Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 23

Sponsored Links

Haba jama’ar annabi ku kawo min ɗauki mana, ni ba tumatur ba ba gwanda ba amma gani a firinji sai ɗaukan sanyi nake” Cewar Inna cikin ɗaga murya tana jin wani kuka na taho mata. Wata atishawa ce ta taho me haɗi da majina saboda sanyin da ya gama ratsa ƙasusuwanta, so take ta yi ihun da kowa zai ji ta, a san cewa tana cikin na’urar bada sanyi dan ta lura duk kwakwazon da take ba wanda ya ji ta.

“Halimatus Sa’adiyya, ki bar micijin nan ki taho ki buɗe firinji kafin in yi ƙanƙara, ko masasssara ta kamani Malam ba zai yafe muku ba, Asharofa, Asharofa, ki fito daga bayin nan ki zo ceton rai ” Cewar Inna da sanyi ya gama ratsa muryarta har ta fara shaƙewa ta faɗa tana sakin kuka. Jin shiru babu alamar ma ana jiyo ta sai ta fara magana a ranta.

“Yau ni Azumi wannan yarinyar akwai ƴar ƙundun buhun uba, yarinya ƙarama cakuru kuci cikon bancin ta garƙame a cikin wurin nan firinji sai aikinsa yake ni kuma ina ɗaukan sanyi, wannan ZAMAN WANKA bai ƙare ni da komai ba” Ta faɗa tana sanya hannunta ta rufe hancinta saboda sanyin da take shaƙa kamar wanda aka jefa ƙanƙara a cikin hancin.

“Ƴan nepa ku taimaka ku ɗauke wuta dan shi firinjin ba hankali ba gareshi bare ya san Azumi ce a ciki, ya san ba fura bace ya dakata da aiki” Cewar Azumi tana ɗaga ido ta kalli ɗan ƙaramin ƙwan da ke cikin freezer ya kawo haske abinsa.Hannu ta kai ta zage ƙarfinta duk da a takura take saboda matsi amma a haka ta jimƙe hannunta ta daki jikin ƙwan tana cewa.

“Wallahi gwara na fasaka firinjin ya lalace gabaɗaya a kan ina ji ina gani in ke zaune cikin ƙanƙarar nan, ni ba me rayuwa a turai ba, in zo in sandare in mutu a banza a ɗakko ni a daskare makara ma bata karɓeni ba dan ba tanƙwasuwa zan yi ba yadda nake a tsugunnan nan a haka zan ta zama, ko kabarin na san sai ko a gina min me zurfi a zura ni a ciki kawai, babu damar a kwantar da ni, ko ƴan gaisuwar mutuwata suka zo, na san sai dai suke cewa ashe azumi sa’i ya yi to Allah sa tsugunno hutu ne, dan babu me cewa kwanciya hutu ce, dan a tsugunne nake ba a kwance nake ba”

Ta faɗa lokacin da ta naushi jikin ƙwan amma ko gezau be yi ba bare ta sa ran zai fashe,ssi wani zafi da hannun ya ɗauka. Hannu ta kai ta shafo goshinta inda ta bugu ɗazu a garin gudun ceton rai, wurin ya yi ƙullutu ga zafi, tana taɓawa wani tausayin kanta ya kamata haushi ne ya sa ta shiga bugun freezer ba ƙaƙƙautawa dan ta san idan bata yi da gaske ba haka za ta mutu babu wanda ya sani.

Ƴan cikin loka ƙaran bugujn freezer da Inna take sai suka ɗauka micijin ne ya ƙaraso jikin lokarsu yake bugawa hakan ya sanya kowacce ta tsure, wata ƴar gidan ƙanwar Mama da yake ƴar siririya ce ita ce daga ƙasa sai wata bazawara ƙatuwa ƴar uwar Imran a kan ta tsabar yadda bazawarar ke da nauyi kuma a kan siririyar budurwar take dakyar take jan numfashi dan gabaɗaya ta danne mata har wajen kanta amma saboda tsoro sai bata ce komai ba, wannnan ƙaran da ya sanya suka firgita sai ƙatuwar ta ɗan muskuta ɗuwawunta aikuwa tsabar tsurewa ta saki wata uwar tusa da ta gama ratsa hancin siririyar ji ta yi kamar an saka hancinta a cikin kashi, tsabar wari har wani ɗaci-ɗaci ta ji a maƙoshinta. Kai ta shiga girgizawa, tsabar. Inna da bata san wainar da ake toyawa ba tana ta ƙoƙarin a zo a ceceta dan ta san har ƙwara na cikin lokar sau dubu a kan ita da ke ciki duk ta fara sandarewa dan da wani zai taɓa jikinta yanzu sai ya ji kamar ƙanƙara ya taɓa. Wani uban zabura ƙatuwar matar ta yi aikuwa kanta da ke dab da saman lokar ta ciki ya bada wani gum, gumewar da ta yi a kanta sai kuwa ta sake sakin tusar, gabaɗaya lokar ta haɗe da wari su duka a takure suke, ba dan micijin nan ba da babu wanda zai iya shaƙar numfashi saboda ɗoyi amma tsoro ya sa ba za su fito ba, siririyar nan jin an ƙara sakar mata tusa haushi da takaici ya sa ta ɗan gota kanta daga saitin ɗuwawun matar dan hancinta ma a wajen maraba biyu yake ta tsagar ɗuwawun matar aikuwa cikin fusata ta buɗe bakinta ta gantsara mata cizo a ɗuwawun wani azababban zafi ne ya ratsa matar da ta manta da cewar a ɓoye suke ta hangame baki ta saki wani uban ƙaran ta ce.

“Wayyo ya gantsara min cizo a ɗuwawu” Duk ta ruɗe da zafin cizo sai ta zata micijin ne ya shigo ya cijeta dan ƙuncin da suke ciki ko ƙasa baka iya kallo duka a wuri ɗaya suke a cure. Yarinyar nan me ƙunshi jin an ce an yi cizo a ɗuwawu sai ta fara karkarwa dan ta san ita ma micijin dole ya ganta tunda ya ga na cikin loka ma bare ita aikuwa ta saki wani kuka, ga buhun da ta tuƙunƙuna ta saka a bakinta sai sautin kukan ya bada wani wuuuuu kamar wata jiniya. Inna da ke cikin freezer jin ihun da kuma ambaton da aka yi na an yi cizo sai ta ce.

“Wallahi gwara ku a kaina duk tsiya ai inda sauran kwananku za a sa muku maganin dafin miciji ku warke, idan kuma kuka mutu ai zaku kwanta a kabarinku a kan ni da sai dai ake Allah sa Azumi tsugunno hutu ne” Ta faɗa tana sakin kuka tana da na sanin zuwa ZAMAN WANKAN ma gabaɗaya.
Sauran ƴan cikin lokar kuwa sai tsoro ya ƙara shigarsu ji micijin har ya shigo lokar ya yi cizo banda wacce ta yi cizon da ta san ita ce ta yi cizon ba miciji ba, hakan ya sanya ɗaya kama jikin ɗaya ta damƙe da hannu biyu aikuwa wacce aka damƙa ta wage baki ta saki ihu ta ce.

“Wayyo an damƙe min nono, wayyo ni Allah na, ni ba a min ƙunshi ba amma za a min lahani” Ta faɗa cikin kuka da azabar da ta ji a jikinta, da yake yarinya ce ba wata babba ba irin ƙirgen dangin nan ne ta fara wanda ko ɗan bigewa ka yi a jiki sai ka ji azaba. Ita kuwa wacce ta damƙi yarinyar bata ma san abin da ta yi ba, jin wai an ce ta damƙi nono da sauri ta saka dan ita bata ma san ina ta kama ba ta dai ji fitsarin yarinyar na gangara a kan ƙafafunta.

“Wayyo Allah wallahi da a taɓa min wurin nonona, ko da kuwa da ɗan yatsa ne gwara in bada kyautar naira dubu saboda azabar ciwo amma kin zo kin damƙa kamar kin samu ƙanzo” Ta faɗa cikin kuka, babu wanda ya ce wani abu dan yanzu ta kai- ta kai ake.

“Gwara ke nono aka damƙa, wayyo ɗuwawuna za a cire min fatar” Ta faɗa jin an ƙara cafka da haƙori dan tana sakin tusa ita kuma ta ƙasanta ke gatsara mata cizo.

Inna da ke cikin freezer ta ƙyalƙyale da dariya duk da halin da take ciki, amma jin ana damƙe-damƙen ɗuwawu da nono sai abin ya bata dariya ta ce a zuciyarta

“Yau dai ana dara ga kuma dare ya yi, Hassan duk ya rabawa kowa aikin wahala”

Me ƙunshi ma kukan da take ne ya haɗe da dariya a ranta ta ce.

“Taɓɗi yau da a ce ba a halin ƙaƙanikayi nake ba dariyar da zan yi sai cikina ya yi ciwo, dan ko ni lokacin da na fara ƙirgen dangi ko wanka na zo sai dai in zuba musu ruwa in ɗauraye su, ba na yarda in sa soso in wanke saboda azaba” Ta faɗa tana dariyar da ta kusa fitowa fili saboda yadda dariyar ke cinta.

“Inna! Inna!! Inna!!!” Inna ta jiyo muryar Sadiya tana ƙwala mata kira tun ƙarfi.

“Inna dan Allah ki fito ki tayani mu dawo da Hassan gashi can ya kama hanyar ƙofar gida zai fice kuma ƙofar ba a rufe take ba, ni kaɗai ba zan iya ba dan ya ƙi tsayawa ko ɗaukansa zanyi zulalewa yake” Cewar Sadiya tana kuka ta rasa yadda za ta yi hankalinta ya kai ƙololuwa wajen tashi, bata so ɗan nata ya fice duk da kasancewarsa a siffar muciji tana ƙaunarsa, Allah sarki uwa!

“Mtssss” Inna ta ja wani dogon tsaki ta ce.

“Banza ta kori wofi ma kenan yo Allah na tuba da ba a cikin firinjin nan nake ba ma babu abin da zai sa na zo wallahi, da kaina zan kaɗashi ya tafi, gwara ma ya je ya fice abinsa wataƙila ma wahalarki ce ta yanke, yo Allah na tuba zama da wannan abu a gida ai jafa’i ne, ya je can daji ya samu ruwa ƴan ruwa su ja abinsu mu huta, ga Husaini nan ya isa” Ta faɗa tana ɗaɗɗaga kai take kallon saman freezer.

“Dan Allah ku taimaka mini” Cewar Sadiya tana ɗaga murya.

Ashrof tausayin ƴar uwarta ya kamata amma ga kuma tsoro tana ganin kamar micijin zai iya cutar da ita, amma ita Sadiyar ba lallai ya cutar da ita ba saboda ita ce mahaifiyarsa.

“Ke dalla ɗaga ni kin wani min ɗirkaka a kaina kamar wani buhun hatsi” Ƴan cikin loka ke faɗa saboda sun ji an ce miciji ya kama hanyar fita waje.

“Kan ku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wankana nake “Cewar Inna.

“Ƴan cikin kicin ga Hassan nan ya nufo kicin” Sadiya da ta shawo gaban Hassan daga hanyar gida ya iyo kwana ya dawo gida ta faɗa cikin ɗaga murya ganin gadan -gadan ya nufi kicin ɗin.

Ashrof da ke ƙoƙarin fitowa ta taimakawa Sadiya ta dakata daga ƙoƙarin fitowa daga bayi jin Sadiya ta ce ya nufi kicin.

“Hahahaa na dawo in ji ɗan yawon duniya, yau akwai gwarama” Cewar Inna tana dariya ido na zubar da ruwan hanci ku sai tsiyaya yake kamar an kunna fanfo tsabar sanyin freezer da take shaƙa.

Gabaɗaya masu faɗa a cikin loka sai suka sha jinin jikin su ko kyakkyawan motsi sun kasa yi, kowa bakinsa sai motsi yake alamar addu’a.

Sai da ya je tsakiyar kicin ɗin ya ja ya tsaya tare da fasa kai alamar sara, Sadiya da ke tsaye a bakin ƙofar sai kallonsa take so take ta koma ɗaki ta ɗauki wayarta ta kira Imran amma bata so ta matsa daga wurin wani abu ya faru kuma ma ta san shi ma Imran tsoron Hassan ɗin yake ji idan ya sawaya.

“Kar wanda ya motsa daga inda yake Hassan yana tsakiyar cikin kicin ɗin” Cewar Sadiya cikin muryar kuka.

Ɗif kowa ya yi, me ƙunshi kwa da ta buɗe idonta guda ɗaya ta ɗan leƙo daga cikin buhun da ta lulluɓa da shi. Ganin micijin danƙarere ya fasa kai da alama sara kawai yake son yi, gashi kuma ta san babu wanda zai fi saurin gani sama da ita, a take ta ji ina ma ita ce a cikin freezer kuma freezer a buɗe a kan wannan tashin hankali da take ciki.

Bum-bum ƙaran bugun freezer da Inna take ya karaɗe wajen, duk bugu ɗaya sai micijin ya zabura, zaburarsa kuma ba ƙaramin ƙara razana me ƙunshi take ba, Inna kuma dama da niyya take bugawa saboda ko banza ta san ta rama kaɗan daga abin da yarinyar ta mata.

“Wayyo wannan tsohuwa masifarta ta yi yawa, yanzu sai ta firgita micijin nan ya shiga neman mutumin da zai sara a cikin kicin ɗin, tsoratar da yake yana wata girgiza yana fasa kai ta ko ina hakan ba ƙaramin tsurewa ya sanya me ƙunshi ta yi dan ita kaɗan ke ganinsa na cikin loka da Inna da ke freezer ra san ba za su gani ba.

Shigowar Imran gidan ɗauke da sallama shi ya sanya Sadiya nufarsa da sauri tana kuka tana faɗa masa, wani yawu ya haɗiye muƙut jin wai micijin har ya fara fitowa ya yi waricinsa a cikin gidan lallai babar magana . Haka dai ya daure tare da majewa ya nufi kicin ɗin, a haka ya sanya Sadiya ɗaukan micijin ta nufi ɗaki da shi har lokacin kuka take yi. Imran ganin matan nan na cikin loka ya ɓata mas rai ganinsu cunkushe kamar alhazai ranar arfa, wata da take leƙo idonta ta tsakanin murfin lokar ita ya dakawa wata uwar hararar da ta sanya ta runtse idanu, ƙafa ya sanya ya daki jikin lokar tare da cewa su fito haka, haka suka turo murfin suka fito simi-simi suna ciccira idanu kamar waɗanda suka yiwa sarki ƙarya.Suna fitowa daga kicin ɗin ya tsaya a bakin ƙofar yana binsu da wani mugun kallo dan daga me zarnin fitsari sai wani wari da ya kasa gane na menene.

Me ƙunshi da ke ƙunshe cikin buhu ta buɗe a hankali ta fito daga ckn buhun, da ta lulluɓa, tana fitowa ta kalli freezer a ranta ta ce

“Ke kuma tsohuwa a nan za ki kwana uwar sababin tsiya” Tana zuwa za ta fito ta ga Imran ya yi bake-bake a bakin ƙofar aikuwa ta yi ƙoƙarin bin ta ƴar sauran ƙofar da ya bari, Imran da bai san da sauran mutum a cikin kicin ba sai ji ya yi an ɗan shafi gefen rigarsa aikuwa dama duk a tsorace yake, jin an ɗan taɓa shi sai ya yi zaton micijin ne dan jin an ce micijin da kansa ya fito abin ya matuƙar bashi tsoro sai dai bai faɗa bane. Da gudu ya ruga a sukwane ya nufi ɗaki, sauran matan da suka fito daga loka suka mara masa baya dan duk tunninsu wani abun ne.

Yadda ya zuro a guje babu birki haka su ma suka daddage ƙarfinsu suke binsa da gudun, har da masu tattare zane gudun samun mushkila. Imran da gabaɗaya a gigice yake sai da ya zo falo ya ga Sadiya da miciji a hannu ya ja ya tsaya a ransa yana ganin jarumta irin ta Sadiya yana kuma jaddada soyayyar uwa da ɗa, ganin Hassan ɗin ne ya dawo dashi daga firgici da tsurewar da ya yi sai a sannna ya tuna cewar ashe ma Sadiya ta taho da yaron kawai tsoro ne ya sanya ya ga kamar micijin ne ya biyo shi. Wani yawu ya haɗiye tare da sauke wani numfashi. Matan nan ma ganin ya tsaya sai kowacce ta dakata a wajen dan sun manta da micijin a ɗaki amma ganin Imran na gudu su ma suka fara suna jejjefa idanu kallonsu kawai yake, daga wacce take jige jagaf da fitsari sai wacce ke da ƙunshi ƙafa ɗaya ba a ƙarasa ɗayar ba, sai wacce baƙin lalle ya gogu a fuskar ta koma kamar wacce ta shafa shuni. Wata harara ya musu tare da jan wani uban tsaki, ya wani maje yana harare-harare amma ya kasa shiga ɗakin, hango me ƙunshi a ƙofar kicin ɗin sai lokacin ya ga rashin azancinsa da bai tsaya ya waiwaya ba bare ya gane ba miciji bane.

Harara ya dakawa matan nan da suka biyo shi, dan sun ma kasa shiga falon shi ma cikin wayancewa sai ya juya ya nufi kicin ɗin me ƙunshin da gudu ta bar wajan ganinsa ya taho. Imra n kuwa na shiga kicin ɗin sai ya tsaya a tsakiyar kicin ɗin yana maida numfashi dan ba ya so a raina shi shi yasa bai tsaya maida numfashi a gabansu ba, su ma suna nan tsaye sun yi carko-carko. Dafa kan freezer ya yi tare da ɗora kansa a kanta, Idanu ya rufe ruf yana jin yadda zuciyarsa ke lugude kamar me tseren gudu, hannayensa duka biyu ya ɗora a kan freezer sai ya kwantar da kansa a kan freezer, idanunsa a rufe yana tunano yadda Sadiya ke ɗauke da miciji a hannunta, Inna da tun daɗewa take ta faman magana a kan a kawo mata ɗauki babu wanda ya jiyo ta, dan haka ta raya a ranta za ta shiga jijjiga freezer da ƙarfi dan a jiyo ta a zo a buɗe ta. Wata jijjiga da ta yiwa freezer da Imran ke riƙe da ita gam, hakan ya sanya ya saki wata tusa ta tsurewa ba tare sa ya shirya ba, jin freezer na girgizashi tamkar ana girgizar ƙasa hakan ya sanya ya ƙanƙameta da ƙarfinsa.

Dan gabaɗaya ma sai tunanin guduwa ya kwance masa.

“Allah wannan baƙar wahalar da nake shiga tun ranar da Sadiya ta haihu Allah ka sa kaffara ne” Ya faɗa lokacin da ya saki wani kuka me cin rai Inna kuwa bata daina jijjiga a cikin freezer ba yi take tun ƙarfi.

“Ai wallahi da in mutu a binne ni a tsugunne na gwammace in daddara firinjin nan in bayyana kamar wata ɗan daren goma sha huɗu” Ta faɗa tana lokacin da ta kai hannunt ta ƙwarzani jikin freezer ganin yadda farin ƙanƙarar nan me kamar dusa ta fara baibaiye jikin freezer.

“Oh Allah ni Azumi kamar wanda aka sanyani cikin buhun fulawa ji yadda farin ƙanƙanarar nan ya maida ni kamar furfura ta kar ni, ganin mukullin ya faɗo daga jiki, saboda bugawar da ake, cikin sanyin jiki da tsoro ya ɗau mukullin ya sanya jikin freezer ya buɗe a tsorace tare da ja baya kaɗan bakinsa sai kaiwa da komowa yake wajen addu’a amma baka jin me yake cewa shi kansa be sai me yake karantawa ba.

Yana buɗe freezer sai ya yi baya ya maƙe a bango, yadda ya tsaya kamar ka ce as ya zura a guje, jira yake kawai wani abu ya fito ya arce a na kare, dan ya yi alƙawarin idan ya doshi ƙofar gida sai dai idan ya je ƙofa ya ce kowa ya taho sarkin aljannu a frezer.

Inna ganin an buɗe dan ta ga alama murfin ya ɗan ɗaga da take ɗaga shi sama da kanta, hamdala ta yi a zuciyarta, ta fara kiciniyar miƙewa amma ina, ashe gabaɗaya zanin setin mazaunanta ya haɗu da ɗan sauran ruwan ƙasan freezer ya daskare har zanin. Hannu ta kai ta taɓo sai ji ta yi gabaɗaya ɗuwawunta yana danne da zani da ƙanƙarar.

Bata gama tsurewa ba sai da ta jita gabaɗaya a daskare har ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fasa saboda ta san ita tana jiyo maganar mutane amma ita ta ga duk kwakwazon da take ba a jinta.Zunkuɗa kanta ta yi cikin sa’a kuwa sai ƙoƙon kanta ya buɗe murfin ya yi sama. Imran da ke rakuɓe a jikin bango dan tun lokacin da ya buɗe ya koma ya rakuɓe sai karkarwa yake kamar shi ne a freezer, ganin an buɗe ƙofar sai kawai ya saki kuka yana ta matse ƙafafunsa amma tsoro sai da y sa fitsarin da yake ta matsewa tun daga lokacin da freezer ta fara girgiza ya ƙwace masa ya zubo. Tsoro ne marar misali ya baibaiyeshi.

“Ku min rai dan Allah, in gidan ma kuke so mu bari a yau ɗin nan za mu bari a yanzu ma kuma ko tsinke ba za mu ɗauka ba, ku taimaka mana” Ya faɗa yana ta so ya zura a guje amma gani yake kamar ma rafkoshi za a yi a dawo dashi kicin ɗin.

Inna kuwa gyaran murya ta shiga yi dan muryar duk ta shaƙe. Ai gyaran muryar da ta yi sai ya bala’in ƙara sanya Imran cikin tashin hankali da mummunan tsoro, bai ankara ba sai jin bakinsa ya yi yana faɗin

“Ya kusamu ya mu rasa, ya kusamu ya mu rasa” Sai maimaitawa yake kamar wanda aka sa tilawar ƙur’ani, shi kansa bai san me yake faɗa ba. Ya gama jiƙewa da hawaye da fitsari ga majina duk shi kaɗai kawai sai ji ya yi ta cikin freezer an ce.

“Imirana, Imirana, Imirana” Jikinsa ne ya fara karkarwa be ma san ya aka yi ba kawai dai ya ga ya fara zagaye wani kofi da ke tskiyar kicin ɗin, sai zagawa yake kamar yadda ake ɗawafi yana cewa

“Ya ku samu, ya mu rasa” Dan yadda aka kira sunan nasa ya tsorata shi dan yanzu dai ya tabbatar sarkin aljannu ne dan ya ji an kira shi d sunansa da alama suna ganinsa suna kuma sane da motsinsa. Dan yadda muryar Inna ke shaƙe idan ta yi magana kamar an shaƙewa kuturu wuya haka sautin ke fita, gabaɗaya ma ya manta da wata Inna bare kuma ya gane ita ke kiransa Imirana.

“Imirana, yaka buɗe firinjin nan” Cewar Inna dan duk abin nan da ake murfin freezer ɗagawa yake kawai idan Inna ta buga kai a jiki.Imran kuwa ji ya yi tamkar ya zura a guje, amma ba hali.

A hankali ya taka ya ƙarasa wajen hannunsa na karkarwa ya kama murfin freezer yana sakin wani kuka me cin rai marar sauti, haka ya buɗe freezer cikin cika umarninsu amma sai ya rufe idanunsa gam dan gani yake idan suka yi ido huɗu ganinsu zai sa ya haukace.

“Oh ni Azumi matar Malam sai yanzu kuka kawo min ɗauki” Imran da ke riƙe da murfin freezer ido a rufe hawaye na kwaranyowa sai karkarwa jikinsa ke yi ya tsinkayi muryar Inna daga cikin freezer da sauri ya buɗe idon aikuwa idanunsa ya sauka a kan Inna da ke cikin freezer ita ba a zaune ba ita ba a tsugunne ba, ga wani ɗankwalinta ya yi gefe ɗaya ya mata wani zungurgur kamar hular ibro.Ta yi wani yamutsatsa kamar an tsamo ɓera daga ruwa, Gabaɗaya sai Imran ya manta halin da yake ciki na damuwa, a take ya saki wata dariya dan har ya hango dalilin shigar Inna freezer.

“Hassan” Ya faɗa a zuciyarsa, wato dai saboda miciji ta shiga freezer ya baiwa kansa amsa.

“Ko wa ya kulleta kuma?” Ya faɗa a ransa.

“Tabbas a kwai ayar tambaya da…

“Imirana tsamoni dan Allah”Cewar Inna murya a shaƙe.

“Me kika ce ” Ya faɗa dariya na fitowa daga bakinsa irin dariyar ƙetar nan, Wani haushi ne ya turnuƙe Inna dan ita babu yadda za a yi ta fito dan ɗuwawunta daskare yake a jikin zani”

“Ni yau na ga abin mamaki ɓatan nono a ƙirjin budurwa” Cewar Inna cikin shaƙewar murya

Lura da Imran ya yi cewar Inna a daskare take sai ya miƙa hannu zai fiddota, aikuwa ya finciko ta da ƙeta.

“Wayyo mafitar kashina, wayyo Allah na haba Imirana ƙanƙara fa na yi” Cewar Inna cikin shaƙeƙƙiyar murya.

Dariya Imran ya ƙyalƙyale da ita, dan daga yadda ya finciko hannun Inna ya jita a manne da freezer, amma a haka yake ƙoƙarin fiddota amma ta ƙi ɓanɓaruwa.

“Haba Imirana ka kashe firinjin mana mazaunan nan nawa su ɗan saka mana, amma kake janyoni baka ji yadda muka yi tif da taya ni da firinjin ba kamar an manne tangaran da sufagilu” Cewar Inna cikin fuskar tausayi, haka dai ya kashe soket ɗin sai da ta ɗan saka ya taimaka mata ta fito, amma dariya na cinsa, haka ta fara takwa dakyar saboda yadda jikinta duk ya yi tsami ga karkarwa da atishawa da take yi a kai- a kai. Haka ta dudduƙo ta fito daga kicin ɗin tana dudduƙawa, tana ta kwashewa yarinyar nan me ƙunshi albarka, a haka ta fito ta kwa yi ido huɗu da sauran matan nan tsaye cirko-cirko har Ashrof lokacin ita ma ta fito sai maida yanda aka yi suke. Ganin Inna a yanayin da take sai kowa ya zura mata ido. Banda yarinyar da aka riƙewa mamanta, ta daddage sai masifa take a kan an riƙe mata nono a loka har sai da ta yi fitsarin wuya.Ita kuma ɗayar sai bata haƙuri take ta ce ba da niyya ta yi ba amma sai masifa take. Inna na ƙarasowa ta kalli yarinyar a shelaƙe ta ce

“Ni ina dalili kin damu mutane tun ina cikin firinji nake jin kina an damƙe miki nono, wai a nan ina nonon yake? Ba dan fuskarki ba ma babu yadda za a yi a banbance gabanki da bayanki, abu kamar an sawa muciya zani ba gaba ba baya, amma a haka kike cewa an damƙi nono, yo an damƙi nono ko dai an damƙi fata da fatar ma kika ce da daɗi, dan ban ga nono a nan ba wannan ƙirji naki kamar ƙirjin babe”

Back to top button