Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 23

Sponsored Links

Page. 2️⃣3️⃣

 

Yana sanye da suit white color se bakin takalminshi ga agogon diamond adaure ahannun shi yasha bakin son glass fuskan nan ahade kamar hadari bakaramin masifar kyau yayi ba azaad kyakyawane nakarshe bugu da kari half-cast ne duk Wanda yakalleshi baya mishi kallon hausa fulani kallon balarabe akemai saboda yadauko umminsa ne kirar jikine yadauko na Abba sekuma farinsu daya hada shisa yakasance fari sosai dan duk yafi mutanen gidan fari tsabar hutu fatar jikinsa Kamar kataba jini yafito, babban abinda yakesa mata suke rushing akansa kenan gashi dogo me murdadden jiki ga manyan idanu farare tass hancinsa kuwa kamar shiya zana abinsa dogon hanci bakin nan dan karami dashi pink yanada dimple Wanda ko magana yakeyi sesun lotsa gashin kanshi yasha gyara atare yake sosai andan sha gefe da gefe seyayi kamar fonk, kunsan irin gashin turawa da na larabawa base nafada muku ba yanada kwantaccen saje baki Wanda shima yasha gyara daga dan gefen wuyanshi akwai zanen tattoo daya fito waje alaman jikinsa akwai tattoo azaad cikekken namijine wanda ko wace mace zatayi mafarkin samu amatsayin miji( nikuwa ISHAM nace aibanga laifin su nusaiba da aneesa ba dasuka nanike masa kamar magnet) Saukowa sukeyi daga matakalan jirgin cikin takun kasaita , hannun azaad narike da jacket din suit dinshi, tunda suka sauko suka tadda yan jarida sun kewaye ko Ina na airport din ga manyan abokanan kasuwancin su tako Ina, ga sojoji kewaye dagurin domin basu tsaro se fadawa dakuma yan uwansu yan masarautar gombe dasuma yanzu suka iso domin tarbansu cika airport din yayi bako matsaka tsinke, tambayoyi Yan jarida suke ta aika musu dakuma faman daukansu hoto ko takansu basubi ba sukaci gaba da tafiya, kirari fadawan nan suka farayi tare da busa sarewa, karasowa fawwaz da areef sukayi atare suka rungume Abba suna mishi sannu da hanya cikin farin ciki da jindadi Abba yake shafa bayansu yana murmushi kafin suka zame jikinsu suka rungume azaad ko wannen su kagani zakaga farin ciki dauke afuskokinsu amma banda azaad da fuskan nan take kamar kullum, bubude musu murfin motar sukayi suka shiga ajere motocin suke, suka jera akan titi suna tafiya slowly, motocin sojoji ne agaba wanda akalla zasu kai motar 10,se motocin gidan sarkin gombe color su fari Suma akalla zasukai guda 8, se motocin gidan MAINASARA family bakake ne su sunkai goma sha hudu 14, daga tsakiya Kuma motocin abokanan kasuwancin su ne wanda kowa da kalan motar sa se karshe motocin polisawa ne wanda suka taho daga government house se jiniya kawai kakeji yana tashi, duk masu ababen hawa sun faka suna jiran wucewarsu , minti 40 ne yakawosu gida Bude musu motar akayi suka fito atsaye a compound din gidan suka samu su ummi, zeenat,anty Amina da itama dazun tazo da yaranta, mommy , Mansoor, anty Zainab ,anty shayida duk suna tsaye suna jiransu, da gudu zeenat tafada jikin Abba tana murna ” oyoyo yarinyar abbanta ! Yar autan abbanta ” cewan Abba dake rike da zeenat din sakeshi tayi tana kare masa kallo cikin zolaya tace” wow abbana kaga yanda ka Kara kyau da kumatu kuwa Meye sirrin !?” Ta tambayesa tana rike da duka hannayensa biyu dariya jamaan wajan sukayi saboda tabasu da dariya dakuma burgesu yanda suke da mahaifin nasu, lakatan hancinta Abba yayi” uhmmm zee Meye kuwa sirrin daya wuce kwana biyu nahuta da rigimanki Kinga aidole nayi kumatu ” nanma kara tuntsirewa akayi da dariya saboda dama Abba ba bayaba wajan barkwanci wucewa ciki azaad yayi dan baze iya da wannan hiran nasu ba Dan yaga bana karewa bane yana mamakin Abba daya tsaya yake biyewa zeenat, da gudu_gudu Faisal babban yaron azaad yabi bayansa yaron sane na amana kusan shekara 10 suna tare Yana mishi hidima black beauty dashi. Part dinsa direct suka wuce Yana shiga dakinsa ya cire necktie dinsa yayi wurgi dashi.

Acikin gida kuwa tunda zeenat taji abinda Abba yafada tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka dariya tabashi yariko hannunta suka fara tafiya Yana ce mata ” haba yar autata am just kidding you” ahaka harsuka karasa kusa da su ummi dasuke tsaye wani irin kallon love Abba yakebin ummi dashi bakaramin kyau tayi mishi ba seyagama kayan hausawa yafi karbanta itakuwa se murmushi takeyi tana sunnar dakai dan ita kunya yake bata agaban yayanta , mommy kuwa bakin ciki kamar yakasheta fuskan nan adaure. Kiran areef Abba yayi yamishi magana akunne Sannan yawuce part din ummi su ummi sukabi bayanshi , mommy kuwa fuuuuu tawuce part dinsu rai abace, karasawa areef yayi yacema jamaan wajan ” Abba yace in fada muku kujirashi a part dinsa ” yawuce ciki.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & Written by (MRS ISHAM )

 

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

Back to top button