Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 51-52

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*51&52*

 

……..wani irin harbawa zuciyar Amaan tayi”tana jin wani irin tsananin farin ciki da nishad’i marar misultuwa A ranta”da sauri tasaka tafikan hannayenta ta b’oye fuskarta dasu tana murmushi me ban sha’awa”yayinda mutumin naku ya gyara zamansa yatsura mata Ido”tun daga fararen y’an duma duman k’afafuwanta har zuwa kanta”duk yake bi da wani irin mayataccen kallo”yana jin komai nata yamasa “saima sannan ya lura da pasincap d’insa daya bata had’e da suwaita d’in sa dasuke Ajikinta”ya sauke Ajiyar zuciya yana jin hankalinsa yad’an kwanta domin Alamomi sun nuna Amaan tashi tana sonsa kenan”cikin k’asa da murya yace”labarin zuciya Akace A tambayi fuska ko?”I’m very happy dabaki wahalar dani ba wajen jamun Ajinku na mata”saidai Allah ki bud’e mun fuskarki ki Amsa mun da bakinki kinyi accepting d’in soyayyata ko kuwa??….itadai tana murmushinta still fuskarta Ab’oye da tafikan hannayenta”Amaan! yakirata cikin k’asaitacciyar muryarsa da yau tafi kullum yima Amaan dad’i “uhmm! kunyata kikeji ne?”uhmm”to kina sona?”uhmm uhmm! hmm nasan wasa kikeyi ko?”tayi shiru”kinji?”inafa sonka”kuma nidai babu wacce kake waya da ita ko?”ta fad’a tana tsuke d’an bakinta”duk yana kallon ta ya kauda kansa”yana tunanin kamar da gayya take turo masa baki”bayan babu Abinda ke yawan burgesa da ita kamar irin tana turo baki ko shagwab’a….hamma kayi mgn mana”ta fad’a cikin shagwab’a tana janye hannuwanta”uhmm sbd kishi kin janye hannuwan naga fuskar”Amma d’azun kina jin kunya”to yanzun kishin yakori kunyar ne?”k’asa mgn tayi “yaci gaba dacin dambun naman da snacks d’in yanata kallonta”Ahankali yace”bayan ke babu wacce nake waya da ita saidai ko akan Abinda yashafi Aikina ko kasuwancina”Asalima bayan ke ban tab’a tsayawa nayi mgn data wuce minti biyar da wata mace ba”ki d’auka sbd ke Aka halicci fahad shariff”daga ke kuma yasaka key ya kulle zuciyarsa insha Allah”nasan mata da yawa sunada zafin kishi saidai nasu shirmene “maza munfi ku zafin kishi”ki tsaya kiyi tunanin yawan fushin dana keyi dake Abaya da hanaki kula duk wani namiji ,ko zuwa duk inda wani namiji yake meye dalilin hakan??toba kishi bane”yayi y’ar dariya yana fad’in na fiki kishi Amaan kawai ki kiyaye Abinda zai tadomun shi”to hamma dani zaka tafi ko?”d’an murmushi yayi Aransa yace”har yanzun dai Akwai k’uruciya atare da ita” Afili saiya girgiza kansa yace”ah ah nan zan barki saidai bada jumawa mutane da yawa zasu kaimunke Amatsayin matar Aurenah”rufe Ido tayi tana murmushi tace”nidai ba yanzun ba “ba karatu zan idaba”shi wancan wawan daya kawo kud’in gaisuwarshi ya Amsa meyasa bakice karatu zaki yiba?”yafad’a yana d’auret fuska”to Ai saura wata ukku na Ida yanzun ko?”kima hutar da zuwa ko kuma idan zaki iya kije ki Ida sbd ki Amshi takardunki” Amma ko kin gama karatu ba Aiki zakiyiba kinga beda Amfani karatun ko?”nidai fa yanada Amfani tunda nasan wasu Abubuwan”hakane kuma”to hamma meyasa zakace bazanyi Aiki ba?”banida tsarin nina fita nema matata ma tafita”sannan zuciyata zata dinga zarge zarge”ba’a kuma son Aure da zargi sbd yana lalatashi”namaga take takenki kamar bakya son Aure nah ko?”nidai hamma Adena maganar”shikenan tunda baki son ki zama surukar Ammi wata kikeso tazama ko?”kallonsa tayi ta banko masa harara”yayi murmushi yana fad’in kinyi kyau “saita kauda kanta gefe”yad’an murmusa yana d’aukar robar lemon yazuba acup yana fad’in gaskiya snacks d’in nan sunyimun dad’i idan zamu wuce gobe kimun naje dashi gida “dama ko baka ceba zan bayar a
Akaima Ammi”shifa d’an Aiken ban dashi?”Eh mana” dukda banice nayiba mommy ce tayi shi “ke kuma kina zaune ko?”yafad’a yana kurb’an lemon”ah ah natayata dayake kasuwancin datakeyi kenan”tanada masu yimata Aikin na biki ko suna idan Anbata”gaskiya yayi mun dad’i sosai”wai hamma da gaske gobe zaka tafi?”uhmm”yanzun dan Allah yaushe har muka gaisa dakai da zaka tafi ka barni?”inada Ayyuka SALFAD shiyasa…kukan shagwab’a tasaka tana juya masa baya”ya Ajiye cup d’in yana matsowa dab da ita cikin wata iriyar murya ce fad’amun yakikeso Ayine?Adaidai nan mus’ab ya shigo da sallama”ya kallesu yana murmushi”sai Amaan ta Amsa ta tsaya da Abinda takeyi ta mik’e tsaye”Ina zakije salfad?zanje ciki nadawo”okay karki jima kinga magrib yakusa ko?”batayi mgn ba tafita”mus’ab ya zauna gefensa yana fad’in wasa tare ci baban? tab’e baki shariff yayi yace”kanaso kaci katafi kana soyayya “kaime ka tsayayi ne?”kaga idan zakaci kaci kona Ida sbd yayi mun dad’i “mus’ab yazuba ruwan yasha kafin yafara da dambun naman”shariff yace”inaga nifa sai jibi zan tafi”meyasa?”Amaan tak’i yadda naga kamar tamayi fushi”dama kafin ka shigo tanamun k’orafin wai duka yaushe muka gaisa dazan tafi?”to bama wannan ba kasanar mata dalilin zuwanmu?”nasanar mata mana ta kuma Amince “inaso idan daddy yadawo muka gaisa kamasa zancen yaushe zan turo Ayi mgn?”dariyar shakkiyanci mus’ab yasaki kafin yace”YAU DA GOBE kenan! dama Aure da mutuwa da haihuwa duk lokacine”da lokacinsu yayi babu fashi”Amma saurin me kakeyi haka?banza shariff yamasa yak’i mgn “mus’ab nata shagalinsa can yace”hmm ! Ina tausayin yarinyar nan taje hannunka”wajen mefa?”kafini sani”shariff yatab’e baki yana mik’ewa tsaye yace”idan kagama kasameni can cikin gidan mu wuce”wai kana manta kai surikine ? irin wannan rashin kunyar da kakeyi yayi yawa”banza shariff yamasa yafita”yana fita Amaan na kawowa zata shigo rik’e da tray babba da warmers d’in Abinci Asama”hamma Ina zakaje?”ta fad’a tana sunkuyar da kai bayan sun had’a Ido dashi “daurewa kawai tayi ta rik’e tray d’in dan jikinta babu k’arfi sbd kaifin idanuwan shariff dake yawo Ajikinta….cikin gidan zan biyoki tunda nagaji da jira”Amma meye kuma kika kawo?”Abinci ne hamma”bana son hamma”kodai kice salfad kovkuma ki canzan suna”yafad’a yana d’age gira”Amaan na k’ok’arin mgn taga diran mutum gabansu”ta d’ago kanta suka had’a Ido da nasir yana binsu da wani irin mugun kallo “shariff ya had’e rai yana nunama Amaan k’ofar parlourn”Alamar ta shiga”K! ki tsaya inason mgn dake”banza ta masa kamar ma bada ita yakeba ta wuce ciki”shariff na tsaye ya had’e girar sama data k’asa Alamar no mutunci”saidai kallo nasir be isheshiba”sai Akayi sa’a sadeeq yadawo yana rik’e da wayar Amaan a hannunsa”har zai wuce saiya lura dasu”hakan yasa ya k’araso sbd d’azun dazai fita sun gaisa da shariff”k’arasowa yayi yana kallon yaya Nasir yana mamakin tsayuwar meyakeyi Awajen? saiya basar yana fad’in yaya shariff sannu da fitowa badai tafiya ba? “ah ah sadeeq kadawo ne?tsaki Nasir yaja yana fad’in banzaye masu son Abin duniya”ka kwaso jiki kazo kanata wani washe hak’ora…sadeeq na k’ok’arin mgn Amaan ta fito daga cikin parlourn”yayinda shariff ke sauraren komai yana danna waya yana fatan Allah yasa Nasir yashiga gonarsa”Anan zai tattakashi yasaka arufesa ta haka kawai zai gane shayi ruwane….mlm lafiya zaka mana tsaye har kana wasu maganganu dabasu kama taba?cewar Amaan cikin k’arfin hali”ke k’aramar kunya! dama ke nake jira ki fito”Ina miki mgn yasaka kin wuce sbd yana Aurenki ko? to nayi total d’in Abinda na kashe miki saiki biyani”ki k’arata dashi dayake hure miki kunne muga zaya iya Auren naki ne…..tun kafin ya rufe baki shariff ya matso gabansa ya turashi da k’arfi yana huci cikin kausasa harshe yace”Amaan tafi k’arfin wani banza ya wulak’antata indai Ina numfashi Adoron duniya!”tir da irin zumuncinka”kaine mitsiyaci kafad’i ko nawane abiyaka?”dukda nasan ba rok’wanka tayiba”yafad’a da wani irin tone”Adaidai nan mus’ab yafito daga cikin parlourn sbd hayaniyar daya fara ji”nasir yagyara wuyan rigarsa yana huci k’asan zuciyarsa yana jin tsananin shakkar shariff “Amaan kuwa kuka ta fashe dashi sbd ganin Nasir na neman kunyatata itada iyayenta….ka fad’i ko nawane nace! cewar shariff cikin d’aga murya “wai meya faru Abokinah?”pls mus’ab kabarni dashi kawai”Nasir na tab’e baki yace”naira Millon 3 ne….wlh k’arya yakeyi yaya shariff cewar sadeeq dake tsaye yana kallon komai”mus’ab na dariyar rainin hankali yace”Ashe kai talaka ne! na d’auka Millon d’ari biyar zakace? Afusace shariff yazaro baby Nokia nasa ya wurga masa Ajikinsa yana fad’in ka rubuta acc details naka za’a baka Millon 100 kaine mitsiyaci ba itaba”inaso kasani gobe goben nan bazan bar garin nan ba saida saka ranata Akanta… yafad’a cikin zafin zuciya yana jin kamar yafara suburbud’an nasir….bazai yuyuba yaya shariff! Abashi Millon ukkun da yayi k’arya sbd son ya kunyata Amaan”wacce badan tana tawaba zan yabeta ,bata tab’a cewa yaka mata wani Abuba”daka mallaka masa million 100 gara ka bayarwa mabuk’ata zasu dad’i…..meke faruwa haka nakejin hayaniya? sukaji muryar daddy Abayansu Adaidai lokacin da Amaan ta fashe da kuka ta wuce ciki da gudu”Nasir nata shan k’amshi ya matso ya mik’ama mus’ab wayar yana fad’in na rubuta account d’in idan yacika d’an halak yatura 100 million d’in….wani zazzafan mari me rai da lafiya daddy ya d’auke Nasir dashi”Azuciye Nasir yadafe kunci yana huci yace”karka koma marina”sbd ka koma wlh saina ram….be rufe bakiba shariff ya fincikosa yana bashi zafafan puncher’s kota Ina”daddy ya girgiza kansa yace”Allah yayi maka Albarka shariff, Amma ka k’yalesa iya haka….dole saiya saka An rufesa confirm ne daddy”sbd yamaka rashin kunya! cewar mus’ab na kallon yadda sharif ke dukan Nasir”gaba d’aya fuskarsa tayi kumburi hancinsa yafashe”Amma sbd taurin rai k’ok’arin ramawa yakeyi,saidai k’arfinsu ba guda ba”jikin shariff ya horu da exercise….saida daddy yakoma yiwa shariff mgn sannan yabarsa yana huci yanufi get yana danna waya”yayinda sadeeq ke korama daddy bayanin yadda Akayi shida mus’ab”oh innalillahi wa inna ilaihir raju’un!! wace irin fitinace wannan?”dana san hakan zai faru da tuni ban Amince da nasir ya zab’i Salma ba Amatsayin Abokiyar rayuwarsa”kuyi hakuri mus’ab kuma bance kubashi ko sisiba”nine zan biyashi”iya Abinda nasani har gobe yana nan a matsayin d’ana”rashin kunya idan yamun shima wata ran za’a masa”bara na wuce naga salma d’in”kafin mus’ab yayi mgn saiga police sun shigo tare da shariff fuskarsa bbu walwala yanuna musu Nasir dake kwance yafara fita hayyacinsa”babu b’ata lokaci suka kamashi suka fita dashi”mus’ab ya k’araso yana fad’in muje muyi sallah daddy nacan zai rarrashi Amaan “kayi hak’uri zuwa gobe kasaka Asakesa tunda dai nasan ya gane kuransa,kuma kaga d’an uwantane”danginsu zasu iya ganin laifin daddy dakai”zancen biyan kud’i daddy yace ka k’yalesa shine zai biyashi”k’in mgn shariff yayi sbd ya riga ya hau kan dokin zuciya”hakan da mus’ab ya lura dashi yasaka ya k’yalesa suka wuce masallacin Anguwar…..
da kuka Amaan ta shigo cikin parlourn su”mommy dake zaune tana Azkhar ta bita da kallo gabanta na fad’uwa tace”ke lafiya wani abu yafaru ne kike kuka??”keda Abin kuka baya miki wahala”zama tayi ta fara yimata bayanin komai daya faru” mommy ta sauke numfashi cikin b’oye damuwarta tace”dama soyayya kukeyi dashi ne?”kanta ak’asa tace”uhmm” yanzun ma yasanar mun yana sona Ai “ta fad’a tana rufe fuska tana murmushi”mommy ta girgiza kanta tace “marar kunyar k’arya”Ai dama nasan kema kina sonsa”ki mance da batun Nasir”dashi da uwarsa hassadace kawai ke damunsu”kuma yanzun na fahimci cewa”Allah ne yacanza miki sharif bisaga Nasir “fatana Allah yasa shi Alkhairi ne agareki”idan Nasir yayi haka da nufin ya tozar tamu yabamu kunya kansa ya bamawa”bance kiyi gaba dashiba adinga gaisuwar zumunci”kud’i kuma shine matsiyaci saiya Amsa Ai….sallamar daddy ta katse mata mgn”Amaan ce ta Amsa tana sunkuyyar dakai k’asa”bayan ya zauna yashiga sanarwa mommy yadda Akayi …Abinda yayi shine daidai Alh”kaima kasan idan yusuf ko khalifa na tsaye be isa har yanemi yamaka rashin kunya ba”kud’i kuma kabiyashi be kamata shariff yabiya shiba…nizan biyashi kud’insa mommy”duk hidimar daya mun bata kai ta million guda ba Amma sbd zalama yace”wai million 3″adai bari mugani zuwa goben zan bama shariff d’in hak’uri yasaka su sakesa”wlh inda bacin sbd kai daddy wlh hamma nah zai iya sakawa Ashafe babinsa Adoron duniya” daddy ya girgiza kansa yace”ah ah komai me wucewane “wata ran zaiyi nadama”Ashe shariff d’in zuwa yayi? Eh da yamma nan yazo bayan jiya ta gama kukan ita Amaidata wajensa sbd ba hankaline da itaba”Amaan ta rufe fuska tana murmushi”to sai d’azun bayan yazo suna sitroom Amminsa ta kirani take tambayata yazo ne”nace mata Eh”nan take sanarmun shima wai haka yadameta tayi waya Amaido masa ita”daddy na murmushi yace”son junafa sukeyi gaba d’ayan su”Amaan na dariya ta wuce d’aki Aguje”mommy suka cigaba da mgn”daga bisani daddy yatafi masjeed….bayan sallar isha’i Amaan takoma wanka alAgurguje “bayan ta fito ta shirya cikin k’ananun kaya ta Aza dogon hijab sama “sosai tayi kyau tanata zuba k’amshi”zama tayi gefen bed ta d’auki wayarta”saida taji k’irjinta yabuga dataga 2miss call na shariff da kuma text message nasa”da sauri ta bud’e text message d’in kamar haka *I’m waiting for you my baby* ta sauke numfashi ta fito parlourn “duk mazan na zaune suna kallo sbd Akwai nefa”ta kalli mommy kanta ak’asa tace “mommy zanje wajen su hamma shariff”sun dawo daga masallaci tun d’azun “hamma yusuf yace”Eh tare muka dawo dasu Autar mommy”Allah dai yasa daddy yabama yaya shariff ke sbd yana ji dake sosai”Amaan tayi murmushi batace komai ba”mommy na kallonta tace” okay kar dai kikai k’arfe goma”dato ta Amsa ta fita daga cikin parlourn”Ajiyar zuciya mommy ta sauke Aranta tana mata Addu’ar Allah yamata zab’in Alkhairi…. Ahankali Amaan ta…..✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button