Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 17

Sponsored Links

PAGE* 1⃣7⃣

Bayan ya fito shiryawa yayi sannan yahau saman bed d’insa yakwanta tare da jawo wayoyinsa yakashesu gudun kar adamesa da kira, nan yayi ta tunanin yadda zai 6ulloma lamarin, domin kwata-kwata bayaso yasa dada cikin maganar gudun kar tatarwatsa komai.

kiran sallar magrib ne yafarkar da shi daga tunanin da yakeyi, jiki babu k’wari yaje yad’auro alwallah yaficce masallaci.

 

Bayan sallar isha’i yarima fada yaje domin yagana da memartaba, lokacin memartaba da wazirine kawai cikinta suna tattaunawa akan wasu kud’i da za’a ware akai gidan marayu da gajiyayyu, yarima gaishesu yayi, nan suka amsa masa cike da sakin fuska da fara’a, sannan yasamu gefe d’aya yazauna yajanyo wayansa yana dannawa yana jiran sugama.

ganin yarima a wannan lokacin ya tabbatar ma da memartaba fa akwai magana dan haka cikin sauri ya sallami waziri.

Bayan waziri ya fita memartaba kallonsa yamaida ga yarima yace suhail na tabbatar akwai magana me muhimmanci da take tafe da kai domin kwata-kwata ban saba ganinka a wannan lokacinba.

yarima murmushi yayi yace ranka yadad’e tabbas hakane akwai maganar da take tafe da ni.

memartaba murmushi yayi yace ina saurarenka ka sanar da ni.

yarima kunyace takamasa yafara kame-kame yace am dama ranka yadad’e….. sai kuma yayi shuru.

memartaba murmushi yayi a karo na biyu yace suhail kayi min bayani mana.

ahankali suhail yad’ago kai yakalli memartaba cike da nutsuwa yace ranka yadad’e kagafarceni daman aure nakeson k’arawa ammah idan ka amince.

memartaba cike da mamaki yace aure kuma suhail? yarima gyad’a kai yayi yace ammah amincewarka nafi buk’ata ranka yadad’e domin ba zan iya zartas da hukunci batare da amincewarkaba.

memartaba shuru yayi nad’an lokaci yana nazari sai kuma chan yace suhail ba zan hanaka raya sunnar ma’aikiba, idan nace zan hanaka aure to natauye maka hak’inka kuma bazanyi jayayya da maganar ubangijiba domin shine yayi umurni da muyi aure, saidai bansan ko kuna samun matsalaba da matarka domin baku ta6a kawo k’arar junaba, inma akwai wata matsakar ba zance dole sai nasantaba domin wannan sirrinkune, ko da aure nufine na ubangiji, yanzu dai katashi katafi gida zanyi shawara in Allah yakaimu gobe zan nemeka.

yarima rissinawa yayi yace Allah yak’ara maka tsawon rai nagode sosai atashi lafiya,

memartaba gyad’a kai kawai yayi, ahankali yarima yamik’e yabar wajen yana sak’e-sak’e cikin ransa yadda za’a kwashe da su dada domin shi k’wata-k’wata baya jin ta gimbiya sumayya dan ashirye yake da yafad’a mata.

 

ko d’s yakoma shirin bacci yayi yakwanta duk yadda yaso yayi baccin ammah ya kasa juyi kawai yake saman gado takaici duk ya cikasa ganin kamarsa ammah ace sai anza6a masa matan da zai aura, takaicinsa ma ba’a ma basa za6in kansa saidai aza6a masa saikace wani k’aramin yaro, tsaki yaja. haka yayita tunane tunane da sak’e-sak’e cikin ransa a zaciyansa sai yaji yana burin ace memartaba bai aminceba, wani irin dad’i yaji nan yasaki murmushi mai sauti ahankali yace Allah ma yasa memartaba yace a’a, ahaka bacci yayi awon gaba da shi.

 

 

*WANSHE KARE*

Yarima suhail cikin sauri yagama shirinsa kasancewar yayi late a gurguje yad’anyi breakfast sannan yaficce yanufi wajen aikinsa.

 

Bayan sallar la’asar zaune yake a parlour d’insa yana kallon wrestling cike da nishad’i kasancewarsa yanason kallon irin boxing da wrestling, wayarsa ce fara neman agaji, tsayar da kallon yayi tare da d’auko wayansa ganin memartaba ne yasa yayi picking dasauri tare da yin sallama.

amsa masa memartaba yayi sannan yace kazo turakata kasameni, cike da ladabi Yarima yace toh ranka yadad’e.

mik’ewa Yarima suhail yayi yaje yad’auko alk’yabbarsa yasaka sannan yafito nan guards d’insa suka take masa baya har turakar memartaba da sallamarsa yashiga.

mamakine yakamasa ganin iyayensa da na sumayya sai dada, cikin ransa yana mamakin dalilin da yasa aka tarasu. a k’asa yazauna tare da gaishesu.

 

memartaba ne yayi gyaran murya yace toh Alhmdllh nasan zakuyi mamakin tarakun da nayi, toh ba wata babbar magana bace dan kufad’i ra’ayinku domin wannan taron duk akan suhail akayisa saboda yazomin da wani babban zance.

shuru memartaba yayi nad’an lokaci sannan yace suhail yana da burin k’ara yin aure .

gaba d’ayansu suka rikice a firgice dada tace aure kuma? wane irin aure? duka-duka yaushe akayi aurensa da sumayya?

Sultana Sadiya tanaso tayi magana ammah bata iyawa saboda memartaba yana wajen,
wani k’ululun bak’in cikine yatsaya mata harara tashiga wurga ma yarima suhail.

Memartaba murmushi yayi yace dan baidad’e da yin aureba wannan ba matsala bane domin yana da ikon auren sama da mata d’aya kuma baidace atauye masa hak’insaba inda matsalar take shine yasafke ma kowace mace hak’inta da yarataya a wuyansa,
kallonsa yamaida ga sultan Ahmad da Abban sumayya yace toh ku iyayensa kuyi magana ya kuke ganin ya dace.

Abban sumayyane yayi karaf yace ranka ya dad’e abarsa yayi aurensa tunda yana da iko kar a tauye masa hak’insa.

Daddyn suhail yace ammah…… dasauri Abban Sumayya yakatsesa yace yaya dan Allah kar kace wani abu abarsa kawai yayi aurensa Bayan wannan ma yana da ikon k’aro wasu matan biyu.

Sultana bilkisu da Sultana Sadiya sudai basuce komai ba saidai binsu da suke da ido, sultana sadiya haushin mijinta taji ganin za’ayi ma d’iyarsa kishiya ammah bai damuba sai ma turawa da yakeyi.

dada ce cikin 6acin rai tace suhail inbanda abunka miye na gaugawa shi fa aure lokacine, kaduba kaga mutuncin matarka ‘yar uwarka.

memartaba murmushi yayi yace dada kubarsa yayi aurensa tunda yana da burin yi.

dada tace ranka ya dad’e gaskiya ni ban aminceba ban yarda yawulak’anta min jikaba daman nasan yanayin zamansu kuma kaduba kaga….. memartaba d’aga mata hannu yayi yace ya isa haka k’ara auren da zaiyi ba shine yake nufin zai wulak’anta sumayya ba kuma na yarda da suhail nasan ko fiye da mata biyu aka basa zai iya kula dasu domin yana da hankali.

dada shuru tayi batace komai ba.

memartaba yace ko akwai me magana acikinku?

gaba d’ayansu sukace a’a ranka ya dad’e.

memartaba kallonsa yamaida ga Yarima suhail da yake zaune k’asa kansa sadde a k’asa yana sauraransu domin shima kansa baiso amincewarnan da akayiba dan dai ba yarda zaiyi ne kuma yanason cika umurnin iyayensa, muryar memartaba ce yaji yace suhail ka fad’ama iyayen yarinyar zamu tura a neman maka aurenta, dafatan dai ka fad’a ma matarka zaka k’ara aure?

Yarima Suhail girgiza kai yayi yace a’a ranka yadad’e bata saniba, memartaba yace toh shikenan kaje kasanar da ita nasan sumayya batada matsala zata amince.

Yarima Suhail yace toh ranka yadad’e.

memartaba yace zaku iya tafiya idan ba mai magana.

gaba d’ayansu duk’awa sukayi suka kwashi gaisuwa sannan suka tashi suka ficce.

Yarima bai koma 6angarensuba motarsa yashiga yaficce yatafi asibiti saboda akwai theater d’in da zai yi ma wasu.

 

Sultana Sadiya cike da tashin hankali takoma 6angarensu a parlour tayada zango tare da korar duk ma’aikatan da suke ciki nan tafara saffa da marwa tana jiran Sultan Abbas da yatsaya suna magana da Daddyn yarima.

Bayan kamar minti biyar sai gashi ya shigo, da mamaki yatsaya yana kallonta yace lafiya Sadiya naganki haka?

Cike da 6acin rai tace haba Abban sumayya wannan wane irin cin mutuncine yaron nan yakeson yi mana, kaduba kaga duka yaushe akayi bikkinsu dukaba shekara d’aya da rabi kenan ammah wai aure zai k’ara.

Murmushi Sultan Abbas yayi yace toh menene dan zai k’ara aure?

Sultana Sadiya tace kai wai naga kamar baka damuba d’iyarka fa ce za’ayi ma kishiya saikace bakasan ciwontaba?

Murmushin takaici Sultan Abbas yayi yace sadiya nine bansan ciwon Sumayya ba? nine mahaifinta kuma ita da suhail basuda banbanci dukansu ‘ya’yanane kuma bari kiji dakaina ma zan iya zuwa inneman masa aurenta dan haka idan zaki sa d’iyarki tanutsu tabi mijinta toh inkuma taje garin haukanta takashe aurenta toh baruwana dan haka shawara tarage taku, yana kaiwa nan yaficce yabarta nan tsaye.

 

da harara sultana sadiya tarakasa tace ai zamu gani, wayarta tad’auko takira sumayya.

Lokacin Sumayya tana kishingid’e tsakiyar kuyanginta nan aka mik’o mata wayar tayi picking tace ummah ya dai?

ummah cikin fad’a tace ke jakkar inace mijinki yana nan yana shirin k’ara aure.

‘yar dariya sumayya tayi tare da mik’ewa tanufi bedroom d’inta tana cewa haba dai yariman nawa? taya zaiyi aure?

Sultana Sadiya ta k’ule sosai cikin tsawa tace ke wace irin bahuwace? ina fad’a miki ammah baki ma damuba.

Sumayya zama tayi saman bed d’inta tace ummah ai nad’auka tsokanata kike.

Sultana Sadiya tace wace irin tsokana yanzu muka zauna da iyayenku akayi maganar har da memartaba kece kawai baki saniba.

 

Sultana Sumayya a firgice tamik’e tsaye tace ummah yariman nawa zaiyi aure batare da na saniba?

Ummah tace k’warai kuwa sumayya abun bak’in cikinma har da mahaifinki cikin masu goya masa baya.

sumayya k’asa tazauna tare da fashewa da kuka tace ummah yanzu yarima ne zai yaudareni yak’ara aure?

ummah tace ai saisa naso kihaihu ammah kika k’i d’aukar shawarata daman abinda nake guje miki kenan domin nasan halin yaudarar maza saboda basuda tabbas.

Sumayya cikin kuka tace wlh bazan yaddaba babu macen da zata auri yarima duk ma wadda tayi gigin shigowa wlh sai na kasheta domin bazan zauna da kishiyaba.

ummah tace kisa kuma sumayya? kibari mubi komai a hankali nima kinsan ba zan ta6a amincewa ayi miki kishiyaba domin farin cikinki shine nawa.

Sumayya cikin kuka tace kuma dada tasan da maganar? Ummah tace babu fa Wanda bai saniba.

K’ara fashewa tayi da sabon kuka cikin d’aga murya tace wlh k’aryane babu macen da ta isa ta auri mijina wlh ko ma wacece sai na kasheta, tana fad’in haka tayi wurgi da wayarta tare da duk’ewa tana wani irin kuka me tsuma zuciyan mesaurare dasauri tatashi tafito tanufi 6angaren yarima ammah tana shiga taga baya nan.

dan haka tafito tadawo d’akinta tana wani sabon kukan nan tafara watsi da kayan d’akinta dan dressing mirror d’inta batabar komai ba duk ta watsesu k’asa masu fashewa sunayi masu zubewa sunayi sumbatu tafarayi wlh sai nakashe ko wacece ba zan ta6a yadda a auremin mijiba saman gado tafad’a tana me cigaba da risgar kuka,

ma’aikatanta tsaye sukayi daga wajen d’akin sukayi cirko-cirko suna jinta ammah ba mai iya shiga d’akin gudun kar suma 6acin ran yashefesu…..

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_*Wannan page d’in na sadaukar da shi agareku Mamansadiq, Mummyn khadija nd Mrs Dawud ina alfahari da ku a kodayaushe, godia ta agareku bazata ta6a gushewaba wlh ko da page ko ba page nariga na ajeku waje guda acikin zuciyata*_

 

Back to top button