki.

gimbiya sumayya komawa tayi takwanta tare da juya masa baya tace ni ba zan iyaba gaskiya, yarima binta yayi yana lallashi dakyar ta amince masa shima saida taita masa k’orafin ta gaji kan dole a k’arshe yahak’ura yabarta batare da ya ida samun nutsuwaba,

toilet d’inta yashiga yayi wanka sannan yadawo yakwanta tare da juya mata baya cike da mamakin yadda sumayya tasauya hali .

 

gimbiya sumayya ko murna takeyi ganin ta d’an ci nasara har Yarima suhail ya zo d’akinta yau, kuma ya aje girman kai da sarautar ya lallasheta.

 

 

Tun daga lokacin yarima shi yake biyota d’akinta ko da ace ya yi mata wulak’anci a wani wajen ita kuma sai ya nemeta take ramawa sai ya-yi dagaske yake samun hak’insa a wajenta ahaka suka haura wata shidda ammah ko 6atan wata bata ta6a yi ba,

dada ta fi kowa damuwa domin tisata gaba take a d’aki tana tambayarta ko akwai abinda take sha ita dai gimbiya a’a take cewa, dada tace a’a gimbiya indai akwai abinda kikeyi, gimbiya saidai tayi dariya tace dada inda ina yin wani abu ai da kun gane, dada saidai tace toh Allah yakawo.

 

ko da yarima yazo yagaishe da dada bayan sun gaisa dada tace yarima wai har yau ba wani labari?

yarima shuru yayi saida yayi kusan minti biyu sannan yace dada labarin me kuma?

dada tace hmm ciki mana.

murmurshi kawai yayi yace dada ai haihuwa lokacine, idan da darabo zamuyi.

dada tace toh Allah yakawo mai albarka yarima yace Ameen.

 

sannan yarima yatashi yafita dogarawansa da suke tsaye bakin k’ofa suna ganin ya fito nan suka fara masa kirari yana gaba suna biye da shi tun kan ya isa wajen jerin motocinsa da yasa aka tanadar masa dan yafita dasauri aka bud’e masa dank’areriyar motarsa da take tsakiya nan yashiga baya yahakimce sannan dogarawa suka shiga sauran motocin akasa tashi a tsaka nan aka kama hanya.

 

asibitoci yaje yakai ziyara yaduba marassa lfy yayi musu kyauta sannan yawuce gidan marayuwa yabada kayan abinci kowa yaji dad’in ziyarar da yakawo domin daman halinsane kyauta,

daga nan suka kama hanyar gida, ko da suka isa bai shigaba saida yatsaya yasa aka tara ma’aikatansa yaraba masu kud’i nan suka zube suna ta godia daganan yawuce part d’insa yana shiga yacire kayan jikansa yafad’a toilet yayi wanka, bayan ya shirya saman gado yafad’a yana hutawa bud’e k’ofar da akayine yasa yabud’e idonsa dayake a lumshe,

ganin gimbiya sumayya ce yasa da mamaki yakalleta domin yasan bata shigowa d’akinsa sai idan tana buk’atar wani abu, maida idanunsa yayi yalumshe,

takowa tayi tahau saman gadon tazauna gefensa ganin baida niyar bud’e ido yasa tace ashe har kadawo tun d’azun nake aikowa adubomin idan kana nan,

yarima batare da ya bud’e idanunsaba yace ya akayi kika shigo min d’aki ba’a fad’a miki nace kar wanda yashigo ba? gimbiya sumayya murmushi tayi tace yanzu dan zan shigo d’akinka har sai anbani izini a matsayina na matarka?

banza yarima yayi yakyaleta, ganin baida niyar tanka mata yasa takwanta a jikinsa ta d’auka zai gwalisheta ammah taji ya yi shuru baice komai ba, dan haka takai hannu tana shafa fuskarsa daga nan tafara kissing d’insa daman abu ga mai nema nan yarima yabiye mata,

 

ya yi mamaki yadda yau bata hanasa kantaba domin yasan hali da ya fara zata fara cewa ta gaji, ammah yau saida yagaji dan kansa sannan yabarta.

 

rungume take a jikinsa cikin shagwa6a tace my sweetheart dan Allah inaso kabani 2 million,

yarima baiyi mamakin jin hakan daga garetaba, domin daman yasan za’a rina ba zata ta6a bashi kantaba sai da dalili,

bud’e idonsa yayi yasafkesu akan fuskarta kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace mezakiyi da kud’i?

Sumayya batare da damuwaba tace business nakeso inyi kaga zaman hakanan ai baya yuwuwa zamu had’a jari da k’awata zinat zata dinga zuwa tana saro mana kaya, zamu bud’e babban boutique a chan Abuja.

yarima tunda tafara bayanin yatsareta da ido har takai aya sannan yace yanzu ke bakiji kunya ba kice zakiyi kasuwanci akwai abinda narageki da shi ne?

gimbiya Sumayya d’aure fuska tayi tace kai fa matsalata da kai kenan to shi business dole sai marar wadata yakeyinsa?

yarima janye jikinsa yayi yace idan ke bakida hankali toh ni ina da shi kuma ba zakiyi ba, yana gama fad’in haka yawuce yashige toilet domin yayi wanka.

 

gimbiya Sumayya binsa tayi da kallo cike da takaici tace tsiyata da kai bakasan arzik’iba saida nagama baka kaina sannan kanemi kawulak’antani toh wlh baka isa kahananiba dan haka muzuba mugani,

tana gama fad’in haka tajanyo kayanta tasaka tatashi fuuuuu tafita tabar d’akin.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

 

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*~Sak’on gaisuwata agareki Mummyn khalil fatana Allah yabaki lafiya, Allah yasa zakkar jikine~*_

 

_kuna ina Kuzo yau ranar takuce wlh ina ji daku har cikin zuciyana *My k’anwa Safiyya Aliyu, Mrs Abubakar, Ma zeenart, Hafsat Kanty, Cool Angel, Chubby, Asma’u Yusuf Beji, Husnah, Mugirat Musa, Maman Sadiq, My k’anwa Khairyy, Maman Haidar, Hadiza Abubakar, Maman Amira, Kubcy Auwal, Dr Xeey Xeey, Aisha Baba Audu, ummu walid nd Abdul, Maman khaleesat, Sadiya Abubakar, Billy….* da ma sauran wad’anda ban lissafoba, wannan page d’in nabakushi Allah yabar k’auna_

Back to top button