Ni da Patient Dina Book 2 Page 63
PAGE 6️⃣3️⃣
Batare da yan Nigeria sun san da zuwan nasu ba karfe shida nayi suka wuce airport jirginsu yatashi zuwa gida Nigeria, karfe hudu na asuba jirginsu yayi landing a gombe lawanti international airport, taxi suka shiga zuwa gida tunda suka taho a cikin jirgin babu wanda Mr azaad yayiwa magana acikin su har suka shiga taxi zuwa gida se hiransu sukeyi uffan be ce musu ba daga karshema surutun nasu ma ya fara damunshi yaja dogon tsaki suna jin haka sukayi shuru da bakinsu .
*Horn me taxi yayi , fitowa baba me gadi yayi dan ganin su waye , ganin Mr azaad ne dasu Fawwaz yasa ya wangale musu gate yaname murnan ganin Mr azaad*
Fitowa yayi yabarsu suna sallamar me taxi , shigowa cikin part din yayi jin motsi a kitchen yasashi ya tsaya daga bakin kofa ya ce ” ƴata na wajen waye ?” Dasauri abu ta juyo jin muryan da batayi zato ba , cikin farin ciki ta washe baƙi ” yallabai Azaad kaine alhamdulillah sannu da hanya , tunkwal na wajan ummi” yar harara ya watsa mata jin yanda takira sunan twinkle da tunkwal barin kitchen din yayi ya shige part din ummi dake bathroom taje dauro alwala zatayi nafila. Hawa kan gadon yayi yadauki twinkle dake baccinta peacefully yana kallon fuskanta da bashida maraba dana fanan yanajin tsananin kaunar twinkle aranshi ,ahankali yafurta ” sleeping beauty” ya mannata ajikinshi tashi yayi dauke da ita ahannunshi yafice a bedroom din ummi ya nufi nashi bedroom din, kwantar da ita yayi akan makeken gadonshi yasake rufeta da blanket sannan ya shiga toilet yayi wanka da alwala yazo yafara nafilfilu yana addu’a Allah ya kare mishi fanan yakuma sa tadawo rayuwarsu be tashi na har seda aka kira asuba yayi Sallah sannan yahau gadon yashiga blanket din yajawo jaririyar shi kusa da shi yana kallon fuskanta,ahaka bacci yayi awon gaba da shi .
Fitowar ummi daga toilet tadauro alwala kenan ta kalli kan gadonta fuskantar dauke da murmushi, gabanta ne yafadi lokacin dataga babu twinkle akai dasauri ta karasa izuwa gadon kamar wasa bataga twinkle ba hankalinta yayi matuƙar tashi ba shiri ta fice a part dinta saukowa downstairs tayi taga abu , abirkice ta ce ” abu dan Allah akwai wanda kika gani yashiga part dina ne?” Murmushi abu tayi ta ce ” eh ummi! Yallabai Azaad ne yashiga kuma naga fitowar shi da tunkwal a hannu ” shuru ummi tayi jin abu ta ambaci sunan Mr azaad tunani tafara yaushe suka dawo to kenan hakan na nufin yasamu lafiya murna ne yakamata da sauri_sauri ta nufi part din nashi, bedroom tasamesu suna bacci zama tayi akan gadon tana shafa kanshi tanajin matsanancin farin ciki yana ratsata , ahankali yafurta ” ummiii” batare da yabude idanunsa ba , ” na’am son , fatan kundawo lafiya ?” tashi yayi yazauna ya ce ” uhmmm” tundaga jin amsar daya bata ummi tasan he has changed completely ganin gaba daya fuskar shi ba walwala, riko hannunshi tayi ta ce ” son kaga our little feena ko , babu abinda yarabasu da my feena, aduk sanda na kalli fuskar ta inaga ganin my feena atattare da ita, son yakamata yanzu kayi move on ko dan amanar twinkle da feena tabaka kazama uba na kwarai inkana cikin wannan yanayin taya ne zaka kula da twinkle? Hakuri shine Yakamata muyi ,mudauki dangana da juriyar rashin feena nasan is not easy for you my son, but you have to for the seak of twinkle ka ji ” gyada mata kai yayi kawai batare da ya iya cewa komai ba yaname kwantar da kanshi akan kafadarta slowly ya ce” thanks ummi ” ummi ta ce ” son yaune sunan twinkle wani suna Yakamata asa mata ” ajiyar zuciya Mr azaad yayi ya ce ” Fatima za’a samata sunan wifey tun ranar da aka haifeta nayi mata huduba da Fatima ” murmushi kawai ummi tayi tanajin dadi aranta a part din tayi Sallah. Karfe 7:00am aka raɗawa twinkle suna da sunan mahaifiyarta fanan, kafin gari yagama wayewa duk family kowa yasan Mr azaad yadawo cikin koshin lafiya , anty shayida tazo da yaranta yan biyu mata ta haihu satin da yawuce sukayi arba’in sunansu adeema da adeena ,haka anty zainab tazo tare da yaronta daya dawo daga egypt ya kammala karatu , yan uwa duk anzo suna su hairah da auta da amira tun karfe 8 suka zo gidan , haka mahaifiyar yaseer ma tazo , shigowa gidan baba da Abba sukayi suna part din Abba da wasu abokan abba suna hira Mr azaad yashigo da twinkle ahannunshi tana sanye da kayan jarirai me matukar tsada , zama yayi akan kujera rike da ita ya gaidasu suka amsa fuska asake Abba ne ya ce ” to kabamu ita mu ganta mana” kamar baze bada twinkle din ba se kuma ya miƙawa baba ita , murmushi baba yayi yace ” Fatima na biyu kenan , Allahu Akbar Fatima ta tafi Fatima ta dawo Allah yarayaki ya albarkaci rayuwarki” haka baba yadinga mata addu’a sannan yamikawa Abba ita shima karbanta yayi yana yi mata addu’a, yana zaune yana jiran su gama su bashi yarshi yayi tafiyarsa , karbanta yayi a hannun Abba . yafice abinshi ya nufi part dinshi afalo ya tsaya yana kallon katon hoton enlargement din hotonshi shi da fanan fuskantar dauke da ƙayitatciyar murmushi ta riƙe hannunshi tana kallon fuskanshi , shikuma yazagayo da hannunshi yana rike da kugunta fuskanshi asake dayan hannun kuma yakama kumatunta . Murmushi yayi lokacin daya tuna sanda akayi hoton , ranar da suka dawo daga shopping ne suka tsaya a garden suna hiransu gwanin sha’awa tashi sukayi zasu tafi yajawota jikinshi yayi yadaura hannunshi akan waist dinta dayan kuma kuma yariƙe kumatunta itakuma tana sakar mishi tsadadden murmushinta dake kara mata kyau , suna ahaka basu sani ba Fawwaz dabesan suna cikin garden din ba yashigo burgeshi sukayi sosai yasa yafito da wayarshi yafara daukansu hotuna,yayi musu hoto yafi guda goma ankara dashi Mr azaad yayi yagalla mishi harara ganin inda yake kallo ne yasa fanan juyawa tana ganin Fawwaz ne awajen dasauri taraba jikinta da na Mr azaad cike da jin kunya tabar garden din da gudu, da karfi Fawwaz ya ce ” haba antynmu kiyi hakuri kidawo bari in baku guri ” damkar kunnenshi Mr azaad yayi ya ce ” wato labe kakeyi mana nida matata ko ? ” Kara Fawwaz yasa yana ” sorry Babban ya’ya wallahi kun burgeni ne yasa nake muku hoto” hararanshi Mr azaad yayi ya ce ” kafin awa daya kazo min da enlargement din hoton in kuma beyi kyau ba zakayi bayani ” yasakeshi yabi bayan fanan. Dariya fawwaz yayi ya ce ” salon soyayyar ku na daban ne ya azaad da anty fanan Allah yabarku tare ” ya ida maganar yaciro waya yakira layin wani photographer yatura mishi hotunan ya ce yanaso ya mishi katon enlargement nan da anjuma akawo. Haka yazauna a garden har aka kawo enlargement din da akayi rapping dinshi shiga part din Mr azaad sukayi da shi basa falo suna cikin bedroom dinshi , manna enlargement din akayi ajikin bangon falo yazauna sosai yanda suka fito sukayi kyau ajikin hoton Kamar a kirasu su amsa. Fitowa Mr azaad yayi yaga harsun manna enlargement din ya ce ” Allah yataimake ka ” murmushi Fawwaz yayi suka fita shida wanda yakawo hoton , jin sunfice ne yasa ta fito ” habiby kazo ka nunamin wanne zansa” tayi maganar batare da ta lura da enlargement din jikin bangon ba , nuna mata yayi da hannu zaro manyan fararen idonta waje tayi sosai ta rufe baƙinta ta karaso gaban hoton tasa hannu ta shafa ta ce ” yaushe akayi wannan hoton , wallahi yayi matukar kyau sosai” tafada tana rungumeshi.
Murmushi yayi bayan ya gama tunawa yasa hannu yashafa hoton dede fuskar ta ya ce ” i missed you so much baby rayuwa yamin zafi sosai da babuke aciki, ki kalli our little twinkle , na miki takwara sunanta Fatima ina fatan itama tazama jajirtacciya irinki me kyawawan halaye. Bazan taba cire rai da dawuwar ki ba ina nan ina zaman jiranki ”
Kuka twinkle tafarayi jijjigata yayi yana murmushi ya ce” karfa kidauko min rigimar mommynki ” kamar tasan me yafada tayi shuru yana tsaye agaban hotonsu zeenat tashigo kallo daya tayiwa hoton bata sake kallo ba saboda tasan intaci gaba da kallo tasan yanzu zata fara kuka ɗan ji takeyi tafi kowa missing din fanan ” ya azaad ummi ta ce kabada twinkle ” ya ce” kifice ki bani waje bazan bada ita din ba” da sauri tafita mishi a part din shi tsaki yaja yashiga bedroom yazauna abakin gado har time din yana rike da ita, fadawa ummi yanda sukayi da Mr azaad zeenat tayi,ummi dama tasan zaarina mikewa tayi dakanta ta tafi part din nashi tace yabata twinkle be mu sa ba ya mika mata ita takoma falo tabawa umma rahina da sukazo da mama, mama ta dade bata shiga farin ciki irin na yau ba jitakeyi kamar tana rike da fanan ne , haka akayi suna nagani nafada baby twinkle tasamu kyaututtuka me tarin yawa ,an yanka manyan shanaye guda biyar da raguna anyi sadaka dasu komai anyi awadace karfe hudu na yamma aka watse kowa ya koma gidajensu, dare yayi yagama komai yazo ze kwanta zasuyi bacci twinkle tafara kuka rarrashin duniya yayi mata amma takiyin shuru daukarta yayi yanufi part din ummi tunkafin ya karaso ummi tajiyo kukan twinkle dama abinda take jira kenan saboda bataci abincin dare ba haɗa mata madaranta tayi a feda yana shigowa ta ce ” dama nasan zaku dawo ai ta fada tana karban ta tafara bata madaran shuru tayi tanasha , gama sha tayi yakarbeta sannan yasa hannu ya kwashi kayan madaran nata ummi de binshi da ido tayi harya fice .
Tunda twinkle tayi arba’in yafara fita da ita duk inda zashi yana rike da ita ummi da Abba sunyi mishi magana harsun gaji akan yadena fita da twinkle amma hakan be hanashi daukar yarshi ba duk inda zashi a gida ma sosai twinkle take samun kulawa kullum tana tare da ummi ko Abba ko suhaima da sauran yan gidan haka zeenat da yaseer suma suke zuwa gida akai_akai ɗan ganin twinkle haka su ya usman ma suna zuwa , haka duk sanda Mr azaad yatashi daga office yana biyawa gida da twinkle yakaiwa su mama ziyara .
irin kulawar da take samu awajen familyn ta guda biyu na musamman ne takara girma kowa sonta yakeyi duk abinda suka gani na jarirai zasu siya mata shi musamman me gayya me aiki daddynta duk sati se yayi mata shopping din lafiyayyun kayan madaranta da kayan sawa daduk wani abinda yaro yake bukata ga dakin da aka ware mata anzuba mata kayayyakin wasa aciki , sau daya twinkle takesa kaya bata sake maimaitawa duk kayan data saka baa kara samata shi komai nata special ne kuma masu mugun tsada ,hatta kayan da zatasaka komai dinta. gata iya gata twinkle na ganinshi .
Sosai ummi tayiwa Mr azaad fada kafin nan suka samu yadena fita tare da twinkle, tana da wayo sosai gashi bata da ƙiwiya saboda kowa tasan fuskarsu musamman yanzu da tafara zama daga zaran taga daddynta yadawo zata fara bude baki tana dariya hade da miko hannu yadauketa haka zedauketa yana dariya haka take tabasu nishadi agidan , safiyar yau zeenat ta tashi da naƙuda aka kaita asibiti ta haifi namiji kyakkyawa me kama da babanshi yaseer, seda suka dawo gida tukun suka kira family suka sanar dasu aikuwa sunyi farin ciki da jin labarin haka sukaje yi mata barka , bayan sati daya akayi suna aka yiwa baban yaseer takwara yakubu suka mishi inkiya da ashraff.
bayan ta haihu da sati biyu hairah ta haihu amma bata iya haihuwa da kanta ba seda aka mata operation ta haifi ya mace taci sunan mama wato sumayya akayi mata inkiya da samha gida aka dawo da hairah saboda kulawa da ita kuma mama na iya kokarinta wajen kulawa da ita yanda Yakamata su ya usman anzama baba , Amira ce take ta ja da nata tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe , suhaima haryanzu shuru kuma daga ita har Fawwaz din hakan be damesu ba .
Duk sanda Mr azaad yatafi da twinkle Company ma’aikata sun dinga yi mata wasa kenan saboda tana da farin jini ga rashin ƙiwiya , duk da Mr azaad baya basu ita saboda be yarda da kowa ba se Faisal, shi kadai ne duk sanda Mr azaad yazo da ita suke tare dama tun faɗan da ummi tayi mishi akan fita da ita yadena se de duk ranar Friday yana fita da ita .
Amira ma ta haihu ta haifi na miji anyiwa baba takwara suna ce mishi musin duk anje suna Bauchi bayan angama suna kuma suka dawo .
haka rayuwa yaci gaba da tafiya abubuwa nata faruwa aciki me dadi da akasin haka Mr azaad de yana bawa twinkle datayi wayo sosai kulawa shida yan gidan suna nuna mata gata , areef yafara zuwa aiki a kamfanin Abba , hafiz kuma ya zana papper anfara nema mishi addimission a gombe state University , kuma yasamu yafara zuwa.
Allah yayiwa Alh Ibrahim tijjani rasuwa kuma yayi ta tonawa kanshi asiri daga karshe ya haukace sannan ya mutu , ga aneesa da ciwo yafara cin jikinta tadawo gida ta nutsu duk irin rashin kunya da wulakancin data dingayiwa mahaifiyarta Hajiya Zainab daga karshe ita ce, take kula da ita saboda uwa ce ita bazata iya kauda kai akan yarta ba dukda kuwa abubuwan datayi mata haka taci gaba da kulawa da ita sukaje asibiti aka daurata akan magani , alhamdulillah maganin yanadanyi mata aiki amma ba sosai ba saboda HIV yarigada yayi tsanani ajikinta yafara kashe duk wani garkuwar jikinta.
Abangaren nusaiba da lukman suma suna nan suna rayuwar farin ciki da yaronsu namiji da ta haifa wata biyu dasuka wuce .
__________________________________________
NASMINAYA.
” Sarauniya kar muce zamu biyewa zuciya, kar ayi wannan yakin yanzu koda kuwa za’ayi muma mu rama irin abinda sukayi mana mu farmakesu a lokacin da basu sani ba nan ne zamu iyacin galaba akansu amma wannan sakon dasuka turo yanuna kancewa sun rigada sun shiryawa yakin kafin suka turo mana da saƙo” cewar wazirin nasminaya .daka mishi razanannen tsawa sarauniya tayi, a harzuke ta ce ” yanda suka bukaci ayi wannan yakin dole za’ayi shi mudin ba matsorata bane , ai wannan nuna tsorone bamu cika ainihin jarumai ba inhar de bamu taresu gaba da gaba ba dole ne ayi kare jini biri jini , amma maganar kai musu hari batare da sun sani ba duk shirme ne “tafada tana kallon fuskokin ko wannensu kafin taci gaba da fadin ” muma zamu nuna musu mudin masu nasara ne , hankalina baze taba kwanciya ba senaga bayan wa’yannan azzaluman dan haka kufara shirin yaƙi, sannan ku maida musu da saƙon cewa na amince da wannan gwabzawar da za’ayi , abashiyya ke kuma kitafi masarautar kusfah ki fadawa sarki habar muna bukatar dakaru saboda yaƙin dazamuyi . Dole wannan ƙaron ayi dayan biyu ko mu ko su ” gimbiya afroza ce ta ce ” yake sarauniyata tabbas iname goyon bayanki dari bisa dari amma muna bukatar dakaru masu matukar yawa, saboda wa’yanda zamu fuskanta kungiyoyi biyu ne kuma shu’umai ne marasa tsoron Allah ” yarima ahil yace ” nayarda da Maganar ki gimbiya amma fa kisani, masarautar nasminaya yafi karfin duk wasu kungiyoyi munada karfi dakuma kwarjini , kar ɗan sun kasance kungiya biyu ne su daga mana hankali da yardar Ubangiji munfi karfinsu” murmushi sarauniya tayi wanda tunda tazo masarautar ba ta tabayi ba ta ce ” wannan gaskiya ne yarima ahil ” suna cikin wannan tattaunawa wani tsohon dattijo yashigo fa da hannunshi rike da wasu abubuwa masu tsayi yarufesu da farin tufafi , dakatar da shi fadawa sukayi suka hanashi shiga yayi yayi subarshi domin yanada magana da sarauniya amma suka hanashi da karfi yayi magana ” yake shugaba me adalci zasu kibawa wannan bawan naki daman yin muhimmiyar magana dake dan Allah dan Annabi” daga musu hannu sarauniya tayi suka barshi yashigo nuna mishi wajan zama jakadiya tayi , yazauna ya ce ” shugabata zanso abamu waje” kallon su tayi suka ɓace yarage daga ita se gimbiya afroza da yarima ahil se jakadiya, galadima abdud Shakur,se waziri iya sune sukayi saura a fa da. Sarauniya ta ce ” dattijo zanso kafadamin dalilin dayasa kakeson yin magana dani” mikewa dattijon yayi ya ajiye abun hannun nashi akasa yabude tufafin da ya rufe su dashi nan take wukake guda biyu suka bayyana, wukane da akayi domin yaƙi anyi shine da baƙin narƙekken dalma se yalki da daukar ido sukeyi, duk kallonshi sukeyi suna jiran ƙarin bayani daga wajan shi .
” Ya shugabana wannan wukar ni na hadashi da hannuna domin bada nawa gudunmawan , a iya karfafa bincike na danayi shubumbum da tanzarzar zallar wuka babu abinda zeyi musu , shisa naje har birnin sin wajan uban gidana shine yafadamin abinda ze kashesu , bayan nadawo ne nahada wa’yannan makaman domin baki su nasan ze taimaka dan Allah shugabata ki karbi nawa gudunmawan ” yafada yana zubewa akan guiwansa jinjina kai sarauniya tayi itada su jakadiya ta ce” na karbi wannan kyautar taka amma kafadamin amfaninsa me kyau , saura mara kyau din ” zama yayi ya ce” shugaba ko min yaya kar ki bari wannan wukar ya yankeki domin yanda zeyi miki illa haka suma zeyi musu illa ” murmushi tayi ta ce” Masha Allah ” galadima abdud Shakur ya ce” tabbas sarauniya da yan fa da sunyi matukar godiya da kuma jinjinawa wannan gudunmawan naka ” sosai dattijon yayi murna yayi musu sallama yatafi.
Sarki habar yaturo musu da dakaru masu matukar yawan gaske haka masarautar nasminaya sungama shirya duk dakarun su domin fita yaƙi, masu kai saƙo wa kungiyar SATANIC da BAPHOMET duk sunje sunkai.
Fitowa sarauniya tayi cikin azabebben shiga na yaƙi ga khairaty na hannun daman ta dakuma dakaru mata dasuke biye da ita, haka gimbiya afroza tafito itama cikin shigar yaki da yarima ahil ga shufan da shufaina yaran jakadiya da ita kanta jakadiyar duk sunyi shiga cikin kayan yaƙi. tsofaffi dakuma yara na masarautar sunatayi musu adduo’in samun nasara dakuma dawuwa lafiya .
Hawa kan dawakai sukayi suka fara firewa akan dokunansu har suka dira a babban filin dazaa gabatar da yaƙin .
Tanzarzar yazo da mugayen aljanun dakarun shi haka shima shubumbum yazo da nashi dakarun masu yawan gaske , yaƙi aka fara yi baji ba gani kowa burinsa yaga yayi nasara yakashe makiyinshi , anyi kashe_kashen da bazasu san adadin su ba , inka duba bangaren sarauniya kisa kawai takeyi idonta yarufe burinta kawai takawo bayan wa’yannan azzaluman dasuka addafi ƙasa, jikinta duk yayi gaja_gaja da jini duk wanda ya shiga hannunta kisan wulakanci takeyi musu ga drygon dinta dake feso musu aman wuta , haka abangaren gimbiya afroza itama kisa takeyi bana wasa ba , harta khairaty ba’a barta abaya ba duk da ankashe musu mutane dayawan gaske amma hakan besa sun sare ba acikin faɗane aka kashe yaron jakadiya abashiyya wato shufan, sannan ankashe galadima abdud Shakur sauran kuma anji musu mugun raunin da bazasu iyayin yaƙi ba duk sun jigata musamman abashiyya da khairaty sunji rauni sosai, sarauniya ganin haka ne yasa ta kara kaimi , isowa gabanta tanzarzar yayi yana fadin ” sarauniya karkiyi zaton keda mutanen ki zaku bar nan araye , kiduba munci galaba akanku , dake da jaaazana duk nawane hhhhhhhhhhh” yakarasa maganar nashi yana muguwar dariya ,dirowa shubumbum yayi gabansu ya ce ” karya kuke yi nine kadai zan mallaki jaaazana dan haka inkun isa mu gwabza mugani ” yafada yana zaro sharɓebiyar wuka, duk su biyun sun mata kewaye ga ta yar karama agaban su , gwabzawa suka farayi suna kaiwa junansu hari cikin zafin nama sarauniya tafito da wa’yannan wukaken da aka bata , tayi wani irin tsalle da seda tayi sama tana ihu me karfin sannan tadawo ƙasa tana caka musu dukkansu biyu lokaci daya nan take shubumbum yazube awajan babu rai duk wasu mutanen shi nan suka fara marmashewa izuwa toka suna mutuwa , karfin hali tanzarzar yayi yazaro wukar acikinshi kafin sarauniya ta ankara ya caka mata acikin ta ya ce ” dole sede dukkanmu mu mutu , tunda kikayi nasarar ka war dani abangon duniya dole kema ki mutu ” yana karishe maganarsa yazube ƙasa jikinshi yakama da wuta ya marmashe yazama toka yabi iska , haka duk wasu mutanen shi haka suka dinga marmashewa suna komawa toka duk seda suka mutu yayi saura iya yan masarautar nasminaya kadai afilin dagan , ganin halin da sarauniyarsu take cikine yasa yarima ahil da gimbiya afroza da sauran dakaru suka nufota da gudu kamin su iso tafadi aƙasa babu rai atattare da ita zare mata wukar cikinta yarima ahil yayi kafin yadauketa yasabata a kafadarshi suka ɓace , duk wa’yanda suka jigata suma ɓacewa sukayi zuwa masarauta , duk wanda suka gansu sunsan cewa sunyi matukar shan gwagwarmaya a yaƙin da akayi suna shigowa aka fara buga kararrawar nasara nan take kuma lokaci daya masarautar nasminaya ta tashi da labarai guda biyu daya na farin ciki daya na bakin ciki, wato na kashe musu mutane da akayi gakuma sarauniyarsu da aka dawo da ita itama babu rai sekuma na nasarar dasuka samu .
AFTER THREE YEARS ( bayan shekara uku)
Misalin ƙarfe 6:30am na safiya
_____ ” twinkle ki tsaya kidena wannan gudun zaki fadi Please kitsaya ” suhaima ce tayi maganar dake bin twinkle abaya itakuma tana gudu tana dariya , ashe ba iya suhaima ce take binta ba harda Fawwaz da Hafiz duk iya yinsu sunkasa samun nasarar kamata dan taki tsayawa gudu kawai takeyi , karasawa tsakiyar falon nayi dan nide sunan twinkle kadai naji suna kira amma ban gantaba seda nadawo cikin falon sannan nasamu ganin ta , yarinya ce yar kimanin shekara uku fara tas kamar baturiya yar duma_duma da ita jikinta tsabar yanda hutu yazauna ajikinta ko alamar ƙashi babu tana sanye da kayan baccin pjmas orange color kafarta sanye da takalmi slippers irin nasu na yara gashin kanta brown color ne an raba mata shi gida biyu an yi fakin dinsu idonta brown color fuskanta na dauke da manyan ido ga dogon hancinta tanada zara_zara eyelash , dan mitsintsilin baƙinta nadauke da red libs , babu inda twinkle tabaro fanan akama kamar fanan sanda take karama sede ita fanan gashinta baƙi ne sannan idonta ba brown bane , juyowa tayi tanayi musu gwalo da muryanta irin na yara ta ce ” you can’t catch me bazaku iyabaaaaa” tafada tana jan maganar kokarin cafke ta Fawwaz yayi ta zille ta bugi Center table dake dauke da glass flower nan take kwalbar flowers din yafado ƙasa ya fashe ganin tayi ɓarna ne yasa tazaro idanunta waje tasa hannu ta rufe baƙinta aikuwa da gudu tashige cikin kitchen tasamu abu na shirya mata breakfast dinta abu tana ganin shigowarta ta ce ” tunkwal bazakije school yau bane ?” Cike da iyayi tarike kugu harda gyara tsayuwa kamar wata babbar mace ta ce ” well anty Abu kinsan next week is my birthday so teachers dinmu sunbani hutun wata biyar ” sa ke baƙi Abu tayi tana kallon twinkle jin abinda ta fada tana kokarin yin magana Hafiz yashigo yana haki ya ce ” haba my baby twinkle kiyi hakuri ki tsaya kinga time fa na tafiya zakiyi letting a school” make mishi kafada tayi ta ce ” am not going anywhere se bayan birthday party dina” dafe goshi Hafiz yayi sannan yayi kokarin kamota garin guduwa ta tunkude bowl din dake dauke da sauran fulawar da aka mata sandwich dashi yazube aƙasa sannan bowl dinma yafashe , tafi ce da gudu haka suka dinga wasan tsere_tsere da twinkle amma sun gagara kamata.
Bacci yakeyi akan makeken gadonshi jin ƙarar fashewar glass dakuma hayaniya yasa shi gane da waye ake rikici bude sexy eyes dinshi yayi yazauna ya ce ” my sturbon baby twinkle ta tashi kenan , wifey your daughter is very stubborn as you , kidawo kiganta yanda ta girma ga surutu kamar wata yar shekara biyar ” yasan yanzu duk rigimar da akeyi da ita be wuce akan zuwa school ba , dan kusan kullum haka ake fama da ita akan maganar makaranta duk da batafi wata uku da akasata ba tana nursery one ,amma kwata_kwata twinkle batason zuwa makaranta tafiso tazauna agida tayi ta wasa da kannenta minal yarinyar suhaima se yaron zeenat ashraff da yake gidan wajan ummi . Tashi yayi fuskanshi ahade yasauko downstairs sanye da jallabiya hango twinkle yayi zaune akan kujera sukuma masu bin nata sunyi saronda suna zaune akan kujeran suna maida numfashi, tana ganin shi ta tashi da gudu tana ” daddy ! daddy” daukanta yayi sama yanayi mata cakulkuli tana dariya juyawa yayi da ita zuwa part dinsu suna shiga ya ce ” meyasa twinkle din daddy tafiye rigima ne? ” cuno baƙi tayi ta ce ” sorry daddy” toilet yashiga da ita yayi mata wanka yashafa mata lotion dinta sannan ya gyara mata gashinta yashiryata cikin uniform dinta ya sa mata sandal sannan yadauki school bag dinta ya ce ” wow twinkle din mom and dad, yanzu se muje kiyi breakfast” ta ce ” okay daddy ” fitowa sukayi falo yana rike da hannunta tayi kyau gwanin sha’awa tsayawa sukayi agaban hoton fanan yaɗago ta sama kan kafadarshi ya ce ” oya talk to mommy before leaving ” hoton fanan ta mannawa kiss dede kumatunta da muryanta da maganarta be gama ƙwari ba ta ce” good morning mommy , i missed you , nida daddy muna jiranki bye zantafi school wish me all the best ” ta fada tana kara mannawa hoton kiss murmushi kawai Mr azaad yakeyi , shima kiss din ya mannawa hoton sannan ya ce ” wifey Ina matukar kewarki sosai ban cire rai da zaki dawo gareni ba muna jiranki nida little fanan ” twinkle dake dauke akan kafadarshi da karfi ta ce ” yessssssss daddy mommy takusa dawuwa daga tafiya , daddy kafada mata birthday party dina next week ne ?” Barin falon sukayi suka sauko upstairs nan ne ya bata amsa ” twinkle shiiii surutunki is too much darling, mommynki tasan birthday dinki yazo , ta ce bazata samu zuwa ba se next month” Jin abinda yafada ne yasa ta ɓare ba’ki zatayi kuka jin wai mommynta bazata zo birthday party dinta ba , ummi da tasauko downstairs ne taji maganar dasukeyi yasa ta girgiza kai ta ce ” my twinkle waye yafada miki mommynki bazata zo ba , zatazo kinji don’t cry kinji kishiyata” da gudu taje ta rungume ummi tana dariya ta ce ” Yes i know mommy na zatazo kuma sannan bazan yanka cake ba harse tazo zamu yanka tare ” murmushin yaƙe ummi kawai tayi dan tafadawa twinkle hakane ɗan ta kwantar mata da hankali daukanta ummi tayi suka zauna akan kujera ta kira Abu takawo mata breakfast din twinkle anan tayi feeding dinta sandwich dinta da tea ga lunchbox dinta da aka shirya mata ɗan ita bata cin abinci makarantar da ake bawa student shisa akeyi mata nata kullum inzata tafi , tagama ummi tagoge mata bakinta da tissue, ta ce” grandma Ina my grandpa ?” dariya ummi tayi ta ce” grandpa yayi tafiya amma zedawo before birthday dinki ” suhaima ce tafito hannunta rike da minal ta ce ” ummi yau kinsan irin exercise din data samu sekinji tausayinmu , gashi yarinya nan narasa ya akayi ta iya gudu kamar wata yar tsere” tazauna tana magana hade da murmushi tana kallon twinkle dake kan cinyar ummi ga Mr azaad agefensu, dariya ummi tayi dan tanajinsu ta ce ” to bagashi yanzu tasaku kunyi exercise ba ” dariya ummi da suhaima sukayi gaishe da Mr azaad suhaima tayi ya amsa da ” lafiya ” daukanta yayi ya ce ” muntafi ” harsuka fita tanayi musu bye-bye suma sunayi mata fuskokinsu dauke da murmushi.
Dropping dinta yayi a school har cikin class dinsu yakaita sannan ya koma gida yakoma bacci .
Karfe 11:30 Faisal yakirashi yasanar dashi ankawo order furniture na company da sukayi a London” okay ” kawai yace yakashe wayarsa yatashi yayi wanka yashirya cikin suit yafita zuwa Company dan ganin kayan da aka kawo.
Ya Usman da hairah suna zaune afalon gidansu ga yarinyarsu samha tana wasanta akan keken yara ya usman ya kalli hairah ya ce ” honey ki kalli samha da kyau ” juyawa hairah tayi ta kalli samha din bataga komai ba ta ce ” meye ajikin samha din ya usman?” ganin bata fahimci abinda yake nufi bane ya ce ” bakomai kawai de naga Yakamata ace tasamu kanwa ko kanine yanzu fa two years take ” lokaci daya hairah ta ɓata rai wanda shima seda ya fahimci haka ta ce ” ya usman Ni fa daga kan samha bazan sake haihu ba saboda azaban danasha a haihuwar ta kaɗai ya isheni” calmly ya usman ya ce ” Yes Honey nasani amma ko da daya ne semu sake haihuwa planning din ya isa haka in yaso kika kara daya se abar haihuwar haka kinji Please” ” ah ah ya usman bakasan wahalar danasha ba ni kadai nasha wahala ta ɗan haka nide gaskiya bazan iya haihuwa ba shine kawai ” tafada tana haɗe fuska , ran ya usman yayi matuƙar ɓaci ganin yana lallabata amma tana tuɓurewa sekace akanta aka fara haihuwa mata nawane suka sha bakar wahala wajan haihuwa bayan sun haihu din kuma suka sake dauka wasu cikin amma ita tace daga yarinya daya bazata sake haihuwa ba rai abace ya ce” hairah planning ko kinaso ko bakyaso se an tsayar dashi saboda ni inason yara inke bakyaso nagama magana ta ” zuciya da shedan suna zuga hairah gakuma tarin yarinta ta ce” to kuwa sede kanemi wacce zata haifa maka yara amma nikam nagama ” girgiza kai yayi ya ce” haka kikace ko? Shi kenan karki damu basekince innema ba zannemo kuma zan aurota zata haifa min adadin yaran danakeso ” yana gama fadin haka yadauka car key dinshi yafita yabar mata gidan , kuka tafashe dashi jin wai ze sake aure kukanta tasha ma’ishi sannan ta wanke fuskanta tazo tadau samha suka shiga daki .
” Ya yaseer Please inason zuwa gida kusan kwana na uku banga twinkle ba kuma nayi missing su ummi” dariya yaseer yayi ya ce ” beb yanda kikace haka za’ayi anjuma da dare zamuje ! nagama ko tambayar ashraff bakyayi ko shi bakiyi missing dishi bane? ” gyara kwanciyarta tayi ajikinshi ta ce” to ai nayi missing din shi shima in mukaje yau aiduk zan gansu ” ya ce” okay,mubina tayi bacci ne?” Ya tambayeta karamar yarsu kanwar ashraff da take da shekara daya ta bashi amsa da” tayi bacci fah tun dazun ” ” bari inje office” mikewa sukayi atare tarakashi ya hau motar yafita.
Yau auta bataje makaranta ba wai kanta na ciwo suna zaune suna hira da mama , areef da yatashi a office ne yabiyo gidan , yayi sallama mama ta amsa mishi ya shigo gaisheta yayi yazauna kallonshi auta tayi ta ce ” ya areef ina wuni ?” shima kallonta yayi kafin ya ce ” lafiya lau auta ya akayi yau bakije makaranta ba?” rike kanta tayi da hannu ta ce ” yau da ciwon kai natashi se inji kaina yanason faɗowa ” mama ta ce ” ko kuma yau bakiyi niyar zuwa ba kawai ” dariya areef yayi ɗan yasan bawani ciwon kai din da auta takeyi tafadi hakane ɗan kartaje makaranta ya ce ” wai gaskiya ciwon kai be kyautaba sannu kinji ” narai_narai tayi da ido ta ce ” yawwa ya areef! Ina twinkle sarkin rigima da iyayi ” yanda tayi maganar yayi matukar basu dariya mama kam girgiza kai tayi kawai ɗan ita tafi yarda da duk wani hali irin na auta shi twinkle ta gaɗo ga iyayi ga manyance da surutu , ga shi twinkle din tayi saurin magana Shisa insuka haɗu ga auta ga twinkle sede kawai tazuba musu ido , tsagaitawa da dariya areef yayi yace ” mama kiji min ikon Allah wai kura ne zecewa kare maye , ke yanzu auta dan Allah har zakicewa wani yanada surutu da iyayi ?” ɓata fuska auta tayi ta ce” ya areef banaso kaga kai kullum seka tsokaneni, nide nasan banida surutu ” sa ke tuntsirewa da dariya areef yayi ya ce” eh hakane kam bakida surutu mamar twinkle, birthday din twinkle ranar Friday ne zanje indauki aslam da kawarki Islam se inzo indauke ki daga nan se mu biya mu dauki samha da kuma yan biyun anty shayida adeema da adeena ” yar dariya mama tayi ta ce” lallai sannunka da kokari areef” dariya shima yayi daga kai sama auta tayi tana yar tunani ta ce” oh my god ! inata nazarin gift din da zanbawa my twinkle as a birthday gift ” mama kam mikewa tayi dan iyayin auta ya isheta dama bacci takeji ta shige dakinta tabarsu a falo se surutu take zubawa areef shikuma ya tsaya biye mata yanacin dariya.
Karfe 5:00pm Mr azaad daga office dinshi shida Faisal suka wuce matrix dauko auta dan yasan sun tashi , suna isowa gida tafara kokarin bude kofar motar zata fito ɗan ta hango suhaima da ashraff da minal a gefen part din suna zaune akan lallausan carpet ga fruit dake wajen ga kuma kayan madaran minal damko hannunta Mr azaad yayi ya ce” twinkle inazakije?” nuna mishi su ashraff tayi ya ce” yanzu kibari kiyi wanka sekije kuyi wasan ” to ta ce suka nufi part dinsu Faisal yabi bayansu da school bag dinta da lunchbox din , wanka yayi mata yasa mata riga da wandon jeans yasa mata hula yana gamawa ta manna mishi kiss a kumatu ta ce” bye-bye daddy ” tafita da gudu hafiz na zaune afalo yaga wucewar ta ya ce” to anty twinkle se ina? ” saurin da takeyi ne yasa bata tsaya mishi magana ba kawai tanuna mishi kofa tayi waje abinta suna zaune suka hango ta rungume suhaima tayi ta ce ” i missed you mom one ” dake haka take kiran suhaima zeenat kuma ta ce mata mom two shafa kanta suhaima tayi ta ce ” missed you too my baby twinkle” bata fruit tayi dasuke a slice tafara sha hartace ta koshi sannan ta hau wasa da ashraff da minal, kan mangrib suka tattara suka koma Ciki ɗan yin Sallah.
Bayan sallar isha yaseer, zeenat da mubina sukazo seda suka kai goma kafin suka koma gida.
Ana gobe birthday party din twinkle Abba yadawo tunda yadawo ta koma part dinshi ita da sauran jikokin shi sauran da basa gidan kuma gobe za’a kawosu, Abba idan yakallesu sanyi yakeji har ranshi ganin shima yanzu yatara jikoki masu yawa alhamdulillah, kuma kaff cikinsu babu mafi soyuwa agareshi irin twinkle yana matukar sonta ko kuka tayi in yana nan tofa seyaji dalili son dayakeyiwa mamanta fanan ne yaƙaru yakoma kanta .
Washe gari da safe bayan sunyi breakfast aka dauko kwararren me decoration yazo yayi decoration me masifar kyau a main falo white and pink color falon bakaramin kyau yayi ba , kamar yanda areef yafada haka kuwa yayi gidan anty amina yaje yakwaso aslam da islam anty amina ta ce se bayan sallar juma’a zatazo sannan yabiya yadauko auta ilham nan suka bude sabon fagen iyayi da surutu ita da islam ɗan itama ba baya ba wajan surutu areef de ta cikin madubi yake kallonsu shida aslam dasuke gaba daga nan yaje yadauki samha se sukaje gidan anty shayida yadau adeema da adeena , gidan anty firdausi sukaje suka dau junior sukayi gida , yau jikoki sun cika gidan hayaniya tako ina se barna dasukeyi acikinsu mubina ce kawai baazo da itaba itama se anjuma zasuzo itada zeenat da yaseer din .
Bayan ansauko daga jumma’at ne anty amina da anty shayida sukazo atare , se yaseer da zeenat kowa ya hallara agida suna nan amma banda anty zainab ita sunyi tafiya garin dangin mijinta, anty amina ita da kanta tayiwa twinkle birthday cake pink color and white babba me three steps yasha decoration a saman an rubuta’ happy birthday twinkle ‘ ga snacks da sweet din da akayi ga drinks da rago an gasa shi komai yazama ready afalon bayan sallar la’asar, anty shayida da zeenat sukayi musu wanka suka shiryasu cikin hadaddun kaya sukaje main falo suka zauna kowa ya hallara a falon harta Abba da kowa suna zaune ana jiran fitowar birthday girl, wanka akayiwa twinkle anty shayida ta shafa mata lotion hade mata gashinta tayi waje daya tayi fakin dinsu tabar mata wasu agaba suka zubo tayi mata light make up kayan barbie girl da ummi tayi mata order daga Dubai tasa mata gown din pink color rigar kansa abin kallo ne dauko mata wasu mayun takalma tayi masu kama da sandals amma yanadan hill kadan white color ta samata , tasamata dankunne dakuma chain din gold da bangules tasa mata crown silver color ta fesheta da perfumes, twinkle tayi matukar kyau bana wasa ba ta hadu iya haduwa , ta daurata asaman mirror kallon kanta twinkle tayi ta zaro brown eyes dinta ta ce ” haaaaaa! Haka nayi kyau ” tafada tana juyawa tana kallon kanta dariya kawai anty shayida takeyi mata sannan tadinga mata hotuna kala_kala sannan ta dauketa a kafadarta suka fito tunda suka fito suke kallon twinkle suna sakin murmushi musamman Mr azaad sauketa ƙasa anty shayida tayi nan take suka fara “woww baby twinkle kyau kenan ” dariya itakuma takeyi wajanta auta taje tace ” wow my twinkle you so gorgeous” tafada gyara mata zaman crown din kanta da maganarta na yara ta ce ” thank you anty” wani abu ne yasoki Mr azaad azuciya sedayaji kamar yazubar da hawaye saboda zafin rashin fanan gaba daya jikinshi sanyi yakeyi aduk sanda twinkle ta tambayeshi yaushe mommynta zata dawo daga tafiya wani lokacin ya mata karya wani lokacin yama rasa meze fada mata .
Mikewa sukayi dukka aka daura twinkle akan kujera yanda tsayinta ze iso cake din nata suka fara mata wakar ” happy birthday to you! Happy birthday to you! happy birthday dear twinkle happy birthday to you” haka suka dinga mata wakar itakuma tana dariya, zeenat tace mata ta wure wutar candle din aikuwa haka tayi ta sunkuyo da karamin baƙinta tawure wutar candles din suka mutu nan sukayi tafi mika mata wuka Mr azaad yayi ya ce” now cut the cake ” karba tayi harta daura wukar akan cake din seta fasa ta ce” aini nace bazan yanka cake ba se mommyna tazo ” dam seda sukaji kirjinsu yabuga jin sabon rigimar da twinkle takeson daukowa Mr azaad ne ya ce” baby your mom is coming kiyanka cake din” turo baƙi tayi ta ce” nooo i won’t cut it se mommy tazo” ummi kam shuru tayi takasa magana domin twinkle ta fama mata inda yake mata ciwo Abba ne ya ce” haba amaryata ki yanka cake din mommynki na hanya” ” nooo grandpa” ta fadin haka ta fashe da kuka rarrashin duniyar nan sunyi mata takiyin shuru kuka takeyi harda ajiyar zuciya da shesheka tana kiran ” mommy please come ” duk jikinsu yayi sanyi tausayinta yakamasu run rasa mezasuyi mata tayi shuru, muryar Mr azaad na rawa dakyar ya iya cewa ” twinkle kidena kuka , in angama birthday party zan kaiki wajen mommynki kinji ” yanda yake maganar kadai duk wanda yaji yasan akwai babban ciwon dake damunshi acikin zuciyarshi yau kuma anfame mishi , twinkle na kuka ta ce ” noooooooo” dafa kafadarshi yaseer yayi da shima jikinshi yayi mugun sanyi , suhaima da zeenat se hawaye suke yi . Cire crown din kanta tayi ta yardashi aƙasa tana cigaba da kukanta.
Unexpected sukaga wutar gidan yadauke sannan falon yayi dubu dishi_dishi kawai suke iya gani tunani suka farayi meyake faruwa suda wuta steady ne baya ta ba dauke musu , zazzakar muryanta ne yakatse musu zancen zucin dasukeyi muryanta me dadi da amo yana rera wakar ” happy birthday to you! Happy birthday to you, happy birthday dear my daughter happy birthday to you” ko amarfaki sukaji wannan muryar bazasu taba mantawa dame itaba koda kuwa shekara ɗari aka dauka bazasu taba mantawa da wannan muryar ba arayuwarsu ,yau gashi sunji muryanta shin amafarki ne kokuma gizo ne , rabon da su ji muryanta shekara uku da watanni kenan. Wutar gidan ne yadawo suna tsaye awaje daya sunkasa motsawa zuciyoyinsu nacike da al ajabi da mamakin abinda sukaji , daga kai twinkle tayi ta kalli upstairs da karfi ta ce ” yeeeeeeeh my mommy is here” tafada tana saukowa daga kan kujeran tanufi upstairs da gudu , maida kallonsu sukayi upstairs din da twinkle tanufa , idanunsu ne yayi arba da fanan dake saukowa ta tunkaro twinkle itama tana sanye da abaya fara sol tayi rolling din gyale akanta , suman tsaye sukayi suna binta da kallo kamar a film musamman Mr azaad da idanunshi suka ƙada sukayi jaa.
Da gudu tanufi twinkle da take kokarin haurowa upstairs din suka rungume juna fanan ta fashe da marayan kuka tana furta kalmar ” am so sorry my baby girl ! am sorry mommynki yanzu ta dawo bazata sake barinki ba ” ta fada tanayi mata kiss tanata kallonta tana kuka , yan dugul_dugul ɗin hannayenta tasa ta riƙe fuskar fanan tana girgiza mata kai sannan tasa hannu tana share mata hawayen fuskanta sake fashewa da kuka fanan tayi ta mayar da twinkle jikinta ta rungumeta gam tana jin dumin jikin yarta da tun ranar da ta haifeta batasake ganinta ba ko jin muryanta amatsayinta na uwa , wani irin sanyi ne taji yana ratsata yana shiga dukkan sassan jikinta maida kallonta tayi kan Mr azaad da ya kafeta da rinannun idonshi yana kallonta kamar a mafarki, twinkle dake manne ajikinta ne ta ce ” mommy dama nasan yau zakizo birthday dina, I love you mommy” murmushi fanan tayi da muryan kuka ta ce ” i love you too mommy’s angel ” raba jikinta da na twinkle tayi tana kallonta da itama ita take kallon da gudu auta ta rungumeta itama ta rungumeta atare zeenat da suhaima suka rungumesu suna kuka , hada baƙi sukayi wajan fadin ” anty fanan kece dagaske kokuma gizo kikeyi mana dan Allah karki sake tafiya kibarmu ” tana kuka itama ta ce ” ba kizo bane zahirine nice ba wata ba” tabbas yanzu sun sake tabbatarwa da gaske ne fanan dince bawai gizo ba dagaske ita ce ta dawo rayuwarsu addu’a dasuka dade sunayi yau ga shi Allah ya amsa musu roƙonsu matsanancin farin cikin dasuka shiga baze taba misiltuwa ba duk wani bakin ciki dake zuciyarsu lokaci daya sukaji yatafi farin ciki yamaye gurbinsa, raba jikinta tayi danasu tanufi ummi dake zubda hawayen farin ciki ta rungumeta ummi ta ce ” my feena nayi kewarki sosai” ” nima haka ummina ” tafada tana yar murmushinta dake kara mata kyau.
Shafa kanta Abba yayi ya ce ” alhamdulillah Fatima munyi matukar farin ciki da dawuwarki cikin rayuwarmu ” ta ce” nima haka Abba ” cikin tafiyarta kamar mahauniya ta nufi inda Mr azaad yake tsaye kamar wanda aka shuka a wajen , dukkansu ido suka zuba musu suna kallon wa’yannan masoyan na haƙiƙa da labarin soyayyarsu yakai matsayin a rubuta shi a tarihin duniya , kallon cikin kwayar idon juna suke yi bako kyaftawa idonta daya cika da hawayene ya gangaro ta ce” habiby ko de bakayi farin cikin ganina bane ?” sa hannunshi yayi yajawota jikinshi ya rungumeta gam kamar ze maida ita ciki yana mayar da hawayen dasuke kokarin zubowa daga idonshi ya ce” nafi kowa farin cikin ganin ki wifey dama inada yaƙinin za ki dawo gareni bantaba loosing hope ba ” murmushi tayi ta ce” karfin son da nake maka ne yadawo dani gareka dakuma son danakeyi ƴata da ahalina Allah nagode maka dayasa ban mutu ba kasake bani dama na biyu domin yin rayuwa da wa’yanda sukafi soyuwa agareni ” sake rungume juna sukayi suna fadawa junansu kalamai masu dadin gaske , yaseer da Fawwaz, areef se video sukeyi musu da hotuna gwanin burgewa sosai suka burgesu kuma sunyi matukar farin cikin ganin wannan ranar arayuwarsu, ganin sun manta da suna tsaye awajen ne yasa Abba cikin zolaya yayi gyaran murya dasauri fanan taraba jikinta dana Mr azaad kunya yakamata sosai dan tsabar wutar soyayya yasa ta manta dasu Abba na tsaye awajen sunkuyar da kanta ƙasa tayi sukuwa dariya sukayi kawai Mr azaad yariko hannunta yana kallonta kwata_kwata yakasa janye idonshi akanta gani yakeyi inya dena kallonta zata sake tafiya tabarshi , Hafiz ne ya ce ” yeeeeh what are we waiting for let’s celebrate” aikuwa dukkansu suka sa dariya harda Mr azaad,anty amina ta ce ” ahh lallai yau kam Azaad na cikin matsanancin farin ciki rabon da muga dariya akan wannan fuskantar taka tun bayan tafiyar feena” murmushi kawai yayi yana sake matse hannunta cikin nashi daukan twinkle Fawwaz yayi ya mayar da ita kan kujeran. aka bata wukar daura hannunsu Mr azaad da fanan sukayi akan nata aka yanka cake din ta yanka tabawa fanan abaki tasake yanka tabawa Mr azaad abaki duk wa’yanda ke falon seda tabawa kowa abaki haka akasha birthday party sosai suka dinga mata hotuna da bata gifts masu masifar tsada , har kan mangrib sannan suka samu aka gama ana kiran sallah mazan suka tafi masallaci matan kuma kowa yayi , fanan a bedroom din ummi tayi sallah . Bayan sun dawo ne aka shirya dinner table sukaci abinci dare sannan suka dawo falo suka zauna , sallaman ya usman sukaji tare da na mama, baba da hairah suka shigo amsawa sukayi tundaga bakin kofa mama take kallon fanan kamar a mafarki jin muryan mama ne yasa fanan ta tashi dasauri tanufi mama ta rungumeta, mama da ke hawaye ta ce ” dama nasan zaki dawo gareni fanan ga shi Allah yadawomin dake nayi matuƙar kewarki sosai” ta ce ” nima haka mamana ,nayi farin cikin dawuwata” karasawa cikin falon sukayi suka zauna suka gaggaisa suna taya junansu murna dawuwar fanan, suna tsaka da farin ciki sukaji sallamar me martaba da waziri se galadima ga kuma Fulani zama sukayi aka sake sabon gaisuwa , dama suhaima ita takira ya usman ta sanar dashi fanan ta dawo sannan takira yan Bauchi nan ma ta sanar dasu , Fawwaz kuma yakira me martaba yafada mishi.
Bude taro da addu’a Abba yayi , me martaba yayi ya kalli fanan dake zaune aƙasa akan carpet kanta a ƙasa ya ce ” Allahu Akbar lallai babu abin bautawa da gaskiya se Allah shi kadai ,me kowa kuma me komai meyin yanda yaso ah lokacin dayaso , muna me gode mishi da yadawo mana da yarmu Fatima cikin rayuwarmu. Munyi matukar godiya da hakan kuma munyi murnar dawuwarki Fatima , kuma alhamdulillah kinje kin isar da sakonki wajan ganin bayan wa’yannan azzaluman kin ƙa war dasu adaron ƙasa Allah ne kaɗai ze biyaki domin kinyi na mijin kokarin kin taimaki rayuka da dama , lallai ke din cikakkiyar yar baiwa ce medauke da abubuwan mamaki Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwarki da zuri’arki ” du ka suka amsa da” Ameen ya Allah ” sannan me martaba yadaura daga inda ya tsaya ” Fatima zamuso ki fada mana yanda Allah yayi kika dawo domin mun san ke din kinrigada kinzama shugaba a masarautar nasminaya ” duk ka sa kunne sukayi ɗan sunason suji ya akayi wannan lamari yakasance,gyara zama fanan tayi tafara basu labarin yanda akayi ta dawo ” aranar da muka fita yaƙi nayi nasarar kashe su dukkansu biyu na tarwatsa kungiyar nasu , sede tanzarzar yayi galaba akaina yasokamin wukar danayi amfani dashi wajen kasheshi wannan wukar kuwa bakamar sauran wuƙaƙe yake ba yana fitarwa mutum duk wani karfi dayake jikinshi sannan seyasa maka guba ajikinka sekuma mutuwa , dasauri suka daukeni suka maidani fada aka kira ainihin wanda ya ƙirƙiri wannan wukar, shi yadingamin magani har na tsawon shekaru uku da ikon Allah se nasamu lafiya amma sede jaaazana dake cikina ya gurɓace adalilin wannan gubar dake jikin wukar , seyazamana babu wani karfin iko atare dani , ganin hakane yasa natarasu gaba dayansu afada nasanar dasu kan cewa ni yanzu babu wani irin taimako da zan iya basu amatsayina na sarauniyarsu domin narigada narasa karfina dan haka nace zanbawa yarima ahil mulkin nasminaya amma duk se suka nuna sude ahaka sunason inci gaba da mulkarsu dakyar de nasamu na nusar da su illar haka , sannan na naɗa yarima ahil amatsayin sabon sarkin nasminaya. sannan nayi musu bankwana nadawo duniyar bil’adama ”
Jinjinawa wannan lamarin sukayi sude tunda abinda tajeyi ta aiwatar, su sunyi murna da dawuwarta .
Baba ya ce” tabbas baa cire rai da rahamar Allah ga shi da yardar shi kindawo garemu ” haka sukayi ta murna awannan rana sun dade suna hira sannan kowa ya koma gida cike da tarin farin ciki.
Dare yayi Mr azaad yafita ɗan,tana kwance ta sa twinkle dake bacci akan makeken gadon bedroom dinta agaba tana kallonta duk suna sanye da kayan bacci, taji anbude handle din bedroom Mr azaad ne yashigo hawa gadon yayi ya ce” kina kallon twinkle din mune ?” Murmushi tayi ta ce” ehh bana gajiya da kallonta habiby ” shima murmushin yayi ya ce” komai nata irin naki fuskanta, yanayin maganar ki rigimarta everything, sede surutunku ba iri daya bane na mommynta auta ta dauko ” dariya sukayi atare ta ce” habiby ban taba tunanin zan dawo inci gaba da rayuwa daku ba ashe inada rabo da kasancewa da mijina da kowa nawa” sa hannu yayi yatallafo habarta ya ce” nikuma bantaba cire tsammani da damuwarki ba kullum zuciyata rayamin take komin daren dadewa kina nan zuwa gareni ” yagama maganar yana ɗaukarta kamar yar baby ya ce” ina bukatarki shekaru uku ba wasa ba ” dariya tayi sukafito yana dauke da ita yajawa twinkle kofa yarufe yanufi bedroom dinshi kwantar da ita yayi akan bed yayi mata rumfa da faffadar kirjinshi sannan ya hade bakinsu waje daya , wani irin hot romance suke yiwa junansu kowa na kewar dan uwansa burinsu awannan daren su gamsar da kansu domin kewar dasukayi yanada matukar yawa , cire mata kayan jikinta yayi ya cire nashi yafara sex da ita itama tana mayar mishi da martani, ina yar goge kwallar tausayinsu danaga abin nasu yanason wuce gona da iri kawai nafito narufo kofar ahankali dan kar in dakatar dasu nashige bedroom din twinkle nayi kwanciyata anan.
Rayuwa me dadi Ako wani ɓangare sukeyi cikin farin ciki da jin dadi twinkle me mommy’s dayawa ga ainihin mommynta ga kuma su suhaima da zeenat, Mr azaad da fanan da twinkle, Fawwaz da suhaima da yarsu sukaje Bauchi kai musu ziyara sunyi murna sosai da ganinsu satinsu daya suka dawo domin Ramadan yakawo kai saura kwana hudu .
Haka suka gabatar da ibadar Ramadan sallah yazo akayi bikin sallah cikin nishadi da tarin farin ciki, lokacin zuwa aikin hajji nayi kuwa Mr azaad yabiyawa kowa harda su mama suka tafi suka je sukayi ibadarsu .
Bayan sundawo ne aka rabawa dangi da abokan arziki da mabukata tsara ba.
Wata rana Mr nazaune a office dinshi sakatariya jamila tashigo ta ce wata ta ce tanason magana dashi da kamar zece ah ah sekuma yace ” abarta ta shigo ” bayan ta shigo ne yaga aneesa ce duk tabi ta rame kamar ba itaba ta koma saliha,shi inbama yanzu da yaganta ba mantawa yayi da ita , neman yafiyarshi tayi akan takurawa rayuwarsu da tayi sannan ta ce yabawa fanan itama hakuri , sannan ta sanar dashi itama tayi aure ta auri amjad, yatayata farin ciki sannan yace mata bakomai yayi musu addu’a samun zaman lafiya.
Babban private hospital Mr azaad ya ginawa fanan ga doctors din dayasa mata, akasa mishi suna ‘ fanan hospital’ yabatashi kyauta sannan ya bata manyan motoci guda biyu , bakaramin murna tayi ba tayi mishi godiya sosai family’s sunje sungani harda doctor ammar da matarshi sunje sungani kowa se Allah sanya alkhari yakeyi mata .
Hairah tayarda zata sake haihuwa dan tanason ya usman tana kuma son abinda yakeso ga kuma tsoron kishiya datakeyi hakan yasa suka dakatar da planning suka cigaba da kulawa da yarsu samha gwanin burgewa suna nunawa junansu so da kauna.
Haka Amira da ya al ameen da suke da yara biyu musin da hamnat suke rayuwarsu cikin jin dadi suna nunawa junansu soyayya.
Abangaren nusaiba da lukman ma suma sede Muce Masha Allah.
Zeenat da yaseer ma soyayya suke sha kamar ba gobe ga kuma yaransu ashraff da mubina.
Haka suhaima da Fawwaz suna nunawa junansu kulawa da soyayya ga minal se son barka.
Abangaren love bird kuwa nasu kankat ne ruwan soyayya kawai suke sha basa iyayin awannin batare da sunga junansu ba ko kuma sun jin muryan junansu ba soyayyar su na matukar burge kowa zazzafar soyayya Mr azaad da fanan sukeyi sunayiwa junansu tsabtacciyar soyayya.
Hafiz da areef ne sukaje suka samu abba suka sanar dashi suna son anema musu auren auta da Islam Abba yace bakomai kar su damu bayan tafiyarsu ne Abba yakira baba yasanar dashi areef ya ce yanason anema mishi auren auta baba yace yabashi ita nan gaba kadan inta kara girma se ayi auren nasu. Bayan sungama waya yakira sirkinshi wato mijin anty amina yasanar dashi dan wajen shi Hafiz yanaso anema mishi auren Islam daddyn twins ya ce yabashi ita. Abba yasanar dasu yanda sukayi bakaramin farin ciki sukayi ba.
Wata rana Mr azaad yana driving da kanshi ,ya wuce wasu samari masu faskaren itace daya daga cikinsu ne yayi murmushi ya ce ” Allah yaci gaba da kareka yallabai azaadu ” dayan yace tofa kaikuma aina ƙasanshi dariya saurayin yayi ya ce “shine wanda nabaka labarin yayi hatsari na taimake shi din nan ” dayan ya ce ” Allah sarki Allah yarabashi da makiya” haka sukaci gaba da hiransu sunabin bayan motar da kallo ,duk maganar dasukeyi Mr azaad yajisu dukda nisan dasuke dashi domin ya wucesu sosai nan ne ya tabbatar da baiwarsa na ji yadawo, reverse yayi yakoma wajansu yayi packing yafito babu kyama yamika musu hannu sukayi musabaha ya ce ” naji hiranku da kukayi kaikuma nagode sosai na ceton rayuwarta da kayi ” dukda sunyi mamakin ya akayi yajisu amma sunyi farin cikin rashin nuna kyamar dabeyi ba agaresu dukda suna talakawa, cikin mota Mr azaad yashiga yafito da bandir_bandir din kudade dasukafi million daya yabasu yace gashi ku raba sannan yabasu katin shi yace gobe suzo Company shi yadaukesu aiki , tsabar murna harda kuka sukayi suna gode mishi murmushi yayi kawai yatafi.
Bayan ta tashi daga asibiti ne taje gida suka sha hira da mama da baba dan ta samu be fita ko ina ba yau sundade kafin taje makarantar su twinkle ta daukosu ita da ashraff da minal suka koma gida dukkansu apart din suhaima tabarsu ta wuce part dinsu tayi wanka tana daure da towel tashiga bedroom din Mr azaad akwance ta sameshi dagashi se boxers alamun be dade da fitowa daga wanka ba jin kamshin turarenta ne yasanar mishi da shigowarta , batare da ya dago kai ba ya ce ” naji kun shigo gidan nan keda su twinkle shine kika barta agurin suhaima ” dariya tayi tana hawa kan gadon tayi ta kwanta ajikinshi ta ce” to mijina dan baiwa majiyi abin alfahari na inasanka sosai” sa hannu yayi yazame towel din jikinta yana binta da mayen kallo ” wifey gaskiya kedin na dabance komai naki na daban ne musamman ma wannan breast din naki suna burgeni sosai ” yafada yana shafasu fari tayi da ido ta ce ” habiby kaima ai na dabanne shisa kullum nake sake sonka mijina ” salon yanda take mishi maganar yasa sha’awar ta dayakeyi yasake tashi ya ce ” wifey yau din nan zanyi ajiyar kanwa ko kanin twinkle acikin wannan shamulallen cikin naki” yafada yana shafa cikinta ya gangarar da hannunshi zuwa mararta yana shafawa , lumshe idanunta tayi tana cize libs dinta romancing juna su sukeyi sosai ” baby you’re very sweet my wifey , please fadamin meye sirrin gaskiya dole inyiwa anty amina kyauta, inason kamshin jikinki wifey I love you so much ” yayi maganar da wata iriyar murya wanda dakajita kasan yana cikin matsananciyar sha’awa, ita kanta wutar sha’awa ya hanata yin magana , suka fara shayar da junansu dadi suna gabatar da sunna.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya soyayya da kulawa suke nunawa junansu me ban sha’awa dakuma tafiya da zuciya, twinkle kullum tana tare da mommynta da daddynta , rayuwa me dadi suke gaba daya familyn suna cikin matsanancin farin ciki da annashuwa tare da kaunar junansu.
*To Alhamdulillah Alhamdulillah ala kulli halin nan nakawo karshen wannan littafin nawa NIDA PATIENT DINA sai mun hadu daku acikin sabon book dina me suna ASHE ZAMUGA JUNA karku bari abaku labari ɗan wannan littafin zezo muku da salo kala_kala*
*Ɗinbin godiya da tarin jinjina a gareku yan NIDA PATIENT DINA gaisuwar ban girma da tarin jinjina da fatan alkhari yan NIDA PATIENT DINA comments section group, Ina matukar godiya da comments dinku dasuke karamin karfin guiwa sosai da sosai Allah yabar zumunci da qauna*
*Sakon jinjinawa agareku manya_manyan members na masu karamin karfin guiwa ta hanyar min ruwan hot comments dinku kullum bakwa gajiya tabbas bazan manta daku ba*
1. Maman shurem
2. Eysher raj
3. Maman afra
4. Maman widad
5. Maman junior
6. Esha kitchen
7. Rabi b bello
8. Oum Maryam
9. Umamah Abbas
10.bilkisu Billy
11.baby maimuna
12. Aysha kwaishe
13. Anty rukkaya
14. Mum basma
15.mhizz dejeer
16.hauwa
17. Halima zinder
18.snacka craving
19. Jermy
20.ninarh malle
21.ummu shaheed
*Da sauran wa’yanda bansamu kiran sunan su ba wallahi You really means alot to me in harde kasan kanamin comments tom Ina matukar sonku sosai nagode da karfin guiwa Allah yabar zumunci*
Jinjina agareku admins na masu kokari ina matukar godiya Allah yabar zumunci.
Duk wa’yanda nayi wa laifi atarayanmu a NIDA PATIENT DINA yamin afuwa.