Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 27

Sponsored Links

Ikram tace “sbda me” yace “sbda ba
sunanta Anty ba” tayi shiru tana kallonsa snn
tace “kai ya sunanka to” ya wara ido yace “au
baki san sunana ba Ikram” ta gyada masa kai ya
kamo hannunta yana kallon cikin idonta yace
“Aliyu ne sunana” tace “nima Aliyu xan dinga ce
mka” ya girgixa mata kai yace “yayana xaki dinga
cemin” tace “to bani sweet din yayana”
murmushin jin ddi yyi snn yace “to ki fara min
duk abnda nayi maki tukun” tace “to” ya daura
hannu kan dimple dinta ita ma tayi masa hka, yyi
murmushi ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta
ita ma tayi masa hka, dariya yyi ya rungumeta a
hankali yace “I luv yhu bbyna” ikram ta wara ido
tana kallon fuskarsa tace “lah ni ba bby bace, ni
da na girma” kmr ance ya daga kansa sama yaga
Khaleel xaune cikin balcony din dakinsa laptop
gabansa yana kallnsu, suna hada ido da Aliyu ya
fashe da dariya har da sauka daga kan kujera
Aliyu ya mike tsaye yana kallonsa ya hade rae
yace “wats funny guy” mikewa Khaleel yyi ya
shige dakinsa yana ci gaba da dariya, Ikram ta
bude baki tace “lah ashe yana dariya, ni ban sani
ba” Aliyu bae ce komai ba ya xauna ya sauke
ajiyar xuciya yana kallonta yace “je dauko sch
bag din ki” ta mike da gudu tayi cikin gida, A falo
ta tar da Khaleel ya fito daga kitchen rike da cake
da juice a plate, ta wara ido alamar mamaki tace
“yaya Khaleel ashe dama kana dariya ni ban sani
ba” ya xabga mata harara yace “kinsan Mami
bata nn dukan tsiya xan maki idan baki shiga
hankalinki ba” ta harare sa tace “to ae yayana
yana nn” Jummai tace “lah ashe baku je da nisa
ba” Ikram bata ce komai ba ta wuce sama tana
murguda ma khaleel baki ya bi ta da kallo yana
gyada kai a hankali alamar xae yi maganinta,
yana nn tsaye ta sauko rike da jakar makarantar
ta, ya fixgota da karfi yace “wa kike harara”
muryar Aliyu yaji yana cewa “hey ka taba ta kaga
idan ban rama mata ba” Khaleel ya juya yana
kallonsa ya fashe da dariya yace “girma dae ya
fadi, wae yar cikin ka ka xaunar kke ce ma I Love
Yhu, na sha suprise dinka Aliyu, ina manyan
babes dinka” dariya ssae yake ya haura sama,
Aliyu ya ma rasa me xae ce masa ya bi shi da
kallo don bae yi xaton yaji ba, Ikram tace “ni
baxan taba son yaya Khaleel din nn ba sbda yana
da bad habit, yau a sch Anty tayi mana Moral
Education ta gaya mana menene Bad Habit”

Back to top button