Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 13

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 13…… Ganin Ammi bata da niyyar cewa komai har lkcn sae kallon Mami take da mamaki yasa Mami tace “kinyi shiru kuma maman Ikram” nan da nan hawaye ya xubo ma Ammi tana sharewa tace “me kuwa xan ce Hajiya, ae maganar taki ce naji ta wani banbarakwae, wae kina nufin yar tawa xan dauka in baki ba dangin iya ba na baba? Kmr warce karan hauka ya cixa, a kan wani dalili? Ca nayi maki neman kai nake da ita koko gajiya nayi da ita, to talaucinmu bae kai mu sayar da yar mu ba, idan ‘ya’ya mata kike so kije gidan marayu mana ae sun fi dubu a can, ” Murmushi Mami tayi, matar da suke tare tace “Ayya baki fahimcemu bane Maman Ikram…” da sauri Ammi ta katseta ta hanyar cewa “fahimtar me xan maku a nan, don Allah ku tashi ku bar min gidana” Ammi na kai wa nn ta mike hankalinta a tashe ta shiga daki da niyyar shiryawa taje ta dauko Ikram daga sch ko ba a tashi ba, Aminiyar Mami Hajiya Zuwaira tace “na gaya maki Amina, it wil b so hard 2 seperate dem frm dia dota” Ammi na fitowa Mami tace “ki sauraremu Maman ikram ni ban ce sayar min da yar ku xa kuyi ba, wllh taimakonku kawae nake son yi don Allah, in kince kullum na dinga kawo maki Ikram kina gani ma wllh xan dinga kawo maki ita, kuma ba hka kawae xan dauketa mu tafi ba, ae sae da ixinin mahaifinta….” a rude Ammi tace “yau na shiga uku ni Aisha na hadaku da Allah da annabi mutanen nn ku tashi ku tafi ku ban waje” Ammi tayi kofar fita da sauri don xuwa dauko yar ta daga makaranta ta kai ta gidan yayarta kawae, karo suka ci da Ikram da ta shigo a guje, bata bi ta kan Ammi ba tayi dakinta da gudu ba tare da ta lura da su Mami dake tsakar gidan ba ta kulle kofar, yara ne fiye da goma suka shigo gidan kowa da abinda yake fadi, daya a cikinsu nata ta rusa kuka rike da bokitin awarar ta, da kyar Ammi ta iya cewa “me ya faru” cikin kuka yarinyar tace “yarinyar da ta shigo gidan nn ne ta kwabar min da bokitin wara na ya xube cikin kasa yara suka wawashesa don tace in bata wara biyu biyar nace bbu, ynxu iyah dukana xata yi ta fasa min jiki” Ammi ta kasa cewa komai sae bin yaran take da kallo, Muryar Mami taji tana cewa “xo nan yarinya nawa ne warar gaba daya?” yarinyar na share hawayenta tace “ta dari takwas da naira talatin ce, dama na dubu daya aka sa min na sayar da na dari da saba’in” Mami ta bude jakarta ta ciro dubu daya ta mika ma yarinyar tace “maxa ki tafi gida kinji yarinya, kiyi hkuri” kai yarinyar ta gyada mata snn ta juya ta fice sauran yaran na biye da ita a baya, Ammi dake tsaye har lkcin kmr kwai ya fashe mata ta kasa juyowa, don tasan yau da matar nn bata nn da sae dae suyi kashin dubu daya daga ita har ubanta. Ikram ta bude kofa ta leko a hankali don ta tabbatar da muryar warce take ji, da gudu ta fito ta rungumeta tana cewa “lahhh wllh ita ce da gske, ashe ke ce Anty yaushe kika xo gidanmu ina wnn yaron naki dogo” Mami dake murmushi ta dago kanta tana kallon fuskarta tace “haba Ikram, me yasa xaki xubar masu da kayan saidawar su?” Ikram ta xumburo baki tace “to ba ita bace nace ta ban biyu biyar tace min ya kare alhalin ina ganin waran cikin bokitin, shine ni kuma na barar suka xube kasa nace mata meye wnn xaki ce min bbu, kawae sae na gudu suka dinga bina ina ta gudu suna bina har na shigo gida na shige dakina da gudu na kulle kofar, sae naji muryarki na fito kuma ashe kece, to ina wnn yaron naki me kyau” dariya Mami da kawarta ke yi suna kallon Ikram, ikram tace “Anty yau xaki kai ni gidanku ko” Fixgota Ammi tayi tayi waje da ita ta bar su xaune cikin gidan hankalinta a tashe, ikram tace “A’a Ammi ina xaki kai ni ga Anty taxo tafiya dani gidanta, dama tace min xata xo” mari Ammi ta shiga xuba mata ta rufeta da duka kofar gidan, mutane suka yo kansu ana ba Ammi hkuri duk da sun san magana ta dauko don sun ga yan makaranta da yawa sun shiga gidan, Ammi bata bi ta kansu ba ta ja Ikram dake ta rusa kuka suka yi gidan yayarta da ita tana hawaye a hanya.

 

Back to top button