Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 22

Sponsored Links

PAGE* 2⃣2⃣

Abbah gyara gidansa yayi sosai akayi masa fenti yacanza ma mama kujerun d’akinta, d’inkuna kala ukku-ukku yayi ma su mama.

 

khairy ko da tazo taga zarah rikicewa tayi cike da murna tace sis anya kuwa kece ba canza mana wata akayiba mai kama da ke?

murmushi zarah tayi tace toh indai ana canza mutum toh nima an canzani,

khairy tace wlh kuwa dan ma bakiga yadda kika koma wata ‘yar gayuba, ke ni ya maganar rabon invitation card gashi saura kwana biyu bikki ammah ba Wanda muka gayyata.

ta6e baki zarah tayi tace ba wanda zan gayyata domin ba abinda zanyi ayi bikkin kawai a haka.

khairy rik’e baki tayi tace kai zarah ammah dai bakida mutunci yanzu saboda Allah bazaki gayyaci kowaba? gaskiya bai daceba ace kamarki zaki auri yarima guda ammah ba ayi wani shagaliba,

zarah cikin rashin damuwa tace ba fa zanyiba kema kinsan auren nan zanyisane kawai ba dan ina soba.

zaro ido khairy tayi tace zarah kar dai kice min har yanzu baki daina son malam bello ba? yarima fa yafisa komai.

murmushin takaici zarah tayi tace har yau har gobe ina son malam bello, saidai idan nayi aurene zan daure inga na nisantar da zuciyata daga tunaninsa gudun kar injefa kaina ga halaka.

dariya khairy tayi tace kin dai karanta a islamiyya kuma kinsan babu kyau ehe.
ke wlh yaci ace kin cire son malam bello a ranki kifad’a sabuwar soyayya.

murmushin takaici zarah tayi tace kar fa kimance da tsohuwar zuma ake magani.

dariya khairy tayi tace injiwa? ai itama sabuwar zuman tana magani wani lokacin ma tafi wata tsohuwar, zamu dai zuba ido mugani.

 

su Hajiya sa’adatu sune ummi tasa sukaje sukayi jeran zarah, part d’aya aka fitar mata dashi daga cikin gidan yarima suhail,
d’akine mai d’aukeda parlour nd 2 bedrooms sai kitchen, kaya aka zuba mata na gani na fad’a a duka bedrooms d’inta sannan aka tsara mata parlourn ta yayi gwanin kyau, kitchen d’inta cika mata shi akayi da kaya, antsara ma zarah part d’inta sosai kamar na wata d’iyar wani attajirin mutum.

 

Abban sumayya ma canza ma d’iyar tasa kayan d’aki yayi masu kyau da tsada, sumayya taji dad’i sosai sai a lokacin ta safko daga fushin da take da mahaifinta akan auren da yaje yanemo ma yarima.

 

ana gobe bikki sultana bilkisu ta aiko da mota akazo aka d’auki zarah aka kaita wani hadad’en shagon gyaran jiki wanda sai amaren da suka amsa sunansu suke zuwa.

saloon akayi mata sannan aka zizira mata k’unshinta tayi kyau sosai.

gidan sarautar hidima ake ta gani ta fad’a ko da kowa 6oye murnarsa yake a ciki, ammah sumayya da mahaifiyarta a fili suke nuna basason auren.

gimbiya rahma ita take zuwa tana kwantar ma da sumayya hankali tun da bikkin ya matso kasancewar itama ba’a son ranta yayan nata zai k’ara aureba saboda tana ji da sumayya sosai tun k’uriciyarsu suke abota, taso ace ummi ta hanasa yak’ara auren ammah ummi tace babu ruwanta ita taje ta samesa tayi masa magana, jin haka yasa taja bakinta tayi shuru dan tasan bama zata iya tunkarar yarima da maganar ba.

 

________________

zarah bayan angama mata gyara around 3:30pm aka maidota gida, mamakine yacikata ganin mutane da suke shiga gidansu, kanta bai ida d’aurewaba saida tashiga cikin gida taga kowa ya shirya, Yaya rauda ce tafara hango zarah tace yauwa ga ma tanan ta dawo.

dasauri khairy da Aysha suka zo wajenta sukace tun d’azun muna ta jiranki please kizo kishirya lokaci yana k’urewa, zarah cike da mamaki tace ban fahimcekuba me zanyi?

jawota sukayi suka nufi d’aki da ita suna cewa koma dai minene kizo dai kishirya.

zarah fizge hannunta tayi tace wai mi za’ayi? ya naga kowa ya shirya?

dariya aysha tayi tace kai yaya zarah wa’azi fa za’ayi?

zarah da kanta ya ida d’aurewa tace wa’azi kuma? wa yashiryasa? muryar yaya rauda sukaji tace mune nan muka shiryasa mun gayyaci mutane, munga idan muka biye ta naki toh babu abinda zakiyi dan haka kiyi sauri ki shirya.

zarah turo baki tayi tace kai dan Allah yaya rauda meyasa zakuyi min haka?

yaya rauda d’aure fuska tayi tace isarmu ce tasa mukayi miki haka dan haka kiyi sauri kije kiyi wanka ko inje inhad’aki da mama.

zarah jin za’a had’ata da mama yasa cikin sauri tawuce taje ta shiga wanka tana fushi.

bayan ta fito kwalliya akayi mata sosai sannan aka d’auko mata material ash nd black colour tasaka sai aka d’aura mata alkyabba black colour mai ratsin ash daga saman kayan, tayi kyau sosai ya yaba da kyaun da tayi.

su yaya rauda ne suka fito da ita, a tsakar gidansu ya cika da jama’a a nan aka zauna akayi wa’azi, manyan malamai mata guda biyu sukayi wa’azin, wa’azin aure mai ratsa jiki inda aka jawo musu ayoyi da hadissai, ba zarah ba hatta sauran mutanen da suke wajen saida suka koka.

bayan angama su yaya rauda suka raba kayayyakin da suka tanada zasuba mutane, zarah dai mamakine yacikata cikin ranta tace nasan zaku aika tunda dai khairy tamatsa sai anyi wa’azi, chan kuma sai tayi murmushi cikin ranta ta ji dad’in hakan.

nan mutane suka watse kowa yana fad’in albarkacin bakinsa.

 

_*RANA BATA K’ARYA SAIDAI UWAR ‘DIYA TAJI KUNYA*_

A yau juma’a masallacin juma’a da yake anguwarsu zarah cike yake da jama’a dan saida aka rasa masaka tsinke saboda yawan mutane anguwar cika tayi sosai dan har memartaba saida yahallara wajen.

Bayan anfito masallacine aka d’aura auren *Yarima Suhail Ahmad Umar* da *amaryarsa Fatima Zarah Musa* akan sadaki naira dubu d’ari,

a chan tsakiyar taron nahango ango da shaheed, ango yasha kyau har ya gaji sanye yake cikin shaddarsa fara wadda tasha aiki da bak’in zare, hularsa da takalmansa duka jajayene nan mutane sukaita zuwa suna gaisawa tare da yi masa Allah yasa alkhairi shidai yarima yana murmushi ne kawai dan saboda memartaba kawai ya amince yazo d’aurin auren.

takeaway aka shiga rabama mutane kowa yaci yasha aka watse cike da farin cikin auren nan masu tsegumi sunayi masu murna nayi.

 

gidan su zarah cike yake da ‘yan uwa da abokan arzik’i abbah yayi k’ok’ari sosai wajen ganin anyi abinci na azo gani wanda kowa zaici yasan yaci hatta naman kaji sunyi kuka sosai a ranar.

A chan tsakiyar gadon mama nahango zarah zaune ta ci kwalliya ta had’e cikin less d’inta pink colour mai ratsin blue head ne blue a saman kanta tayi kyau sosai sai sharar k’wallah take gefenta su yaya rauda ne da Khairy suna lallashinta dan ita gani take duk wasane auren saida tajiyo hayaniyar mutane suna gud’a ana and’aura aure sannan ta tabbatar dagaskene.

mama ce tashigo d’akin taganta cikin wannan halin tace haba zarah miye abun kuka hak’uri zakayi domin shi aure haka yake.

zarah cigaba tayi da sharar k’wallarta ganin haka yasa mama taficce tana fad’a,

zarah da take kuka jin sallamar mutane da tayi yasa tashare fuskarta cike da mamaki take kallon jama’a buya guda da sukazo, nima kaina natsorata saida najawo My Hafnan muka koma gefe nace kin gane mutanen nan da sukazo?

hafnan harararsu tashiga yi tace hmm nagane wasu man wacchan tawagar masu pink d’in atamfa ‘yan group d’in *yarima suhail fan’s* ne, sai tamurga baki tare dagwada masu anko d’in blue tace wannan kuma na *Hibbatullah* fan’s ne, sannan sai masu red d’in anko *Intelligent writer’s fan’s* ne, sai kuma tanuna wasu tace masu green *Nazir* fan’s ne, masu coffee kuma *Aufana true fan’s* da *sainah true fan’s*, Masu navy blue kuma *Zaynav mtz fan’s* sannan *Mummyn khalil fan’s*, *Surbajo fan’s*, *Sadnaf true fan’s* ke da dai sauransu.

rik’e baki nayi nace chab nashiga ukku my hafnan yanzu saboda Allah duk wa yagayyaci wad’annan uwayen mutanen? murya muka jiyo daga bayanmu ance yoh wa fa yagayyacesu k’wak’wace takawosu kawai, juyawar da zanyi sai ganin My blood sis aufana da mummy sainah ummun meenal nayi, dafe kai nayi nace nashiga ukku kukuma wace k’wak’war takawoku? My blood hararata tayi tace yoh mu da tun d’azun muna nan damu akaci aka sha, su Mummyn afrah, meenah abbah, k’anwarki janaf, haleemah H.A.S, sis Aysha ke dama sauran intelligent writer’s duk suna nan yanzu haka sunje kar6o mana nama kinsan mummy zill da ‘yar mutan zariya basa barin nama,

had’e fuska nayi nace toh wlh wannan abun kunyar ba da sis nerja’art ba dole kowa yazo yakama gabansa babu wanda zai zauna, nan nakorasu nace muje inda muka fito nima nafasa zaman, kallon zarah sukayi sukace toh gimbiyarmu sai mun dawo wani taron,

murmushi kawai zarah tayi bayan sun fita takalli yaya rauda tace wad’annan masoyanmune fa nasan basu ganekuba saisa, yaya rauda dariya tayi tace haba saisa naga rawar kansu yayi yawa saikace Maman sadiq da mrs dawud ke wani abun ma sai ummie adnan da mugirat ammah basukai mummyn khadija ba, aini naji dad’i da aka korasu.

 

Bayan sallar magrib wanka akasa zarah tayo bayan ta fito hafnan nd Aufana makeover ne suka zauna suna shirya amarya, kwalliya sukayi mata sosai wadda ita kanta zarah da takalli madubi saida tayaba kanta, atamfa tasa riga da skirt sun mata cif sannan aka murza mata d’aurin kallabi inda kyaun nata yak’ara bayyana.

 

bayan sallar isha’i aka aika da motoci biyu d’aya wadda amarya zata shiga, d’aya kuma na kuyangin da sukaje sutafo da itane saboda cewa akayi babu wanda za’aje da shi kai amarya, amarya kawai za’a tafi da ita.

 

wajen su mama aka kai zarah sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki duk dauriyar mama kasa daurewa tayi saida tayi kwallah, zarah tana kuka aka rik’ota aka fito da ita.

 

‘yan unguwa sunji haushi sosai domin kowa yaci burin yaje yagane ma idonsa, wasu kuma burinsu suje suga sarki, wasu kuma suje suga yarima, wasu kuma burinsu suje sugano kwakwaf, Aysha kuka tayi sosai dan taso tabiyo ‘yar auwartata, dole suka hak’ura suna gani aka fito da amarya an nad’eta da lifaya, jakadiya ce rik’e da zarah sai kuyangi biyu da suka take musu baya ahaka aka shigar da ita mota tana kuka.

nan ‘yan unguwa wasu sukaita tsogumi ai iyayen zarah saboda son abun duniya suka siyar da d’iyarsu babu wanda yasan inda za’a kaita

 

haka akaita tafiya ita dai zarah ji take kamar ba a mota takeba saboda wani irin k’amshi mai dad’i da yake ratsata da d’in motar, bata d’ago kantaba har alokacin hawaye take tana tausayin kanta da takaicin iyayenta da suka amince suka aura mata wanda bata so.

 

ko da aka isa da zarah gidan sarautar tana ji bushe-bushe suna ta tashi batasan lokacin da aka tsayaba saidai gani tayi anbud’e mata k’ofa

nan jakkadiya tace ranki yadad’e kifito anzo, zarah ahankali tasafko k’afarta daga motar har a lokacin fuskarta na a rufe dasauri bayi da kuyangi suka zube k’asa suna k’awar gaisuwa angaishe da gimbiya angaishe da tauraruwar mata takawarki lafiya gimbiya, zarah duk jin abun tayi wani iri saboda bata saba jin hakaba sai a film tunda ita ba zuwa gidan sarauta takeyi ba ammah yau itace ake gaishewa ta bangirma.

muryar jakadiya tajiyo tana cewa ranki yadad’e muje mana, jakkadiya da wata kuyanga suka rik’eta inda sauran kuyangi da bayi suka zagayesu aka sa su tsaka ahaka ake tafiyar har aka isa turakar dada, duk mutanen da ke wajen taga sun duk’a suna kwasar gaisuwa a wajen dada, zarah har zata duk’a dada tace a’a akawota nan tazauna.

jakkadiya takamota takaita har kusa da kujerar da dada take zaune, zarah dasauri tazauna k’asa har a lokacin fuskarta a kulle take kyarma kawai take domin gani take kamar a mafarki.

nan duk sauran kuyangi da bayi suka bar d’akin, d’akin yad’auki shuru daga dada sai zarah, dada ce tayi gyaran murya tace barkanki da zuwa wannan gida namu mai albarka fatanmu kizauna da kowa lafiya, domin kinsan gidan sarauta sai anji ank’i ji, agani ak’i gani, kizauna da kishiyarki lafiya indai kikabi sumayya sau da k’afa toh zaku zauna lafiya domin ita batada matsala ko da kema da alama daga ganinki ba zakiyi matsalaba.

itadai zarah sauraren dada take batace ufanba har a lokacin kanta na sunkuye a k’asa ahaka har dada tagama nasiharta sannan takira jakadiya domin tazo tatafi da zarah 6angarenta, zarah duk’awatayi cikin muryarta da tadashe tace nagode sosai insha Allahu ba zan kawo muku matsalaba zan zauna da kowa lafiya,

dada taji dad’in lafazin zarah a karo na farko da taji ta d’an burgeta domin taga da alamu zatayi hankali.

dada tace zaku iya tafiya, jakadiya tace to ranki yadad’e muje,

zarah mik’ewa tayi suka fito nan duk sauran kuyangi suka take musu baya suka nufi part d’inta,

 

bedroom d’inta aka wuce da ita aka zaunar da ita bakin gado sannan jakkadiya tace ma kuyangi sutafi nan kuyangi suka zube suka kwashi gaisuwa wajen zarah itadai zarah tana jinsu batace komaiba daganan suka mik’e tare da cewa afito lafiya gimbiya, daganan suka fita daga d’akin.

nan jakkadiya tashiga toilet tahad’a mata ruwan wanka wanda yasha turaruka sannan jakkadiya tafito tad’auko towel tarussuna ta aje sannan tace ranki yadad’e ruwan wankanki sun had’u zaki iya shiga,

zarah tace a’a ba ma sai nayi wankaba,

jakadiya tace kigafarceni ya shugabata umurnin sultana ne nake cikawa kuma wannan tsarin gidan nan ne,

zarah tana jin haka tamik’e tare da janye lullu6inta, gabantane yashiga fad’uwa tana bin d’akin da kallo cike da mamakin tsaruwarsa cikin ranta tafara kokwanto anya wannan nawane?

muryar jakkadiya taji tanacewa ranki yadad’e akwai abinda zan iya taimaka miki da shi?

zarah d’aukar towel d’in tayi tare da cewa bana buk’atar komai daga nan jakkadiya tanufi 6angaren wardrobe d’in zarah,

nan zarah tacire kayanta taje tashiga toilet ko da tashiga tsayawa tayi tana k’arema tsarin toilet d’in kallo cikin ranta tace lallai idan kana duniya zakayi kallo, tsoron Allah ne taji ya k’ara ratsamata zuciya nan tashiga cikin ruwan da yayi mata dad’i dan saida tadad’e tana wanka sannan tafito.

ko da tafito jakkadiyace da wata kuyanga tsugunne a k’asa ganinta yasa suka mike cikin sauri tare da cewa takawarki lafiya gimbiya.

zarah wajen dressing mirror tanufa nan suka bi bayanta suka mik’a mata mai hadad’e mai k’amshi tashafa waccan kuyangar ce tayi mata ‘yar simple makeup sannan kayan baccine masu kyau da tsada jakadiya tafito mata dasu,

doguwar rigace silk har k’asa mai hannun vest nan zarah tasaka, su jakkadiya suka dinga yi mata 6arin turaruka a jiki masu sanyin k’amshi, suka tufke mata gashinta da rubon Sannan aka sakamata had’ad’ar alkyabbar da aka tanada.

ko ni kaina da naga zarah saida nace wow masha Allah kamar ba zaran da nasani bace saboda kyaun da tayi

su kansu su jakkadiya saida sukayita santinta suna yaba kyaun da tayi itadai murmushi kawai take nan ma suka k’ara fesheta da turaruka, sannan sukace ranki yadad’e idan ba wani abu da za’ayi zamu iya tafiya.

zarah fuskarta d’auke da mamaki tace ina zamuje?

jakkadiya kanta a sunkuye yake cike da girmamawa tace d’akin yarima zamu rakaki.

zarah saida gabanta yafad’i jin an ambaci yarima dakewa tayi tace da munyi zamanmu a nan.

jakkadiya tace a’a ranki yadad’e ai tsarin sarautar gidan nan ne yau d’akin mijinki zaki kwana.

zarah batace komaiba tawuce gaba suna biye da ita a cikin ranta mamaki kawai take ganin komai na gidan sarauta a tsare yake, ko da suka zo parlournta nan sauran ma’aikata suka zube suka kwashi gaisuwa sannan suka take mata baya, jakadiya tana gaba ta rik’e zarah inda sauran suka bi bayansu,

zarah gabanta fad’uwa kawai yake domin batasan irin wulak’ancin da zata fuskantaba wajen mutumin da yake a matsayin mijinta.

 

yarima bai dawo gidanba sai wajen k’arfe takwas da rabi na dare fuskarsa babu annuri atattare da ita duk wanda yaduk’a yakwashi gaisuwa saidai yatashi hakanan domin yau ko d’awar hannun da yake musu basuda arzik’in samu.

ko da yashiga part d’insa komai yadda aka gyara masa ya burgesa direct bedroom yawuce nan ma Komai very need, mamakine yakamasa ganin farin bedsheet mai kyau da aka shimfid’a masa saman gado,

cikin ransa yace toh ba za a daina wannan al’adar ba yanzu aure nabiyu ammah shima ba za’a barni inhutaba, tsaki yaja cike da jin haushi yawuce yashiga bathroom,

bayan ya fito saida yatsane jikinsa yashafa mai sannan yad’auko kayan baccinsa yasaka yazauna bakin gadonsa yajawo laptop d’insa yacigaba da wani aiki nasa akan drugs d’in da yake buk’ata ayo masa order d’insu.

knocking d’in k’ofar da akayine duk atunaninsa gimbiya sumayya ce dan haka yace yes.

jakadiya ce tana rik’e da zarah suka shigo da sallamar jakadiya, yarima kallo d’aya yayi musu yad’auke kai jakadiya takowa tayi tazo gaban yarima sannan tasaki zarah ita taduk’a cikin girmamawa tace ranka yadad’e daman sultana ce tace akawo maka amaryarka, yarima cigaba yayi da aikinsa bai tankaba bare yace wani abu, zarah ma k’asa tazauna jikinta sai 6ari yake,

jakadiya ganin yarima baida niyar yin magana yasa tace Allah yaja da ranka akwai abinda ake buk’ata, yarima batare da ya kalletaba yayi mata nuni da k’ofa jakadiya cike da girmamawa tace ranka yadad’e nabarku lafiya, Sannan takalli zarah tace ranki yadad’e atashi lafiya sannan jakadiya tatashi tafita tare da jawo musu k’ofa

 

daga nan d’akin yad’auki shuru tsoro da fargaba duk suka d’arsu a zuciyan zarah, yarima ko kamar wanda aka ajema kayan wanki ko inda zarah take bai kallaba,

zarah dai har lokacin tana zaune a k’asa fuskarta a rufe cikin ranta tana cewa wannan wane irin mutum ne ko dai bebe ne aka auramin, ahaka tayita sak’e-sak’e a zuciyanta har tsawon awa d’aya tana zaune daga k’arshe bacci yafara d’ibanta,

nan k’asan ta ida kwanciya bata dad’eba bacci yayi awon gaba da ita, yarima sai wajen k’arfe sha biyu sannan yagama abinda yake kallo d’aya yayi ma zarah da take takure waje guda tana bacci, sannan yahaye saman gadonsa yakwanta cike da takaici wai ace kamarsa yakeda mata biyu duk friends d’insa daga mai d’aya sai wad’anda ma basuyi auren ba, gloves yakashe kad’an-kad’an ya yi tsaki ahaka bacci yad’aukesa……..

 

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_*Alhmdllh nasamu sauk’i, nagode, nagode da addu’o’inku agareni my fan’s hak’ik’a kun nunamin so da k’auna zallah dan ni kaina saida nayi mamakin yawan callings da messages d’in da nasamu daga gareku, bansan irin godiyar da zanyi mukuba, bazan iya lissafokuba saboda yawanku, wad’anda ban samu naduba messages d’insuba kuyi min hak’uri ammah inaso kusani ana mugun tare, Sis Nerja’art tana sonku over Allah yabar k’auna*_

 

_~Wannan page d’in mallakinkune my fan’s kuyi yadda kukeso da shi akodayaushe ana tare~_

Check Also
Close
Back to top button