Yar Zaman Wanka 45-46
Tun da suka saka ta a mota ta fara wurwurga idanu, mutum huɗu ne a cikin motar gabaɗaya suna sanye da kayan sojoji, ɗaya yana jan motar shi kaɗai ne bashi da kayan sojoji. Mutum biyu ne suka sanya Inna a tsakiya kallonsu take tana so ta ga ko ta taɓa ganin wani, amma babu wanda ta gane, baki ta buɗe za ta yi magana amma ɗayan ya ɗaga bindiga ya ɗora mata a kan ta hakan ne ya sanya Inna ta ja bakinta ta yi shiru dan duk abin ta bata wasa da rai da lafiyarta.
Gum ta yi da bakinta bata sake yinƙurin yin magana ba su ma kuma duk cikinsu tun da ta shigo motar bata ji wani daga cikinsu ya yi magana ba.
Wata unguwa suka nufa da babu hayaniya sosai a ƙofar wani get suka tsaya horn aka yi mai gadi ya zo ya buɗe ƙofar suka shiga ciki Inna kuwa sai rarraba ido take yi dan ta kasa gane dalilin da ya sa aka ɗakko ta. Tunani ta fara yi ko ƴan yankan kai ne suka ɗakkota, duk da dai ta gansu da kakin soja a jikinsu amma hakan ba zai hana ta zargesu ba saboda yanzu ƴan bindiga suna kashe sojoji su ɗauke kayansu suke sanyawa, dan dai ta san wancan karon da aka ɗakko ta daga gidan masu kuɗin wannan jeji aka nufa da ita saɓanin yau kuma da aka nufo cikin gari kuma ƙeraren gida na gani na faɗa.
Haka dai ta daure saboda bakin bindigar da ke kanta. Suna fitowa ita ma haka ta bi ayari ta fito bisa bin umarnin da aka bata, tun da suka fara tafiya zuwa ainihin cikin gidan take ta kalle -kalle har suka samu nasarar shiga cikin wani falo madaidaici mai shegen kyau. Su duka wuri suka samu suka ƙame babu wanda ya nemi wurin zama Inna kuwa ganin tsayuwar ba za ta mata ba sai ta zauna a ƙasan kafet gudun kar ta hau kujera a harbeta.
Suna nan, sai ga wata yarinya ta fito cikin wasu ƙananan kaya tana riƙe da abin wasanta, Tun da ta fito Inna ta ƙura mata ido tana mata kallon sani sai dai ta kasa tuna inda ta san yarinyar tana ta kiciniya da ƙwalƙwalwarta a kan ta barta ta tuna ina ta san yarinyar amma kafin hakan sai ganin mutum ta yi ya fito daga cikin wani ɗaki shi ma sanye da kaya amma ba na sojoji ba. Kallo ɗaya Inna ta masa ta gane shi a take ta tuna da inda ta san yarinyar ma.
“Sojojo kai ne dama nan gidan ka ne ina tsohuwar matarka mai shegen tsoron nan kamar farar kura, ko da yake ma ba ita kaɗai ce matsoraciyar ba har da…
Wata uwar tsawa da ya daka mata ita ce ta hana Inna da ta washe baki tana ta kauɗi da karaɗi ƙarasa maganar, dan tun kan ya ƙaraso ma tsakiyar falon ta fara zuba.
Cikin ɓacin rai ya ƙaraso tsakiyar falon gabaɗaya suka shiga sara masa kujera ya nema ya zauna har lokacin ransa a matuƙar ɓace yana aikawa Inna wani mugun kallo. Ƴar tasa ce ta zauna a kusa da shi tana ta raɓewa a jikinsa da alama dai bata manta da inda ta ga Inna ba.
“Ke inyamura ina uwaki take, yo ina so in miki magana amma na san bakya jin hausa, ina so in ce ki kira min uwaki tsohuwa mu gaisa ko yau ma tana can tana kwalliyar tana shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa sai…
Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙara yiwa Inna tsawar da ta sanya ta yi shiru sai dai yanzu tun da ta ga abokin Imran gaba yake da su, wato ogansu ne sai ta ji duk bata tsoronsu dan ta san dai duk tsiya ba lallai su harbe ta ba.
“Oh ni Azumi Allah ya tsaga min bakina amma ku hana ni magana, na rasa ma mai yasa kuka ɗakko ni duk da dai na san ruwa ba ya tsami banza amma dai da walakin goro a miya”
Babu wanda ya mata magana dan abokin Imran ya ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.
Kallon su ya yi cikin bada umarni ya ce
“A kai ta wannan ɗakin” Da kallo Inna ta bishi tana mamakinsa amma sai ta miƙa hannunta ta taɓo saitin aljihun ɗan tofinta ta ji abin da ta ajiye yana nan hakan ya sanya ko gardama bata musu ba suka tafi da ita. Har sun je ƙofa za su fita ta juyo ta ce
“Gobe sunan Hassan dai mutuminka ina fatan za ku je” Wani haushi ne ya rufe shi yana ayyanawa a ransa tabbas tsohuwar nan yau sai ta banbance tsakanin aya da tsakuwa, dan sai ya tabbatar ta gane akwai banbanci tsakanin kiɗa da karatu. Ƙeyarta suka tisa har ɗakin da aka bada umarni a kai ta, ɗakin a can bayan gidan yake kuma a rufe yake sai da suka buɗe ɗakin suka shigar da ita ciki wani daga cikinsu wanda ya zo a kujerar mai zaman banza lokacin da suka taho a motar har ƙeya ya tallewa Inna, amma bata ce komai ba sai dai ta ayyana za ta rama ne.
Sai da suka gama harare -harare da wani tsawace -tswacensu sannan suka fito suka rufe Inna a cikin ɗakin suka sanya mukulli sai dai basu cire mukullin ba daga waje suka barshi a jikin ƙofar.
Sai da suka yi kamar minti goma da fita Inna ta tashi ta yi dibara ta ɗan buɗe windown sai da ta tabbatar babu kowa a kusa sannan ta buɗe windown duka, wani dogon icce da ta samu a ɗakin ta ɗauka ta sanyo shi ta windown a hankali cikin dibara ta saƙala iccen a jikin ƙarfen key holder na jikin mukullin, cikin dibara ta cire mukullan daga jikin ƙofar sai dai tana ƙoƙarin shigo da iccen ta windown sai mukullin ya zame daga jikin iccen ya faɗi ƙasa.
A haka ta rinƙa yin dibara har dai ta ci nasarar ɗakko shi a jikin iccen, daga ƙasan ta shigo da shi cikin ɗakin, jijjiga kai kawai take tana dariya ta ce
” Ta yaro kyau take bata ƙarko, tabbas yaro bai san wuta ba sai ya taka, lallai yau allura za ta tono garma, su a ganinsu sun garƙame ni, basu san na fisu wayo ba ko dan dogaye ne dan bashaushe ya ce dogo da hankali dace ne” Cewar Inna tana ta ƙoƙarin cire mukulli ɗaya daga jikin key holdern dan gabaɗaya mukullan iri ɗaya ne hakan ya nuna duka na ɗakin ne.
Bayan ta cire ɗaya sai ta sanya a cikin aljihunta, bayan ta ɗakko wata ƙaramar farar leda ƙulle da wani abu, tana gyaɗa kai alamar za ku gani. Sai da ta adana mukullin da ta cira ta yi murmushi ta ce
” Mu je zuwa da ni Azumi kuke zancen ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha”
A hankali ta lallaɓa ta sake leƙawa har lokacin bata hango kowa ba kuma bata ji motsin kowa ba ga la’asar ta yi lis haka ta sanya mukullin ta buɗe ƙofar a hankali ta fito daga ɗakin, tana fitowa ta maida ƙofar a hankali ta rufe bayan ta rufe sai ta bar mukullin a jiki, cikin sanɗa ta fara tafiya tana ta waiwaye abinka da marar gaskiya ko cikin ruwa gumi yake. Cikin ikon Allah har ta ƙaraso ɓangaren da suka fara zuwa ita da sojojin nan wato inda ogan nasu yake abokin Imran. Shigewa ta yi dan a hankali ta tura ƙofar har ta ƙaraso falon babu wanda ya lura da ita. Laɓewa ta yi a jikin bango wani ɗan loko take leƙo falon yana zaune ya rungume ƴar sai matar ita ma daga ɗaya gefen nasa ta zauna ta kwantar da kanta a kafaɗarsa ta yi wani turum da tsohon cikinta.
” Wai da gaske an samo matar nan ta gidan abokin ka?” Cewar matar cikin gurɓayacciyar hausarta.
“Eh wallahi har nan aka shigo da ita amma saboda ƙarfin hali har tambayarki take tana miki wulaƙanci wai ko kina can kina shafa jambaki bakin ki kamar akuya…
” Haba wato kaima maimaita abin da ta ce za ka yi, tabbas yau bayan ka hukunta tsohuwar nan sai ni ma na mata hukunci mai tsanani za ta san da ni take magana”
“Ayyo to ke ma ashe shegiyar kan ki ce da ban yi niyyar miki komai ba shi kaɗai zan yiwa to tun da ke ma mummunan ƙudiri ne a ranki har ke zan haɗa, ƴar taku ce dai ba zan yiwa ba saboda ƙanƙantar ta, dan kar in ɗau alhaki” Cewar Inna a zuciyarta.
“Ayya ba dan na ɓata miki rai ba na yi baby, amma tabbas yau za ta karɓi hukunci dan kuwa zan ɗauke idanuna daga kallon tsufanta in manta alaƙarmu da Imran duk da shi ma ya ce min ta addabeshi, amma yau sai ta san wa ta yiwa abin da ta yiwa ranar nan wai dan wulaƙanci ni take cewa sojojo sai ka ce wani ɗan ƙwaya” Ya faɗa cikin gurɓatacciyar hausarsa.
“Ai kawai ka bari tsohuwar nan za ta gane kurenta, ai na gode Allah da ka aamu hutun sati biyun nan jiya gwara da ka sa aka ɗakko ta mu ga tsiya” Cewar matar tana dariya.
“Za mu ga wanda zai gane kurensa ni da ku ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, kuma iya gani iya ƙyalewa ni Azumi zan nuna muku ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu” Cewar Inna a zuciya.
A hankali ta since farar ledarta wacce ta zubo ƙaiƙayin hatsi ta haɗa da barkono ta daka ta zuba a leda ta ƙulle. Ya daɗe a ajiye a cikin jakarta dan tun kafin cikin Halima ya tsufa ta ajiye saboda idan za ta je ZAMAN WANKA ta ajiye saboda shirin ko ta kwana. Ledar ta since ta lallaɓa cikin falon da suke da yake sun baiwa ƙofa baya ne basi san me ke faruwa ba idanunsu a kan TV. Sai da Inna ta je bayansu kawai sai ta ga matar za ta juyo da sauri ta durƙusa Allah ya sa ma matar bata ganta ba sai da ta bari ta ɗan jima ta ji suna ta hirar yadda za a azabtar da ita, ta tashi ta zuba musu ƙaiƙayin nan mai barkono a cikin wuyan rigarsu sai da ta barbaɗawa mata da mijin ta lallaɓa ta fice. Ta baya ta bi tana yi tana laɓewa dan so take ta gano inda sauran sojojin nan suke wanda suka ɗakko ta. aikuwa ta hangosu zaune a kan benci sun bata baya suna cin wani abu haka su ma ta lallaɓa ta je sai da ta zubawa kowane a cikin wuyan rigarsa cikin hanzari ta bar wajen ta koma ɗakin da aka ajiyeta. Ta maida mukullin yadda suka ajiye shi a jiki ta rufo ƙofar sai dai bata kulle ba.
Sojojo suna kallo bai ankara ba sai ganin ya yi ya miƙe tsaye zimbet yana zazzare ido dan raɗaɗin barkonon da ya ziyarci fatar bayansa ya haɗe da ƙaiƙayin ya bashi wani azababben zafi da raɗaɗi. Yatsina fuska matar ta yi tare da taɓe baki ganin abin da mijin nata yake yi kamar wani mahaukaci sabon kamu. Tana shirin masa magana sai ita ma a take ta ji wani raɗaɗi ya ratsa fatarta kamar wanda aka tsatstsaga mata fatar bayan da wuƙa ko reza aka zuba gishiri ko yaji haka ta ji a take ita ma ta miƙe suka shiga zarzage -zazzage sai idanu take zarewa kamar ta yi ƙarya an zo mata cakar ƙarya.
A take suka shiga zirya a falon babu wanda ke iya taimakawa ɗan uwansa kowa ta kai ta kai yake kowa ɗauki yake nema sai ife-ife da soshe-soshe suke kamar za su karce fatar jikinsu amma kuma ƙaiƙayin ƙaruwa yake . Su sa suke hannu bibbiyu dan shi mijin ma ya yi xaman ƴan bori a ƙasa sai susa yake amma kamar ya yi hauka ga ƙaiƙai ga raɗaɗi , ita ma matar da ta gaji sai zaman dirshan ta yi ta miƙe ƙafa tana sosawa shi ya kalli gabas ita ta kalli yamma sun raba jaha mijin da matar, can ya gaji ya kwanta a ƙasa yana gurza bayansa a ƙasa amma ina jin abin na neman wuce gona da iri sai ya fara kiciniyar cire riga, yana gama cirewa ya cigaba da soshe soshe ƴarsu na musu sannu.
Hakan bai masa ba sai da ya tuɓe kayansa duka daga shi sai gajeren wando, tashi tsaye ya yi sai zagaya falon yake yana wani dira ƙaƙafu, matar ma kiciniyar cire riga ta fara ganin tana neman cire kayan ya doka mata wata uwar tsawar da ta sa ta suka shige ɗaki ita da ƴarta shi kuma ya yi hakan dan kar wani cikin yaransa ya shigo duk da dai basa shigowa sai ya musu izini amma dai idan wani uzurin ya tashi zasu iya shigowa bare yau da ya san ya ajiye Inna a gidan ya san ba za a rasa nono a ruga ba.
Suna shigewa ɗaki da ya ji bala’in ya yi bala’i a sukwane ya fito daga part ɗin nasa ya fito yana ƙwalawa yaran nasa kira, daga inda suke suna ta tutumurtu suka rugo wurinsa a guje cikin son cila umarninsa ganinsu su duka a tuɓe da gajerunan wanduna kowa hannu a jiki kowa na susa kamar su yi hauka.
Shi ma yana susar ya kalle su yana wani zare idanu.
“Meye hakan kuma kuke yi kuna min yawo a gida a tuɓe?” Ya jefa musu tambayar yana soshe soshe. Sara masa suka yi suna ta susar kowanne idanunsa jajur.
” Oga wallahi kawai muna can baya a zaune sai kowa ya fara jin ƙaiƙayi da raɗaɗi mun rasa menene” Suka haɗa baki wurin bashi amsa har lokacin kowa susar yake har ogan.
Yana shirin yin magana ai da ya ji wani azababen ƙaiƙai sai ya manta da basu amsa tun yana yi a tsaye har ya kwanta reran a ƙasa sai birgima yake su ma maimakon su taimaka masa sai ƙaiƙan ya ci ƙarfinsu suka kwanta a ƙasan daga gefe duk da halin da suke ciki amma sun san Ogan su ne basu jeru da shi ba, yana gefe yana birgima da gurza bayansa a ƙasa suma suna gefe suna yi kamar yadda yake, sai da suka ji ƙaiƙan ya ɗan lafa suka dakata Oga ne ya fara tasho sai wani cin magani yake yana wani harare-harate shi a dole kar a kawo masa raini cikin haɗe rai ya ce.
“Ina tsohuwar nan?”
“Tana ɗakin da ka ce a kai ta”
“Kun kulle ta kuwa”
“Eh Oga da mukulli ma”
Sai lokacin ya ɗan ji ya daina zargin Inna dan ya san dai babu yadda za ta yi ta fito ɗaki a kulle amma da ba zai taɓa yadda ba ita ce silar shigarsu halin da suke ciki ba sbd ya san za ta iya yin komai sai dai ai babu wanda ya ga wanda ya aikata wani abu kowa ya tsinci kansa ne a halin dan haka sai aka dangana hakan da ko aljannun gidan ne suka musu hakan.
Ɗakin da Inna take suka nufa domin a je a mata hukunci tun yau za ta fara karɓar hukunci dan ya yi alƙawarin sai ta kwana uku suna azabtar da ita sannan za a maidata sunan da damun mutane da shi ma ba za a yi tana nan ba sai dai a bata labari haka ya ƙudurta a ransa.
Inna da ke cikin ɗakin tana ta addu’a a kan Allah ya fitar da ita daga gidan sojojo lafiya dan ta sha jin ana cewa sojoji basa ragawa mutane babu ruwansu sai su zartarwa mutum hukuncin da ya musu, tana kuma fatan kar su gane wani shiri da ta musu dan ta san shirin shi kaɗai ne zai ƙwace ta daga uƙubarsu, tana nan zaune tana ta jan sunayen Allah sai ta fara jiyo maganarsu, hakan ya sanya ta cigaba da addu’a, suna zuwa ɗaya daga ciki ya sanya hannu ya murɗa mukullin bai lura cewa a buɗe mukullin yake ba, dan haka shiga kawai suka yi.
Inna da tun da suka shigo ta kafe su da idanu dariya na cin ta yadda gabaɗayansu suka yi ankon gajerunan wanduna ga wata ƙasa tun daga kan su har bayansu. Cikin izza Ogan ya kalli Inna zai fara magana sai kuwa ya ji ƙaiƙayin ya dawo sabo dal, kamar an haɗa baki su ma sai suka ji hakan a take suka layu a jikin bango suna susa da jikin bangon kowa yana goga bayansa dan lokacin ma sun manta matsayin Ogan nasu a wajensu kowa ta kai ta kai yake.Inna sadda kanta ƙasa ta yi tana dariya ƙasa-ƙasa ganin duk sun haukaci lokaci guda.
“Oh ni Azumi ko ina matar sojojon take, tana can ita ma tana fama ga ƙaton ciki ga susa, ai dama in zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wato kun kawo ni za ku azabtar da ni gashi nan ido ya juye da mujiya. Cewar Inna a ranta.
Sai da suka ɗan dakata da su sar sai kawai idanunsu ya sauka a kan wani miciji da ke can gefe kusa da Inna sai dai ba su yake kallo ba ya basu baya, sai dai ya fasa kansa. Gabaɗaya sai suka sha jinin jikinsu, gashi ko bindiga babu a wurinsu lokacin bare su ce za su harbeshi, a take Inna ta gane tarkonta ya kama su.
” Kuna gani na haka to wallahi ni lunbu-lunbu wutar ƙaiƙayi ce, kuma murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya, wa ya faɗa muku barno gabas take ai wallahi faɗa da aljani ba daɗi, wai ku nan wayon a ci an kori kare daga bakin ɗinya, ai iya gani ƙyalewa” Cewar Inna a zuciyarta tana tashi tsaye daga inda take zaune da ta fahimci tarkonta ya kama tsuntsu.
Sai da ta ɗaure mayafinta a tsantsa sannan ta turo ɗankwalinta gaban goshi ta taka a hankali ta isa wajensu da suka takure a waje ɗaya su duka dan gabaɗayansu Oga ya basu labarin micijin gidan Imran da ya faɗa musu jariri ne yake zama micijin, dan haka kuma abin da ya ƙara ɗaure musu kai sun san dai su suka kawo Inna ita kaɗai suka kulle ta a ɗaki ita kaɗai amma yanzu ga miciji tunaninsu micijin aljani ne dama shi yasa ya biyo ya ceci Inna. Tana zuwa gaban abokin Imran ta kama tsantsa ta ce.
“Sojojo har ni za ka sa a kamo a kawo gidan nan a kulle ni dan ka cutar da ni, to ga Hassan nan ya biyo ni zai cece ni dan haka sai ku shirya artabu da shi”
“Dan Allah ki taimaka mana ki ce ya tafi wallahi za mu maidaki gida yanzu ba tare da mun taɓa lafiyarki ba” Suka haɗa baki wurin faɗa. Wata dariya ce ta zo wa Inna ganin yadda suka yi buɗu-buɗu da ƙasa kamar wanda aka tono daga cikin rami wai duk garin susa suka zama kamar wasu fatake, danne dariyar ta yi ta kallesu ta ce to ni zan tafi na barku tate da shi a sha gumurzu lafiya ai kai sojojo ina fatan baka manta ba da karonku da shi”
Gabaɗaya sun ruɗe da maganar Inna dan haka suka shiga ihu da kururuwar bata haƙuri ba ga Ogan ba, ba ga yaran nasa ba.
“Ai ya faɗa min ba zai juyo gareku ba sai na bashi umarni dan haka yanzu zan bashi umarni ya cika aiki” Ta faɗa tana ɗakko mukullinta daga cikjn ɗan tofinta dan Ogan da suka shigo sai ya kulle ƙofar ya cire mukullin dan haka mukullin yana hannunsa.
“Ka ga mukullin da Hassan ya kawo min yanzu da ya zo” Ta faɗa tana nuna musu mukullin hannunta tsabar tsorata sai jikinsu ya shiga karkarwa dan sun yarda aljani ne.
” Bani mukullin hannunka sojojo ko yanzu lahira ta yi baƙo” Ta faɗa tana miƙa masa hannu ya damƙa mata, dan wanda ta cira a jiki ta yi amfani wajen buɗe ƙofar ganin ƙofar ta buɗe sai suka ƙara tabbatarwa, tana fita kuwa ta kullo ƙofar ta sa mukulli dan ta ga sun iyo ayari a guje za su biyo ta, ganin ta kulle sai suka koma inda suka baro suna takurewa a waje ɗaya.
“Tun da na fito yanzu nan zan bashi umarni ya cika aiki” Cewar Inna da ta leƙo ta window tana kallonsu har hawaye sun fara musu zarya a fuska.
” Haba sojojanni marmari daga nesa duk jarumtarku ku fara kuka tun yanzu?”
“Haba Inna ya zaki rufe mu ɗaki da wannan abun ki ce ba za mu yi kuka ba, a haɗa ka ɗaki ɗaya da mutuwarka wato ajalinka” Suka faɗa suna hawaye yaraf-yaraf.
“To in bakwa so na bashi umarni sai kun yi abin da na ce”
“Faɗi ko menene za mu yi” Suka haɗa baki wajen faɗa.
” Hassan kar in ga ka juyo ka tsaya a yadda kake kamar gunki kar ka kuskura ka motsa sai na baka umarni” Cewar Inna tana nuna Hassan da yatsa.
“To ya amince, babu abin da zai muku sai dai wanda ya ga baya yin abin da na saka ku zai zo wajensa wataƙila ma ya haɗiye shi”
“Zamu yi ma”
“To ku hau layi ku daina cakuɗewa a waje ɗaya a hau layi, sai a fara yiwa nigeri’a kirari amma duk inda sunan nigeri’a ya fito kar wanda ya kuskura ya ce nigeri’a Azumin Malam za kuke sawa a duk inda aka ambaci nigeri’a”
Kallon kallo suka fara amma ba yadda suka iya, haka suka ƙame suka fara taken nigeri’a (National anthem) Kuma duk inda aka ambaci Nigeri’a a cikin national anthem to sunan Azumin Malam suke sawa, bare duk basu hausa sosai Ajimum Mayan suke cewa amma a haka suke ta yi suna dawo wa farko har sai da Inna ta gaji ta ce su dakata.
“Yanzu kuma abin nan da kuke cewa leee ray(left right) Wanda kuke yi kuna ɗaga ƙafa dama da hagu kuna bugawa a ƙasa wanda da ake cewa mai tsumman (letf) Marar tsumman(right) Shi za ku yi amma a maimaikon leee, ray, sai kuke cewa Azumi (left) Malam (right).
Babu yadda suka iya haka suka fara bin umarnin Inna suna buga ƙafa suna kiran sunanta da na Malam a maimakon left right.
Tun suna yi da ƙarfinsu har sai da suka gaji sun jigata sosai, sannan Inna ta dakatar da su, ta ce su fito su kalli gabas za ta shiga ɗakin su yi magana da Hassan ta bashi haƙuri ya ɓace, bayan sun mata alƙawarin mayar da ita gida ba tare da ko lakuci ba, har rige-rigen fitowa suke daga ɗakin da ta buɗe ƙofar suna fitowa suka kalli gabas wato sun baiwa ɗakin baya tana shiga ta kulle ƙofar sai da ta tabbatar basa gano ta sannan ta ɗaga micijin robar da ta tsinto a wannan gidan da ƴan kidnapping suka ɗauketa, lokacin tana ta zagayawa a cikin gidan ta ganshi, da farko ita ma ta tsorata amma daga baya sai ta gane ba na gaske bane saboda matuƙar dai baka taɓa shi ba ba za ka gane ba haka yake kamar micijin gaske sai ka taɓa za ka ji wani latsotso kamar wata leda mai laushi amma ba roba bane.
dan haka sai ka ɗaga wajen cikinsa a nan ne tillar da ake hura micijin take a rufe da murfinta, dan haka da sauri Inna ta buɗe tillar ta sace micijin ta linke ta mayar ɗan tofinta ta zige zip ɗin. Dama tun lokaci da ta gani a gidan ta ɗakko dan idan ta koma ƙauyensu take hurawa tana tsorata Tasalla, to ganin ranar nan daga fitowarta ana sace ta a matsayin wata dan haka ta ce yanzu duk inda za ta je da shirin ko ta kwana za take tafiya saboda tsaro ba dan tsoro ba. Shi yasa ma ta taho da ƙaiƙayinta mai barkono da ya daɗe a ajiye a jakarta ashe kuwa da walakin goro a miya sai gashi sojojo ya sa an ɗakko ta sai ta yi amfani da su ta dan ceton kan ta gashi kuwa sun mata rana.
Sai da ta tabbatar ta gama ta ce su shigo su gani, ai daga window ma suka leƙa dan a tsorace suke, ganin babu micijin babu dalilinsa sai suka ƙara shan jinin jikjnsu.
Haka ta ce sai abokin Imran ne ma zai kai ta gida haka ya shiga ya sako kayansa babu yadda ya iya ya buɗewa Inna mota ta shiga ya rufe kamar yadda ta buƙata. A hanya ma haka ta sa ya tsaya ta rinƙa sa shi siyayya ta babu gaira babu dalili har sai da ya ji ya yi da na sanin, sanin Imran ma ba ma da na sanin ɗakko ta kaɗai ba, har ƙofar gida ya kawo ta, ta ce ya shiga su gaisa da su Sadiya ya ce mata a’a .
“To sojojo ka gaishe da matarka tsohuwa mai shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa” Cewar Inna da ke tsaye riƙe da ledoji hagu da dama riƙi-riƙe da kayan siyayyarta. Wani kallon takaici ya mata ganin sai dariya take ya ja motar ya bar wurin a sukwane.
” Sai ni Azumin Malam wallahi ni gaba ta kai ni gobarar titi” Cewar Inna tana juyawa ta shige gida abin ta.
Masu fitar mn littafi ku ji tsoron Allah, da tsoron haƙƙina.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134