Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 11-12

Sponsored Links

1⃣1⃣&1⃣2⃣

 

…………….rikota yayi zuwa jikin shi tana zamewa yace “wait Naziya please magana zamuyi kawai. zama yayi agefen gadon, ya dorata akan kafarshi, “Kiyi hakuri da duk Abinda yake faruwa that’s our destiny, komai zaizo karshe, nasan kinada tarbiya kinada hakuri please keep it up, zamuci ribar Abun, idan kikaci gaba da tafiya a haka banida wata damuwa, yakamata ace yanzu mun zama daya, yakamata ace muna cikin bargo daya, yakamata mu zauna muyi hira in kula dake kamar kowane miji, but don’t worry komai zai wuce, yafada yana zagaye west dinta da hannayen shi, tareda kwantar da kanta cikin kirjin shi, wani irin Abu takeji yana mata yawo a cikin jiki duk lokacin da ya tabata, kodon bata taba experiencing irin haka a Rayuwar ta bane. Jin yanda yake cusa kanshi a wuyan ta yasa take d’an zamewa domin tanajin yanda yake kokarin daga hijabin jikinta tareda nufar kirjinta yana so yaji how they are. Tayi Saurin riko Hannun shi tareda Saurin juyawa tana girgiza mai kai cikeda marai raicewa. Kallon ta yayi cikeda roko yanaso tabarshi yayi yanda yakeso ko zai rage zafi domin yasan bazai yuwu ya nemeta a dakin khaleel ba, kuma yana falo zai iya jinsu domin yasan bakaramin aiki zaiyi ba, kuma yasan zata iya mai kuka tunda ko kirjinta bai fara tabawa ba . “Naziya ” yakirata cikin wata irin murya, “inaso intaba inji, nonon ki nada kyau dazu kamar inyi tsalle in cafka nakeji Dana ganki ba hijab, kibani Dama ingansu inyi wasa dasu ko kadan ne. Wani irin tsalle tayi tareda zamewa ta rufe fuskar ta saboda kunya da maganar shi ta bata, kai namiji baida ta ido, saikace ba Ahmed innocent man ba yafada har yana dariya, “is OK tashi in rakaki wata rana da kanki zaki bani insha. Saurin mikewa tayi ya dafata “da munkwana tare da tuni sunzama toy dina, Amma lokaci ne. Kunya kamar ta nutse kasa, shikuwa ko ajikin shi,
Fitowa sukayi yana tsaye a falon rikeda ruwa mai sanyi yana kwankwada idanun shi cikin nata karab, idan ba gizo idanun ta suke mata ba tana ganin irin kallon rainin hankalin da yake mata, hartayi Saurin kwace Hannun ta ta wuce da Sauri, yana “baby ba Sallama, ita kuwa bazata iya tsayuwa kusa da d’an rainin hankalin nan bane Sam, mai halin yahudawa, ace mutum kullum cikin guntayen kaya kamar wani nakan dutse, mtsww.

Saurin wucewa dakin yayi yana karewa gadon nashi kallo yaga yanda zanin ya zame gaba daya, saboda zaman da sukayi a gefen shi, kuma bakaramin jujjuyawa Ahmed yarikayi ba saboda mugun feelings din da yakeji, shigowa yayi yace “Sorry Bari in gyara mana gadon, shiru yayi har yagama ya wuce bathroom, yana kallon yayan nashi bai ce tak ba, ganin yayo wanka yafito yaganshi a tsayen yace “yadai ko wankan kaima zakayi? “No ba munyi wanka ba kaima naga weather din is OK why you bath again? “Hhhh oh come on brother ko bakaga ma tata ta shigo ba kaima kasan dole inyi wanka ai. “in ten minutes? Ya fada batareda ya san maganar ta fito ba, “of cos is enough for me. Ya bashi Amsa tareda hayewa gadon ya kwanta cikeda farin ciki, kafin ya tuno da tea ya diro ya tsiyaya ya farasha yana lumshe idanun shi.
Komawa yayi kan kujera ya zauna yana danna waya har Ahmed yagama ya haye gadon yana cewa “ga coffee idan zakasha narage maka. “Uhm. Kawai ya Amsa, ganin Sam bazai iya bacci ba ya mike ya shiga bathroom wanka yayi tareda Alwala yadawo dakin yatada sallah.

 

Gefen Naziya kuwa, tayi bacci cikin kwanciyar hankali tareda farin ciki, tasan Allah yabata miji mai halin kwarai kuma da yardar Allah zata tayashi yiwa mahaifiyar shi biyayya.
Sabo da tashi da wuri Karfe hudu ta tashi, saida ta yi sallar nafila kafin biyar tayi farillah, ta zauna Azkar zuwa Karfe shida ta fito cikin karamin hijabi zuwa kitchen, ta shirya musu breakfast mai lafiya. Kafin bakwai da rabi ta kammala ta gyara ko Ina takoma tayi wanka, shiryawa tayi cikin Riga da zani, tafito tsab, tana kamshi.
Kiran mommy yasa ta fito da gudu tana amsawa ta ganta hakimce, dukawa tayi ta gaida ita, “ke bakisan kiyi pleasing uwar miji ba ta hanyar shiga dakina ki gyaramin da kuma dakin khaleel, toh daga yau gyaran dakunan mu na Hannun ki idan kin tashi. “Toh mommy. “Oya a shirya mana breakfast anan yau ma.
Fitowa Ahmed yayi idanun shi kur akanta yana aika Mata da sako tareda murmurshi mai cikeda sirrika. Itama tayimai tareda dukar da kanta tafara aikin ta,
“Ina Ibrahim din? Bacci yakeyi jiya baiyi bacci da wuri ba yace sai ya tashi. “Aa nifa banason wasa da ciki, ke Naziya yi Sauri ki kaiwa dana Abinci a daki karya kwanta da yunwa. “Mommy da kin Bari ya tashi. “Wuce maza ki kaimai. tafada, tana cewa “jeki zanyi serving din mu maza ki tabbatar yaci kafin ya kwanta. Jim tayi kamar bazataje ba tace “me kike jira? Cikin tsawa, da Sauri ta dakko tray ta shirya mai komai nashi ta wuce jiki a sanyaye “Allah yagani itadai jinin ta bai hadu dana gayen nan ba, baiyi mata ba Sam, da Sallama ta shiga dakin, yana kwance a tree seater a kudun dune, fuskar shi ce kawai a bude. Idanun shi biyu yana kallon sama, Sallamar ta yasa ya d’an juyo cikeda yanga, ta tsaya daga nesa muryar ta na rawa ga shi inji Mommy, ta dora akan karamin table zata juya, “Serve me. Yafada cikin isa, tayi Saurin juyowa “wannan mugun d’an rainin wayau ne, batason musu don haka cikin Sauri ta juyo batareda ta kalle shiba ta hada mai komai tafita cikin Sauri.
“Hmmm kawai yace yafara cin Abincin shi. Yana lumshe idanun shi.
Komawa tayi falon tace tabashi. Kafin ta zauna tafara nata Karin.

Toh haka dai kwanaki keta tafiya yau Naziya ta kai wata daya cur Agidan komai na gidan tundaga gyaran dakunan su zuwa kitchen ya koma Hannun ta, complain din momy ya riga ya shiga jikinta, Ahmed kuwa yanzu ganin shima gagarar ta yakeyi domin dokar mommy tayi nisa yanzu, tun yana rokonta harya hakura ya zura ido, sai rama yakeyi a tsaye saboda damuwa baya ko son haduwa da Naziya saidai suyi chart da wayar da ya siya mata katuwa wadda ta boyeta a dakin ta bata Bari mommy tagani ba, by now ta fuskanci muguwar kiyayyar da mommy ke mata. Idan ya fita aiki kuwa yana kiranta kullum bata hakuri yakeyi,. Tana kwantar mai da hankali domin ta saki jiki dashi sosai, yanzu har marmarin ganin shi takeyi akusa da ita she is missing his touch, rabon da ya rungume ta tun a dakin Khaleel, kullum Aunty Raliya shawarwari take bata wainda Sam basuda Amfani a wurin ta tunda an hanata sakewa da mijin ta. Iyakar ta dashi sai ban hakuri tareda Sanya mata Albarka a kullum “Naziya ke Y’ar Aljannah ce, watara na zakiyi farin ciki, ki Kara hakuri komai mai wucewa ne.

Bikin khaleel Ansa rana wata daya mommy sai shiri akeyi An shirya event Kala Kala, khaleel ko a jikin shi domin Amaryar ma ko wayar ta baya dauka, Wanda ta watsa shi a kwandon shara tunda dai uwar miji na sonta ai zata wataya kuma dole ya sota.
Zaune suke a office din yayan nashi ya kalle shi “brother sai ramewa kakeyi are you Alright? “Am not khaleel, yama zan zama cikin kwanciyar hankali bayan kana ganin me yake faruwa? “Am sorry Yaya bansan yanda zantaimake kaba. “Is OK yanzu kaga maganar shigo da kaya zai zo dai dai da lokacin Auran ka naso kaje da kanka, ko zaka Bari kaje honey moon gaba daya? Yafada yana d’an murmurshin karfin hali. “Noo wane irin honey moon? Zantafi kawai idan nadawo ai ba guduwa zatayi ba. OK kafadawa mommy ba ruwana.

Karfe biyu suka shigo gidan, an baje akwatunan sunkai saiti bakwai an narka dukiya kamar za asiyo mutum, suna shigowa tace “Yauwa khaleel zoku gani komai yaji? Tafada cikeda farin ciki, ya zauna yana kallon kayan tareda mamaki ” mommy kayan Waye duka? “Ga rainin wayau, na Matar ka ne mana. “Duka? Yes gaskiya aa a raba biyu abawa Naziya rabi. “Why zan bata rabi? Saboda am sure ba ayi mata irin haka ba. Yafada cikin zafin rai, “bazan bayar ba domin batasan darajar suba, fitar kunya nakeson inyi dasu gidan minister guda dole akai Abinda baza a raina muba, Kuma ka nemo motar da za a hada mai tsada ta mata. Ahmed ne ya katse maganar “Zamuyi placing oder momy na kayan mu sai kasa a turo motar da kakeso kafin katafi.
Saurin kallon shi tayi tareda cewa “Ina zaije? “China zai shigo mana da wasu kaya. “Yaushe? Nan da sati uku. “Saboda mugunta? yaro zaiyi Aure ya Amarce shine zaka turashi wajen kwaso kaya? “Mommy, ni nace zanje ba Yaya ya sani ba, I want to go. “You are not going don haka ya shirya shi yaje, tunda nashi Auren baida Amfani, idan kanaso kaji dadi Ahmed sai ka Auro zabin zuciya ta Amma Indai Inada rai bazan hada iri da yar masu zama akan buzuba a mallake min da’.
Kallon momyn yakeyi wani iri, sometimes sai yaji kamar ba ita ta haifeshi ba, domin duk uwa tana son farin cikin d’an ta. Tashi yayi kawai yayi dakin shi dai dai tana fitowa ya ganta Amma saboda ciwon da kirjin shi ke mai yakasa ko tsayawa yayi mata magana. Kallon shi tayi sosai, taga ramar shi a yau tareda yanda yayi sanyi sosai, duk da ba mai hayaniya bane,
Jikin ta yayi sanyi, Allah yagani yanzu ba Abinda takeso irin su zauna suyi hira ido da ido ita dashi domin kullum soyayyar shi karuwa takeyi a zuciyar ta.
Kallon momyn khaleel yayi “mommy me kike nufi da d’an uwana? “Kamar ya? “Momy ki barshi ya samu natsuwa mommy don’t you see how sad he is? Bakya ganin yanda yake ramewa? Mommy Yayana na cikin damuwa sosai, I beg of you kibarshi ya huta haka. Wani irin kallon zanci ubanka tayi mai kafin ta mike cikin fada tayi dakin Khaleel din, “zanje inji dalilin da zai rika hadani da kai kana titsiyeni kamar ubana.
Binta yayi yana yi mata magana tayi banza tayi dashi. Zaune yake yana dafe kirjin shi, ta shigo “toh kanin uwata Wato da kun hadu saika rika zugo d’an uwan ka yana titsiyeni kamar ubana ko, toh ka fita I dona kuma ka saurare ni, nayiwa Kawata magana Hajiya sa’ade maganar Y’ar ta Salifa idan ka shirya zama da Matar son taka toh ka yarda ka Auri zabin rai na lokacin zanbaka damar da zaka zauna da Matar son taka.
Kallon mahaifiyar tashi yakeyi tareda yin tagumi saida ta ci gaba da fada yace “am sorry momy bazan iya musu dakeba kiyi duk Abinda ya dace insha Allahu zanyi miki biyayya. “What Yaya? Me kake fada? This is too much gaskiya Haba momy p…… “Quit Khaleel Yafada cikin dakamai tsawa, tareda nuna shi da yatsa “not a word again, why are you challenging our mother? Kar in kuma jin kalma daya daga bakin ka. Fita tayi kawai tana amsa wayar fauzy tana dariya “Y’ar Albarka wane irin product kike Amfani dashi na kayan kwalliya?
Wani irin bakin ciki khaleel yaji tareda kallon Ahmed din ya wuce domin shima ya batamai rai. kwanciyar shi yayi kawai yana kallon sama. Dawowa yayi ya tsaya akan shi “Yaya what ever is happening is not right. why zaka zuba ido kana over looking komai, how could you accept the second marriage? Ka manta me kafadamin, kaman ta kafadamin bazaka taba hada Naziya da wata mace ba? She didn’t deserve All this life Yaya, she deserve to be happy. “Hmmm ya kakeso inyi Khaleel? Inyi disobeying mommy oh what? “She is my mother Ina so mu rabu lafiya, and Naziya yes I love her more than my life, yazanyi dole inbi mommy in inaso inga dakyau, ba wata mace da zata samu matsuguni a zuciya ta, ita kadai nakeso ita kadaice zabina, if Auren da mommy zatayi min shine zaisa tabarni da matata in zauna lafiya then be it, am ready to obey what ever she said that’s final. Yafada yana mikewa cikin fushi yayi bathroom.

“She didn’t deserve it. Yafada yana naushin iska, he feels as kamar shi yafi kowa jin ciwon Abinda akeyi mata, ita kanta nuna wa take ba Abinda ke damun ta, tun ranar da tazo gidan nan yaganta tana kuka bai kuma ganin ta cikin bacin rai ba, sai kace bata da zuciya?
Fita yayi fuu dai dai tana shiga kitchen, cikin zafin zuciya ya bi bayan ta, kafin ta ankara jin hucin mutum kawai tayi yana fesa mata numfashi cikin zafi a bayan wuyan ta, kurawa kwantacciyar Sumar dake wurin idon ta yayi, idanun shi sun kada, he don’t really know why zuciyar shi ke tafasa, he is trying to control his Anger da baisan dalilin taba.
“Auzubillahi. Tafada tana ja baya da Sauri domin tsayuwar da yayi a bayan ta ya kaucewa tsarin Addini, kuma shi ba muharramin ta bane, wani irin kallon bakada tarbiya take watsa mai tareda nisan ta kanta daga kusa dashi, he can clearly read her reactions, don haka tuni zuciyar shi ta Kara hawa, “what? Why are you looking at me like that? Yafada yana describing da hannun shi, A haka zaki karasa zaman Rayuwar Auren naki you don’t care about your husband, kawai kiyi bacci ki tashi ki dafa Abinci, shine damuwar ki, you are pretending as if you don’t care about All this wealth, you are such a jocks, kin zauna kin baje ba Abinda ya dameki sai kici kiyi bacci you forget All your responsibilities, look if anything happen to my brother because of you, I won’t forgive you.
Tunda ya fara magana kallon shi takeyi, kuma irin kallon you won’t get away with this, yanayin shiru ta gyara tsayuwar ta tareda daga gira daya, and she look very cute, “oh really? So nice bansan responsibility dina ba? Saboda nayi shiru Ina kallon komai, waya fada maka Ina farin ciki da duk Abinda yake faruwa da zaman Aure na? Nice nakeda complain ba yayan kaba because I know my right, and da kake cewa duk Abinda ya samu yayan ka bazaka yafemin ba, ni kuma in wani Abu ya same ni fa? Kana tunanin iyaye na zasu yafe muku? “And don’t forget he is my husband, kuma munyi Aure saboda Ina son shi ba kiyayya ba, this house Hmm who told you am happy in this house? hakuri nakeyi bisa ga irin tarbiyar da aka dorani akai, iyaye nagari suka daga rayuwata, yawo da shigar da bata dace ba duk iyayen mu sun hane mu, shiga hurumin da bana muba duk iyayen mu sun hane mu, Saboda sudin iyaye ne nagari……… “Nice ba uwar kwarai ba kenan? Mommy tafada cikin tsananin bala’i
Jikin Naziya na rawa tayi Saurin kame bakin ta, tareda dana sanin biyewa zuciyar ta ta tsaya kula khaleel bayan hakan ma bai dace ba, yanzu tun ba aje ko inaba she is regretting……. 🖊

 

 

*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus: 🌻🌻AUREN GADO🌻🌻

 

*Matar soja ce*

 

Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,

Ga masu son su biya ga account details dina, *NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* sai Ku min magana ta wannan number 09069200154

 

🆓 page

Back to top button