Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 18

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E18_

 

*Daga alƙalamin Boss Bature*

 

 

*DAULAR OBIE ESTATE*

A katafaren ɗakin Hajjaty head maids ta gidan obinna, tsabar haɗuwarsa tamakar bana ƴar aiki ba.

fitowar kenan daga bathroom, ga dukkan alamu wanka tayi, ta ɗaure ƙirjinta da towel fari, iya gwiwar ƙafafuwanta ya tsaya mata, fatarta da lemar ruwan wankan da ta yo, a gaban mirror ta tsaya tana kallon kyakkyawan fuskarta har yanzu akwai sauran make-up ɗin jiya da ta yi jan bakin bai goge ba, don ita bata rabo da kwalliya a fuskarta.

Har ta miƙa hannu zata ɗauki man shafawarta cikin jerin mayukanta, ba zato ba tsammani muryarshi ta ratsa kunnanta”My heart beat” ras taji gabanta ya faɗi, sam bata ji shigowarshi ba, A hargitse ta yi saurin wurga idonta kan fuskarshi

Yana daga kishingiɗe saman gadonta, farar singlet ce a jikinsa da short.

Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, muryata na rawa ta furta sunan shi”PRAVIN”!

Dafe kai tayi da hannu ɗaya, tsananin fargaba ne ya kamata.

“Nashiga uku, why Pravin meyasa zaka yi min haka! Kana so ne kaja min bala’e? Yanzu idan wani ya faɗo ɗakin nan me kake tunanin zai biyo baya”? A ruɗe ta ke yi mashi magana tana faman zazzare dara daran idanuwanta,

“Haba pravin baka min adalci ka riga da kasan ko’ina na kusurwar gidan nan cctv ne za’a iya ganin duk motsin ka”

Tun da ta fara magana, Pravin ya tsareta da manyan idanuwanshi, har sai da takai Aya, tukunna Ya sauko daga saman gadon ya nufe ta kamar wani zaki, dab da ita Ya tsaya ƙamshin turaren jikinsa ba ƙaramin Illa Ya ke yi mata ba tuni ta fara shiga yanayi.

“My honey, ni ban zo donna 6ata maki rai ba, haƙƙina nake so, Nakasa jurewa ina buƙatarki, kinsan bani da haƙuri in dai akan buƙatar kaina ce, sannan ki kwantar da hankalin ki, babu wanda yasan na shigo ɗakin ki, daga ni sai ke”

Ya ƙare maganar yana faman sakar mata shu’umin murmushin nan nashi, Idanuwanshi akan ƙirjinta da suka tsone mashi ido.

Jikinta sai kerma yake yi kamar wadda sanyi ya kama, tana matuƙar jin tsoron wani ya faɗo masu a ɗakin, ita kanta a buƙace ta ke da shi tana son kasancewa da shi sai dai tana tsoron wani ya gansu.

Still sautin muryarta adabarbarce take furta”Pravin ni ina fargaban wani ya gan….” bata kai ga ƙarasa maganar ba, yai saurin zura harshen shi acikin ƙaramin bakinta, hannayenshi biyu ya ɗaura saman manyan mazannanta ya ci gaba da murzasu, nan take numfashinsu ya fara hauhawa yana fita da sauri sauri alamun sun fara hawa kan network, ko’ina na jikinta ya ke bi yana matsawa da hannunsa, Sosai yake kissing ɗin ta tamkar zai cire mata la66anta, Zame tongue ɗinsa yai daga bakinta, tun daga kan wuyanta ya fara manna mata hot kiss har izuwa ƙirjinta, ya warware towel ɗin da tayi ɗaurin gaba dashi gefe ɗaya ya jefar da shi, gaba ɗaya ya ɗauketa ya jefar saman gado, doguwar sumar kanta tuni ta tarwatse saman mattress, Ya sanya hannu ya zame Singlet ɗin jikin shi Ya haye saman gadon Yaja bargo Ya ƙudundune su, To jama’a nidai bansan me sukeyi a cikin bargon ba, na dai ji sautin gurnaninsu tamkar namun nawa na fafatawa. Bargon da suka lullu6a dashi sai yamutsewa yake yi yana motsi kamar ana dambe a cikinsa, ba yau bane karo na farko da ya fara biyan buƙatarshi da ita ba, sam basa gajiya da juna pravin da divya wato hajjaty, Babu wanda yasan suna harƙalla atsakaninsu.

(To fa, akwai gwarama yasin Ana wani abu agidan Obinna, Ko ina hajiya saratu taje? Ana nan za’a 6ata mata tarbiyar Miji)

A hankali danƙareriyar Motar Hajiya saratu ta kunna kai Cikin Villa dinsu adai dai parking space security ɗin da ke driving nata yai parking na motar, Da sauri Ya fito daga driver seat Ya zagaya Ya buɗe mata ƙofa, ta zura ƙafarta dake sanye cikin High hills, dawowarta kenan daga meeting da suka yi a ministry of Health tare da manyan ministocin Kiwon lafiya da suka kawo masu ziyara daga Who (world health organization) don inganta Lafiya.

Tsadadden leshi ne fari a jikinta, riga da zani daga sama ta ɗaura lap coat, fararen idanuwanta na amanne da glass fari matar fa akwai Iya ɗaukar wanka, ta ko’ina Jikinta ƙamshi yake fitarwa.

Saukowa ta yi daga Cikin motar, da sauri ta nufi cikin gidan hannunta ruƙe da hand bag ɗinta, duk inda ta gifta masu aiki ne ke safa da marwa, cikin girmamawa su ke gaishe da ita, idan ta gama dama ta amsa idan bata ga dama ba sharesu take yi.

A katafaren Main palour na gidan ta shigo, Tafkeken gaske A ƙalla Yana ɗauke da Royal sofas two set saboda faɗinsa.

“Sannu da dawowa Hajiya” muryar Safa ce ta dakatar da ita daga Yin tafiyar, Fuskarta babu annuri a ɗaure take tamau kamar wadda aka 6ata ma rai”Pravin Ya dawo ne”? Tambayar da ta jefa mata kenan.

“Bani da masaniya, da ya ke mu na yin aiki a kitchen ne bansan ko ya dawo ba”

Gyaɗa kai Hajiya saratu ta yi”Okey, zan shiga ɗakin baba, kafin in dawo ki tabbatar kin kai min lunch ɗina a ɗaki, bana son 6ata lokaci” amsa mata tayi da toh hajiya.

Da sauri safa ta nufi kitchen don ta shirya mata abincin.

Kaitsaye hajiya saratu ta nufi sashen obinna.

Tana gab da zata shiga ɗakin Dr jazz ya fito Yana sanye da suit black colour. Ko da suka haɗa ido da ita gabansa ba ƙaramin faɗuwa yai ba.

Muryarshi asanyaye ya furta”ina wuni mommy” harara ta wurga mashi

“Kai bana ce kar na kuskura na ƙara ganinka acikin gidan nan ba? wannan wata irin mayuntaka ce? Meye haɗinka da babanmu”? Tafa Hannu ta yi haɗi da ruƙe ha6a.

Muryarshi adabarbarce ya furta”ai ba anan nake zaune ba tun lokacin da ki ka ce bakison ganina, na koma gidan daddy da zama…” daƙyar ya ida maganar ganin irin ƙasƙantaccen kallon da take wurga mashi.

 

“Uban waye daddyn naka? In banda yaudarar kai yaushe Yaya mubarak ya zama uban ka? Kai fa ba ɗan kowa bane a family ɗin nan, ka daina ɗaukar kanka wani shege, ai tun ranar da aka faɗamin cewa hada kai ake tsegumin ƴa’ƴana, naji na ƙara tsanar ka matsiyacin banza, in banda zaƙewa da shisshigi da kutsu da samun wuri irin na ɗan talaka ina kai ina haɗa kafaɗa da masu asali a dangi eyeh? A faɗace take yi mashi magana tamkar zata rufe shi da bugu, Bawan Allah dr jazz tuni hawaye sun cicciko idon shi.

Ta6e baki tayi”dallah jibarka, sai uban tsawo kamar fal waya ba ƙiba, duk irin arziƙin da ku ke ci a ƙarƙashin inuwar mu har yau baka ƙara komai ba, Sai Iya gulma da munafunci shashasha kawai, dallah ni bani wuri in wuce kar na ham6are ka” jiki na rawa ya matsa mata hanya, ta shiga ɗakin obinna.

Idanuwanshi sun kaɗa jawur, babu mai yi mashi gori irin hajiya saratu ƙiri ƙiri take nuna ta tsane shi, sam ya kasa motsawa saboda jirin da ke shirin ɗibarshi, a hanzarce ya dafe bango da hannu ɗaya, Ƴar ƙwallar da yake 6oyewa tuni ta gangaro saman kuncinsa, a hankali yake cizon pink lips ɗinsa haɗi da lumshe idanuwanshi.

“JAZZ”! Ras Ya ji gabanshi ya faɗi sam bai ji takun tafiyarsu ba, a fakaice Ya zaro hanky daga trouser pocket ɗinsa Ya share ƙwallarsa, Kafin ya ɗago yana kallonsu.

Turai ce mahaifiyarshi tare da Sir mubarak sun shigo gaida baba, jallabiya ce a jikinta ta yafa mayafi akanta, Sir mubarak yana sanye shima da jallabiya ta maza.

Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba ganin damuwa akan fuskarshi

“Jazz lafiya naga kamar idonka ya canza launi”?

Girgiza mata kai yai”bakomai mommy am ok, idona ne ke yi min ciwo, yanzu nike shirin zuwa gida…..” Sir mubarak ne ya katse mashi hanzarinshi.

“Jazz meke damunka ne? Sai kace wani ƙaramin yaro? Idan ba ka da lafiya baka san Hanyar zuwa asibiti bane? Ba za ka je aduba maka idon naka ba”?

Cikin sanyin murya yace”zanje in sha Allah, nagode da kulawar ka daddyna.

Hankalin turai bai kwanta da abunda ɗan nata ya faɗa mata ba, Matsawa tayi kusa dashi, ta ruƙo hannunshi acikin nata

“My Son, ka je gida ka kwanta ka huta, idan muka dawo zamuyi magana” cikin kulawa take yi mashi magana

Amsa mata yai da toh mommy, bayan yayi masu sallama ya kama hanyar fita daga gidan.

Hajiya saratu na zaune saman carpet, sir mubarak yai sallama hannun shi ruƙe dana matarshi, daƙyar ta amsa masu sallamar, A saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ganin ita ta zauna saman carpet su kuma sun Haye saman sofa.

“Yaya mubarak Ina wuni, Ya iyali”
“Lafiyalou saratu, Ya naki aikin ya kuma Iyali”Alhamdulillah” ta amsa mashi

Sir mubarak yace”baba baya nan”? Yai maganar yana bin ɗakin da kallo
Hajiya saratu tace”ya shiga toilet ne, shine yace min Injira shi” sir mubarak Ya furta Okey, ina mijin naki na shigo gidan ban gan shi ba, Ko ya tafi office ne” yai tambayar ne don yasan aikin nasu na Companynsu har Saturday suna zuwa banda sunday and Friday.

“Tun da safe muka rabu da shi, yana shirin tafiya office, bai dawo ba ne”

Ran turai ba ƙaramin 6aci rai ba, ganin hajiya saratu da tayi a ɗakin obinna ya tabbatar mata da cewa Itace silar halin da Jazz ya shiga, batun yau ba tasa ba yi mashi gori.

“Saratu Baki gaishe da Auntyn taki ba” kamar yayi magana da bango, Ta haɗe fuska ba annuri
Da ɗan tsawa Sir mubarak Yace”Saratu baki Ji ina magana bane” sai da ta mula tasha iska tukunna tace”yaya ai bani ya dace in fara gaishe da ita ba, saboda ni ce agaba da ita,” Ran Sir mubarak ya 6aci, zuciyarshi ta motsa, Tsawa ya daka mata har sai da turai ta zabura saboda firgitar da tayi.

“Kada ki kuskura ki bari in sake nanata maki! Nace ki gaishe da ita tunkafin na 6ata maki rai” sanin halinshi yasa ta wurga ma turai harara kafin tace”Ina wuni matar yaya”
Cikin sanyin murya ta amsa mata Lafiyalou.

Fitowa Dattijon arziƙi yai daga toilet, jikinsa sanye da jallabiya, dogon gemunsa kamar ana ƙara mashi tsawo fari fat, fuskarshi ɗauke da murmushi yake binsu da kallo

“Gayu mutanan Allah, wa nake gani kamar turai? Rufe fuska turai tayi da mayafin jikinta, Sir mubarak na murmushi yace”yau surukar taka tazo gaidaka, tun ɗazu da safe tasa naci akan saita shigo, nace tabari mu zo atare”

“Amma nayi farin ciki, ni nasan ɗiyata tana son zuwa duba babanta, kaine dai ka hanata zuwa mubarak, Allah ya kamaka, dama Ana kawo min tseguminka, akan ƙuntata mata da ka ke yi kana yi mata kulle agida”

Ƴar dariya Sir mubarak yai yana faɗin”gaskiya kowaye ya faɗa maka haka baba to ka bincike shi, Ni nasan ma baya wuce Jazz ne, Aiko inda shine yau a headquater zai kwana”

Dariya suka sanya banda hajiya saratu data ɗaure fuska, muryarta aƙula ta soma magana

“Baba dama na shigo ne don in gaishe ka, inaso zan wuce” Ganin tana yunƙurin miƙewa sir mubarak yai saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Koma ki zauna sarkin fushi, indai saboda mune kike ta 6ata fuska yanzu zamu koma gidanmu,” ya ƙarasa maganar tare da kallon Baban nasu, hankalin shi na akan fuskar saratu

“Zamu wuce baba”

“Ban gaji da ganinku ba, ku zauna muyi fira mana” acewar Obinna

“Auta Ya meeting ɗin naku?

Yamutsa fuska tayi”lafiyalou, baƙin har sun tafi, shiyasa na dawo gida”

“Masha Allah,” ya ambaci hakan tare da shafa gemunshi

“Ya shirye shiryen tarbar baƙinmu na gida da zasu zo? Ko kun manta da shagalin da zamuyi ne”?

Sai lokacin Saratu ta sassauta fushin fuskarta jin anzo inda tafi so”A’a baba taya zamu manta da rana mafi mahimmanci agaremu ranar da mahaifinmu abun al’faharinmu yazo duniya,” Kalaman saratu sun faranta mashi ranshi.

Sir mubarak yace”Ai nafi kowa zumuɗin ranar tazo baba, naso ace ni aka ba damar ɗaukar ɗawainiyar duk wani abu da za’ayi a ranar, sai dai kash Hateem yai min kutse, gaskiya ban ji daɗi ba, Haka last time Sharafuddeen ne ya ɗauki nauyin gudanar da shagalin”

Da murmushi akan fuskar obinna yace”ai ba wani abu, dakai da su din duk abu ɗayane awurina, ina matuƙar alfahari da ku, kuma Inajin daɗin yadda kuke nuna mini ƙauna”

Ya ƙare maganar tare da kallo Turai, da zolaya yace”Surukar wannan karon wani kalar wanka zaki ɗauka”? Duƙar da kai ƙasa tayi fuskarta ɗauke da murmushi.

Hajiya saratu tace”anko ne zamu fidda ae, zanyi magana da zahra ɗaya daga cikin matasan Yaran da suka yi mana decoration lokacin birthday din twins, ta ƙware wurin iya tsara anko in yaso ma sai su yi mana decoration ɗin”

Jinjina kai Obie yai’naji daɗin jin haka, nima na yaba da aikinsu, yarinyar da kike magana akanta ai na ganeta ƴar gidan ɗan Iya ce, suna da mutunci mutanan kuma mahaifinta yana yi mana hidima sosai, Yakamata ayi masu magana da wuri, tun da mun shiga watan”

“Insha Allah idan na koma ɗaki zan Kira zahran awaya in sanar da ita, amma baba kowa da kowa zai hallara ko? Dan banason inga babu wani adanginmu”
Sir mubarak yace”dolensu ma su zo ai, ƙwan su da kwarkwatarsu, babu wanda zamu yi ma uziri acikinsu, da na gida nigeria da na ƙasar wajen kowa zai zo, Inyaso mutun zai Iya komawa aranar da yazo don wlh bamu raga ma kowa, just rana ɗaya kacal zamu taya mahaifinmu birthday, banga dalilin da zai hana mutun zuwa ba” a tsanake obinna ke kallonshi, yana matuƙar jin daɗin girmama shi da su ke Yi.

“Ku kwantar da hankalinku, in sha Allah kowan nan su zai zo, munyi waya da lateef da abdul razak duk sun tabbatarmin da zuwansu, dama ni banida matsala dasu, Mutun ukun nanne suka fi shiga busy, sharafuddeen da Hateem inayi masu uziri sosai saboda yanayin aikinsu, to su dinma dai Alhamdulillah sun tabbatarmin da zasu samu damar halatta, hada sauran jikokina owais dai ne bani da tabbacin zai zo ko kuwa, har yau dai bansamu wayarshi ba,” muryarshi da rauni ya ƙarasa maganar.

ta6e la66a hajiya saratu ta yi aranta tace”sai kace wani ɗan gwal duk yabi ya dami kanshi akan owais, kamar shi kaɗai ne jikanshi”

Muryar sir mubarak ce ta fargar da ita daga yin zancen zucin”indai owais ne yana sane da wannan ranar mai muhimmanci, duk mun busy din da zai shiga bazai manta da ranar nan ba, saboda ƙaunar da yake yi maka, don haka ka kwantar da halinka baba, In sha Allah Jikanka zaizo.

Nauyayyar ajiyar zuciya obinna ya sauke, zallar farin ciki ne kwance akan fuskarshi har ya ƙosa ranar ta ƙaraso ko dan yaga Jikanshi daya daɗe yana mamarinsa.

“Baba Ni zan wuce ciki” hajiya saratu ce tayi maganar a yayin da take miƙewa tsaye tana gyara mayafinta.

“Har mun gama magana”? Ya jefa mata tambayar, murmushin yaƙe ta ɗan saki”inaso ne in shiga ciki, namanta na sanya mai aiki ta kaimin abinci, idan naci na huta zan Kira zahran awaya duk yadda muka tattauna da ita zanzo na sanar maka”

Gyaɗa kai obie yai”nima nafi so ki huta autana, ki ci abinci ki ƙoshi idan takama ki kwanta kiyi bacci” dariya ta dan saki tana kallon baban nasu, maganar shi ta tuna mata ƙuruciyarta, shi dai burinshi saratu taci abinci ta kwanta ta huta idan ta dawo daga makaranta, bayason tana aikin wahala.

“Nagode da kulawarka akaina baba, Allah yabar mana kai abun alfaharin mu”

Amasa mata yai da amin, Juyawa tayi ta kalli Sir mubarak da turai

“Ni zan wuce yayana, a huta lafiya” bata jira amsarsu ba, da sauri ta fuce daga ɗakin.

Bayan fitarta, tattaunawa suka cigaba da yi game da yadda za’a tsara komai na shagalin da za su yi.

Tun da ta shigo ɗakin, komai na ciki agyare ta same shi, Safa ta kawo mata lunch ɗinta yana asaman table ta ɗaura mata shi.

Cire lapcoat din jikinta tayi a saman Hanger ta sagala ta, shaf shaf ta canza kayan jikinta zuwa, rigar shan iska, daga bisani ta koma gefen gadon ta, ta zauna domin cin abinci, farawa da bismilla ta kai hannu ta damƙi haɗaɗɗan cup na cofee ta kur6e shi, bayan ta gama ta soma shan farfesun naman kaza da zafi zafinshi, cikin ƙanƙanin lokaci ta shanye shi ta kuma damƙar Chips ta cinye ta cakumi cheese burger ta tura abaki hankalinta kwance take cin abincinta.

Ringing ɗin wayarta ne ya janyo hankalinta ga duban hand bag dinta dake ajiye saman pillow.

Ba ta yi niyar ɗaga kiran ba, don ita a ƙa’ida bata picking call idan tana cin abinci saita kammala, hakanan dai tayi ra’ayin duba me kiranta, tissue ta yaga ta goge bakinta, kafin ta yunkura ta ruko handbag din, duba sunan me kiran nata tayi sunan ya fito 6aro 6aro asaman screen ɗin iphone ɗinta

*Princess Mujeedat* murmushi hajiya saratu ta saki da zumuɗi ta ɗaga kiran cikin harshen turanci ta soma yi mata kirari

“Uwargidan shugaban ƙasar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa! Sarauniya ɗaya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ƙari mun kulle ƙofa” sautin ƙayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya karaɗe kunnuwan saratu, da alama taji daɗin yabon da saratu ke yi mata.

bayan ta gama yi mata kirarin ta ɗaura da cewa”Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem ɗin baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke” (idan kaga hajiya saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba ƙaramin mutun bane, babban gorone magogin ƙarfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da kalar yadin)

Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice ɗinta zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arziƙi waɗanda suka gaji abun, da izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata.

“Ba abun da ki ke tunani bane ƙanwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma na kira don mu gaisa” itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa.

“Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka ƙasarmu” fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana.

“Naji daɗin kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ƙara godewa Allah daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, haƙika ban ta6a danasanin auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ƙarƙashin inuwa ɗaya har Allah ya azurtamu da samun zuri’a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna nuna min ƙauna sosai nima Ina sonku”

Hajiya saratu baki yaƙi rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta ƙarasa haɗiye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya.

“Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu ƙanwata baki daina ciye ciye ba ko”? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta sai ƙara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara neman izni ba to bata ɗaga kiran nashi.

*A GIDAN ƊAN IYA*

Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su ɗan ƙara kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu cewa Ai sun samu gidan da zasu zauna a abuja ya 6oye ne bai sanar dasu, harma ya samu aiki a companyn sharufuddeen, ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba sun tayashi murna sosai, musamman da suka ji cewa bazasu raba Aneelerh da junaid ba ko da yakai shekarun da zasu Iya kar6ar shi ne, Zasu haƙura ne har Allah ya bayyanar masu da su Uzair, dama rashin ɗan nasu ne yaja har suke son kar6ar shi, Aneelerh hada kukan farin Ciki, Ta ƙara jin son surukan nata, ba ita kaɗai ba hatta su mami sun ji dadin ziyarar da suka kawo masu sun kuma jinjina ma ƙoƙarinsu na barma Aneelerh ɗanta, su kansu sun fahimci ba ƙarami so suke yima yaron ba tun da gashi ta dalilinsa sun dawo abuja da zama, ba su kai ga barin gidan ba, abie ne ya dakatar da su yace su ɗan jira akwai malaman da zai sanya su yi masu safkar alƙur’ani a sabon gidan su, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, don su basuyi tunanin yin hakan ba.

Hankalin Mahboob yaƙi kwanciya tun da yayi tozali da hoton Angel, a daren ranar daƙyar Ya iya runtsawa, saboda fuskarta da ke yi mashi gizo, ya kwana da mamakin baiwar Kyan da Allah Yayi ma yarinyar, bai ta6a ganinta ido da ido ba sai dai ahoto yasanta tun tana ƴar ƙaramarta, Aneelerh take ɗaukar ta hoto da video tana sanyawa a status dinta to anan yasanta, a ƙarshe daya gaza haƙara bayan sun dawo daga sallar asubahi, ya lalla6a yaje ɗakin aneelerh, tsabar Iya fadanci hada Kiranta da aunty, bai ta6a kiranta hakan ba sai yau da Allah ya jarabe shi da son sanin komai dangane da Angel.

Tambayoyi ya tsare Aneelerh da su akan ta fada mashi dagaske yarinyar mutunce bata haɗa jinsi da aljanu ba? Don shi gaskiya bai yarda da kyanta ba, Ya zarce na jinsin mutane, tun da yake kallon indian film, da korean drama bai ta6a ganin jarumar da ta kama ƙafar Yarinyar a kyau ba.

Aneelerh taci dariyar wautar Mahboob, har tambayar shi ta yi ko dai sonta ka ke yi ne? Naji kanata zuzuta kyawunta, ” da sauri ya dafe ƙirjinshi da hannu Yana faɗin”Sai kace dai bani da hankali aunty Aneelerh? Ae rijiya ba wurin gaɗar makaho bane, Nasan ciwon kaina ban shirya yin jinya a gadon asibiti ba, ni kawai kyanta ne ya ruɗe ni ba wani abu ba, tsakani da Allah yarinyar ba matar yaku bayi bace, ko makaho ya shafa fuskarta zai shaida hakan tafi dacewa da Manyan ƴa’ƴan masu kuɗi waɗanda suka jiƙe da naira, ni yanzu idan nace zanso ta, ko zan aureta, Aunty Aneelerh ina zan samu kuɗin ɗaukar ɗawainiyarta? Kuɗin man shafawarta dana zuwa saloon kaɗai sun isa su takaita jarin mutun balle ni da ba kuɗi gare ni ba”

tsabar dariya Aneelerh hada hawaye, shiko fuskarshi a daure yayi mata maganar bada wasa ba, ya ƙara da cewa”ƙwara na auri ƴar talaka wadda ba ta da tsayin gashi, sai yafi min sauki, in manna mata ƴar naira ɗari biyar taje gidan kitso ayi mata, man shafawa a jiki kuma Ko vaseline na siya mata ya wadatar, Iya kuɗin ka iya shagalin ka, Amma wannan Ifritun yarinyar wlh aunty Aneelerh duk talakan da ya aureta ya cuci rayuwarta, yasin ni har kotu zan Iya kai ƙarar shi, ita kanta idan ta auri talaka batayiwa kanta adalci ba fisabilillahi.

Lamarin mahboob sai addu’a, Haka ya dinga santin kyan Angel, Har faɗi yake shi ya kosa A gano su, in sha Allah zai tayasu da addu’a akan Allah ya bayyanar dasu, burinshi idan Allah yasa ta dawo gidansu da zama zai zama na hannun damanta saboda idan ta auri basarake ko wani mai ji da naira, ya dinga samun ƴan canjin kashewa.

Saboda Angel Ya manta da zancen neman zoben shi, gaba ɗaya ya ɗaura burin duniya akan Angel, harya fara ƙiyasta kuɗin da zai tatsa wurin Mijin da zata aura.

Daƙyar Aneeleerh ta samu mahboob Ya fita daga ɗakinta, ya addabeta da zancan kyawun Angel.

Alhamdulillah, a yau labarin 6acewarsu Angel ya dawo tamkar sabo a shafukan sada zumunta, ta ko’ina buga labaransu Akeyi tare da hotunansu, tun da Ont suka fara yaɗa labarin nan take sauran gidajen jaridu suka bubbuga labaran da gidan radio. Ta ko’ina zancen su akeyi kamar yau abun ya faru, labari ya dawo sabo, Yanzu shine Top story dake trending a social media, mafi yawan mutane Kyawun Angel ke ruɗarsu har su kaiga ɗaukar labarin su karanta sannan suyi share ɗinshi don ataimaka a gano su.

Fuskar Aneelerh tun safe da annuri akanta, Mutane sai kiranta sukeyi awaya sunayi mata jaje haɗi da tambayarta wasu bayanai da suka danganci Angel, a ƙarshe sunayi mata fatan Alkhairi, Numbobinsu ne akan labaran da akayi share nasu shiyasa mutane ke ta kiransu suna yi masu jaje.

Ta natsu saman mirror chair, turkish gown ce a jikinta launin maroon tayi bala’en yi mata kyau, babu mayafi akanta zallar sumar kantace
Hannunta na aruke da wayarta, tun ɗazu take maimaita karanta labarin su Angel da akayi posting ɗinsa a shafin Ont na insta

“Mommy” muryar junaid ce ta janyo hankalinta ga kallonshi, ta cikin mirror, Hajiya adama tayi mashi gayu don yau ma a ɗakinta Ya wuni, ita tayi mashi wanka, tasa Aneelerh ta kawo mata kayan shi ta santa mashi jeans da shirt fara, sumar kanshi tasha gyara.

Ƙarasawa yai gaban kujerar da take a zaune, ya daura kanshi saman laps ɗinta, ƙamshin turaren jikinsa na Hajiya adama ne da ta shafa masa
‘Wow my baby boy, kayi min kyau sosai, lallai granny ɗin nan taka tana matuƙar sonka irin wannan gayu haka da tayi maka”

Ɗaura wayar tayi gaban mirror, ta sanya hannu biyu ta ɗago da junaid ta ɗaura shi saman laps ɗinta, langwa6ar da kanshi yai saman kirjinta

“Mommy namanta ban faɗa maki ba, jiya wani mutun ya kira awaya har yace wai in faɗa maki….” katse shi tayi”yaushe aka kirani? Bana son ƙarya fa”
Muryarshi da shagwa6a ya ce “mai ƙarya fa ɗan wuta mommy, ni dai Allah ba ƙarya nake maki ba” miƙa hannu Aneelerh tayi ta ɗauki wayar, tana shiga call logs tayi arba da New number da aka kira kuma an ɗaga kiran.
“Junaid bana hanaka ɗaga min kira ba”?
Zumbura mata maki yai’to ai nayi tunanin Angel ce ke kira, kuma baki a ɗakin shine na ɗaga, kuma yace in kai maki wayar ku yi magana ni kuma naƙiya nace sai dai ya faɗamin in gaya maki” tun da ya fara magana ta ƙura mashi ido tana kallon shi, komai nashi burgeta yake yi, musamman in yasanya shagwa6a a maganar shi.

“Meyasa baka kawomin wayar ba”?
Ƙura mata ido yai ba tare daya furta kalma ba
Sam hankalinta bai kwanta da baƙuwar number da ake yawan kiranta da ita, tuntuni take ganin missed calls daga Number taƙi yarda ta ɗaga kiran don har yanzu bata daina fargabar mutanan nan da suka ɗauketa da sunan jami’an sirri.

“Junaid, daga yau karka kuskura ka ƙara ɗaga min kira kaji ko”? Ɗaga mata kai Yai alamar eh, tace”yanzu zan sanya number ɗin a black list, hankalina zaifi kwanciya’ ta yi maganar a yayin da take cigaba da daddana wayar hannunta, blocking number din tayi saida ta kammala baby junaid yace
“Mommy namanta ban gaya maki ba yace wai in faɗa maki daddyn um am….” natsuwa ta yi tana kallon shi,
“What”? Shine yace min wai ince maki daddyn ummm…” sam ya kasa tuna sunan duk ta ƙagara da sonjin ƙarashen sunan
“Kai nake sauraro ka fadamin mana”
“Wai ma daddyn…..” girgiza kai ya ɗanyi”mommy kaina ya cunkushe na manta, idan na tuna zan gaya maki”

Murmushine shimfiɗe saman la66anta, Idanuwanta akan face dinsa

“Shikenan My baby boy, yanzu faɗa mun Ina ka 6oye zoben Mahboob? Na duba cikin rigar pillow ban ganshi ba, yakamata mu maida mashi abunsa kada ayi mana kallon 6arayi”

Gatsina mata hanci junaid yai haɗi da murmura idanuwanshi yace”tab ae Allah bani bashi, Na angel ne na 6oye shi wani wuri inda ba wanda ya sani, Allah Angel zan baimawa shi, kuma kada ki fada ma kowa in baki so mu 6ata dake,”

Dariyace ƙumshe abakinta”kai junaid babu kyau fa, da guminsa ya sayi zoben taya zaka ce ba za ka bashi ba? Kana so Angel ɗinka ta sanya abun sata? Kayan haram da ba mallakin ka ba?
Girgiza mata kai yai”a’a mommy, to ai bani da kuɗin da zan siya mata wani”

Shafa sumar kanshi tayi”mommynka tana da kuɗi, zan siya maka wani but pls ka maida ma mahboob zoben shi kaji my boy”

Ɗaga mata kai yai”Toh zan maida mashi badan halinshi ba, kuma Allah idan ya ƙara cinye min chocolate ɗina saina sanya shi kuka” fashewa Aneelerh tayi da dariya, ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.

*DAULAR ALHAJI MUSA*

Ya kasa fita ko da ƙofar ɗakinsa ne, tun jiya da ya zo gidan baƙunta yake yi masu, fitowa yai daga Cikin bathroom jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, ya ɗaure igiyarta a tsakiyar cikinsa daga can ciki akwai short da ya sanya, sumar kansa ta manne ma fatarsa saboda lemar ruwan wankan daya jiƙata, Dr shureim ba dai kyau ba, ta ko’ina sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikinsa, ya ji daɗin dawowarshi gidan uncle ɗinsa baida wata damuwa, musamman tarbar da ya samu awurin Hajiya sarah, ta nuna farin cikin ganinshi kamar ɗan cikinta haka take tarairayarsa.

Walking slowly ya nufi dressing mirror Don Ya kimtsa kanshi

Gyaran muryar da aka yi mashi ne yasa shi yin saurin juyo wa baya don ganin wanene

Lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya yana kallon uncle ɗin nasa
Yana daga tsaye bakin ƙofa, kayan gym ne a jikinsa, short da riga sun ɗame jikinsa, mutumin akwai ƙira kamar ɗan wrestling.

Da fara’a akan fuskar shureim ya furta”My Uncle” yai maganar yayin da yake tunkarar shi, gabanshi sai faɗuwa yake yi ya rasa gane dalilin dayasa a duk lokacin da ya yi tozali da uncle din nashi sai yaji faduwar gaba.

Kyakkyawar fuskar Alhaji musa, mai ɗauke da ƙayataccen saje, ba murmushi sai dai yaɗan sakar mashi fuska.

“Fushi nakeyi da kai shureim baka iya takowa kazo ɗakina ka gaishe ni, ko dama jira kake inzo room ɗinka”? Cike da izza da nuna isa yake yin maganarsa.

Yawu shureim ya haɗiya”ba haka bane uncle, yanzu nake ƙoƙarin zuwa part ɗin naka”

Yamutsa fuska Yai”okey, nima na fadi ne kawai ba don wani abu ba, ko akwai abun da ka ke buƙata”?

Girgiza kai shureim yai”a’a aini ka gama min komai kawuna, nagode sosai da kulawarka agareni, Allah yabarmun kai” matsawa Alhaji musa yai dab dashi, Ya janyoshi a jikinshi yai hugging nashi tightly, in a whisper ya furta”idan akwai abun da kake buƙata ka sanar dani, idan ma baka Iya fadamin ka tura min ta text message, sannan akwai saƙo da za’a kawo maka zuwa anjima, ya ƙarasa maganar tare da raba jikinsu daga na juna.

Still face din Uncle musa ba fara’a, haka Allah ya halicce shi baida sakin fuska.

“Nagode sosai uncle, tun jiya da nazo gidan nan akayi min kyakkyawar tarba naji daɗin Hakan sosai”

“Shureim ba’ayi min godiya, next time kada ka ƙara” fuskarsa a ɗaure yai maganar
Cikin jin shakkar shi shureim ya furta”in sha Allah” ya ƙara da cewa”burina ka canza rayuwarka shureim, banason ganinka acikin damuwa, kaman ta duk wani abun da ya faru a rayuwarka, shiyasa na dawo dakai gidana saboda nasan zaka fi samun kwanciyar hankali, sannan Inaso naji ra’ayinka, bance ka bani amsa yanzu ba, nafi so sai ka natsu kayi nazari tukunna.

Jinjina kai shureim yai, idanuwanshi na kallon ƙasa, saboda ƙwarjinin alhaji musa bai iya jurar kallon fuskarsa.

“Bazan hana Ka Yin duk wani abu da za ka yi don jin daɗin rayuwarka ba, sai dai ban goyi bayan zamanka a cikin gida ba aiki ba, abu na biyu kuma Aure, kasan shi sunnah ce ta manzon Allah SAW, Aure yana ɗaga darajar mutun yazamto mai cikar kamala da natsuwa, rayuwarka zata canza idan ka yi aure, Na gaji da ganinka a matsayin tazuru” Yai maganar yana ɗaga mashi gira, da zolaya akan fuskarshi, kunyace ta hana shureim furta komai, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, Yana jin nauyin uncle din nasa.

“Da ace kayi aure da wuri da yanzu mun samu ƙaruwar babies” da sauri shureim Ya juya mashi ƙeya ya rasa ina zai tsoma ranshi, hakan da yai ba ƙaramin nishaɗi yaba kawun nashi ba
“Zeenatu ta shigo kun gaisa”? Muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mashi da”eh jiya tazo”

“Okey, pls, shureim inaso kana taimaka mata, Kuna fita yawo atare, still ƙanwar taka bata canza ba, sam bata da natsuwa, ni ban ta6a ganin mahaddaciyar ƙur’ani mara natsuwa irinta ba, zaka ga duk min rashin natsuwar mutun indai yana yawan karanta al’ƙur’ani natsuwa na shigarshi amma ita kullum abun nata ƙara gaba yake yi”

A hankali shureim Ya juyo ya kalle sa, mamakine ƙarara akan fuskar Shureim wai yau shine kawu musa keyi ma magana har haka? Mutumin da bai Iya surutu ba.

“In sha Allah uncle, zanyi ƙoƙari wurin ganin na taimaka mata, ” gyaɗa kai yai”haka nakeson Ji, Ni zan shiga Ciki, idan ka yanke shawara game da abunda na faɗa maka, ka same ni a ɗaki ka sanar dani ko kuma ka kirani awaya”

Amsa mashi yai da toh, sallama Uncle musa yai mashi kafin ya fuce daga dakin

Ajiyar zuciya shureim ya sauke, hannun shi ɗaya dafe da ƙirjin sa.

Lokaci ɗaya zuciyarshi ta fara tariyo mashi haukan zeenatu na Jiya, murmushin gefe fuska ya saki, aranshi ya ayyana ko ta na ina yanzu, yasan zai yi wuya ta jure rashin ganinshi.

Ai tun Jiya data bar ɗakinshi Cikin sanɗa ta nufi ɗaki akan hanya suka ci karo da Tani, Abunka game saurin kuka nan take ta ƙware mata baki tana kuka ta faɗa mata abunda ya faru

Lallashinta tani tayi tana fadin to menene aciki, Ki kwantar da hankalinki dr shureim dai ɗan uwanki ne ba wani bare ba, yanzu bari na baki mayafi na ki ɗaura a qugunki, ni kuma zanje ɗakin nashi in ɗauko maki zanin, Ai mantawa nayi ban baki undy kin sanya ba jiya, ke kuma baki tuna min ba,”

Cikin shessheƙar kuka take faɗin Na tsani kaina Tani, bani da hankali, sai yaushe ne zan daina hauka, sam bani da natsuwa, meyasa na kasance haka”? Cikin kwantar da murya tani tace”karna kuskura na ƙara ji kince haka, in banda abunki ma, meye na damuwa?, Haka Allah ke son ganinki, don haka ki share hawayenki, ai ni wlh ba ƙaramin burgeni kikeyi ba saboda kina da hankali, dayawa wasu ƴa’ƴan masu kuɗin basa girmama ƴan aikinsu amma ke kin ɗauke mun tamkar iyayenki, shiyasa nake ƙara ƙaunarki”

“Tani ba zaki gane ba, ni duk ba wannan ba, Yaya shureim bazai ta6a ɗauka na a matsayin mace ba, idan har ban daina wannan haukan ba” tsabar kukan da takeyi make up din fuskarta ya ca6e mata, jan bakin har saman kumatuntu.

Ɗaura mata Mayafi Tani tayi asaman waist dinta, tace”ki koma ɗaki, zan shigo muyi magana” ta amsa mata da toh, ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
A daren ranar daƙyar Tani ta lallasheta, ta kwantar mata da hankalinta akan tadaina cewa ta tsani kanta saboda yarda Allah ya halicce, kowa da irin tashi ƙaddarar, bawa bai ta6a zama 100% batare da an samu naƙasu atare da shi ba. Sannan Idan saboda yayanta shureim ne takeyin kuka waya fada mata rashin natsuwarta zai hana shi sonta? Wata’ƙil ma haukan nata ne zai ƙara mashi ƙaunarta, don shi so babu ruwan shi da yanayin mutun abu ƙalilan ke haifar dashi indai mutun ya kasance ƙaddararka.

Kafin Tani tabar ɗakin sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali tukunna ta fuce, tsakar dare Zeenatu ta farka, ta shige toilet ta ɗauro alwala kamar yarda ta sama tashi yin nafilfilin dare, yawanci addu’arta duk akan Allah ya bata natsuwa take yinta, abun yana damunta.

(Abunda Ya faru a daren Jiya kenan bayan zeenatu ta baro ɗakin Dr shureim)

Tun safe baiwar Allah taƙi fitowa daga ɗaki, tarasa ya zatayi, kunyar duniya ta ishe ta, aƙarshe ta janyo al’ƙur’ani ta cigaba da karantawa, har rana ta fito tukunna Ta ajiye shi ta shiga bathroom tayo wanka, ta fito ta sanya doguwar riga ta zura hijabi maroon har kasa, ko make batayi ba, cikin sanɗa ta fito daga ɗaki tana tafiya tana waige waige kamar wata munafuka, a haka ta ƙaraso part din daddynta.

A lokacin bai jima da fitowa daga wanka ba, tun bayan da ya baro room din shureim, Ya dawo nasa ɗakin, Jallabiyace a jikinsa launin milk mai kyan gaske, Yana daga kishingiɗe saman doguwar sofa ta cikin katafaren ɗakisa, tsayawa zayyana kyawunsa 6ata baki ne hankali ma bazai ɗauka ba.
Ya ɗaura kansa saman pillow, Yayin da apple laptop ɗinsa ke a saman flat tommy ɗinsa.

Idanuwanshi suna a lumshe ya natsu yana kallon wani abu a laptop din nasa, ga dukkan alamu video call ya ke yi, sautin muryarshi baya fita yayi low sosai, yana magana eyes dinshi suna lumshewa.

Kusan sau Uku zeenatu tana ƙwala mashi sallama baiji ba, saboda hankalin shi baya atare da shi.

Tasan baison ashigar mashi room batare da an nemi izininsa ba.
Jin shiru bai amsa mata ba, Yasa ta haura ƙafa ta shiga ɗakin tana tafiya babu natsuwa sai faman zumbula sauri take yi burinta kawai ta ƙasa gare shi, duk da fargabar shi da take ji.

Cikin rashin sa’a, garin sauri hijab ɗin ta da ke ja da ƙasa Ta harɗe ƙafarta ɗaya, wani irin sul6i ne ya kwashe ta, gaba daya ta rubza saman Sofa table din gabanshi, wanda ke ɗauke da Cup na coffee mai zafi da aka ajiye mashi, gaba ɗaya Cup din Yai tsalle Ya fada mashi ruwan ya wanke Laptop dinsa da gaban jallabiyarshi, zeenatu kuwa tunda ta kife saman sofa table din bata ɗago ba, jikinta sai kakarwa yake yi hankalinta idan yai dubu to ya tashi, zufa ta ko’ina take tsastsafo mata, duk da sanyin A.c ɗin ɗakin. ko gizau baiyi ba idonshi akan keyboad ɗin laptop nashi da ruwan coffee ya jiƙa, Tashin hankalin da ba’a sama shi data

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button