Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 15

Sponsored Links

page 1⃣5⃣

Malam musa yace gaskiya ba zamu iya amincewa da buk’atarkiba domin kunfi k’arfinmu ku masu kud’ine mu kuma talakkawane, kinga ba zaiyuwuba ace masu sarauta kamarku sun had’a zuri’a da muba.

sultana bilkisu tace kar kudamu ai anzama d’aya kar kumance da talakka da maikud’i duk Allah ne ya haliccesu kuma shi yakeba Wanda yaso yahana wanda yaso, jahiline kawai zai iya gudun talakka, ammah duk wanda yasan abinda yakeyi toh ba zai gujesaba domin yasan wake azurtawa da hanawa, a lokaci guda Allah zai iya maida talakka mawadaci sannan yamaida mawadaci talakka, toh tayaya kuke tunanin zamu gujeku? saidai idan kuna tunanin d’iyarkune kar mucutar da itane, insha Allahu ba zamu nuna banbanciba zamu kula da ita kamar yadda zamu kula da ‘ya’yanmu da muka haifa a cikinmu, burina kutaimaka ku amince kubamu auren zarah.
mu musulmaine munsan girman alk’awali dan haka nayi muku alk’awali zamu kula da ita bakin gwalgwado.

gaba d’ayansu shuru sukayi suna saurarenta, yanayin yadda sultana tayi maganar yasa suka yadda da ita, kuma sunsan adalci da kirki irin na sarkin garin indai shi zuri’arsa suka biyo mutunci toh ba zasu samu matsalaba.

chan Abbah yakalli mama yace tataso suje suyi shawara dan haka mama tatashi suka shiga d’aki suka bar sultana zaune wajen tana dannar waya,

a chan d’akin abbah yakalli mama yace zainabu abun nan yad’aure min kai kina ganin zai yuwu mubasu d’iyarmu? nifa ina tsoron su wulak’anta mana ita domin su masu arzikine mukuma talakkawa.

mama jinjina kai tayi tace nima abinda nake tunani kenan gaskiya kar mubasu domin bamusan yadda gaba zata kasanceba, ace duk matan garin nan surasa wadda zasuce sai zarah, so suke sujamana zagi da surutun mutanen gari.

malam musa jinjina kai yayi yace ni bama dai wannan ba kiduba kiga bayanin da tayi mana tabbas daga gani tasan daraja da mutuncin mutane daga jin kalamanta, ta ni bandamu da surutan mutaneba saidai inajin tsoron su wulak’antamin zarah domin yarima suhail ya wuce ajin zarah wajen komai, ammah kuma ina jin nauyinta bana iya hanasu zarah.

ummah tace hakane malam ko dan matsayin da darajar da ke garesu kaduba kaga bata nuna mana k’yamaba nima wlh ta wajena babu matsala domin halayyarta ta yi min kuma nasan indai d’antane takeson hadawa da zarah toh bamuda matsala saboda da alama zai kasance mai irin kyawawan halinsu saidai ba a nan takeba matsalar tana wajen zarah.

malam musa jinjina kai yayi yace tabbas zarah itace matsalar ina tsoron taki amincewa saidai nasan zarah akwai biyayya zata iya bin ra’ayinmu ko da ace bataso, dan haka idan kinga hakan ba matsala toh muje mu amsa mata,

mama tace toh nan tabi bayan malam musa suka fito, yadda sukabar sultana haka suka dawo suka taddata, suka koma mazauninsu suka zauna.

kallonsu sultana tayi tace dafatan kun yanke hukuncin da kuke ganin ya dace wlh Indai baku aminceba zamu iya hak’ura domin ta yuwu zarah ba matarsa bace.

malam musa yace ranki yadad’e mun ma amince domin darajarki da martabanku yasa bama iya ji zamu iya hanaku zarah fatanmu dai zaku rik’eta kukular mana da ita tsakani ga Allah.

sultana bilkisu tunda taji ya ambaci sun amince wani irin farinciki yakamata kasa 6oye murnarta tayi tace gaskiya naji dad’i kuma nagode sosai insha Allahu zamu kular muku da ita, sannan zanje muyi magana da iyayensa koma dai mekenan zamuyi waya, takalli mama tace bani number d’in wayanki nan mama takaranto mata sannan sultana bilkisu takira kuyanginta suka dawo, fuskarta d’auke da fara’a tace naso ace naga d’iyartawa ammah tunda batanan zamu had’u wani lokacin.

mama tace a’a ranki yadad’e ai sai inje inkirata tana chan bayan layin nan sunje kitso, sultana tace a’a kibarta kawai zamu gaisa wani lokacin, kar6ar jakkarta tayi a wajen d’aya daga cikin kuyanginta tazaro 100k ta aje musu sannan tamik’e tace bari inwuce.

Abbah yace a’a kibar kud’inki mu dan Allah mukayi.

sultana murmushi tayi tace karkadamu nima dan Allah nayi domin babu kud’in da zasu iya sayan zarah, kuyi hak’uri kyautace.

Abbah da mama sukayi godia, har wajen mota suka rakata saida sukaga tafiyarta sannan suka dawo cike da farin ciki.

 

Mama kallon Abbah tayi tace malam toh yanzu ya kake ganin za’ayi idan zarah tadawo? kana tunanin zata amince?

Abbah murmushi yayi yace kar kidamu kibar komai a hannuna.

mama tace toh Allah yashige mana gaba.
Abbah yace Ameen.

daidai lokacin su zarah suka shigo gidan suna dariya, mama da Abbah kallon juna sukayi sannan suka maida kallonsu ga ‘ya’yan nasu suna murmushi, su zarah isowa sukayi tare da duk’awa sukayi ma iyayennasu barka da rana, mama tace ‘yan albarka har kunyo kitson?

sukace eh mama, gaba d’ayansu suka mik’e zasubar wajen, abbah yace kudawo kuzauna munason magana da ku.

A tare suka zauna suna jiran Jin abinda iyayennasu zasu ce, Abbah ne yayi gyaran murya yace duk inda kuka tsinci kanku kukasance masu dogaro ga Allah, kurik’e gaskiya sannan duk mijin da Allah yaza6a muku kukar6esa hannu biyu domin ita rayuwa ta yuwu abinda mukeso ba alkhairi bane wanda bamuso zai iya kasancewa shine mafi alkhairi, gaba d’ayansu shuru sukayi suna sauraren mahaifin nasu da suka kasa gane dalilinsa nayi musu wannan nasihar,

mamace tacigaba da cewa ku ‘ya’ya matane ba zaku dauwama a k’ark’ashinmu ba wata rana dole kubarmu kukoma k’ark’ashin mijinku a kullum addu’anmu Allah yahad’aku da mazaje nagari kuyi aure.

Abbah yace tabbas zancenki hakane zainabu sannan yamaida kallonsa ga zarah yace saidai kuyi hak’uri domin munyi wani karambani a matsayinmu na iyayenku munyi abinda muke gani kamar daidaine saidai a wajenku bansan yadda zaku d’aukesaba musammanma ke zarah!

gaba d’ayansu mamakine yacikasu sun ma rasa gane inda zancen abbah yanufa, zarah ce ta nisa tace Abbah bana tunanin akwai abinda zakuyimin yazama laifi wlh duk hukuncin da kuka d’auka kaina daidaine domin kun cancanci hakan.

Abbah dogon numfashi yaja yace hakane zarah ammah kiyi hak’uri da maganar da zata fito daga bakina, zarah munyi miki miji.

zarah a razane tad’ago kai takalli abbah muryanta yana kyarma tace abbah miji kuma? Aysha da Rauda sukace miji!!!

Abbah gyad’a kai yayi cikin rashin damuwa yace tabbas miji kuma nasan zaki sosa kema bakowa bane face d’an sarkin garinnan *Yarima Suhail*

zarah a tsorace tamik’e tsaye tare da ja baya tace abbah aura min wani zakayi ba malam bello ba?

Abbah yace zarah kidawo kuzauna inyi muku bayanin komai,

zarah hawaye tafara tare da dawowa tazauna, nan abbah da mama suka kwashe labarin zuwan sultana bilkisu da yadda sukayi da ita babu abinda suka 6oye masu hatta kud’in da tabasu.

Zarah fashewa tayi da kuka tace Abbah kuyi hak’uri wlh bana sonsa shima nasan ba zai soniba dan Allah kubarni in auri wanda nakeso wlh malam bello shine za6ina.

 

Aysha da Rauda murmushi sukayi suna jin wani irin dad’i a ransu.

mama ce tace haba zarah ya kamata kid’auki k’addara muma ba a son ranmu hakan takasanceba dan dai babu yadda zamuyine kinga ba zamuk’i amincemataba tunda har tazo gida tanemi alfarmarmu.

Zarah mik’ewa tayi tsaye tana kallon iyayen nata tana girgiza kai, cikin kuka tace kawai dai kuce kun siyar da ni, yanzu kud’i zasusa kubayar da ni? bakwa tsoron suwulak’antani? wlh bana sonsa kuma ba zan ta6a sonsaba inma dan kud’insu yasa kukayi min haka toh wlh saidai kumaida musu kud’insu domin ban aminceba, ni malam bello zan aura.

 

Yaya Rauda tace zarah wai minene haka kikeyi?

zarah cikin d’aga murya tace kubarni yaya rauda ba zan ta6a amincewa ba.

Aysha tace yaya zarah su abbah fa kike d’aga ma murya.

Zarah dasauri tatoshe bakinta da hannuwanta tana girgiza kai tace kugafarce ba zan iyaba, tana gama fad’in haka tashek’a da gudu tashige d’aki tafad’a saman katifarsu tana wani irin kuka saikace wadda aka aikoma da sak’on mutuwa.

gaba d’ayansu jikinsu yayi sanyi musammanma su Abbah da mama da basu d’auka abun zaiyi zafi hakaba.

Rauda ce takalli iyayennasu tace Abbah kuyi hak’uri 6acin rai ne yasa zarah tayi haka ammah ai tana da sanyi natabbata zata sauko daga fushin da take.

mama tace kar kudamu nasan halin d’iyata ni zan shawo kanta da kaina.

Abbah dai girgiza kai yayi takaici duk ya cikasa

Aysha ce tace Abbah kayi hak’uri zata safko yanzu tad’auki zafine saisa, ammah fa naji dad’i da zata auri yarima wlh ya had’u sai ma da nagansa a wajen safkarsu.

Rauda tace wlh kau ni har nahango sunyi match sosai, cike da murya Aysha tace yayata zata zama *Gimbiya Zarah* matar *Yarima Suhail* dak’uwa mama tayi mata tace gidanku munaso murarrasheta tasafko sai kinja ta jiyoki.

Aysha cike da farin ciki tarik’e bakinta da hannu tace afwan na daina.

mama kallon Abbah tayi tace malam kar kadamu insha Allahu Zarah zata safko ni zanma je na lallasheta har tafahimcemu.

malam murmushi yayi yace toh Allah yasa tafahimta inma dai bata aminceba zan fasa basu domin ba zanyi mata doleba, duk yadda kukayi da ita sai kufad’amin yanzu dai bari intashi infita koma mekenan sai nadawo

gaba d’ayansu sukace adawo lafiya.

 

bayan Abbah ya fita Rauda kallon mama tayi tayamutsa fuska tace mama yau naman kaza nakeson ci, murmushi mama tayi tace Rauda kin cika kwad’ayi tashi ga 1,500k kuje wajen dauda mai kaji yayanka yafige sai kuzo kuyi mana pepper kowa yaci.

Rauda cike da jin dad’i tace toh mama yanzu ko zamuje muna godia.

Aysha ma cikin murna tace Allah yabarmana ke maman gimbiya.

Mama duka takaima Aysha tagoce suna dariya ita da rauda, mama tace sai naci gidanku inbakuyi wasaba.

mik’ewa mama tayi tace kuyi sauri kuje kudawo ni bari inshiga wajen d’iyata in rarrasheta.

mama ko da tashiga lokacin zarah ta ci kukanta, kwance take kanta yana kallon ceiling d’in d’akin hawaye kawai suke zuba ta gefen idonta, mama gefen inda zarah take kwance tazauna tana mai k’arema zarah kallo da duk idanuwanta sun kumbura.

A hankali mama tace zarah kuka kikeyi ko? shuru zarah tayi batace komaiba, mama cigaba tayi da cewa kiyi hak’uri zarah wlh muma ba’a son ranmu hakan takasanceba dan dai babu yadda zamuyi mubijire ma buk’atarta domin yadda tazo ta aje girma da matsayinta tana rok’onmu mu amince mata muba d’ansu aurenki, hmm zarah munsan zakiyi tunanin ko k’wad’ayine yasa mukayi miki haka ammah wlh ba haka bane *k’addara ce* kawai, domin kowane iyaye suna burin ganin farin cikin ‘ya’yansu koya suke suna son ganin farin cikin yaransu ko da ace zai tauye nasu farin cikin, canzawar yanayinki yasa abbanki ya ji ba dad’i domin har ya fara tunanin yaje da kansa yafad’a musu ya fasa badake, domin kowane iyaye suna burin ganin ‘ya’yansu sun auri mijin da yacancanta mutumin da zai kular masu da ‘ya, wanda yake sonta kuma danginsa suma suna sonta.

zarah lumshe idanuwanta tayi hawaye suna zuba tana jin wani iri a ranta, mama cigaba tayi da cewa saidai mu kuskuren da mukayi a baya har yanzu akwai sauran tabonsa bai warkeba a zuciyan zarah, zarah har yanzu kallonmu take a matsayin kwad’ayayyun iyaye, idan barinki ki auri wanda kikeso zaisa kigane cewa ba dukiyarsu muke k’wad’ayiba toh mun amince kije ki auri bello domin shima mutumin kirkine saboda farin cikinki shine namu fatanmu kigane cewa tuni iyayenki sunbar wacchan rayuwar da sukayi a baya, ko da ace za’a kallemu a matsayin k’ananun mutane masu magana biyu toh bazamu damuba saboda munfi buk’atar naku farin cikin.

zarah dasauri tatashi tarungume mama tare da fashewa da sabon kuka tace mama kuyafemin wlh ba haka nake nufiba, na amince da za6inku bana fatan ayi ma iyayena kallon marassa cika alk’awali koda ace zan mutu toh nagwammace inmutu ta dalilin faranta ma iyayena rai, tabbas nasan bazaku ta6a yimin za6in da zai cutar da ni ba wlh na hak’ura da malam bello wanda kuka za6amin shine zan aura, tana kaiwa nan tasake fashewa da kuka tace mama kuyafemin.

mama ma hawaye takeyi cike da tausayin d’iyartasu tace zarah bakiyi mana komai ba saima mu da mukayi miki.

zarah girgiza kai tayi tace mama kidaina cewa haka duk abinda kuka yanke akaina daidaine kuma cancanta da matsayine sukaja hakan.

mama rungume d’iyarta tayi tana hawaye tausayin zarah duk ya kamata, lallashin zarah tashiga yi har saida taga tayi shuru.

zarah mik’ewa tayi tace bari inje inba baba hak’uri nasan fushi yake da ni, mama tace ai baya nan ya fita.

zarah komawa tayi tazauna tace toh idan ya dawo zan je.

Mama murmushi tayi tace Allah yayi miki albarka zarah wlh kin cika d’iyar kirki, Allah yayi muku albarka gaba d’ayanku.

Zarah murmushi tayi tace Ameen mama.

Mama mik’ewa tayi tace bari inje nasan yanzu su Rauda zasu dawo

 

zarah batace komai ba, tana ganin mama ta fita yasa tatashi tashige toilet tare maida k’ofa tarufe anan tafashe da sabon kuka mai tsuma zuciya duk tausayin kanta da na malam bello yakamata domin tasan so d’ayane yakeyi mata batasan yadda zai fahimci maganarba idan taje masa da ita, saida taci kuka mai isarta sannan tawanke fuskarta tare da tad’auro alwallar magrib tashinfid’a darduma tad’auko alk’ur’ani tana karantawa domin samun sauk’in abinda takeji a ranta.

 

 

Bayan sallar isha’i zarah zaune tayi a d’akinsu har lokacin fuskarta babu walwala duk yadda su Rauda sukaso tasaki jiki ammah ta k’i, abincima dakyar tad’anci kad’an.

wajen k’arfe takwas tanajin dawowar Abbah saida tadaidaici daidai lokacin da yagama cin abinci sannan tataso tanufi d’akinsa jikinta a sanyaye tayi sallama.

 

Abbah da yake zaune hannunsa rik’e da redio yana sauraren labarai amsa mata sallamar yayi tare da rage k’arar redion.

Zarah shigowa tayi taduk’a k’asa muryarta tana rawa tace Abbah dan Allah kayafe min abinda nayi maka wlh na amince zan auri za6inku domin nasan ba zaku ta6a cutar da rayuwataba duk hukuncin da zaku zartas akanmu daidai ne burinku a koda yaushe kuga farin cikinmu, wlh akoda yaushe ashirye nake da incika umurninku domin 6acin ranku daidai yake da rugujewar farin cikina.

 

Abbah murmushi yayi cike da jin dad’in maganar zarah yace wlh zarah bakiyimin komai ba, indai baki sonsa kifad’a min wlh bazanyi miki doleba zan aura miki wanda kikeso domin farin cikinki nafi buk’ata.

 

zarah girgiza kai tayi tace Abbah wlh wanda kaza6amin shi nakeso ashirye nake a koda yaushe in amshi za6inka.

 

Abbah kasa 6oye farin cikinsa yayi yace nagode sosai zarah Allah yayi miki albarka kema Allah yabaki wad’anda zasuso farin cikinki, insha Allahu wannan auren zakiji dad’insa, Allah yayi muku Albarka gaba d’ayanku, zarah cike da jin dad’in addu’an da abbah yayi musu tace Ameen Abbana nagode sosai.

 

 

 

Zarah tunda takwanta kasa bacci tayi juyi kawai take abin duniya duk ya isheta tana tunanin yadda za’ayi ta auri wanda bata so, tunowa tayi da yarima suhail lokacin da yazo walimarsu yadda yake shan k’amshi, ba ya ma kallon kowa, tsaki taja tace wannan d’an jin kan zan aura, hawaye ne suka zubo mata tunawa da tayi da malam bello ta yaya zata fuskancesa da maganar zata auri wani ba shiba batasan yadda zai fahimci maganarba, tana ta sak’e-sak’e a ranta a haka bacci yayi awon gaba da ita batare da tashirya yinsaba……..

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_
?

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Yau page d’in nakune k’annena nakaina *JANAF nd SAFIYYA ALIYU* inaso kusani ina sonku irin totally d’innan Allah yabarmu tare_

Back to top button