Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 26

Sponsored Links

PAGE* 2⃣6⃣

yarima ko da yafito daga turakarsu dada tasu yakoma direct part d’in zarah yawuce, lokacin zarah tana kwance saman bed d’inta kanta yana kallon ceiling,

a parlour kuyangintane zaune ganinsa yasa suka zube suna kwasar gaisuwa yarima baice musu komai ba yawuce yashiga bedroom d’in zarah,

zarah da take kwance jin anbud’e k’ofa yasa tad’ago kai ganin yarimane yasa cikin sauri tamik’e tare da d’an rissinawa cikin girmamawa tace sannu da zuwa,

yarima takawa yayi yaje yazauna bakin bed d’in nata tare da yi mata nuni itama tazauna jikinta sai 6ari yakeyi, ahankali cikin tsadaddar muryarsa yace ya jikin naki?

zarah murya tana rawa tace nawarke, yarima kallonta yayi nad’an lokaci sannan yakai hannu yata6a wuyanta, yace kinsha drugs d’in da na’aje miki? zarah gyad’a masa kai tayi.

yarima har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, saida yad’auki kusan 2 minutes sannan yamik’a mata ledar da take hannunsa tare da mik’ewa.

zarah ganin yana shirin fita batare da yayi mata bayaniba yasa tace aje maka zanyi?

yarima tsayawa yayi da tafiyar da yake batare da ya juyoba yace kyautar da su dada suka bakine sannan a garke akwai shanuwa daga memartaba sai raguna daga abbah da daddy, yana gama fad’in haka yafita yabar d’akin.

zarah binsa tayi da kallo har yafita sannan tabud’e ledar tana kallo dan daman jakadiya tayi mata bayanin komai, ‘yar k’aramar sak’ar da tad’auke mata hankaline tad’auko tana dubawa tare da yin murmushi dan ko ba’a fad’aba tasan babbace, bayan ta gama duba kayan tashi tayi taje tasaka cikin wardrobe d’inta sannan tad’ibi kud’i taba wata kuyangarta tace takaima jakadiya.

tun daga ranar zarah bata k’ara taka d’akin yarima ba, shima kansa bai waiwayetaba ahaka har suka cinye sati d’aya.

A ranar da zata cika saki d’aya zaune take parlourn ta tana cin apple ammah hankalinta yana wajen kallo, bata ankaraba sai ganin gimbiya sumayya tayi ta shigo ba ko sallama,

fuskar zarah d’auke da murmushi tamik’e tsaye tare da d’an rissinawa tace sannu da zuwa,

gimbiya sumayya tsaki taja tana bin d’akin da kallo chan sai ta ta6e baki tace eh balaifi talakkawan iyayen naki sunyi d’an k’ok’ari wajen ganin sun fitar da ke kunya Allah dai yasa ba bashi sukaciba dan indai ma suna tunanin zaki samu kibasune toh bazaki ta6a samuba.

zarah da tunda tafara maganar tazuba mata ido cike da takaici tace sumayya duk wulak’ancin da zakiyi kitsaya a kaina kidaina saka iyayena a ciki.

dariyar rainin wayau sumayya tayi tace aikam dole ne iyayenki sushiga tunda kwad’ayi yasa suka bada aurenki, sannan inaso kisani yarima na gimbiya sumayya ne ita kad’ai babu macen da ta isa tara6i mijina tazauna lafiya, kinci sa’a da har kika iya had’a shimfid’a da mijina batare da nad’au matakiba, wama yasani ko kwad’ayayyun iyayenki suka cinna masa ke dan bana tunanin yarima zai iya son d’iyar talakkawa kamar ki.

zarah cikin 6acin rai tace haka dai kikace ammah ai shi yariman ba jahili bane yasan… katseta sumayya tayi cikin tsawa tace kar kisaki kid’aga min murya yakamata kisan da wadda kike magana
girgiza kai sumayya tayi tace hmm idan bakiyi gaggawar fita harkar mijinaba toh wlh zan iya yin komai, dan haka shawara tarage naki
tana kaiwa nan tajuya tafita tabar d’akin

zarah haushi ya ida cikata komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tace wannan wace irin rayuwata? dole in samar ma kaina mafita dan wannan matar nalura bazata ta6a barina inhuta ba, chan sai zarah tayi murmushin da ita kad’ai tasan ma’anarsa.

 

_*After 1 week later*_

gimbiya sumayya ce nagani cikin shirin bacci ta fito sai karairaya take tanufi part d’in yarima,

ko da tashiga yarima kansa saida yayi mamakin ganinta shareta yayi yacigaba da kallonsa, sumayya ganin bai kulataba yasa ta isa wajen da yake zaune tazauna gefensa tare da kwantar da murya tace haba my sweetheart daga shigowata sai kad’auke min kai? yarima shareta yayi yacigaba da kallonsa,

sumayya kwantar da kanta tayi jikinsa tace kana fa jina, sai alokacin yace toh sumayya me kikeso ince miki? ko kina buk’atar wani abune wajena?

sumayya haushi yacikata cikin ranta tace wannan mutumin fa baida mutunci, chan sai tayi murmushi tace bana buk’atar kowa sai mijina rabin rayuwata.

yarima kallonta yayi alamun rashin yadda sannan yamaida kallonsa ga T.V

Sumayya kallon agogo tayi sannan tace sweetheart bacci nakeji please muje mukwanta.

yarima batare da ya kalletaba yace zaki iya tafiya kikwanta ni ba yanzuba,

gimbiya sumayya gyara kwanciyarta tayi a jikinsa cikin shagwa6a tace toh ni nan zan kwanta sai katashi kwanciya.

yarima baice mata komai ba yacigaba da kallonsa sai wajen 11pm sannan yatasheta suka shige master bedroom.

ahaka sumayya tayi kwananta biyu a d’akin yarima ko da sau d’aya bata yadda ta6ata masa rai ba.

 

 

zarah dai a kullum tana k’unshe a d’akinta bata yadda talek’o ko da wajen part d’inta ne.

 

yau dakanta tashiga kitchen tahad’a breakfast kasancewar ta tashi da wuri kuma tana da burin yarima yafara cin abincinta, dan tana ganin kamar hak’intane ita yafi cancanta tagirka masa ba masu aikiba.

had’add’en yam ball tayi sannan tahad’a kunun gyad’a wanda yaji madara peak.

bayan tagama, wanka taje tayi tare da shiryawa cikin gown white nd black colour har k’asa rigar take tana ja da k’asa sannan tayi rolling d’in kanta da bakin veil tare da feshe jikinta da turaruka,

kitchen takoma tajera kular da flask d’in saman tray sannan taba kuyangarta d’aya tad’aukar mata nan tafito tanufi part d’in yarima, duk inda ta gifta gaisheta akeyi tana amsawa cikin sakin fuska, tun kan ta ida isa guards suka hangame mata k’ofa tare da rissinawa suka gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa sannan tashiga,

a saman dining taba kuyanga umurni tad’aura tray d’in sannan tasa tasafke breakfast d’in da taga anje masa, bayan ta gama zarah tace zata iya tafiya.

bayan ta fita fargaba da tsoro duk suka kama zarah dan tana tunanin wulak’ancin da zata fuskanta a wajen yarima, ta dad’e tsaye sannan daga baya tabud’e bedroom d’insa tashiga.

tsaye zarah tayi bakin k’ofa tana kallon baiwa da take sharema yarima d’aki.

ganin zarah yasa baiwar taduk’a tagaisheta cike da girmamawa, zarah hankalinta ya tashi sosai tace mekikeyi nan?

baiwar kanta a k’asa tace ranki yadad’e daman nice wadda gimbiya sumayya ta wakilta ina gyarama yarima d’aki.

daidai lokacin yarima yafito wanka, baiwar saida ta tsorata domin bata d’auka yarima yana nan ba tad’auka ya fita.

zarah batare da ta kallesaba tace mata daga yau kar kikuma shigowa d’akin nan nadakatar da ke daga gyaransa.

duk’awa kuyangar tayi tace ranki yadad’e Allah yahuci zuciyanki yadda kikeso haka za”ayi.

zarah hanya tanuna mata, dasauri kuyangar tafita, zarah ma a tsorace tafito tadawo parlour, nan tahau gyarawa mamakin gimbiya sumayya yacikata cikin ranta tace duk ajin nata ammah bata ji zata iya gyaran d’akin mijinta.

 

bud’e k’ofar da akayine yasa tad’ago takalli gimbiya sumayya da tashigo ranta a 6ace.

zarah d’an rissinawa tayi tace barka da safiya, wata uwar harara sumayya tawurga mata tare da cewa ke har kin isa insa ayimin abu kihana?

zarah kallonta tayi tare da kallon kuyangar da take tsugunne k’asa sannan tayi murmushi tace ban fa isaba saidai nima ina da right inyi abinda nagadama tunda d’akin mijinane,

sumayya a harzuk’e tace ke kar kisaki kiyi min rashin kunya,
bawani maganar rashin kunya idan ke kikaso kigyara to zaki iyayi ammah wlh ban amince ‘yar aiki tadinga shigomin d’akin mijiba yadda kike da iko da shi nima haka ina da iko, dan haka indai ke bazakiyiba toh ni zaniyi.

sumayya tayi mamakin zarah domin bata kawo ma ranta zata iya magana hakaba, ‘yar dariya sumayya tayi tace lallai talakka bai iya samun wajeba idan yasamu sai yanuna yafi masu gida zak’ewa.

murmushi zarah tayi ko da taji ciwon maganar da sumayya tayada mata ammah bata nunaba, tace Indai shi maigidan ya kasa gyarawa ai ba laifi bane dan an zak’e, tana gama fad’in haka tawuce tacigaba da gyaran d’akin tabar sumayya tsaye tana ta balbala bala’i saida tagaji dan kanta sannan tawuce a zuciye tashiga bedroom d’in yarima suhail.

duk abinda suke akan kunnuwansa dan yana saurarensu, ko da sumayya tashigo ko kallonta baiyiba yacigaba da abinda yakeyi, sumayya a k’ule tace yarima yanzu saboda Allah…. d’aga mata hannu yarima yayi tare da nuna mata k’ofa, tsaye tayi tak’i tafiya,

d’ago kai yarima yayi yaimata wani irin kallon da yaja ba shiri tafita tabar d’akin.

zarah ko da tagama gyara masa parlour ganin har lokacin bai fitoba yasa taje tayi knocking tare da bud’e k’ofan tashiga.

yarima da yake zaune ahankali yad’ago kai yakalleta.
zarah d’an rissinawa tayi tace ga breakfast d’inka chan a dining.
yarima shuru yayi baice komai ba, sai chan yamik’e yafito.

dining yaje yazauna zarah dakanta tayi serving d’insa sannan taje bedroom d’insa tagyara masa tass, bayan tagama tafito takoma part d’inta.

yarima ya d’anci ba laifi dan rayuwarsa yana son abincin gargajiya shi da memartaba halinsu ya zo d’aya.

bayan ya gama bedroom d’insa yakoma yad’auki wayoyinsa yafito yanufi wajen aiki.

zarah saida tatabbatar da ya fita sannan tafito tanufi part d’insa ko da taduba abincin taga yaci balaifi, har cikin ranta taji dad’in hakan, kuyangarta tasa takwashi kulolin tace suje suci, ko da tadawo part d’inta tunani tashiga yi me zata girka masa a k’arshe dai tayanke hukuncin tayi masa tuwon shinkafa miyar ganye dan daman ummi ta fad’a mata yarima yanason abincin gargajiya sosai,

kitchen tashiga bata yadda kuyanginta suyi mataba cewa tayi subarsa saidai gyaran kayan miya da blending kawai sukayi mata.

haka tazage tad’and’ara girkinta tasaka masa acikin had’add’un culars d’inta, nan kuyangi suka gyara mata kitchen tas.

 

Gimbiya Zarah saida ta tabbatar da dawowar yarima sannan tasa aka jera abincin asaman tray kuyanginta suka d’auka tana gaba suna biye da ita a baya har sukaje 6angaren yarima nan guards d’insa suka gaisheta cike da girmamawa sannan suka bud’e mata k’ofa tashiga, kuyangi a saman dining suka jera abincin sannan suka zube tare da cewa mun cika umurninki ya shugabanmu, gimbiya zarah gyad’a musu kai tayi sannan tace zaku iya tafiya.

suna fita cikin takunta tanufi bedroom d’in yarima suhail tayi knocking yarima da yake tsaye gaban mirror yana shiryawa jin ana knocking yasa yace yes saboda a tunaninsa gimbiya sumayya ce.

gimbiya zarah bud’e k’ofar tayi a hankali tashigo daga d’an nesa da shi kad’an tatsaya tad’an rissina kad’an tare da cewa ur lunch ix ready.

yarima suhail d’auke kansa yayi daga kallonta yacigaba da abinda yakeyi kamar ba zaiyi magana ba sai da suka share kusan minti biyu a haka sannan yace ohk am coming.

gimbiya zarah d’an rissinawa tayi sannan tafito tadawo parlour tazauna saman d’aya daga cikin kujerun d’akin, saida tayi kusan Minti goma a zaune sai ga yarima ya fito sanye da kayansa na alfarma yana takun nan nasa na k’asaita, zarah tana ganin ya fito tamik’e tsaye yana gaba tana biye da shi har sukaje dining ganin ya yi tsaye yasa tagane abinda yake nufi dan haka tajanyo masa kujera yazauna,
sannan tayi serving d’insa itama tajawo kujera tazauna tana dannar wayarta, ta gefen idonta tana kallon yarima suhail yana cin abincinsa ahankali yana yatsina fuska kamar Wanda akayi ma dole, yana cikin ci aka kira wayarsa, baici wani abun kirkiba yamik’e.

itama mik”ewa tayi tabi bayansa suka nufo k’ofa zasu fita, zarah tayi knocking dasauri guards suka bud’e k’ofar nan suka duk’a suna kwasar gaisuwa wajen yarima da gimbiya zarah,

yarima hannu kawai yad’aga musu sannan yawuce gimbiya gefensa tatsaya nan guards suka take musu baya.

 

gimbiya sumayya da tadawo daga 6angaren iyayenta kuyangi suna take mata baya tsayawa tayi cak tana kallon yarima da yake jere da zarah suna tafiya, dasauri tanufi inda suke tana zuwa tasha gabansu tatsaya, yarima suhail kallonta yayi batare da yace komaiba, gimbiya zarah d’an rissina ma sumayya tayi tace barka.

gimbiya sumayya harara tawurga mata sannan tamaida kallonta ga yarima tace yarima inason ganinka.

yarima suhail cikin rashin damuwa yace toh ai gani kin ganni, gimbiya ta6e baki tayi tace ai ba irin wannan ganinba magana nakeso muyi.

 

yarima suhail shuru yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace ina saurarenki,

gimbiya cikin fushi tace haba yarima dan zanyi magana da kai ba zaka zo muke6eba kaduba kaga wannan ‘yar talakkar tana nan kuma ga bayi da kuyangi gabansu kakeso inyi?

zarah murmushin talaici tayi tare da d’an rissinawa tace ranki yadad’e nabarku lafiya, har tajuya zata tafi da mamakinta kawai sai taji yarima ya rik’o hannunta dasauri tajuyo takallesa fuskarta d’auke da mamaki ammah shi kuma yarima ba ita yake kalloba fuskarsa tana akan ta gimbiya sumayya.

gimbiya sumayya cike da mamaki take kallonsa ganin baida niyar yin magana yasa tace yarima ya haka magana fa nakeso muyi miye nawani rik’o wannan gajar?

yarima suhail fuskarsa babu alamun wasa yace itama matatace kamarki kuma indai kinsan ba zaki iya maganar a gabantaba toh kibari kinzo room d’ina kisameni yana gama fad’in haka yaja hannun gimbiya zarah suka bar wajen nan guards suka take musu baya.

 

gimbiya sumayya takaici ya cikata ga kunyar dizgin da yarima yayi mata gaban ma’aikatansu jinjina kai tayi tace lallai yarima ni kawulak’anta kafifita bare akaina toh wlh ba zan yardaba, juyowa tayi takalli kuyanginta da suka sunne kansu k’asa domin sunsan yadda ran gimbiyarsu ya6aci toh suma sai ta6anasu, tsawa tadakamusu tace uban mi kuka tsaya kuyi min a nan watau saurare kukeko? jikinsu yana kyarma sukace a’a ranki yadad’e kigafarcemu, hanya tanuna musu cikin fushi tace kubar nan, dasauri har suna rige-rige sukabar wajen.

gimbiya sumayya cike da takaici tashiga zagaye wajen tana jin tsanar zarah tana dad’a k’aruwa a ranta.

zarah har wajen motarsa tarakasa saida taga ya shiga sannan tasunya jikin window tace adawo lafiya,

yarima hannu kawai yad’aga batare da yayi maganaba yabada izini akaja motar.

zarah ko da takoma part d’inta saman gadonta tafad’a murna shar takeyi dan tana ganin ko bakomai yarima yanuna itama tana da d’an matsayinta a wajensa ko da ace ba haka bane a cikin zuciyansa.

murmushi tayi tace yanzu zan nuna miki talakka ma daidai yake da kowa.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

Back to top button