Yar Zaman Wanka 39-40
“To Allah raya ya kuma ɗayyaba, ai sai na baku addu’a ma kafin na tafi wacce za a yi taro lafiya a gama lafiya” Cewar Malam yana ƴar dariya.
“Amin ya rabbi, ni kuwa zan tuna maka idan za ka tafi” Cewae Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.
“Tabbas lokacin da za ka tafi ba lallai ka tuna da takalmanka ba ma bare addu’ar da za ka bayar”
“Kar ki tuna min ai ni na ce zan bayar kuma ba sai kin tuna min ba dan ba na mantuwa”
“Ah to in kwa haka ne na yi katsalandan” Inna ta faɗa tana ƴar dariyar wasa.
Sa’adiyya ki zauna a nan ni zan raka su wajen marar lafiyar” Cewar Inna tana ƙoƙarin yin hanyar bedroom.
“Kamar ya Inna cikin ƙuryar ɗakin za ki kai su…
“Ikon Allah wai kina nufin marar lafiyar kuka haɗa ɗaki ɗaya da jaririn nan da aka fiddo? Kenan yana cikin ɗakin nan ba kwa tsoron faruwar wani abu?” Cewar Malam cikin mamaki dan shi ya ɗauka ɗaki aka ware wa marar lafiyar.
” Ah jikin ne dai yau da sauƙi amma ko jiyan nan gidan nan sai da kowa ya nemi mafaka har da masu shiga tukunyar jego, da masu shiga ƙasan gado, kai har ma da masu hawa saman bishiya, dan nan marar lafiyar yake bin kowa a guje” Cewar Inna cikin nuna tausayawa.
“Allahu akbar kin ga abin da ake gudu ko in ce dai ba makami yake ɗauka ba, ai wannan aikin manyan baƙaƙen aljannu ne” Cewar Malam yana kallon fuskar Inna da ya kasa gane kamar dai tana nuna alamar dariya.
“Ka dai bari Malam ai idan abin ya motsa sai dai du’a i”
“Yau kuwa za a yi maganinsu yau bacci zai yi har da munshari su kuma mu fatattake su, su bar jikinsa ba za mu ƙyalesu ba sai mun dangana su da kukar bulukiya, ko ma mu aika su bangon duniya, ke wasu ma har ƙasar sin muke aika su”
“Kai gaskiya gafarta Malam ka iya aiki yo irin wannan aiki ai ko miliyan aka baka ba a faɗi ba”
“Shi ya sa ai raina ya ɓaci da kika musa wato kika nuna na muku tsada in aka haɗa da ƙoƙarin da zan muku ai abin sadakar ba wani mai yawa na a zo a gani ba na faɗa”
“To ba komai ” Cewar Inna tana yin gaba.
“Ai ba da ke za a shiga ba mu kaɗai za mu shiga dan ba ma son kowa ya shiga saboda idan muna dukan aljannu kar a samu mutum” Cewar Malam yana kallon Inna.
Sadiya saurin miƙewa tsaye ta yi jin an ce wai za a yi duka. Wata harara Inna ta doka mata ta ce.
“In ba a nema masa lafiyar ba haka zai yi ta zama”
“Rabu da ita mana a mata bayanin da hankalinta zai kwanta, ba fa shi za a duka ba aljannun za a duka kuma da zarar mun ga sun fita za a dakata da dukan ki kwantar da hankalinki, ina ga ma sai an rufe ƙofa in muka shiga saboda ƙara da kururuwar alajannu kar ma ta yi zaton marar lafiyar ake duka ta zabura ta je ɗakin ko kuma shi ya fito a guje ya je ya ji muku ciwo kun san aljannu da shegen ƙarfin tsiya dan ma dai na taho da Ƙasimu da Habu” Cewar Malam yana kallon almajiransa da suka washe baki jin an ambace su dan suna da ƙarfin danne mai aljannu.
“Koma ki zauna” Cewar Inna tana kallon Sadiya. Komawar kuwa ta yi ta zauna duk da ta san dai tun da ta ga Inna tana ɗan kanne mata ido a ɓoye tabbas akwai ayar tambaya.
“Ƙasimu ku ɗakko kayan aikin maza” Ya faɗa yana gyara zaman rawanin hiraminsa.
Inna ce a kan gaba sai Malam sannan ƴan rakiyarsa, sai da suka gama shigewa cikin ɗakin Inna ta tsaya a jikin mudubi, Malam kuwa ajiye carbunansa ya yi a ƙasa yana cewa.
“Sai ni Malam Isuhu mai maganin duk wani shegen aljani, ban fito ba sai da na shirya gaba salamun baya salamun” Ya faɗa yana wani sunkuyawa ya ɗan naɗe ƙafar wandonsa, su ma sauran tattare hannuwan rigarsu suka yi tare da na ƙafar.
“Ina yake ne?” Cewar Malam yana kallon ɗakin da mamaki ganin bai ga marar lafiyar ba.
“Aifa sai kun yi da gaske dan yana ƙasan gado can yake shigewa ba ya son ma a zo kusa da shi” Cewar Inna tana kallon Malam.
“Allah sarki duk fa ba yin kansa bane, amma komai zai zo ƙarshe yau, jeki waje, inda hali ma rufo mana ƙofar dan wannan aikin ba na wasa bane” Cewar Malam.
“To shikenan bari na je daga wajen a yi aiki lafiya, to kuwa zan rufe muku ƙofar kamar yadda ka buƙata har mukulli ma zan saka” Cewar Inna tana ɗan juyawa da sauri ta fito daga ɗakin.
“Ƙasimu ku taho mu san yadda za mu fito dashi daga ƙasan gadon nan dan da alama aljanun nasa ma kafirai ne tun da basa son mutane” Inna ta tsinkayo muryar Malam lokacin da ta sanya mukulli ta rufe ƙofar.
“Habu ɗauki galan ɗin ruwan addu’ar ɗora shi bisa mudubi kar garin artabu a hankaɗar da shi, gwara in mun samu nasarar fito da shi sai a ɗakko shi idan za a fara ruƙiyyar” Cewar Malam da ke wajen drower yana ƙoƙarin sunkuyawa ya leƙa ƙasan gado.
“Malam kar fa garin janyo shi a ji masa ciwo, gwara a ɗage katifar yadda za a fito dashi salin alin” Cewar ƙasimu cikin girmamawa.
“Eh to kai ma ka kawo shawara gwara a ɗaga katifar” Cewar Malam yana mai fasa leƙa ƙasan gadon. Sai da Ƙasimu da Habu suka fitar da katifar suka jingine ta sannan suk shiga ɗaga filankin gadon, suna cire na ƙarshe sai ganin wani ƙaton miciji suka yi a kan wani lallausan bargo na yara ya fasa kai alamar sara.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Malam da almajiransa ai kan ka ce kwabo Malam ya kai bakin ƙofa cikin ruɗewa.
Ƙasimu ma sai gashi yana neman shan gaban Malam, Habu kuwa har bugar kafaɗar Malam ya yi. Amma Malam ya ma manta matsayinsa da yadda suke bashi girma burinsa kawai ya riga kowa fita daga ɗakin. Tsalle ɗaya Hassan ya yi sai gashi a gabansu ya ƙura musu ido gabaɗaya suka jingina a jikin ƙofar duk da wurin ya musu kaɗan amma a haka suka cakuɗa.
“Waye a kusa ne a zo a buɗe ƙofa” Cewar Malam da ya daddage ƙarfinsa kamar yana magana da waɗan da ke ƙofar gida. Inna da ke zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta saki dariyar mugunta ta kalli Sadiya ta ce
“Kin gani Halima ko ai ba mai taɓa miki ɗa da har kina damun kan ki yo Allah na tuba ina suka ga ƙarfin gwiwar taɓa miciji” Ta faɗa tana kallon Sadiya da ta saki baki galala tana kallonta, mamaki take duk tunaninta Inna ta wuce wurin lallai Inna gwana ce ta bugawa a jarida.
“A buɗe Malam mai sittin wata kan wata ne ke magana” Cewar Malam da ya dage ƙarfinsa yana tura ƙofar kamar zai karya ta almajiransa suna taya shi.
“Gafarta Malam har an fitar aljanun? Ka kai shi birnin sin ɗin?” Cewar Inna cikin ɗaga murya yadda za su ji.
Malam na shirin bada amsa miciji ya ƙaraso kusa da su hakan ya sa maganar da Malam ke ƙoƙarin yi ta sarƙe sai zare ido suke shi da almajiransa.
Cikin hanzari ya wani bangaje su Ƙasimu tsalle ɗaya ya yi sai gashi a kan gado, da yake an ɗage katifar sai ya faɗa kan filankin da ba a ɗage ba ji kake ƙumm ya bugu da jikin katako, wani zafi ne ya ratsa kansa da ya bugu ga mazaunansa da suka yi zaman ƴan bori a kan katakon idanu ya runtse ya buɗe a hankali aikuwa ya sauke su a kan Ƙasimu da Habu suna neman wajen mafaka sai zare ido suke ana kallon kallo.
“Wannan an yi gardawan banza wallahi, in ce dai nan kuke danne mai aljannu ƙaton gardi da ƙarfin tuwonku amma kun gagara mana maganin miciji ɗaya maimakon ku damƙeshi in samu ni da nake gaba daku in fita in ya so ku kwa san yadda kuka yi kuka kuɓuto” Cewar Malam yana zare ido cikin takaici da jin haushin almajiran nasa.
Babu wanda ya kula shi bare ya tanka masa dan basu da nutsuwar da za su tuna matsayinsa a wurinsu kowa ta kai ta kai yake kamar a filin ƙiyama. Ganin micijin ya ƙurawa Habu idanu Ƙasimu ya yi wani tsalle ya hau gadon inda Malam yake sai gashi ya faɗa kan Malam ɗin, ji kake gwaraf,ƙasusuwa da kayuwansu sun bugu wuri ɗaya, Malam na shirin yin ihu dan jin ƙaton gardi a kansa sai ya ƙara jin wani uban nauyin da ya fi na farko ashe Habu ne shi ma ya yi wata alkafira ya faɗa kan Ƙasimu da ke kan MALAM gabaɗaya sai suka yi ɗaya a kan ɗaya Malam ne a can ƙasa.
“Ku ɗaga ni mana kun min talibge fa, Malam ne fa Baban Jamila da Jamilu Malaminku ne ko baku shaidani ba idan a ɗimuwa kuke na ganin miciji ku dawo hayyacinku dan zan iya yin addu’a yanzu ku koma alade gabaɗayanku” Cewar Malam dakyar dan ji yake kamar an ɗora mas manyan duwatsu.
“Ka dawo da waccen marar lafiyar da yake a miciji sai mu samu salama gabaɗaya” Cewar Habu cikin kuka dan micijin ya nufo inda suke kuma shi ne daga sama ya san shi micijin zai fara kaiwa hari kafin su.
“Habu, Habu ni kake ƙurewa, wato taƙure zaka mini, har ni kake faɗawa magana ko, dan ka ganni a wani hali to wallahi kar ka kuskura in ɗauki jarbuna na masu dubu-dubu dan wallahi zaka yi da na sanin faɗar hakan” Cewar Malam. Habu kuwa bai ma san me Malam ya ce ba dan lokacin micijin ya fara sulalowa kan gadon dan haka sai kunnuwan Habu suka bada wani dimmm ba ya jin komai. Ganin micijin ya gama hayowa kan gadon ya fasa kai a saitin su Habu ya yi ta maza ya faɗa gefe guda sai gashi jingine jikin katifar da aka jingine ta, ai yana ɗaga Ƙasimu sai shi ma Ƙasimu ya hangi micijin dan dama Habu ya rufe masa har saitin idanunsa, shi ma gefe ya yi cijin zafin nama ya zama na sai Malam kaɗai ya yiwa micijin ƙurii da ido shi ma miciji kallonsa yake. Cikin jajircewa da kuma ƙarfin hali Malam ya yi yaƙi da bakinsa da ke son gagararsa yin magana ya ce
“Dan Allah ku dawo ku danne ni Habu ku min talibgen wallahi ƙwara nauyinku sau dubu da wannan ganin tashin hankalin”
Babu wanda ya ce uffan. Habu ne ya lallaɓa a hankali ya sauka daga gadon shi ma Ƙasimu ya take masa baya suka sauka daga kan gadon su duka sai Malam da miciji. Neman wurin ɓuya kawai suke a ɗakin amma kuma sun kasa samu sai rarraba ido suke.
“Ashe haka duniya take wato ka yiwa mutum rana ya maka dare tun baku san ciwon kan ku ba kuke hannu na amma yau ni kuka kasa taimako na ko Ƙasimu?” Cewar Malam cikin zubar hawaye kamar an kunna famfo.
” Haba mai maganin aljannu kai da kake maganinsu ka fitar da su amma kuma kana neman taimakon almajiranka” Cewar Inna da ke jikin ƙofar ɗakin tana dariyar mugunta.
“Dan Allah matar nan ki buɗe ƙofa na san dai wuyarta ki buɗe ƙofa dole za mu san yadda muka yi muka tsere daga ɗakin, ni kuma na miki alƙawarin za mu raba duk abin da aka bani, dubu hamsin ɗin ce kawai zan baki dubu biyar amma ƙwaryar nono ke ɗaya ni ɗaya, ta zuma ma rabwa za mu yi, ƙwaryar dabino ma raba dai dai za mu babu wani abu da nawa zai fi naki sai kuɗi kawai” Cewar Malam yana ɗaga muryar kamar ai ari baki, ganin micijin ya juya kansa yana kallon su Ƙasimu da suka takure a waje ɗaya sai salati suke.
“Hahahaha na dawo in ji ɗan yawon duniya gaskiya Isuhu ka iya duniyanci yo Allah na tuba ni Azumi wane dare ne jemage bai gani ba ai wallahi sai dai ranar mutuwarsa ce kaɗai za ta masa gagarar ya ganta, har ni za ka zo wa da rainin hankali wato za ka bani jaka ashirin da biyar (5K) To sai ka bari har sai ka yi aikin sannan idan an baka kuɗin sai ka yi wannan in ce dai ga ka nan ga wanda za ka yiwa aikin kana roƙon a rabaka da shi to yaushe za ka masa aiki kuma?”
Wani kuka Malam ya saki mai ƙarfi sai ka ce jiniyar ƴan sanda, ganin miciji ya matso da bakinsa kusa da na sa.
“Ni kike kiran suna na tsirara babu Malam a jiki, sai ka ce wanda… Maganar ce ta katse ganin micijin ya dawo kusa da shi ya miƙa bakinsa kusa da na Malam ɗin
” Kar ka min kiss dan Allah, wallahi kana sa bakinka a nawa na san mutuwa zan yi ga tsoro ga kuma dafin da ke cikin bakinka ka min rai dan Allah ba zan sake zuwa gidan nan ba ni na ɗauka mutum ne mai aljannu ashe abin ya fi ƙarfin Malam Isuhu” Cewar Malam yana zazzare ido.
“Kai ana dara ga dare ya yi” Cewar Inna tana da dariya abinta sai nishaɗi take dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya dama tana sane wai karuwa ta taka matar aure, ta san sai an yi artabu dama. Sadiya kuwa kallonta kawai take ita dariya ma Innar ta bata ganin irin abubuwan da take ita kullum Inna ta san ta kan mugunta, sai dai hakan ya yiwa Sadiya daɗi dan ba a cutar mata da ɗa ba.
Habu da Ƙasimu kuwa suna nan a durƙushe a takure wuri ɗaya ganin micijin a wurin Malam sai Habu ya ware jikinsa daga jikin Ƙasimu cikin zafin nama ya tashi tsaye Ƙasimu bai ankara ba sai jin Habu ya yi ya taka gadon bayansa, kafin ya ɗago ka ce me Habu ya kama drower ya ƙanƙameta cikin sakan biyu sai gashi ɗare-ɗare a saman drower, har wani murmushin jin daɗi ne ya kuɓucewa Habu ganin ya sha, dan ya san dai miciji iya ƙasa zai tsaya ba zai hau sama ba kuma ma jikin drower ɗin santsi gareshi miciji ba zai iya hawa ba. Wani haushi ne ya kama Ƙasimu ganin Habu ya tsira ya barshi.
“Habu ya ka min haka tun muna yara muke tare ko bara muka je in baka samu abinci ba nawa nake baka mu ci tare amma yau za ka mini halin ɗan adam yanzu da ka taka ni ka haye ni kan wa kake so in taka in hayo?” Cewar Ƙasimu kukan takaici na fito masa.
“Taka Malam ka hayo shi dama ai ya ci duniyarsa saura mu tun da ya tsofe ko yanzu ya mutu to dai dai ne” Cewar Habu har wani fito ya saki dan daɗi. Ƙasimu saitin Malam ya kalla amma ya ga Malam bai ma san me suke cewa ba bakinsu na kusa da na juna shi da miciji kawai ruwan hawaye kake iya hangowa daga idanun Malam suna rige-rigen sauka, ga majina sai zuba take rawanin nan ya kalle gabas maso yamma bakinsa kuwa kamar an kunna inji sai zuwa yake yana dawo wa. Ganin haka Ƙasimu sai dibara ta faɗo masa dan yana so shi ma ya haye wurin Habu su bar Malam tun da dai hankalin micijin na wurin Malam ƙwara ya haye kafin micijin ya ankara. Da sauri ya tashi ya hau kan mudubi ganin wuri ya yi nisa da drower ya sauka, wani uban tsalle ya yi sai gashi ya ɗane jikin drower a haka ya daddage ya haye suka rungume juna da Habu dan daɗi. A hankali micijin ya ja baya kaɗan ya waiwaya bayansa sai gani ya yi babu kowa a wurin da su Ƙasimu suke. Ja da baya ya fara yi har ya sauka daga kan gadon wata uwar ajiyar zuciya Malam ya sauke yana sanya hannu ya ciro rawanin hiraminsa da hularsa ya yi wurgi da su.
” Haba Isuhu mai sittin wata kan wata ya da cire rawanin ban girma kuma” Cewar Inna da ke tsaye a window tana dariya duk abin da ake a kan idonta, dan gani ta yi tsayuwa a jikin ƙofa ba zai mata yadda take so ba shi yasa ta dawo daga window take gani muraran a kan idonta. Malam kuwa jin muryar Inna a saitin windown da yake kusa da gado ya juya aikuwa suka yi ido huɗu da Inna tana masa dariya, ji ya yi kamar ya shaƙo ta ya shigo da ita ɗakin ita ma ta ɗanɗani bala’in da suke ciki. Amma babu hali ɗauke kansa ya yi daga kallon Inna dan za ta iya sa zuciyarsa ta buga kan miciji ya maida ya ga ya bashi baya ya tsaya cak kuma bai waiwayo ba bai kuma cigaba da tafiya ba. Malam sai ya fara tunanin ina almajiransa suke ganin bai ga ko ɗaya ba. Wani tsoro ne ya ziyarceshi dan duk tunaninsa micijin ne ya haɗiye su a taka ya saki fitsarin wahala dan gabaɗaya ya gama tsurewa cewa saura ahi za a haɗiye Hannu ya miƙa ya taɓo wandonsa jin lema jagaf ya ƙwalalo idanu yana ayyana cewa shi Malam ne uban Jamila da Jamilu da fitsarin wando yau, lallai firgici ya yi firgici.
*Masu fitar min littafi ku daina dan haƙƙina ne masu karantawa ma basu biya ni ba haƙƙina ne kowa ya san Allah na gafarta zunubai baki ɗaya amma baya gafarta haƙƙin wani a kan wani!*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134