Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 7-8

Sponsored Links

7⃣&8⃣

…………… A tsaye ya samu Ahmed yanata sintiri, yana ganin shi ya rikoshi “kuka takeyi ko brother? Yatanbaya cikeda damuwa. “No Yaya tayi shiru nabata ledar da ka Ajiye a falon relax am sure zataci ta kwanta. Yana gama fada ya haye gadon ya kwanta tareda juyawa yayan nashi baya. “Tank God, and tanks to you brother. Yafada yana d’an samun natsuwa, bathroom ya shige yabarshi idanun shi kur, baya kojin bacci, saida yaji fitowar Ahmed ya rufe idanun shi kamar maiyin bacci. Saida ya shimfida dadduma ya fara jero sallolin nafila tareda Addu’oi masu zafin akan Rayuwar shi data Matar shi, ba Abinda yake nema sai farin cikin Naziya a wurin Ubangiji tareda neman zaman lafiya a tsakanin su.
Ganin har Karfe biyu shima yakasa baccin ya diro tareda dauro Alwalar ya tada sallah shima, haka gefen Naziya bayan ta kulle bathroom tafara nema saida tayi da gaske ta gano inda zata latsa ruwan yafito kafin tayi Alwala tafito, dadduma tagani a gefe da Qur’ani ta tada sallah, saida tayi raka’a biyu ta zauna tana jan k’ira’a a zuciyar ta. Domin fadar manzon mune aduk halin da mutum ya shiga to ya koma ga Allah,

:(Fadhkuroonee adhkurkum washkuroo lee wa laa
takfuroon
“So remember Me; I will remember you. And be
grateful to Me and do not deny Me.) :
Wanda duk ya tuna da ubangiji shima bazai manta da shiba a duk halin da yashiga.
Sai Asuba ta tada sallah saida tayi nafila raka’a biyu kafin farillah, taci gaba da karatun ta, sai Karfe shida ta kwanta a kan daddumar, wani irin bacci mai cikeda salama ya dauke ta domin Qur’ani maganin damuwa ne Idan har kayi Imani da Allah.

Haka gefen Ahmed da Khaleel basu runtsaba saida sukaje Mosque suka dawo, saida Ahmed ya duba kofar dakin nashi yajita a rufe, bai bugaba domin kar momy taji, dakin khaleel suka koma, kwanciya yayi yana murmurshi “daga yau bazan kuma kwana nikadai ba, ko tareda kai “am going to sleep on my wife shoulder, yafada with so much excitement, Runtse idanun shi yayi tareda yin shiru yarasa abunda yakeji a Ranshi, a haka dai sukayi bacci har zuwa Karfe Tara na safe, Wanda Ahmed din ne yafara tashi domin ya matsu ya fita yaga halin da Naziya ke ciki.
Saida yayi wanka ya tashi Khaleel “get up sleeping beauty muje muga momy inaso in duba Naziya Yafada yana goge fuskar shi da towel, tashi yayi yana salati tareda wucewa batareda ya furta komai ba,

Saida yayi wanka ya fito, yasamu har Ahmed ya shirya sai kyalkyale jikin shi yakeyi domin so yake ya burgeta, Idan ta ganshi tasan bata zabi mijin banza ba. Shiryawa yayi shima khaleel cikin shigar tashi ta fama, kallon shi Ahmed yayi “yakamata kasa manyan Kaya zamuje gidan malam later gaisuwa tareda godiya inaso muje tare dakai. “no please banason zuwa wannan unguwar Yaya.”For me please. “OK for you. Amma bazan sa kayan zafi ba sai zamu tafi. “No problem muje”.

Naziya saida mai aiki ta tasheta ta tashi cikin sauri ta bude kofar tace “Hajiya tace kifito kitayamu aikin breakfast. Tace tom tareda gyara zaman hijabin ta ta fito, tareda taimakon mai aikin suka shirya irin Abincin da sukeci wainda idan aka barta bazata iya ko kunna gas din ba bare sauran kayan wutar. Wurin gasa crabs din khaleel ne tasha mamaki, domin ita tsawon Rayuwar ta bata taba ganin ta ido da idoba sai a text book, da kuma manyan d’anyun crayfish da Sam basuda kyan gani a idonta tana kallo aka gasa su a oven aka yanka mai salad da kuma tumatur manya aka jera su crayfish din da crabs din akan ganyen, so takeyi taga wazaici wannan Abun, sai kwai da ko kadashi ba ayiba ansaka mishi kayan kashe k’arni, kawai fasashi akayi a frying pan aka d’an barbada chilli powder asama kadan.
Tana gefe tana kallon ikon Allah sai d’an abinda zata iya yi kawai take tabawa kamar fere dankali da yanka kayan miyan da za’ayi source dasu, Karfe Tara da Rabi suka shirya komai a dining table, dai dai lokacin momy ta fito cikin shigar Alfarma da gwala gwalai, ta kalleta cikin fada, ” Ina fatan bada wainna kayan kika shiga kitchen ba? Kanta tayi Saurin dukarwa tareda gaida momyn Ina kwana. Tace “mu nan wanka akeyi sau goma in antashi domin akwai ruwa basai anje tuka tuka ba ko rijiya ba don haka karki kuma shigar min kitchen da datti, yanzu ma Allah yasa khaleel ya iya cin abincin nan kin shiga kina yimai kakkabi da wannan katon hijabi kamar wadda keda nakasa, ke Kodai wannan kyan naki a fuska ne rufa rufa akayiwa Dana a cikin hijabi? Oya Cire shi yanzu ingani wallahi inkinada ko kuna guda dayane yau sai kunbiya mu sadakin mu. Tafada dai dai y’an kanzagin ta na fitowa tareda kuma su khaleel da suka sawo kai cikin falon.
Dariya Fauzy tayi tace “may be akwai inda keda illah Mommy, Tafada tana tafawa da Aunty zarah dake biyeda ita, “kwarai kuwa a Cire kar a cuci dana,.
Cikin sauri ta Cire hijabin kanta bako d’an kwali sumarta mai tsananin tsawo da kyau kamar buzuwa na nade cikin sabon ribbon, gashine kwance har gaban goshin ta Wanda ke sanarda kai akwai sumar. Kayan jikinta kuwa atamface dai dai talaka wadda malam ya dunka mata tafitar biki akalla zatakai dubu goma, domin kawai ya fitarda Y’ar tashi ranar Aure ya dunka mata su kusan guda uku,
Atamfar mai golden ce blue, dinkin nata nazamani mai kyau na Amare Riga da sket ya mata cif mai d’an shoki ta baya perfect figure dinta ya fito fiyeda tunanin masu sa idon dake wurin, duk sun gama yarda cewa Naziya mace ce kuma kyakkyawa ajin farko ba kamar na Y’ar talaka ba. D’askarewa Ahmed yayi domin yau ne yasan ya tsinci dami akala, yau yake ganin wacece Naziya, wani irin yanayi yakeji, burin shi bai wuce ya ganshi daga shi sai itaba a kebe ya samu ya rage damuwa da wahalar da yasha kafin yasameta.
Gefen Khaleel kuwa bazaka taba gano komai ba sai tsantsar bacin rai da bakin ciki Wanda yarasa dalilin shi, cikin zafin zuciya ya kalli fauzy ” you come and get lost from my house, angama biki ki koma gidan ubanki right now. Yafada cikin karaji da fitinar da ba Wanda yataba jin yayi irin ta. “Aunty zarah I thought Aure kikeyi kema kije gidanki mungode da zumunci we need privacy that’s enough.
Fadan da yakeyi ba Wanda za a iya tsaya wa ayi musu dashi bane, mommy ma mamaki takeyi tareda kallon shi saida ya kuma cewa “I said get lost. Tace “khaleel ” cikin tsawa, “ka kiyaye ni ba inda zasuje, kuma don iskanci ka manta Zarah kanwa tace uwa daya uba daya, don’t forget your manners and Fauzy, karka manta she is your bride to be. “Momy tell them to stay within their limit, ita Aunty zarah ba girman mu tayi ba I can talk to her any how, and Fauzy Auren ta kikeso inyi zan iya fasawa anytime idan naso, don haka before I change my mind leave”. Yafada yana nuna mata hanya.

“Innalillahi, ni Balkisu daga zuwan ki kinfara hada mana gida” Tafada tana nuna Naziya, lallai kuwa yarinya kintabo tsuliyar dodo, Ahmed kaga Abun da ka debo, yarinya mai farar kafa bad luck to our family. Wani irin zafi yakeji tareda kallon momy yana girgiza kai, “no mommy me tayi, Ina bin duk Abinda kikeso momy saboda ingama lafiya please na rokeki kibarmu mu koma gefen mu zamufi samun kwanciyar hankali.
“Naga takaina ni Balkisu kaga ni ko yarinya ta shigo da mugun Asiri, toh wallahi kunyi kadan keda iyayen ki zan nu na muku ni Balkisu in kun kwana akan buzu ni akan dadduma nake kwana mu zuba, daga shigowar ki Dana yafara musu dani. “Momy please stop” this drama is enough. Khaleel yafada yana matsawa kusa da ita tareda riko Hannun ta Alamar lallashi domin yaga Alamar nuna fushin su b’ata Al amarin zai karayi, domin kwanciyar hankalin d’an uwan nashi yace “Fauzy kuzo muyi breakfast Aunty zarah please komai ya wuce OK. “Dama Ibrahim kai raini ne dakai tun kana yaro shiyasa Ahmed yafika Abun kirki.
“Oh am sorry my Aunty yafada yana Dariya kadan, zama sukayi, ita kuma ta wuce dakin da ta kwana tana share hawaye masu ciwo da dumi, domin all her life bata taba tsayawa gaban mutane ba hijabi ba, yau gashi an wulakanta ta saboda me? Saboda tana Y’ar talaka, shiyasa batason tasa Rayuwar ta inda tafi karfin ta.

Ahmed kokarin bin ta yakeyi mommy tace “zonan d’an anace shiryawa zatayi tafito kuma kiyi sauri don bazamu tsaya jiranki ba hamshakiya. Komawa yayi ya zauna tareda zubawa bayanta ido har ta shige, ga koshi ga kwanan yunwa shine wannan.
Gudun fada yasa tayi wanka cikin sauri bayan ta gano inda zata Tara ruwan, domin ko bakomai tanajin labarai tareda gani a TV sometimes duk da ita ba ma’abociyar kallo bace, bisaga Al’adar gidansu na riko da Addini tareda kaucewa duk wata Rayuwa ta nasara, sai gata a yau tana Rayuwa cikin nasara baki daya domin a ganin ta gidan baki daya ma Rayuwar nasara sukeyi.

Ganin bataga kayan taba yasa ta mayarda na jikin ta, tareda daura d’an kwalinta ko mai bata shafa ba ta fito cikin sauri. Suna zaune yanda ta barsu, sai Ahmed da ya rike Haba yana kallon ta inda zata bullo, Ajiyar zuciya yayi ganin fitowar ta, yanzu ya samu damar karewa gabanta kallo da take tahowa toward him, Ajiyar zuciya ya jera tafi goma, domin shidai yana ganin samu da rashi ga mace Allah ya Bashi ta huce takaici Amma mommy taja layi, “bazamuga tsiya ba mudai ki kwana da Kaya ki tashi dasu ki shiga kitchen kifito yanzu kuma kizo ki zauna cikin mu kina tsami, maza ki koma ki canja Kaya, Ahmed kaga illar Auren irin wannan yaran ko? yanzu da akwai bakon ido da munsha kunya. Shiru tayi takasa cewa komai. Cikin sauri Ahmed yace “mommy kayanta na part din mu ne shiyasa duk can aka kaisu, “oh kace kagama planing din tarewa acan to kaje ka kwaso mata kayan zuwa nan ban Amince maka zama da wannan ignorant din ba a cikin wannan gidan ba sai in kashirya yin wani Aure kwa tare da Amaryar Arziki ba wannan ba, Tafada tana nunata sama da kasa, da Alama kalaman mommy nayiwa khaleel zafi fiyema da Ahmed domin yasan d’an uwan nashi hakuri ne kawai yasa yakasa cewa komai shikuwa hakurin shi yafara karewa. “Mommy please am hungry ko intafi ne waje inci yau bazamuci breakfast din ba? “Kizo ki zubawa kowa yarona najin yunwa kinja kin tokare. Matsowa tayi jikin ta NA rawa, ” gefen da Khaleel yake ta fara nufowa kanta akasa bata ma iya kallon idanun mutanen, infact haryanzu bazata iya tantance kamannin fuskokin su ba. Wani irin kamshin turaren wuta d’an mai duguri mai sanyin kamshi, Wanda ya Kama jikinta ya daki hancin shi, Hmmm yana matukar son kamshi a Rayuwar shi, ga wannan da yake shaka mai wani sirri na daban.
Plate ta dauka ta fara zuba musu chips din dankali da source, Ahmed so yake ta kalleshi, just once ko zaiji sauki domin Allah kadai yasan Abinda ke cikin zukiyar shi, damuwar da yake ciki bata faduwa.
Saida ta zubawa kowa tazo kan Khaleel, ya daga mata hannu tareda janyo tarkacen shi gabsnshi domin shi cimar shi daban take a gidan, zuba mai ido tayi tana kallon shi zaici wannan Abun? “Naziya “. Ahmed ya Kira sunan ta cikin wani irin kashe murya tareda tsareta da idanu, batada choice dole tadaga idanun ta takalle shi, nuna mata kujerar gefen shi yayi tareda mata Alamar tazo ta zauna. Ba musu ta nufi gefen shi, mommy nata hararar ta kasa kasa, Su fauzy kuwa kallon village girl suke mata, zama tayi a takure da kanshi ya zuba mata Abincin tareda hada mata tea very thick, “toh shanyayye ita batada hannu ko? Inji mommy shidai shiru yayi, saboda jin ta a zaune kawai a kusa dashi yaji ya d’an natsu kadan.

Tsit kakeji sai karan cokula, ganin hankalin kowa nakan plate ya sauke left hand dinshi tareda dafe Hannun ta daya dake Kan laps d’in ta, gam gam, wani irin zabura tayi, Wanda khaleel ne kawai idanun shi yagani, idanun ta a gefe take kallon Ahmed din tareda kokarin kwace wa ta kasa , wani irin bakon Al amari takeji domin zata iya cewa wannan ne karon farko da namiji ya rike mata hannu, gashi ba rikewar kawai yayiba wani irin murzawa yakewa Hannun kamar kwadayin shi akan Hannun yake,
Har wani irin zafi takeji, shi kuwa laushi da santsin Hannun ne ke rikitashi domin tuni yama daina cin Abincin, jiyake kamar ya dauketa suyi tsuntsuwa subar wurin, he really need privacy with his wife.
A haka kowa ya kammala batareda taci ko cokali daya ba, kuma yunwa takeji ta fitar hankali, domin tunjiya batasa komai a cikin taba, domin ko kallon ledar da khaleel ya Ajiye mata batayi ba.
Shiyafara mikewa tareda barin wurin, saida yaga hankalin mommy zai dawo kanshi ya saki Hannun tareda gyara natsuwar shi da ta dade da zuwa bulaguro sanadin jin shi cikin wani irin yanayi mara misali, bai taba jin kanshi in needs kamar yanzu ba, Hannun ta ya rike duk ya rikice idan ya Rungume ta fa? Ai suma kila zaiyi kai tsaye,

Saurin tashi tayi jin ya saki hanun tayi daki cikin sauri, dakyar ya karasa breakfast yana bawa kanshi laifi domin yaga ko tea bata shaba, mommy ta kalli plate din ta tace “Ahmed aiki ya sameka saikaje ka siyo mata kosai da koko kasan ba asaba da shan shayi ba bare kuma chips, ta fada tana barin dining din zuwa tsakiyar falon ta hakimce tareda su fauzy,
Shigowar y’an matan kawu modu ne yasa ya saki fuskar shi tareda tasowa, yana murmurshi “sai yanzu zakuzo ganin Amaryar? “Yaya Ahmed ai jiya ma muna gidan nan saboda kana hidima ne yasa baka sani ba. “OK kun fita. “Ina Amaryar mu? Tana ciki, and please muje kutayani kwaso kayanta zuwa nan. Yafada yanayin gaba, binshi sukayi,Suna hira a tsakanin. Akwatunan da yayi mata ne kawai ya kwaso mata yabar na Khaleel a can, gudun fitinar mommy, domin ko wainda yayi hanawa tayi akai wai kar su kwaso musu kudin cizo da k’uma, inda Allah ya taimake shi malam yace bayason bidi’ar kawo akwatin abarta a dakin ta idan ta tare, Wanda hakan ya mugun sanyaya mai rai. shigowa yayi da katuwar akwatin zai shige tareda kanin nashi, “Ahmed Ajiye a nan zasu shiga da ita ciki. “Momy bazasu iyaba tanada nauyi sosai. Zabura tayi tace “Zarah kuzo ku kamamin, yana gani haka suka dauka tiki- tiki saboda dai kar Abarshi ya kebe da Matar shi, yadawo tsakiyar falon ya zauna tareda dafe kanshi, Allah yagani angama shiga Rayuwar shi, Mutum yayi Aure Amma jin dadin Aure ya gagare shi.
Fitowa tayi tana sababi tareda zama gefen shi, “na fada maka miji baya zuwa wurin mace ba ayi budar kai ba, don haka karka sake inga kafarka cikin dakin nan bada izini na ba.
Saurin kallon ta yayi “mommy ai yaune kuma shike nan ko? “Nadai na fada maka kar inga kafar ka ciki inba haka ba zan daga maka nono. Tashi kawai yayi yabar gidan cikeda tsantsar damuwa da kuma bacin rai.
Uwa uwace shiyasa kawai baida yanda zaiyi saidai ido.
Dakin Naziya kuwa ta saki jiki sosai da y’an matan wainda sun Cire mata damuwa da kadaici tareda kewar gida, su suka ware suka shirya mata komai na kayan ta a wardrp, da kayan shafan ta wa inda tasan sunja kudi sosai, kayan akwatin sunyi matukar girgiza ta domin saiti biyu ne, wai don ma mommy ta hana shi yayi yanda yaso kenan. Su suka sata ta caba Ado tareda ciro mata wani tsadadden less baki, Abunka da farar fata tuni ta haska ga dinkin kamar angwada ta, suka murza mata dauri, tafito gwanin burgewa, Karfe daya gidan ya cika da y’an uwan ta masu kawo gara Wanda sun kure kokarin su sunyi dai dai gwargwado, inji bahaushe yace ka fada wa mai zuciya biki ba mai dukiya ba.
Mommy ma tasan sunyi kokari saidai hassada da idan bakason mutum ko tsarki da madara kake mai bazai taba kaunar kaba…………. 🖊

 

*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus: 🌻🌻AUREN GADO🌻🌻

 

*Matar soja ce*

 

Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,

Masu son su biya ga account details dina ,
*NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* Sai Ku min magana ta wannan number 09069200154

Back to top button