Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 6

Sponsored Links

*Talented writers forum*

* NASARAR RAYUWATA*

*6* free page

Mmn Nana ta shaidawa inna har yanxu babu labarin Aman inna ta karbi kudaden ta ajiye tace ” gasu nan zan ajiye ko bayan raina a mayar masa da abunsa ” mmn Nana tace ” da kinyi jari dasu malama ” aa babu ruwana bansn mutum ba haka kurum zamu ci kudinsa ” hajjo tana sauraronsu bata saka baki ba , bayan sallar isha ta dakko allonta ta fara karatu tana cikin izu na goma tanayi inna na gyara mata har lokacin tashi yayi taje ta kwanta. Da safe ta tafi boko kafin malaminsu ya shigo taji wasu yan ajinsu suna hiran samari tayi shiru tana sauraronsu har lokacin da maths teacher ya shigo, hajjo na tunani meyasa ita bata da saurayi shin wayene zai zama saurayinta? ta tuna suna cewa kowane kyakkyawan mutum ya iya soyayya kwatsam fuskar Aman ya fado mata a rai murmushi tayi ta kulle idanu kyautar kudin da ya mata ta tuna, da alama sonta yake tunda ya bata kudi mai yawa toh amma ya zatayi ya fara soyayya da ita n ita bata taba ganin mutum mai kyaunsa ba amma yana da kyau kaman mutanen da suke film ” Aisha Suleiman! Malamin ya jefa mata chalk firgigit ta dawo hayyacinta.
Bayan an fito break ta nemo yaran da suke hiran soyayya Habiba tace ” a gidanmu babanmu baya barin mu fita, amma yayata tana da saurayi kullum suna waya suna soyayya shiyasa nake son Allah ya bani saurayi ” hajjo tace ” ni Ina da saurayi amma baice yna sona ba kyakkyawa ne sosai ” Umma tace ” ke wawiya sako zaki tura masa kice I love you too my kiss me heart haka naji anty zali take cewa ya Habule ” hajjo tayi tagumi tace ” inna ta bata da waya ” ” wasika zaki rubuta ki kai masa , kice zuwaga masoyina bayan dubun gaisuwa mai yawa kibiyar sonka ta soke ni wash kash da ma ka zama wata na zama tauraro mu haska duniyar lob, mu bude…” Habiba! Yayarta dake ss3 tazo wucewa sake baki tayi tana kallon ikon Allah, a guje Habiba suka gudu sai hajjo da ta sunkuyar da kai yayar tasu ta wuce tana girgiza kai. Hajjo zuwa tayi wajen wani dan layinsu dake ss1 tace ya rubuta Mata letter tana fadan kalaman da Habiba ta koya mata yaron yace ” waye zaki turowa wannan wasikar ?” ” kai de ka rike alkawari zan na baka awara kullum karka fadawa kowa ” yana murmushi yace ” nayi alkawari ” nan ya rubuta Mata tayi godiya ta karba ta tafi.
Da yamma tayi wanka taci kwalliya kamar mai shirin xuwa biki maman Nana na tsokanarta suna xuwa ta fara ciniki rabin hankalinta na bisa titi tana jiran isowar motar su Ayman can kuwa ta hango motar na xuwa wani almajiri ta kira ta nuna masa motar tace ya mikawa farin mutumin dake ciki , cikin rashin sa’a Aman baya ciki Ayman ne da fauzan nan almajirin ya mikawa Ayman yace ” gashi wata yarinya tace a baka ” ware ido yayi yana kallon letter din yasa hannu ya karba driver yaja mota suka tafi, hajjo tayi murna sosai donhaka ta mikawa yaron 10 note tace ” kullum kazo da yamma na aikeka kaji ” gyada kai yayi ya tafi haka ta kasance cikin nishadi har magariba tayi suka koma gida.

,____________________

Aman na kwance a falo yna buga game din PES Ayman ya shigo ya xauna ” da alama kaji sauki naga har game kake ” yaya son ra’ayinka baka son na warke ne ko so kake na mutu? ” ” idan ka mutu me zan samu, anyway na mnta dat your little girl tana missing naka harda kuka jiya tace don Allah tana son ganinka ” kallonsa Aman yayi yace ” da gaske, bro kasan yarinyar nan tana da kyau fa idan na wanke ta ba karamar first class bace ta gaban mota , I think zan kashe mata kudi ta wanku kawai na fara fita party da ita nasan my friends will be jealous ” tsaki Ayman yayi yace ” Allah ya shiryeka kar ka bata tarbiyar yar mutane ” ” ameen idan da gaske kake ” remote Ayman ya dauka yana changing channel Aman yayi wuf ya kwace nan suka fara kokawa har suka fada bisa 3 seater Ammi ta shigo ta harde hannu tana kallonsu tace ” sannunku kajin Ammi ” Aman ya juya yace ” Ammi ki fada masa ya fita harkata ni ba abokin wasan shi bane ” murmushi Ammi tayi tace ” wannan yayan ka kada kaga sayinku d’aya ka nauka ko mate nakane ya girme ka da 2 years ” ” Ammi 2 years wani abune” ya fada yana hararin Ayman, Ammi tace ” zee tana downstairs tana Neman Ku ” Ayman yace ” wacece zee kuma?” ” oho! Nidai haka house maid tacemin ana Neman waye daga cikinku oho, sai Ku tashi Ku tafi ita tasan wurin Wanda tazo ” daga haka ta juya ta fice Aman ya fara murmushi yace ” awn..dat girl ka manta? Ur crush ” tsaki Ayman yaja ya wuce bedroom. Aman ya sauka xuwa downstairs ya sameta zaune nan suka gaisa mai aiki ta kawo mata lemu tana sipping tace ” ina mutumina ko baya gida ne?” ” yana nan basaraken naki, kinsan halinsa da girman kai bazai fito ba ” tashi tayi tana rataye bag nata wani farin handkerchief ta fitar ta manna bakinta a kai nan tambarin bakin mai dauke da jambaki ya fito ta mikawa Aman ga wani qamshin turare dake tashi a jikin hankin tace ” gashi ka mika masa please since bazai iya fitowa ba , tell him I love him ” ” wow..I like your style ” murmushi tayi ta juya ta fita.dariya Aman yake harda faduwa da sauri ya dauki sakon ya haura xuwa upstairs part nasa ya shiga Ayman baya falo kai tsaye bedroom ya wuce ya samesa kwance daga shi sai boxer’s ” meyasa baka da hankaline Aman, ya zaga shigomin babu sallama ” ” naga dai dakina ne kuma me zan gani a jikinka Wanda ni bani dashi ” ” kai yarone sai ka girma ” tsaki yaja ya tsani a kirasa yaro nan ransa ya baci ya wurgar da hanky yace ” gashi sakon budurwar taka ” ya juya ya tafi, Ayman ya kafa ido yana hango shatin bakin nata da red lipstick ya kauda kai sai yanzu ya tuna da letter da aka basa a hanya. Cikin bag nasa ya duba babu ya tuna da aljihunsa ya dauki wandon yasa hannu ya ciro takardar ya warware ya karanta abunda ke ciki ya nAnata yakai sau uku murmushi yake ya lumshe ido yace ” wannan dai aikin yaranta ne harda wani kibiyar so” murmushi ya cigaba dayi yana jin wani nishadi a ransa a haka bacci ya daukesa.

********************

*kojoli, Adamawa state*

Fattude magaji ( unguwar magaji ) tsofaffi na xaune da yamma a majalisa samari na can gefe kusa da wani shago suna nan suna hirar duniya kamar yadda aka saba wata dalleliyar mota tazo ta tsaya wani hamshakin mai kudi ya fito tare da wani a bayansa , majalisar suka dosa kai tsaye sai da suka karasa da sallama wani ya mike zumbur ya buga kirji ” Sule ,sule Kaine ko idona na min karya ” ya karasa ya rungumi mutumin ” iya nine ba mafarki kake ba ni din ne ” suka rungumi juna mutanen wajen sai salati suke, mai kudin ya mika hannu suka gaggaisa aka bashi tabarma ya xauna wani dattijo yace ” wannan ba magana ta majalisa bace,tashi Ku tafi gida gaban iyayensa ” babu gardama suka tashi suka shiga mota har xuwa kofan gidan malam laido Niko Reefat nace dama iyayensa Nada rai shine inna suka baro garin, sallama sukayi a kofan wani zaure irin na gargajiya wani yaro ya fito yana ganin sule ya ruga a guje xuwa cikin gida, babu bata lokaci sule yabi bayansa nan mutanen gidan suka tsaya cirko cirko suna kallonsa wata tsohuwa ta fashe da kuka ” sule dama kana raye, kai alhamdulillahi” kuka ta farayi ya karasa ya tsaya gabanta tana taba fuskarsa zama sukayi bayan an shimfida babban tabarma, ruwan randa aka debo cikin kwanon sha mutumin yana murmushi yace ” nagode ” Nenne ina Amina take naje gidan bata nan ” kallon kallo suka fara tsakanin yan uwan nasa nenne tayi karfin hali tace ” ko ruwa Baku sha ba ka fara tambayoyi ” mutumin yace ” baiyi laifi ba don ya tambayi labarin mai d’akinsa a tunani na ” shiru ne ya biyo baya mutumin yace ” ba tare da bata lokaci ba sunana Alaji Harouna daga kasar kamaru muka fito, tun bayan barin sule gida ya hadu da hatsarin mota a hanyar shiga kasar tamu a nan aka tafi asibiti dasu inda wasu suka rasa rayukansu , ya dade a gadon asibiti babu danginsa ko d’aya tun ana cigiya har aka gaji a nan na samu labari naje na taimaka masa .ya share shekara guda yana jinya don ya bugu sosai Allah yasa yana da Nisan kwana a duniya da yanxu sai labarinsa, ya sake samun matsalar kwakwalwa Wanda a dalilin haka ya manta da komai baya iya tunawa a hankali Allah ya saukar masa da sauki, da naga ya warware shine naga ya dace ya dawo gida gurin iyalansa shine Allah ya kawomu lafiya alhamdulillahi ” godiya suka masa nan ya cire kudi mai yawan gaske ya ajiye ya musu sallama yace zai tafi, godiya suke har bakin mota suka masa rakiya ya tafi daga nan suka dawo cikin gida sule ya sake tambaya ” ina Amina take ina yata hajjo uwata ta kaina ” sunkuyar da kai kowanne yake Nenne ta fashe da kuka tace ” kayi hakuri d’an nan da labarin da zan baka , koda bayan ranka ne yan uwanka gasu nan su ya kamata su rike iyalinka amma Abu ya gagara,Amina ta zama abin tausayi abin zagi a gari ni kaina bani da hanyan taimakonta don bani da komi sai abinda aka bani, baiwar Allah ta gaji ta tafi ” girgiza kai ya farayi ” meyasa kukayi haka Baku min halacci ba, ta ajiye mulkinta da dukiya da ilimi da yan uwanta ta biyoni nan amma kuka nuna mata kiyayya saboda ita ba bafulatana bace, shin yaushe kanku zai waye Ku daina cewa dole sai anyi auren dangi, kaico yanxu Allah kadai yasan yadda ta fuskanci iyaye da danginta domin mahaifinta yace bai yafe ta sake taka gidansa ba saboda ta bijire musu ta zabeni a matsayin abokin rayuwa amma kash..kunci amanata ” kuka yake nenne tace ” kayi hakuri da maganar da zan fada maka sule, Amina bata koma garinsu ba hasalima guduwa tayi zata tafi Habuja Neman kudi yan kabila suka taresu a hanya kowa ya watse yanxu babu Wanda yasan inda suke ” hawaye wani na bin wani baice komai ba ya tashi ya fice daga gidan, wani kaninsa ya biyo bayansa dakyar ya cinmasa yana bashi hakuri, kudi ya cire a aljihu ya mika masa cikin kudaden da Alaji Haroun ya basa yace ” ka ba Nennne kace ta min adua na tafi Abuja Neman Amina sai ranar da Allah ya dawo dani ” ” haba ya sule da la’asar haka” ” yanzu zan wuce na kwana a yola gobe na wuce Abuja” ” Allah ya tsare ya bada sa’a Allah ya bayyana mana su ” ameen ya amsa ya tafi kan hanya jiran motar xuwa yola yana jin radadi a cikin zuciyarsa.

*NaSarar rayuwata* is not for free ,ki biya 300 kacal ki karanta a sAwwake please be mature n patronize with me, tuntubi 07030077024 don samun account number, littafine mai nishadantarwa, fadakarwa da ilimantarwa zaki koyi abubuwa da dama a ciki mallaki naki akan farashin dari uku kacal.
Thanks fans love you all irin sosai din nan

Back to top button