Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 29-30

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*29&30*

 

……..rintse Ido Amaan tayi tana sakin k’aramar k’ara had’e da yarfe hannunta guda tana fad’in wayyo hamma da zafi fa”ta k’are maganar cikin shagwab’a tana kallonsa”yasakar mata harara yace”meyasa kikayi laifin tunda kina tsoron a hora ki?” toba kaine ka fara jik’ani ba?beyi mgn ba yanufi wajen fridge”ita kuma ta turo baki had’e da masa gwalo ta fice da d’an gudunta tana dariya”shariff yabita da kallo yana jin bugun zuciyarsa na tsananta bugawa”ya lumshe idanuwansa yana sauke numfashi Anutse”can yabud’e fridge d’in ya d’auki maltinah ta gwangwani yabaro kitchen d’in….. Amaan na dariyarta ta fito daga cikin kitchen d’in “saurin katsewa dariyar tata tayi sbd ganin mariya da yayanta Abdul (y’ay’an goggo saratu ne , k’anwar Abban su) suna zaune suna gaisawa da Ammi”sai Abdallah dake gefe zaune yana kallo”tunda Abdul ya d’ora idanuwansa kan Amaan numfashinsa na wucin gadi ya d’auke d’if…lolx”yayinda mariya kallo d’aya tayima Amaan taji ta raina kanta”fatanta Allah yasa batada Alak’a da yaya shariff “namijin data jima tana so Arayuwarta”ta nuna Amma yak’i yagane….. Ammi wacece wannan?”cewar Abdul yana kallon Amaan dake kok’arin rab’asu ta wuce”Ammi na murmushi tace”y’ata tazo tamun kwana biyu ne”Amaan zoku gaisa da bak’i saiki je ki ka musu ruwa ko?…..cak shariff dake k’ok’arin fitowa daga cikin kitchen yatsaya”sbd kalaman Ammi tsab Acikin kunnansa”dukda bai fahimci koma suwaye ba”Amma Atake ya had’a gabas da yamma ya tamke fuska bbu Annuri yadoso cikin parlourn adaidai lokacin da Amaan ke zama gefen kujera tana fad’in sannunku ! Ina yininku ?”Abdul ne dake washe baki kawai ya Amsa”yayinda hankalin mariya gaba d’aya ke akan yaya shariff tanata kallonsa sbd yau yamata masifar kyau “saidai tana Alak’anta hakan da danta kwana 2 bata gansaba…..razanannin idanuwan shariff basu sauka ko inaba sai kan Abdul da yayima Amaan k’uri da Ido”Ammi kuwa kallon shariff takeyi dataga kayansa jik’e da kuma yadda ya had’e rai “,dukda dama tasan koda yaushe haka fuskarsa take bbu fara’a, saidai yanzun d’auretan da yayi yafi na kullum”yaya shariff kana gidan kenan?”Ina wuni?”cewar mariya cikin lankwashe murya”kallo bata isheshiba ya Amsa da lafiya qlau”sai sannan shima Abdul ya gaidasa”ya Amsa Adak’ile yana kallon Amaan dake k’ok’arin nufar hanyar kitchen yace”Amaan zonan! yafad’a idanuwansa Akanta”ta juyo suka had’a Ido”ta sunkuyyar dakai tace”hamma zan kawowa bak’i ruwa ne”kallon Abdallah yayi yasakar masa harara yana fad’in kai zaman me kakeyi da bazaka iya tashi ka kawo ruwan ba?”tun kafin ya rufe baki Abdallah yatashi”shi kuma ya kalli Amaan yana fad’in zo muje ki bani sak’on yafad’a yana nufar d’akin Ammi”Amaan batayi mgn ba tabi bayansa dukda batasan wane sak’o ne zata bashi ba”yayinda Ammi kanta ya d’aure tamau”dama tana lura dashi tunda yadawo daga Abuja yakoma canzawa game da Amaan”yanzun ya hanata kawoma bak’i ruwa duk akan me to?”wata zuciyar tace”kodai kishinta yakeyi…. Ammi! Amaan Anan garin take ne?”muryar Abdul ta katse mata tunani”jikinta Asanyaye tace”ah ah”sai yayi shiru bece komai ba”mariya kuwa ranta yabata k’ilan shariff son Amaan yakeyi…. Amaan daya rigata shigowa cikin d’akin tasameshi tsaye gaban mirror “fuskarsa Amatuk’ar d’aure”gaba d’aya jitayi batama iya had’a Ido dashi sbd kwarjinin daya mata….kina jina?”shine Abinda yafad’a murya Akausashe”uhmm”bance ki koma fita parlourn can ba, har sai bayan bak’in can sun tafi”to shikenan hamma bazan fitaba”bece komai ba yanufi k’ofa….hamma! menene?”ya furta batare daya juyoba yadai murd’a handle d’in k’ofar yayi tsaye be fitaba”saidai miskilin dayaji tayi shiru saiya tab’e baki yasakai yafita”yana jin Abdul da Abdallah na fira”dukda Abdul ba yaro bane zaiyi 32yrs……yana shigowa katafaren d’akin baccinsa ya kwanta gefen bed yana dafe kansa had’e dajan tsaki bbu Adadi”besan dalilin daya saba yaji wani irin tsanar Abdul cikin ransa”why! why??kalmar daya dinga maimaitawa kenan yana hargitsa bak’ar suman kansa…..*salfad* sunan daya fad’o masa kenan cikin zuciya”sai yaji gaba d’aya jikinsa ya mutu murus”ya kalli Agogo “k’arfe 11:5 am”zaune yatashi yacire kayan jikinsa d’an murmushi kwance saman fuskarsa”daya tuna yadda Amaan ta dinga jik’ashi da ruwa tana masa gwalo da dariya….cak ! murmushin sa yatsaya yaja tsaki sbd tunawa da yayi da Abdul dake tambayar wacece Amaan?”gaba d’aya yama rasa wane kalar tunani zaiyi? kawai saiya matsa gaban ward rope”wani yadine sabo dark brown da Akayima kwalliya da zare millk ya d’akko “rigar iya gwiwa ne”cikin mintinah goma yagama shiryawa yana saka link d’in hannun rigar , kafin ya jawo cover shoes nasa dark brown yasaka”sai zabga k’amshi yakeyi harma yafi d’azun yin kyau”wata big boom ce daya shigo da ita jiya da dare ya lura da ita Ajiye saman mirror saiya d’auka ya fito….yana dosowa downstairs d’in yaji muryar Abdul na fad’in wai Abdallah Amaan d’in nan y’ar wane gari ce ita?”Abdallah na k’ok’arin mgn sukaji jarumar muryan fahad shariff yana fad’in miye ribarka najin sunan state nata?”yafad’a cikin izzah had’e da shan k’amshi “gaba d’aya Abdallah da mariya da Abdul dake zaune cikin parlourn suka bishi da kallo”mariya najin inama inama”ita kanta tasan ruwa basa’an kwando bane”cikin Isa ya Ida sakkowa k’asan saidai ya lura Ammi bata cikin parlourn….kayi hak’uri babban yaya idan nayi laifi”banza shariff yamasa”ya kalli Abdallah yana fad’in jeka bakin get kajirani”daga haka yanufi d’akin Ammi…. Anutse yaturo k’ofar yayi sallama”gaba d’aya k’amshin turarensa yacika d’akin”Ammi dake kwance saman bed tabisa da kallo Aranta tana furta masha Allah! Amaan dai na zaune kan sofa itada teddy d’inta”tana ganinsa fuskarta ta fad’ad’a da fara’a “batasan sadda tace”hamma nah kayi kyau ba”dan Allah zan bika kaji?”kasa yimata mgn yyi”yadai kalleta sau d’aya ya maida kallonsa wajen Ammi yana fad’in Ammi badai jikin ba?”sai godiya shariff “nama kira mansoor yana hanya zaizo yadubani”magungunan daka saka sadeeq yaturo sun k’are…..hakan nan yaji zuciyarsa bata son zuwan Dr mansoor Agidan “gashi Ammi tace”yana hanya”basarwa yayi Anutse yace”kodai next month muje Egypt Ammi Adubaki?”haba shariff”ko wancan zuwan da mukayi Anyima wata 4 ?”kawai mak’oshinne ke damuna bayansa bbu wata matsala”tunda dai sadeeq zai dawo next week zaizo da magungunan”bece komai yasaci kallon mutuniyar tasa”tacika fam da fushi idanuwanta har sun ciko da k’wallah “ya girgiza kansa da k’yar yace”tashi muje na kaiki wajen wasanni kiyi”yafad’a yana nufar kofa”meyasa bazaka barta gidaba tunda ga mariya nan tazo zasuyi fira ko?k’in mgn yayi yana dai tsaye”ga Amaan itama ta mik’e tsaye tabar teddy nata tana k’ok’arin saka takalmi ta bishi”girgiza kanta kawai Ammin tayi tana fad’in Allah yatsare Amma karka jima da ita”dato ya Amsa yafita”itama Amaan tabisa Abaya cikin d’oki”Ammi tayi murmushi kawai ta fahimci Amaan nason afita Anguwa da ita”shine Agaba yazaro kud’i rafar y’an 500 guda d’aya ya matsa ya mik’a ma mariya beyi mgn ba yana jin tana masa godiya yayi waje “Abdul kuwa ransa yabashi wannan yarinyar tabbas sonta shariff keyi…be dena kallon Amaan ba saida ta fice daga cikin parlourn”Anutse shariff ke tafiyarsa yaji muryar Amaan Abayansa tana fad’in bazaka jirani ba hamma?”beyi mgn ba yatsaya yadda ta buk’ata”meyasa ka d’aure mun fuska hamma?”ni Allah sai kayi mun dariya”nifa kullum saina maka dariya ko?”ta k’are maganar tana jerawa dashi”ya d’auki kusan second 5 kafin da k’yar yace “meyasa dole saikin koyamun Abinda ban iyaba (surutu)Amaan?meye ne baka iyaba hamma?”be kulataba yanufi had’ad’d’iyar motarsa ta kece raini”tun kafin driver ya iso yadakatar dashi wajen d’aga masa hannu”yana jin Amaan dake gefensa tanata shagwab’a ya k’yaleta yabud’e mata front sit yana fad’in oya zoki shiga”kafin ta shiga motar yaji muryar Dr mansoor Abayansa yana masa sallama…..saida yaji zuciyarsa ta buga”yayi kicin kicin da fuska ya juyo Adak’ile ya Amsa sallamar”yayinda Amaan ke cigaba da zuba shagwab’arta tak’i shiga motar”Dr Mansoor kuwa kafeta da Ido yayi yana jin wani iri sbd shagwab’ar tata…..koma had’e rai uban gayyar yayi sakamakon daya lura Dr mansoor na kallon Amaan dake tsaye ita batama lura dashiba”hannu shariff yabashi sukayi musabuha”ya jikin Ammi?”da k’yar yabashi Amsa da Alhamdulillah”daga haka ya juya yana Aikowa da Amaan da wata uwar harara da sauri tanufi front sit zata shiga….. Amaan zonan! ta maka me idan tazo?”cewar shariff Agadarance yana hura hanci”Amaan kuwa batama kula Dr Mansoor ba tashige ciki ta zauna tana hangensu”wai shariff meyasa kake son mu sami matsala dakai ne?Ido cikin Ido shariff yace”idan mun sami matsalar dakai numfashi zan dena ne Aduniya?”ko d’aya “karka manta ba kaine mahaifin Amaan ba ,bakada hurumin hanata ta kulani”nafi son da bakinta tasanar mun bata sona shine kawai zai saka na hak’ura…. Amma kasani baka Isa ka rabani da itaba tunda Ina sonta”sannan yanzun idan na gama duba Ammin zan mata maganar Ina son Amaan”idan har son…..ya isah haka! cewar shariff dake taune k’asan lab’b’ansa da k’arfi, wad’anda sukayi jajir lokaci guda kamar zasu fidda jini”yana sakin zazzafan huci yanuna Dr mansoor da yatsa yana fad’in ko kaje wajen Ammi ko baka jeba babu kai bbu Amaan”na hanane sbd na Isa”ko yanzun daka mata mgn kaga ta kulaka ne?”saiya saki wani irin mugun murmushi daya bayyanah tsantsar kyawunsa yana d’age kafad’a bayan yakoma had’e rai yace”bazata kulakaba sbd tasan bana muradin hakan”ban damu koda sbd wannan maganarba mu datse duk wata Alak’a dakai”Abu guda kawai na sani ko duba Ammin baza kayiba”kabar nan tun muna sheda juna…..bama saika koreni ba shariff zan tafi badan kuma na hak’ura da Amaan ba”dukda har yanzun bansan Ainahin dangar takarka da ita ba “bazan kuma zurfafa ba akan dole saina sani”saidai kawai zan saka Ido akai”inaso kasani sbd mace bazan bari mu b’ata dakai ba shariff”kamun Alkhairi me girma Arayuwata da bazan tab’a mancewa ba har Abada”bawai Ina jin tsoronka ko tsoron kasaka Amun wani Abuba sbd kanada kud’i na fad’i haka”ah ah nafad’a ne sbd bana manta Alkhairi”insha Allah nida gidanku har Abada na barka lafiya”yana fad’in hakan ya juya yabar wajen”dama Awaje yayi parking d’in motarsa…..sosai kalamansa suka yi tsaye a k’ahon zuciyar shariff “saidai miskilin bbu wata Alama
saman fuskarsa dake nuna kalaman Dr mansoor sunyi tasiri Azuciyarsa”Abdallah dai na tsaye daga gefe duk yana sauraren komai yana kuma kallo”yasha Alwashin kuma saiya sanarwa Ammi”shima ransa yabashi yayansa son Amaan yakeyi”irin wannan masifaffan kishin dayake nunawa kanta kawai ya Isa ya bayyanah Ainahin Abinda ke cikin zuciyarsa”shariff na kok’arin zaga yawa ya bud’e k’ofar driver sit ya shiga ya lura da Abdallah dake tsaye “da hannu yamasa Alamar yazo yana koma had’e rai”saida yaji fad’uwar gaba Atsorace ya iso gefensa”kallonsa yakeyi yana nazarinsa na kusan second 10 kafin yace”nasan kaji yadda mukayi da mansoor ko? “na sake naji maganar nan Abakin Ammi nida kaine”And last one duk wanda yasake yamaka wata banzar tambaya game da Amaan kace kaima baka saniba”da sauri Abdallah yace”to shikenan yaya yanzun na biyoku ko?tsaki shariff yasaki yana bud’e k’ofar ya shiga….. Amaan dai ta bishi da kallo Aranta tana gulmarsa wai hamman nan yacika masifa”kasancewar tana cikin motar tana lura da yadda suke mgn shida Dr mansoor”shiru na wasu y’an mintinah yaratsa”shi yana driving d’in ,ita kuma tana y’an kalle kalle da wasa da yatsun hannunta”hamma ! shiru yamata yak’i mgn”ganin Hakan datayi sai bata koma gigin masa mgn ba har suka iso wani had’ad’d’en wajen siyar da ice creams da kayan ciye ciye”saida yagama parking ya juyo ya kalleta”d’an sakin fuska yayi sbd ganin damuwa Atare da ita….. Amaan! yakirata cikin k’asaitacciyar muryarsa yana kafeta da manyan idanuwansa”kasa Amsawa tayi kanta dai na’a k’asa”yaci gaba da cewa”kinfi kowa sanin halinah bana son yawan surutu ko?”so you have to be care full”yana fad’in hakan yabud’e k’ofar yafito”itama fitowa tayi batare data fahimci me kalamansa na k’arshe ke nufi ba”saidai tayi k’ok’arin daidaita nutsuwarta”gefenta ya matso ya tsaya yana lock d’in motar”idan ka kallesu wuf d’aya zaka d’auka sud’in masoyane dan ba k’aramin marching da juna sukayiba”wuce muje”shine Abinda yafad’a yana juyawa cike da aji had’e da shan k’amshi yafara hawa stars d’in shiga cikin wajen”Amaan batayi mgn ba tabisa”kusan atare suka shiga ciki”maza da mata y’an gayu masu aji kowane na zaune shida friends d’in shi ko budurwasa”directly table d’in da bbu kowa Anan shariff yanufa yaja kujerah ya zauna Anutse”Amaan ma tazo ta zauna tanata b’ata fuska”ya kalleta , fad’amun dame dame kikeso aka miki?”bakace wajen wasanni zamuje ba?”Babu time ,kinga Ammi tace karki jima”zuwa next week zamuje can “is okay?”nok’e kafad’arta tayi ta turo baki”yatab’e baki yana d’age kafad’a had’e da cewa ke kika sani to”hakan yayi daidai da isowar wani ma’aikaci”cikin harshen turanci sukayi mgn da shariff yasanar masa Abinda suke buk’ata”kamar Ance yad’an kalli wajen”yatsina fuska yayi sbd ganin wasu daga cikin matan nata kallonsu”daga can gefe kuma Ibtihal ce zaune tsakkiyar wasu maza suna bata ice cream”tayi wata irin shiga irin ta marassa tarbiya”su kansu mazan daka gansu kasan bana gari bane”tunda shariff da Amaan suka shigo Ibtihal ta lura dasu take binsu da wani irin mugun kallo tana girgiza jikinta”har aka kamusu komai gabansu duk kan idonta”kasancewar Amaan tasan ice cream tunda yana siya mata shi”saidai sauran snacks da shawarma da aka Ajiye musu bata fahimci ko meye suba”roba guda shariff yatura mata gabanta yatsareta da Ido beyi mgn ba”yayinda shima tashi tana gabansa”da k’yar yad’an sha ice cream d’in kusan rabin roba ya Ajiye yana had’e rai “sbd yaji gaba d’aya wajen ya ishesa sbd yadda aketa kallonsu”d’aya daga cikin ma’aikatan wajen yakira”bayan ya iso yasanar masa Amusu take a ways d’in sauran”bayan tafiyar mutumin ya kalli Amaan yana fad’in 5 minit nabaki ki idar mu wuce”batayi mgn ba tana dai tsakuran ice cream d’in”can idanuwanta suka hasko mata Ibtihal dake rik’e da waya tana danne danne”hamma! oh my God”pls Amaan tashi muje “yafad’a yana tashi tsaye”ya Amshi ledojin da ATM card daya basu su zare kud’insu”Amaan kuwa tana rik’e da robar ice cream nata ta biyosa”sai bayan sun shiga mota tace”hamma naga wannan da mukayi fad’a da ita”sarai ya fahimci Ibtihal take nufi saiya shareta yak’i mgn”kai tsaye gidan mlm suka nufa”bayan sun iso nanma saida yamata warning sannan suka shiga ciki”yanayin yadda mlm da babah ladi sukaga Amaan sun tabbatar tana samun kulawa over”wasu magungunan da y’an shawarwari mlm yabashi”yasanar masa sunata Addua da k’ok’arin ganin An karya wannan sihiri insha Allah”itadai Amaan tana zaune bata wani fahimtar meye suke cewa”da zasu tafi Shariff yamusu Alkhairi me yawa sannan suka nufi gida, bayan shariff yakira Abdallah yatambayesa su Abdul sun tafi?yace masa Eh….sai wajen k’arfe d’aya saura suka iso gida….✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button