Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 21

Sponsored Links

Suna zuwa falon Imran ya ja tunga ya tsaya yana ƙoƙarin danne dariyar da take son fitowa ba tare da ya shirya ba, dan yadda ya ga Inna ta wani biyo su kamar wanda suka yi wani gagarumin laifi sai wani muzurai take kamar ta yiwa sarki ƙarya. Sadiya ma sai da suka dangana da falon ta fara jin haushin gudun famfalaƙin da suka yi, dan abin na Inna ya wuce misali.

Inna na fitowa falon ta kasa ta tsare riƙe da makamanta, kallonsu kawai take tana jin haushinsu gabaɗaya, dan kawai gani take shegiyar jaraba ce da rashin haƙuri ya sa suke nema su jiƙawa mutane aiki su ɓallo ruwan da tsayar da shi zai yi wahala, amma fa in ji Inna. Imran ƙarasawa kan kujera ya yi ya zauna tare da wani hakimcewa ya tattaro gabaɗaya jarumtarsa ya dake da ita, kamar ma bai san Inna na hasala tana hatare -harare ba kamar wacce aka yiwa ƙwacen kuɗi.

“Ni dai wallahi zuwa birnin nan da zaman gidan nan ya zame mini masifa da bala’i yo Allah na tuba idan ba masifa ba menene wannan a ce tun da na zo ZAMAN WANKAN nan da raina ban huta ba sai bala’i daga wannan sai wancan kullum da kalar wanda nake hantsilawa a ciki” Ta faɗa tana kallon Sadiya da ta sunkuyar da kai ƙasa.

Babu wanda ya tanka ta dan haka bata yi wata-wata ba ta cigaba da magana cikin hasala.

“Banda rashin mutunci a ce ina cikin gidan nan Imirana kake neman haikewa ƴar nan me ɗanyen jego, kenan ma bani da amfani? Ko dan baka san wahalar ɗaukan ciki da nakuda da kuma reno ba, abin da ka sani kawai ka yi fush ɗan ya faɗo duniya, ai ana barin halal dan kunya” Ta faɗa tana jin kamar ta hau Imran da duka.

“Dan Allah Inna ki yi haƙuri babu wanda ya san kin dawo ma gid…

“Rufe min baki algunguma, irinku ne daga an yi arba’in sai a ji kun fara amaye-amayen jaraba, har kin manta uwar wuyar da kika sha a naƙudar ku ne masu biyewa namiji ya ƙara ɗirka muku wani cikin saboda rashin sanin ciwon kai daga namiji ya fara muku daɗin baki sai ku bada kai bori ya hau a barku da wahala yo ciki da goyo ai wahala ne” Inna ta katse Sadiya cikin harzuƙa.

Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba amma a zuciyarta sai ta ce

“Inna ke kika ga bala’i a zuwanki ko kuma mu muke ganin bala’i kala-kala, tun da kika zo wa ya huta jarabar yau da ban, ta gobe da ban, in ban da neman magana da hana rai sakat a ce muna cikin ɗaki ma sai kin bimu ko ke zaki yi rainon cikin” Cewar Sadiya a zuciyarta.

“Kai kuma Imirana na lura inda aka raba kunya ma baka bi ta wajen ba, lokacin da ake raba sanin ta ido kai kana bacci ina tsaye a ɗakin amma ka yi getse-getse riƙe da mace wai kai ɗan duniya ” Ta faɗa tana kafe Imran da ido tamkar za ta sakar masa muciyar a kansa.

“Matarki ce?” Cewar Imran cikin izza ya kuwa make kamar ma bashi ya yi maganar ba.

Sakin baki kawai Inna ta yi galala tana kallon Imran cike da mamakin kalamansa, ta ma rasa bakin magana.

“Na ga dai sadaki na biya ko kyauta aka bani ita, in kuma…

“Lallai in da ranka ka sha kallo, duk mai rai ba ya rasa ganin abin mamaki, Imirana ni kake cewa Halima matata ce, ban da dai ka ga makwancina, to bari in tuna maka idan mantawa ka yi, ni nan Azumi ni na haifi uban Sa’adiyya tun kafin ai ɗaran akay kwanɗi, da kai yaushe ma ka san Halimar yarinyar da ka san ta bayan uwarta ta gama cin fitsarinta da kashinta”

“Bari na je masallaci” Cewar Imran yana kallon Sadiya ya nuna ma kamar bai san Inna da shi take magana ba.

“Au ga mahaukaciya tana magana, shi yasa za ka barni ina ɓaɓatu, ni na ma rasa me ya kaini na baro ɗakina, ina cikin rufin asirina a gidan Malam na kawo kaina nan inda ake cire min zane a kasuwa, ban da dai ka gan ni a gidanka Imirana har ka isa ka yi watsi da maganar da nake ka ce wai masallaci za ka tafi, in ban da dai ka raina ni kuma kana so dai ka fice ka barni wato ga karya tana haushi, yo na ga yanzu ma aka fara kiran sallar ko gama kiran ma ba a yi ba amma wai kai ga sallau shi ne za ka yi riga malam masallaci” Ta faɗa tana share ƴar ƙwallar takaicin da ta sirnano mata.

Shi dai ko kallon inda take bai yi ba ya sa kai ya fice abinsa dan Inna ta fara kai shi bango tun baya son magana amma duk zuwanta ta hore masa baki tana sa shi yawan magana. Jan hanci ta shiga yi tana cigaba da share hawayen, Sadiya dai bata ce komai ba ta nemi wuri ta zauna.

“Halima kina jin wannan kurman mijin naki wai shi ma ya waye ya yi baki, wai har ni yake faɗawa magana son ransa”

“Haba Inna shi fa babba shi yake siya wa kansa mutunci, duk da kuna kakata amma ai dole ki ja girmanki yadda Imran zai ke shayinki amma a ce abin da huruminki ba kina shiga duk yadd…

Salatin da Inna ta ɗauka kamar ta ga gawar da aka yiwa kisan gilla shi ya sanya Sadiya jan bakinta ta yi shiru dan sai da ta faɗi maganar ma ta gane katoɓarar da ta yi dan ta san ko sama da ƙada za su haɗe babu za a yi Inna ta fahimci maganarta.

“Halima yanzu kenan kin zaɓi mijinki kin bar Kakarki wacce ta haifi ubanki, to in banda ma na haifi uban naki ta yaya ke za ki zo duniya amma kin zaɓi mutumin da kika haɗu da shi da haƙwaransa talatin da biyu kin ajiye ni, ni da na haifi ubanki har ke ma kika samu dirowa duniyar”

“Ba baka nake nufi ba Inna ke ɗaukan ƙafarki yake sanyawa ki ga laifin mutum…

“Ɗakko… na ce ɗakko, ɗaukan hannu gareni ba ɗaukan ƙafa ba, in banda kin raina ni Sa’adiyya har ma ke faɗi in faɗa, to shikenan ɗan halak ka fasa tun da Imirana kika zaɓa daga yau ko gani na yi ya haike miki kina neman ɗauki ƙur’anin Allah ba zan kai miki ɗaukin ba, tun dai kin ce namiji ubana ne akwai ranar ƙin dillanci ranar da za ki mutu marainiya, tun da duk wannan jihadin da na yi, ki kalli hannuna na dama taɓarya, na hagu muciya duk dan in ceto ki daga ɓarakar ɗinki da kuma ciki da goyo amma saboda ke ƴar ƙundun uba ce baki gani ba” Ta faɗa tana yin jifa da taɓaryar da muciyar ta koma inda ledar kayan marmarinta ta faɗi ta ɗakko da ta ajiye, ta juya tana cewa.

“Gwara ma in je in yi abin da zai fishshe ni, na tsaya ina gwagwarmaya ba magriba gashi har ana kiran ishsha’i, kar ma in je ina nan ina ta alkinta miki mafitar ɗa (HQ) Mala’ikan ɗaukan rai ya zo, tafiya da ni, a je a binne ni in zo amsa tambayar kabari na rasa bakin magana idan an ce Azumi me yasa baki yi sallar magriba a kan lokaci ba, kin ga bani da bakin magana, sai dai in ta jejjefa ido yo ai dai ba na buɗi baki ba in cewa mala’ikan ina can ina gwawarmaya da ƙartin mazan da suka saceni, sannan na dawo gidan na shiga ƙwatoki a hannun wancan jarababben mijin naki ba”

“Sacewa kuma Inna? Ke da kika tafi gidan Hajiya waye ya saceki kuma gwagwarmayar me kika yi sannan ya ka yi Inna kika kuɓuto?”

Wani mugun kallo Inna ta jefawa Sadiya kamar ta hauta da duka, ta juya ta fice daga ɗakin ta ɗauro alwala. Sai da ta jera sallolinta ta idar sannan ta tashi tiƙis-tiƙis ta fita jimawa kaɗan sai gata da plate da wuƙa da roba me ruwa a ciki, zaunawa ta yi ta ɗakko ledar kayan marmarin take sakawa a robar tana wankewa sai da ta ɗauki iya yanda take so sannan ta buɗe frige ta sanya sauran a ciki ta shiga yankawa tana cin abinta.

Kallonta kawai Sadiya take tana mamaki ko ta yi bata mata ba kuma ta ma rasa ina ta samo wannan uban kayan marmarin tili guda.

“Meye kika tsareni da ido sai kace wata tsohuwar mayyar da ta daɗe bata ci jariri ba?” Inna da ke kallon Sadiya ta wutsiyar ido ta faɗa lokacin da take yanko wata ƙatuwar abarba ta sa a baki.

“Haba Inna wace irin magana ce wannan ni ce ma tsohuwar mayya, to idan ma ni mayyar ce ai ke ce kat”

“Yo na sani ko wajen uwarki kika yi gado” Ta faɗa hankali kwance.

“Ni uwata ciki ɗaya ce, wai dan Allah Inna ina kika samo wannan kayan?”

“Halima kenan a tarar aradu da ka mana na samo su, dan ke baki san irin sadaukarwar da na yi ba na san da Malam zai san na damƙi mazaƙutar maza har uku wallahi duk da larura ce ta sa na yi hakan da har ya bar duniya da kishi zai mutu” Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma ta ce.

“Na faɗa miki saceni aka yi”

“Wai wace irin sata Inna, a sace ki kuma ki dawo har da kaya tili haka”

“Wallahi sace ni aka yi”

 

Back to top button