Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 25

Sponsored Links

PAGE* 2⃣5⃣

ko da suka shiga part d’in yarima lokacin bai dad’e da dawowa aikiba kasancewar busy yake idan yafita baya samun dawowa sai dare, tsaki yaja ganin bedsheet an shimfid’a masa yace kai dada ba zata ta6a kyaleni inhutaba.

bayan ya fito wanka ya shirya zaune yake bakin gadonsa yana waya jin ana knocking d’in k’ofa yasa yabada izinin ashigo.

zarah ce gaba sai jakkadiya a baya ido hud’u sukayi da yarima sai da gabanta yafad’i tsaye tayi takasa k’arasawa, jakkadiya ce tazube tana kwasar gaisuwa, d’aga mata hannu yarima yayi nan tafara kame-kame am daman… yarima katseta yayi yace zaki iya tafiya.

jakadiya k’ara duk’ar da kanta tayi tace atashi lafiya ranka yadad’e, sannan takalli zarah tace saidasafe gimbiya, zarah gyad’a mata kai kawai tayi.

bayan jakadiya ta fita yarima bai waiwayi inda zarah takeba, zarah tsayuwa tayi na kusan minti biyar ga tsoro da yabaibayeta ga gajiyar tsayuwa har tafara tunanin tazauna k’asa chan sai taji muryar yarima yace zaki iya zuwa kid’auro alwallah.

zarah muryarta tana rawa tace ina da alwallah, d’ago kai yarima yayi yakalleta sannan yatashi yashiga toilet yad’auro alwallah.

bayan ya fito wajen da aka tanada dan sallah yanufa babban dardumane a shimfid’e sai ‘yar k’aramar drawer mai d’auke da alqur’anai da sauran littafan addini.

yarima batare da ya kalletaba yace kizo muyi sallah.

zarah ahankali tace nayi sallah, ganin yarima yajuyo ya kalleta yasa dasauri tazo bayansa ta tsaya, sannan tace banzo da hijab ba.

yarima batare da ya kalletaba yawuce yaje yabud’e wardrobe sai gashi da hijab nan yamik’a ma zarah takar6a tasaka.

yarima yana gaba zarah tana bayansa yaja musu sallah, raka’a biyu yayi musu bayan sun sallame addu’a sosai yayi musu sannan yajuyo yakama kan zarah yayi mata addu’a.

zarah ko da tana a tsorace saida ta jinjina ma ilimin yarima dan bata d’auka yana da addini hakaba.

yarima kallonta yayi nan yayi mata tambayoyi akan addininta zarah a nutse take basa amsa, shi kansa yarima saida taburgesa ammah bainuna mataba, wayarsace da tafara ringing yad’auka yana ta wayarsa akan wata kwangila da zai bada saida yayi kusan minti talatin yana waya har ya mance da zarah da take zaune bayansa a nan tafara gyangyad’i.

mik’ewar da yarima yayi ne yalura da ita, janye wayar yayi daga kunnensa yace kije kikwanta in bacci zakiyi.

zarah batace komai ba tana kallonsa yasa k’afa yafita daga d’akin.

parlour yakoma yasha ruwa sannan yazauna saman cushin yacigaba da wayar.

zarah jin shuru bai dawoba cikin ranta tace ko dai yabar min nan inkwanta shi parlour zai kwana, murmushi zarah tayi nan hankalinta yad’an kwanta tatashi taje saman bed d’insa saida tacire alkyabba da hijab d’in sannan takwanta tare da jawo blanket tarufe jikinta takashe gloves nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

 

yarima ko da yagama wayar d’aga kai yayi yakalli agogon bango ganin 11:55pm yasa yamik’e yanufi bedroom dan yakwanta, kunna gloves yayi nan haske yagauraye d’akin hango zarah yayi tayi daid’aya saman gado sai baccinta takeyi, shi shaf ma ya mance da akwai mutumin a d’akin.

tsaki yaja har ya juya zai fita sai yayi wani tunanin, ahankali yataka yaje saman gadon yahau, kwanciya yayi gefen zarah tare da juya mata baya yana sak’e-sak’e cikin ransa.

saida yayi kusan minti goma sannan yajuyo yana mai k’arema zarah kallo ya dad’e yana kallonta sannan daga baya yakai hannu yajanyota jikinsa tare da rungumeta saida gabansa yafad’i, nan yakai hannu yafara shafar jikinta, wani irin yarr yaji saida yadad’e yana shafarta sannan yafara k’ok’arin rabata da rigar da take jikinta

zarah har k’ara gyara kwanciyarta take a jikinsa alamun taji dad’in kwanciyar jin ta6awar da akeyi mata tayi yawa yasa cikin bacci tayi firgit tafarka ganinta jikin yarima yasa wani tsoro yad’arsu a zuciyanta cike da tashin hankali tashiga turesa tace nashiga ukku menene haka please kakyaleni.

yarima k’ara matseta yayi a jikinsa muryarsa tana rawa yace kinsan dai dole ko bama so sai mun amince ma juna saboda ansa mana ido yin hakan kawai zaisa kar a zargemu.

zarah cigaba tayi da turesa tace nidai kakyaleni wlh bana so, bata ankaraba sai jitayi yarima ya rabata da rigar da take jikinta, fashewa tayi da kuka tare da turesa da dukkan k’arfin.

yarima ganin zata 6ata masa lokaci yasa yakwantar da ita tare da danneta, zarah cikin kuka tace dan Allah kayi hak’uri kar kayimin komai, yarima bakinsa yakai cikin nata yafara kissing d’inta, inda hannuwansa suka kasa tsayawa waje d’aya a jikinta, ba yarima ba hatta ita kanta zarah saida salon yarima yarikitata batasan lokacin da tafara mayar masa da martaniba, sun dad’e a haka sannan daga bisani yarima yanemi hanya……….

kuka, yakushi, cizo babu wanda batayi masaba ammah bai kyaletaba dan yarima tuni ya fita hayyacinsa baisan inda kansa yakeba saida yasamu nutsuwa sannan yamirgina gefe yakwanta yana maida numfashi.

wani irin nishad’i ne da sanyi yaji yana ratsasa ji yake kamar bai ta6a sanin wata maceba sai akan zarah, ahankali yabud’e idonsa yasafkesu kan zarah da hawaye suke zuba idonta, blanket yajanyo yalullu6e mata jikinta sannan yamik’e yashiga toilet dan yatsarke jikinsa.

bayan ya fito d’aure yake da towel saida yashirya sannan yazo inda zarah take har lokacin kwance take tana cize le6e idanuwanta a rufe, hannu yakai yafara yaye blanket d’in da take rufe da shi, dasauri zarah tabud’e idanuwanta da sukayi jawur tare da rik’o blanket d’in.

yarima kallonta yayi cike da tausayi yace ba abinda zanyi miki, taimaka miki kawai zanyi kiyi wanka.

zarah cikin muryarta da tadishe saboda kuka tace ni kakyaleni dakaina zanyi.

yarima yace ai baki iya takawa.
zarah cikin muryar kuka tace zan iya, tashi tayi zaune dakyar tare da k’ara gyara rufin blanket d’in.

ganin haka yasa yarima yatashi yad’auko mata towel yabata, nan zarah tafara kicin-kicin d’aura towel tana kare jikinta, yanayin yadda takeyi taso taba yarima dariya, ganin haka yasa yajuya har saida tad’aura sannan yajuyo, hannu yakai zai ruk’ota nan tafizge tace kabarni zan iya tafiya.

tana cize Le6e tasamu tamik’e, dakyar tasamu tayi taku d’aya nan tatsaya tare da lumshe ido, tana k’ara taku na biyu wani irin k’ara tasaki.

ganin haka yasa yarima yace ai daman nasan bazaki iyaba, d’aukarta yayi bai zameta a ko’inaba sai cikin ruwan d’umin da yahad’a mata, wata irin k’ara zarah tasaki tare da ruk’unk’umesa, yarima maidata cikin ruwan yayi tare da fizge towel d’in da yake jikinta, zarah dasauri takai hannu tarufe k’irjinta cikin kuka tace katafi zanyi da kaina,

jin haka yasa yarima yafito yabarta a toilet d’in, saida tadad’e cikin ruwan sannan tacanza wasu.

saida tagasa jikinta sosai sannan tayi wankan tsarki tajawo towel tad’aura, ahankali take takawa tana cize le6e har tafito, lokacin yarima har yacanza bedsheet

ganinta yasa yanufi wajenta, zarah muryarta tana rawa tace kabarni zan iya.

jin haka yasa yarima yatsaya yana binta da kallo har taje wajen gadonsa tazauna.

Zuwa yayi cikin lallashi yace kikwanta mana, girgiza masa kai tayi cike da tsoro tace a’a nan ma yayi,

yarima haushi yaji ganin yadda yake lalla6ata ammah sai botsarewa take dan haka yawuce yaje yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya.

zarah ganin haka yasa tajingine kanta da gadon a nan bacci yafara fizgarta, daga k’arshe da taga ba dama ta ida hayewa saman gadon ta kwanta chan k’arshen gado tare da takure jikinta har a lokacin tsoron yarima takeyi.

bayan kamar minti goma yarima yajuyo yanayin yadda take baccin yasa yayi murmushi nan yamik’e ahankali yagyara mata kwanciyarta tare da rufeta da blanket.

gefenta yakwanta tare da zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yana kallon yadda take baccin cikin nutsuwa, daga k’arshe yajuya tare da maida idanuwansa yarufe, tunanin darensu na farko da sumayya yafad’o masa a rai, dasauri yajanye tunanin daga zuciyansa gudun kar zargi yashiga,
ya dad’e kwance sannan daga baya bacci yayi awon gaba da shi

saida aka fara sallar asuba sannann yafarka, kallon zarah yayi da taketa baccinta sannan yamik’e yaje yad’auro alwallah bayan yafito, tadata yashiga ammah tak’i tashi,

ganin haka yasa yarima yafara k’ok’arin zareh mata blanket d’in da take rufe da shi, dasauri zarah tabud’e idanuwanta cikin muryar bacci tace na farka.

yarima yucewa yayi yakabbara sallarsa, har yagama sallah zarah tana nan zaune saman gado, saida taga ya juyo ya kalleta sannan tamik’e dakyar tana bin bango tare da cize le6e ahankali take takawa har tashiga toilet.

bayan tayo alwallah rigarta tad’auko tamaida sannan tasaka hijab, nan tasamu tayi sallah.

bayan ta gama a nan k’asa tayi kwanciyarta tare da k’udindine jikinta nan da nan bacci yad’auketa.

 

yarima bayan ya gama addu’o’insa ganin zarah tayi bacci yasa yawuce yahaye gadonsa yayi kwanciyarsa.

zarah juyi takeyi baccin duk batajin dad’insa saboda k’asan da take kwance, juyawa tayi tare da farkawa jin wuyanta zaiyi ciwo yasa tamik’e dakyar tataka taje takwanta chan k’arshen gado nan tacigaba da baccinta.

wajen k’arfe tara yarima yafarka, mamakine yakamasa ganin zarah saman gadon baisan lokacin da tadawoba.

tashi yayi yaje yashiga wanka bayan ya fito shiryawa yayi cikin boyel d’insa fari yayi gwanin kyau, jin ana knocking d’in k’ofa yasa yakalli zarah da taketa bacci ahankali yabud’e k’ofar yafita gudun kar tafarka, a tsakiyar parlour yatarar da jakadiya tsugunne k’asa ganinsa yasa duk ta dabarbarce tare da duk’ewa k’asa tace ranka yadad’e kagafarceni daman dadace ta aikoni.

haushine yakama yarima cikin ransa yace wannan tsohuwar ba zata ta6a barina inhutaba, fuskarsa ba alamun fara’a yace me tace?
jakadiya tace Allah yaja da ranka daman bedsheet ne tace ind’auko a wanke.

yarima zama yayi saman cushin sannan yace zaki iya shiga kid’auka.

jakadiya tun kan ya ida rufe baki ta mik’e ta nufi bedroom d’insa bayan ta d’auko duk’awatayi tace ranka tadad’e… hannu yarima yad’aga mata tare da nuna mata k’ofa.

dasauri jakadiya tamik’e tafita.

yarima tashi yayi yashiga bedroom, kallon zarah yayi da har lokacin take bacci sannan yaje saman bedside yad’auko yawarya, yana d’auka zarah tabud’e idonta nan sukayi ido hud’u da yarima, ahankali yajanye idonsa daga kallonta, saida yafara tafiya zai fita batare da ya juyoba yace zan sa akawo miki kayanki nan sai kiyi wanka ga magani nan saman bedside idan kinci abinci sai kisha, wayarsace da tafara ringing yayi picking tare da fita daga d’akin.

zarah binsa tayi da kallo har yaffice yamaida mata k’ofar yarufe, runtse idanunta tayi hawayen da take dannewane suka shiga kwaranya daga idanunta tana jin wani k’unci a ranta.

yarima bayan ya fita part d’in zarah yaje bayan kuyanginta sun gaishesa nan yake basu umurni sukaima zarah kaya a part d’insa sannan yatafi.

A chan 6angarensu dada jakadiya da gud’arta tashiga part d’in dada, dada jin jakadiya tayi gud’a yasa tafahimci dalilin haka.

jakadiya gaban dada taduk’a cike da girmamawa tace ranki yadad’e, gimbiya ta kawo mana mutuncinta a masarauta, nan jakadiya tabud’e ma dada bedsheet tagani.

murmushi dada tayi tace Alhmdllh daman daga ganin yarinyarnan nasan zatayi hankali, gaskiya naji dad’i yanzu aje ayi sanarwa kowa yasani sannan kuje kugwada ma su memartaba da iyayen yarima.

duk’awa jakadiya tayi tace an gama ya shugabata sannan tamik’e tafita tana gud’a.

A fada memartaba shanuwa guda yaba zarah, sannan yabada babban sa guda yace ayanka kowa yaci, abban yarima rago biyu yabayar, sultan abbas ma rago yabayar, ko da akaje wajen sultana sadiya bak’in cikine yacikata haka tadaure taje tad’auko turmin Holland tabada, sultana bilkisu kuma sark’ar zinari tabayar,

nan gida yakauraye da murna, sumayya ko da taji dalilin murnar shigewa tayi bedroom d’inta tafad’a saman gado tacigaba da risgar kuka kamar wadda aka aikoma da sak’on mutuwa tsanar zarah taji ta k’aru a cikin ranta, dakyar tajawo wayarta takira sultana sadiya, sultana tunda taga Kiran tasan dalilin kiran da sumayya tayi mata.

tanayin picking tajiyo kukan sumayya cike da tashin hankali tace sumayya menene abin kuka? meyasa kikeson 6ata hawayenki akan wata banza ‘yar talakkawa kiduba darajata da ta mahaifinki a gidannan kema kinsan kin zarce kowace mace.

sumayya cikin sheshek’ar kuka tace ummah wlh na tsani yarinyarnan zan iya kasheta saidai nima akasheni.

sultana sadiya cike da tashin hankali tace kisa kuma? haba sumayya nace kidaina ik’irarin kisa kibari mubi komai ahankali,

sumayya cikin kuka tace haba ummah kiduba kigani yanzu anyimin adalci saboda Allah? ni lokacin da na auri yarima duk bansamu wad’annan abubuwan na al’adaba ammah wata bare daga zuwanta ta samu.

sultana sadiya cike da lallashi tace haba sumayya kiyi hak’uri man, nima hakan yayi min ciwo kibarmin komai a hannuna wannan yarinyar dole tabarmiki kidinki kiwala ke kad’ai, ina gargad’inki kar kikuskura kija ta rigima, dan kinsan abun fad’a baya wahala a masarautarnan, kibarta daga ita har wannan miskilin mijin naku duk zanyi maganinsu.

sumayya share hawayen fuskarta tayi cike da jin dad’i tace yauwa ummana saisa nake k’ara sonki.

sultana sadiya saida taga ta kwantar ma d’iyartata da hankali sannan sukayi sallama takashe wayan.

 

A chan 6angaren zarah bayan yarima yafita dakyar tasamu tasafko daga saman gadon saida tagyarasa sannan tashiga toilet, tak’ara gasa jikinta tayi sannan tayi wanka.

mai tashafa, fuskarta powder da lipstick kawai tasamu, knocking d’in k’ofar da akeyine yasa tamik’e tajanyo hijab tasaka sannan tabada izini ashigo.

d’aya daga cikin kuyangarta ce tashigo cike da girmamawa taduk’a tagaishe da zarah, fuskar zarah d’auke da murmushi ta amsa, kuyangarta tace ranki yadad’e daman maigirma yarima ne yace akawo miki kaya.

zarah kar6ar kayan tayi nan kuyangar tamik’e tabar d’akin, zarah gown d’in atamfarta tasaka, tana gaban dressing mirror tana d’aurin kallabi taji ana Knockin dakyar tafito parlour sannan tabada izini ashigo jakadiya ce fuskarta d’auke da fara’a tashigo, duk’awatayi k’asa tace Allah yataimaki gimbiya da fatan kin tashi lafiya?

zarah tace lafiya lou.

zarah ganin bakin jakadiya yana motsi yasa tace jakadiya ya dai?

jakadiya washe baki tayi tace ranki yadad’e ai mu abun murna ya samemu shiyasa nazo inmiki albishir kyauta kika samu mai tsoka a gidannan.

zarah cike da mamaki tace kyauta kuma? ta me?

jakadiya gyara zamanta tayi tace mrmartaba yabaki sa, mahaifin yarima da mahaifin gimbiya sumayya sun baki raguna, mahaifiyar sumayya ta baki atamfa, mahaifiyar yarima tabaki zinari duk suna wajen dada sai yarima yadawo za’a damk’a masa yabaki.

zarah da mamaki ya ida kasheta tace jakadiya duk na minene?

murmushi jakadiya tayi cike da jin dad’in labarin da take badawa tace ranki yadad’e ai nakawo butulcinki da kikayine gidan miji.

zarah saida gabanta yafad’i cikin ranta tace nashiga ukku yanzu saida kowa yasan abinda nayi?

jin tayi shuru yasa jakadiya tace kinsan gidan sarauta mutuncin mace shine taje a cikakkiyar budurwarta.

zarah kwallah tacika mata ido ahankali tace yanzu saboda Allah saida kowa yasan wannan abun?

jakadiya gyad’a kai tayi tace eh ranki yadad’e ai dole kowa yasani dan abun murna da farin cikine, nan jakadiya tak’ara duk’awa tace nabarki lafiya ranki yadad’e.

zarah kasa cewa komai tayi har jakadiya tafita daga d’akin, ahankali tace wannan wane irin tonon asirine, yanzu saboda Allah sai kowa yasan abinda nayi?
kife kanta tayi tadinga rusa kuka saida tayi mai isarta sannan tatashi taje dining tad’anci abinci kad’an sannan tajanyo alkyabbarta tasaka tafito takoma part d’inta.

sama-sama ta amsa ma kuyanginta gaisuwarsu tashige bedroom d’inta, kwanciya tayi kanta yana kallon ceiling ahankali tunanin abinda yarima yayi mata daren jiya yadinga dawo mata a rai, hawayene suka dinga zuba daga gefen idonta, cikin ranta tace nasan ba’a son ransa yakusanceniba tsaki taja tace ina amfanin wannan masarautar da ake tursasa mutum dole, tunowa tayi da malam bello wani abu yatsaya mata a mak’ogwaro tace Allah sarki malam bello ina ma ace kaine kakasance mijina ba wannan ba, dasauri tajanye tunanin a ranta tare da cewa Astagfirrullah, sannan tajawo wayarta takira su mama dan sugaisa.

 

A chan 6angaren sumayya kuka taci sosai a ranar kasa cin abincin kirki tayi, kad’an-kad’an ummah ta kirata tabata hak’uri.

 

yarima ko da yadawo daga wajen aiki ko 6angarensa ba’a barsa yashigaba wani dogari yazo ya isar da kiran da dada takeyi masa,

ko da yaje turakarsu dada bayan yagaisheta dada fara’ar fuskarta takasa 6oyuwa kallonsa tayi tace d’an albarka hak’ik’a naji dad’in za6en da kayi dan ko bakomai takawo mana mutuncinta a gida kuma munasa ran bazata bamu matsalaba fatanmu nan da watanni tahaifo mana magaji.

shidai yarima tun da yazauna dannar wayarsa kawai yakeyi baice ufan ba, dada tana kallonsa tace yarima ina maka magana kayi shuru ka kyaleni, murmushi yarima yayi batare da yad’ago kansaba cike da k’osawa da maganar dada yace ina jinki dada.

dada tace au wulak’ancin nakane yamotsa? shuru yarima yayi baice komai ba, ganin haka yasa dada tace toh nidai nasihar da zan maka itace kazauna da matanka tsakani ga Allah, banda nuna banbanci, kahad’a kan matanka suzauna lafiya.

yarima yace toh dada,

mik’ewa dada tayi taje tad’auko masa kyautukan da zarah tasamu tabashi tace ga kyautukan da matarka tasamu sannan sanuwarta da raguna suna garke.

cike da mamaki yarima yace dada duk naminene? dada tace na mutuncinta ne da takawo mana a masarauta,

yarima murmushi yayi yace kai dada har yanzu dai kuna nan da wannan abun.

dada tace kuma bazamu ta6a dainawaba,

yarima mik’ewa yayi tsaye cike da tsokana yace ranki yadad’e indai kuna raye ba

dada ganin tsokanarta yake yasa tayi shuru takyalesa har yafita daga d’akin.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_~Alhmdllh laifin dad’i k’arewa, my blood zaynav ina tayaki murnar kammala novel d’inki mai suna *BASSAM* Allah yabaki ladar abinda kika fad’a daidai, kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, muje zuwa sai munjiki a sabon novel~_

_*Yau page d’in nakine Sis Harirah nagode sosai da kulawa da soyayyar dakike nunamin Allah yabar k’auna*_

 

Back to top button