Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 13-14

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*13&14*

 

 

https://chat.whatsapp.com/JHvLho4664m0KcDHi1EDmF

1) *Invitation card, video invitation card*
2) *Book cover 3d mackup, normal book cover 3 colors*
3) *Data flyer, Account number sticker*
4) *3d mackup logo, normal logo*
5) *Ideogram ai logo*
6) *How to remove background*
7) *How to download icons*
8) *Yanda zaki haɗa document na littafi,da kuma yanda zaki cire password idan aƙwai a jikin littafi*

9) *Zan bada application guda 3 waɗanda ba’a samun su a play store*

*Kuɗin da zaki shiga Class ɗin da zaki samu wannan garaɓasa ₦300 idan kin shirya ki turo kuɗin ki ta 1632036584 Saadatu Balarabe Access Bank ki turo shaida ta wannan number 07032895551 ko katin MTN*

…….kimanin shud’ewar mintina 15 suna zaune ita dashi Acikin parlourn Amma bbu me mgn Acikin su”ita tana d’an kallo a TV”shi kuma yana danna waya”can Amaan ta saki dariya me sauti tana fad’in yeeeeee! takama shi……tsit tayi sbd idon da suka had’a da shariff”wanda ya kalleta ya kalli TV d’in dan yaga meye takeyiwa dariya?”ita kuwa had’e rai tayi tana fad’in wai hamma bana ce bbu ruwana dakai ba?”yatsina fuska yayi saida ya d’auki kusan second 5 kafin yace”K ! bana son gulma”idan zakizo ki d’auki Abinda kikace na siya miki kizo ki d’auka”idan bakiyi ruwa dani ba sai akace miki mutuwa zanyi ko kuwa fasa rayuwa zanyi ne??”shiru tayi tak’i mgn”bakya jina ne?”kukan shagwab’a tasaka ta mik’e tsaye zatabar masa parlourn”fuskarsa Ad’aure yadako mata tsawar daya jima rabon daya dako mata irinta”jikinta na kirma tazo gefen dogayen kyawawan k’afafuwansa ta duk’a”beyi mgn ba fuska ahad’e ya sakko k’asan ya zauna gefenta yazaro robar ice cream d’in”murya na rawa Amaan tace”na k’oshi ni”bana neman yaddarki ko shawaranki”,Abinda nasani dole kishashi”kuma kikamun kuka na fasa miki baki”na lura 2days sbd kinga inajin tausayinki Ina k’yaleki shine kikemun Abinda kikaga dama ko?”yafad’a yana hararar ta”ta turo masa pink lips nata”ya kawar da kansa gefe yana bud’e robar ice cream d’in”yasaka spoon ya deb’o da nufin yayi spoon biyu yabata sauran sbd yaji ya burgesa”Amamakin sa sai tasaki k’aramin kuka tana fad’in nidai hamma ka bani abuna mana” ni karka shamun kayana”ba nawa bane ba”d’an murmushi yasub’uce masa “wanda tunda take dashi bata tab’a ganin yayi irinsa ba”ta bishi da kallo bbu ko kiftawa dan ba k’aramin kyau yamata ba”cikin sanyayyar muryarsa yace”Amaan yaushe kika rainani har haka wai?”to nama fasa baki”tunda wani iyayi zakimun”yafad’a yana kai spoon d’in bakinsa”ita kuma tayi k’ok’arin tashi…kika sake kika gudu wlh ranki zai b’aci”oya bud’e wannan ledar kiduba turarukan”batayi mgn ba tanata b’ata rai ta d’auka ta duba”body sprays kala biyu dana kaya suma kala biyu”masu kyau da tsada”yana kallonta ta wutsiyar Ido tana d’an murmushi tana kallon turarukan”saita juyo ta kallesa tana fad’in hamma nagode”shima saiya kalleta! Atare k’irjinsu ya buga”har Amaan saida ta dafe nata k’irjin”ya d’auke kansa yana turo mata robar ice cream d’in yace”oya ki shanye yanzun Agabana “tunda kin saka na siyo baki isa kice bazaki shaba yarinya”nidai bana shan saura… what??”ya katseta da mamaki yananzaro mata manyan fararen kyawawan idanuwansa”sai kuma ya banko mata harara ya d’auki robar ice cream d’in ya matso dab da ita har tana jin hucin numfashinsa”ga mayataccen k’amshin turarensa daya cika mata hanci”gaba d’aya sai tajita wani iri”ya deb’o ice cream d’in yanufi d’an mitsitsin bakinta dashi” maimakon ta Amsa saita saka masa k’aramin kuka”yaja kwafa Anutse yace”kinsan Allah koki Amsa kona fasa wannan bakin naki”batayi mgn ba ta Amsa tana lumshe Ido”dama nasan kinaso gulmace ta hanaki”yafad’a yana kallon farar kyakykyawar fuskarta…she is very beautiful! Abinda yafad’a kenan batare daya shirya fad’a d’in ba”sai yaja k’aramin tsaki yana tambayar zuciyarsa Ina ruwansa da kyawunta to?”saima d’aure fuska yayi yanata d’ura mata ice cream d’in “can ta kauda kai tana nok’e kafad’arta tace”ni bana sha”to waye zai Ida shanye miki sauran?”maimakon tayi mgn saita nunasa da yatsa”kallon bakida hankali yajefa dashi”kafin ya koma d’aure fuska yace”oya cigaba da sha….be dena bata ba saida ta shanye”guntayen hayawayenta suka zubo”yatab’e baki yana fad’in tashi kije kiyi sallah lokaci yakusa”to Ai hamma baba ladi tace”ni banayin sallar sbd jinin dayake zubo…..ya Isa pls! yafad’a yana d’aga mata hannu”Aransa yana mamakin wai har yanzun bata sami tsarki ba kenan?”ya d’auka tuni ta gama period d’in”mik’ewa tsaye yayi”hamma Ina zakaje?”d’akina”zan bika can?”kiyi zamanki masjeed zanje”inane kenan?”Amaan wai bazaki barni na huta ba da surutunki?”shiru tayi batace komai ba”shi kuma ya wuce yabar mata k’amshin turarensa”be jima ba Asaman yasakko da farar jallabiya Ajikinsa”fuskarsa da ruwa da Alama Alwallah yayi”satar kallon Amaan yayi yaga tayi tagumi tana kuka”kamar bazai kulataba sbd haushi take bashi idan tana wannan saurin kukan”me akayi kike wani kuka?”da sauri ta kallesa sai kuma ta sunkuyyar dakai k’asa “ba dake nake mgn ba?”nima bansan meyasa ba kawai inajin kukan kuma bansan wacece niba”sosai yaji tausayinta”Ahankali yace “karki koma yin kuka”to hamma nima zaka siyamun kayan wasa da ake nunawa a TV?”kasa mgn yayi ya gyad’a mata kansa kawai”tayi d’an murmushi “sai kuma tace”to yaushe zamuje ka kaini na zab’a?”da k’yar yace”gobe “be jira cewar taba yafita”sbd yasan idan ya biyema surutun yarinyar zai iya rasa jam’i”be dawo gidan ba sai bayan sallar isha’i kamar yadda yasaba”saidai Ahanya ya tsaya ya siyawa Amaan gashashshiyar kaza”wanda shi kansa besan dalilin daya siya mata d’in ba”sai akayi sa’a daya shigo itace kad’ai zaune cikin parlourn “tana ganinsa ta taso aguje tana fad’in oyoyo hamma nah”in bacin yayi saurin kaucewa data fad’o masa ajiki”Amaan meye haka?”ke yarinya ce ne?”idan kika koma yimun hakan saina mareki”dan Allah kayi hak’uri hamma nadena”dama cikin TV naga wata tayima hammanta haka”tsaki yaja ya mik’a mata ledar”k’in Amsa tayi tana jeho masa tambayar hamma ka hak’ura ko?”girgiza mata kansa yayi ya zagayeta ya wuce ya Ajiye ledojin guda biyu saman center table”kafin ya zauna kan kujerah yana danna waya”Amaan kuma kuka tasaka masa”ak’ule yace”K! kukan meye kikeyi?bakai bane baka hak’ura ba”zonan”bbu musu tazo tayi tsaye”ya girgiza kansa cikin gundura da yawan maganar datake yawan sakashi yace”d’auki leda guda ki kaima baba ladi ki dawo”bbu musu ta d’auka ta wuce”ya sauke numfashi yana jingina bayansa a jikin kujera ya lumshe idanuwansa….hamma bacci kakeyi?”yaji siririyar muryarta ta daki dodon kunnansa”bud’e Ido yayi beyi mgn ba”na kai mata tace”ta gode”shiru yayi can yace”jeki kitchen ki d’akko plate kizo kizuba naki saiki ci”to kaima zakaci ko?”girgiza mata kansa yayi da sauri”to nima na k’oshi hamma”tsareta yayi da Ido yama rasa gaba d’aya meye zaice mata”idan yamata tsawa tayi kuka”idan yanuna ta masa laifi shima ta masa kuka”hamma ! Amaan bana son musu kiyi Abinda nace miki ko?”yafad’a cikin zafin rai”batace komai ba ta wuce kitchen d’in ta dawo ta zuba naman a plate”shi kuma yana zaune yana waya da mus’ab”yana lura da yadda take cin naman Ayangance” bayan yagama wayar dashi ya d’auki kiran fareedah da tun d’azun yana ganin kiranta time d’in dayake waya da mus’ab…..da k’yar yayi mintina 10 yana mgn da ita”daga karshe ya yanke wayar “bayan ya sanar mata kansa na ciwo”yana sauke wayar ya lura da Amaan na tsugunne gefensa da robar ruwa da cup Ahannunta tana fad’in hamma nah zaka sha ruwa?nima naga wata a TV ta kawowa wani ruwa….ya kalleta yace”shine zaki gwada dani ko?”yafad’a yana Amsar ruwan ya shanye ya Ajiye kofin yana fad’in thank you”bata dai san meyake nufi ba”tadai Ajiye robar ruwan tace”zanje na kwanta bacci sai nayi addua”kaima hamma kadinga yin Addu’ar ko?”kansa ya gyad’a mata yana tunanin idan tadawo hayyacinta Aka sanar mata tana wannan abun k’ilan sai taji kunya”mik’ewa tsaye yayi bece komai ba ya haye samansa”Abin mamaki daya sakko tana nan zaune lokacin har 9 pm tama d’an gota”wajen TV yanufa yakashe kayan kallon kafin ya juyo suka had’a Ido”saurin k’asa da kanta tayi”tashi kije ki kwanta”Toni muje ka rakani”shiru yayi yana tuna kalaman mus’ab dayace time d’in datake hayyacinta shagwab’abbiya ce”tashi muje d’akin”tana murmushi ta mik’e tsaye tace”to goben hamma zaka kaini na zab’i kayan wasan?”Allah yakaimu”ya Amsa ne sbd kawai ta k’yaleshi”Amma bawai da nufin ya yadda yafita da itaba”k’ofar ya bud’e mata tana d’an murmushi ta wuce tana cewa”hamma kayi addua idan zaka kwanta”karki damu zanyi”daga haka ya rufe k’ofar yanufi k’ofar fita….sadda ya iso gida goma saura”Ammi ce kawai da Abdallah zaune a parlourn”Abdallah na kallon wani indian firm na soyayya”Ahaka shariff yashigo parlourn cikin nutsuwa”fuskarsa kadaran kadahan”Ammi da Autanta! shine Abinda yafad’a yana kallonsu” to miyafi ranmu?”ta fad’a tana murmushi”Abdallah na kallonsa yace”yaya sannu da zuwa”yauwa”ya fad’a yana kok’arin zama kan kujera “cikin shagwab’a Abdallah yace”yaya kaga wannan yaya sadeeq d’in yakira Ammi wai yakusan dawowa nanda wata d’aya na kwashe kayana d’akina zai koma”kuma dama kasan yaya idan yana nan cutata yakeyi yaita cin zalin nawa ko?”to sarkin kawo k’ara “bana sanar masa ba bbu inda zaka koma?cewar Ammi”Abdallah kashe kallon nan kaje ka kwanta ko kayi Assignment kana jina?”cewar shariff yana kallon sa”Abdallah ya kalli Ammi yana rok’arta da Ido wai tayima shariff mgn yabarsa”murmushi kawai tayi tana fad’in koda yayanku be zoba ni zance kaje ka kwanta, sbd nasan baka son tashi sallar Asuba da wuri….yana ta b’ata rai yakashe kayan kallon yabar parlourn”yana ayyanawa Aransa kayan kallo zai zuba a parlourn sa” d’an shiru ya biyo baya can Ammi tace”wai meyasa Acikin y’an kwanakin nan baka san yawan dawowa da wuri kamar kullum”sannan kake fita da wuri ,wani lokacin ko break fast bakayi?? d’an jim yayi yana shafa kansa yace”kinsan yanayin Aikin mu musammun idan muna kan bincike shiyasa Ammi “Amma zan dinga dawowa da wuri ai”to shikenan kasaka arufe gidan dan Alh baya gari”shariff beyi mgn ba Aransa yace”yatafi neman Asiri ko safaran miyagun k’wayoyi kenan?”mik’ewa tsaye yayi yamata sallama”sai bayan yasaka an rufe ko Ina na gidan sannan ya nufi side d’insa”kayan jikinsa yarage yashiga bath room “Abin mamaki yaji Amaan ta fad’o masa rai”Abubuwan da suka faru d’azun da yamma suka masa tsaye Azuciya”sai basarwa yakeyi Amma Abin yak’i barin ransa”da wannan tunanin yafito yayi shirin kwanciya bacci…..
washe gari da safe babu yadda baba ladi batayi da Amaan ba akan tayi break fast Amma saita k’iyi”tace hamman ta take jira yazo zasuje yasiya mata kayan wasa”saima ta hau shiri”da baba ladi ta matsa mata saita saka kuka”,hakan yasa ta k’yaleta”ta barta cikin d’akin tanata duba kayanta can ta binciko lace d’in da shine Ajikinta ranar da shariff yafara had’uwa da ita”da k’yar tasaka kayan sbd ta k’ara y’ar k’iba”kuma ko Abaya kayan sun kama jikinta sosai”mayafin nata ta yafa saman kanta bata d’aure d’an kwali ba”tayi kyau sosai gwanin burgewa”idan ba sanin matsalarta kayiba zaka zata budurwace ita me hankali da aji”parlourn tadawo ta zauna kan kujerah sai k’amshi ke tashi Ajikinta me dad’i”baba ladi dai nata kallonta tana tasbihi da sarkin daya halicci Amaan”kinga hamman yak’i zuwa ko?”hmm! Amaan ki tashi kiyi kari ko idan yazo nasanar masa”nifa bazan yiba karki sanar masa dan Allah baba ladi”yanzun ki kunnamun kallo sai nayi”bazan kunnah ba sai kinyi kalaci”kuka Amaan tasaka harda hawaye shab’e shab’e…..Ahaka shariff yashigo parlourn cikin shiga ta Alfarma me d’aukar hankalin duk Wanda ya aza idonsa Ajikinsa”kasancewar yau satday bbu office”dukda dai a week end yana ziyartar yaransa yaduba komai”sanye yake da wani had’ad’d’en yadi me tsananin tsadar gaske ash colour”yanada taushi da santsi”yabi ya haska choco skin nashi”kansa bbu hula”sumar nan Tasha gyara tana d’aukar Ido”sai fitinannan k’amshi ke tashi Ajikinsa “kamar ko yaushe hakama yanzun kyakykyawar fuskarsa Ad’aure take”baba ladi ta Amsa sallamar tasa ya zauna gefen kujera yana k’arema parlourn kallo suka gaisa”yana lura da Amaan na kuka”saidai miskilin kallo bata isheshiba “ganin yabasar da ita yasaka tace”hamma kaga baba ladi tak’i kunnah mun kallo ko?”ikon Allah! yau kuma k’arata zaki kawo Amaan??”ka ganta nan wlh bbu yadda banyi da itaba tayi kari tak’iyi wai tana jiranka kuje ka siya mata kayan wasa “tunda suke maganar ko gezau miskilin beyiba,kansa aduk’e yana dannah waya” saida sukayi shiru sannan yad’ago kansa anutse yazuba mata Ido”ta turo baki tana sunkuyyar dakai k’asa “tashi kije kiyi break fast”to hamma zaka jirani na gama saimu tafi ko?”ki tashi kije kiyi break fast”yakoma maimaita mata”kukan shagwab’a tasaka ta kwasa aguje ta nufi dining area”baba ladi ta girgiza kanta ta tashi ta wuce kitchen”shariff yaja tsaki yana tunanin Ina zashi da Amaan?”bayan ga yanayin yadda take ciki”kuma shima bayaso aganshi da mace yana yawo mak’iyansa suyi masa wata fassarar”dukda baya tsoro baya shakkar uban kowa”Amma yafiso ya kammala Abubuwan dake gabansa”musammun plane nasa da fareedah”wacce yana tunanin sai monday zaije gidansu ya Amso zobban nan…. Hamma na gama saimu tafi ko?”yaji muryar ta Agabansa”ya d’ago kansa yamata kallon second 3 ya d’auke kansa yana yatsina fuska yace”sai kin koyo yadda Ake gaisuwa da ladabi sannan saimu tafi”sannan kije ki canza kaya zan saka aka miki hijabai da gyaluluwa”Amma hamma nidai bazaka tafi ka barni ba ko?”ta fad’a cikin shagwab’a”shareta yayi yak’i mgn”ganin Hakan yasa ta wuce kitchen tasami baba ladi na wanke wanke “wai baba ladi ya Akeyin ladabi? murmushi tayi tace”ladabi shine idan zaka Amshi abu hannun wani musammun wanda ya girmeka zaka duk’a kasaka hannu biyu ka Amsa”haka idan zaka bashi ruwa ko Abinci saika duk’a cikin ladabi kabashi”kuma idan zaka gaidashi saika duk’a har k’asa,ta nuna mata “daga k’arshe tace”itama mgn Anaso kayi cikin ladabi da iya karya harshe”bawai tsiwa ko d’aga murya ba”shiru kawai Amaan tayi tana tunani can kuma ta fita daga cikin kitchen d’in “d’aki ta koma ta canza kaya zuwa bakar jallabiya”masha Allah! saita fito kamar balarabiya”saidai mayafin saman kanta ta azashi”ta saka takalminta plate shoes ta fesa turare”fuskar ta tayi fiyau sbd bbu make up,ko hoda da kwalli bata shafawa”fitowa tayi tasamesa zaune yana danna laptop d’insa “Ahanakali ta masa sallama ta duk’a gabansa tace”hamma sannu da hutawa”dama na gama shiryawa”da mamaki yabita da kallo ta sunkuyyar dakai “bece komai ya rufe laptop d’insa ya mik’e tsaye yana fad’in Amshi rik’emun na fito”batayi mgn ba ta russinah ta Amshi wayoyinsa guda biyu cikin ladabi”nanma yakoma mamaki “sai kuma ransa yafara bashi kodai yarinyar na hayyacinta?”saiya kawar da tunanin Aransa ya haye upstairs”Ajiye laptop d’insa yyi a parlourn yarufe yasakko k’asan “tana tsaye da Alama tunani takeyi”hamma sannu da fitowa”beyi mgn ba yamik’a mata hannunsa Alamar ta bashi wayoyinsa”saita nok’e kafad’arta “yatab’e baki yafita”ita kuma ta wuce kitchen ta sanarwa baba ladi sun fita”sannan tabiyo bayansa”hangosa tayi yafita get hakan yasa itama ta fito”tanata y’an kalle kalle sbd tunda tazo gidan sai yau ta fito waje”juyowa yayi suka had’a Ido “harara ya balla mata”ta turo d’an bakinta”bani wayata zanyi kira”batayi mgn ba ta bashi k’aramar “ya Amsa ya bud’e driver sit ya shiga”itama sai tabud’e front sit ta shiga”bayan yasaka kira sannan yatashi motar”Assalamu Alaikum yallab’ai”wslm ka Amso sakon?Eh yallab’ai “okay zanzo yanzun na Amsa”daga haka ya yanke wayar “ita dai tana zaune tayi tagumi”harya tashi motar batayi mgn ba hankalinta na wajen wayarsa tanata kallon wayar”Anutse yake driving d’in ya kunnah karatun Alkur’ani me girma”sunyi shiru suna saurare”basufi mintina 10 suna tafiya ba wayarsa babba tayi ringing “da sauri Amaan ta mik’a masa”ki danna green d’in ki karamun”yafad’a sbd yaji ringing d’in daya sakama Ammi ne idan ta kirashi zaiji”Amaan dai d’aukar masa wayar tayi ta kara masa a kunne shi yana driving d’in “garin hakan yatsun hannunta suka tab’o sajensa da gefen kunnansa….dan kallonta yayi sai kuma ya kawar da kansa”tun kafin yayi mgn Abdallah yace”yaya bbu lafiya kana Ina?”meya faru?”ciwon Ammi ne yatashi”gata nan kwance bata numfashi”inata neman inhela d’inta banganiba”yafad’a yana yanke wayar da sauri”shariff ya sauke Ajiyar zuciya yana saka hannunsa guda ya janye hannun Amaan batare dayayi mgn ba”yajuya akalar motar zuwa gidan Ammi “sai bayan sun iso yayi parking sannan yatuna kuskuransa na zuwa da Amaan dayayi Agidan”kallonta yyi murya bbu wasa yace”ki zauna zan shiga na Amso sako”karki sake ki fito”kina jina?”to hamma bazan fita ba”beyi mgn ba ya Aza mata gudar wayar sa saman cinyar ta yafita da sauri…..befi mintina 5 da fitaba k’aramar wayarsa tahau ruri sai Amaan ta fito daga cikin motar ta maida ta rufe”sai kalle kalle takeyi sbd ganin securities tsatstsaye da bindugu abakin get”ga wasu maka makan motoci a haraban gidan fake”gaba d’aya tama rasa Ina zata dosa”sai raba Ido takeyi”can ta hango wata yarinya (Ibtihal) ta fito daga wani corrido”hakan yasa ta wuce wajen”sbd Azatonta bazai mata fad’a ba tunda wayarsa zata kai masa”kallon kallo sukayi itada Ibtihal kafin Amaan tanufi interest d’in shiga cikin gidan”dukda ga yanayin yadda take Amma saida taga kyawun gidan da tsaruwarsa”kamar marar gaskiya haka ta tura k’ofar babban parlourn, adaidai lokacin da wayar shariff keta faman ringing”tun kafin Amaan ta shigo k’irjin shariff yabuga! sbd jin ringing d’in wayarsa”kafin yayi wani abu Akai Amaan ta shigo da sallama cikin parlourn….✍️

zazzafan sharhi yanzun za’a fara wasan

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button