Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 25-26

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*25&26*

 

…….. sheriff yabi bayan ta da kallo yana tab’e baki “k’asan zuciyarsa yana jin dad’in zaman Alh yahaya da mahaifiyarsa da yazo k’arshe….hamma! siririyar muryarta ta katse masa tunani”ya zuba mata mayatattun idanuwansa beyi mgn ba “d’an daburcewa tayi tana kauda kanta cikin b’ata fuska tace”ka bani pls”meyasa dole sai ta jikina kikeso?”yafad’a kamar bashine yayi maganar ba”to Ai banida ita kuma sanyi nakeji”shiru yayi ya k’yaleta”ganin bema da niyar mgn”kawai saita mik’e tsaye da nufin ta koma d’akin Ammi tayi zamanta….Ina zakije?”batare data juyoba tace”wajen Ammi mana”bakyason na baki suwaitar ne?”toba kak’i bani ba hamma”saida yad’an numfasa cike da basarwa yace”zoki Amsa”juyowa tayi tadawo gefensa ta zauna tana kallon yatsun k’afarta daya take d’azun”sai turo pink lips nata takeyi tana b’ata fuska”duk shariff na lura da ita ta wutsiyar Ido”saidai taji ya azo mata suwaitar me masifar k’amshin turarensa Asaman jikinta batare daya furta komai ba “saidai kafin ta juyo ta kallesa ya mik’e yabar wajen”saida ta hamgosa yana hawa stars”ta kauda kanta tana lumshe Ido sbd jin dad’in k’amshin da suwaitar keyi….. Amaan! da sauri ta ware lumsassun idanuwanta taga Abdallah tsaye yana kallonta”hararar sa tayi”murmushi yasaki yace”kije inji Ammi”in kinyi hak’uri fitama wajen ball zanyi”yafad’a yana kallon suwaitar dake a hannunta”bata kulashiba ta mik’e tsaye ta Aza suwaitar saman kayan jikinta….wow! Anty Amaan kinada kyau sosai wlh”harma kinfi yaya shariff kyau nake gani”kai kuma waye kafi kyau?”wannan mugun yaya sadeeq d’in mana”wanene haka?”nan gidan yake yana can london karatu, yakusan dawowa kin gansa can”yafad’a yana nuna mata k’aton pics nasu su 5″wanda b’ata tab’a lura dashiba sai yanzun daya nuna mata”Abbansu ne da Ammi,sai shariff da sadeeq da Abdallah”pic d’in zaiyi kusan 5yrs da d’aukar sa…kunyi kyau “shine Abinda ta fad’a tana d’aukar d’an kwalin shaddarta da shariff ya Ajiye mata kayanta yanzun yabar wajen”Abdallah dai yanata kallonta yakuma yima Ammi tambayar duniya kan ta sanar masa wai Amaan Acikin danginsu take ko kuwa ya Alak’ar su take da ita??…. Amma tak’i sanar masa”ransa na bashi kodai soyayya sukeyi itada yaya shariff…. Anty Amaan! yadakatar da ita tana k’ok’arin shiga bed room d’in Ammi “wai kinada k’anwa ne?”juyowa tayi suka had’a Ido…you are very stupid! yaji kakkausar muryar shariff tana dukan dodon kunnansa”Aguje yabar parlourn batare da yayi gigin kallon gefen da shariff d’in yakeba”Amaan ta juyo ta saci kallon sa”ya canzo suwaitar wacce tafi wadda yabata kyau”kuma irinta dole sai maza ke sanyata”shi kuwa kallon second 5 yamata ya d’auke kansa yana yin kicin kicin da fuska “kai hamma meye kuma nayi kaketa hararata?”tamkar bazai tanka mata ba can yatab’e baki yana fad’in kinfi kowa sani”idan kin gadama ki sameni A parking lot nanda mintina 5 ,idan kika wuce hakan karma kiyi wahalar zuwa”sbd kokin je bazaki sameniba”daga haka yayi hanyar k’ofa yana takawa cike da aji had’e da kasaita”ya zura hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa gudan hannunsa na rik’e da waya”Amaan tabisa da kallo kafin ta wuce d’akin Ammi”tana zaune gefen bed tana waya da yaya sadeeq”tana ganin Amaan ta fad’ad’a fuskarta da fara’a tana fad’in zan kiraka daga baya sadeeq”inye y’ata kinyi kyau”murmushi tayi irin na yara”to yanzun ya Amince zai kaiki ko?”Eh Ammi yace” na samesa parking lot kar in wuce mintina5″okay to maza d’aura d’an kwalin “batayi mgn ba ta matsa gaban mirror tayi d’aurin ture kaga tsiya”ta yafa mayafin kan kafad’arta,kafin ta d’auki sabuwar hand bag nata da takalmin ta saka”Ammi daketa kallonta ta mata Allah yatsare ta fita”sauke Ajiyar zuciya tayi tana tunani indai Amaan ta wuce wata guda bata warkeba,to dole zasu saka cigiyarta A kowane state ko Allah yasa Andace da iyayenta”sbd ta fahimci shak’uwa me k’arfi na k’ok’arin shiga tsaninta da kowa na gidan”sannan kuma gefen zuciyarta tana mamaki da al’ajabin irin yadda shariff yafara canzawa kan Amaan”tana tsoron karya yafara sonta idan tadawo hayyacinta tace bata sonsa”dukda tasan d’anta ya wuce wata y’a mace ta ganshi tak’isa”idan kuma har Amaan batace bata sonsaba”zata iya yuyuwa ko iyayenta sun mata miji matsalar nan tazo ta gifta”wata zuciyar tace” kibisu dai da addua….tunda ya iso parking lot d’in driver ya iso Asukwane gabansa”da hannu yasanar masa baya buk’atarsa”kafin yanufi gaban motar dake goge k’al ya shiga…..yana k’ok’arin rufe k’ofar kiran mus’ab ya shigo cikin wayarsa”yaja tsaki yana d’auka beyi mgn ba”Abokinah kana jina?”da k’yar shariff yace”uhmm! zamu iya had’uwa yanzun?”ah ah”meyasa ?”zamu fita da Amaan ne”mamaki sosai mus’ab yayi”saidai yasan halin shariff baya k’arya iya gaskiya yake fad’a koda kuwa meye zai faru”shariff na kok’arin kashe wayar mus’ab yace”pls ka hak’ura da fitar mu had’u mana”wai menene?”kan cases d’in nan ne”pls mus’ab kasan ba any time nake kasancewa Ina Aiki ba ko?so pls idan kadamu dakoma miye bayan sallar isha’i kasameni Agida”daga haka ya yanke wayar “Adaidai lokacin kuma ya hango Amaan tana nufo wajen cikin nutsuwa”ita kanta tafiyar tata Abin kallo ce”saidai da Alama kamar tunani takeyi”d’auke kansa yayi ya danno mata uban horn”da sauri ta kalli sashen da motocin suke”Anan ta lura da motarsa”tunawa datayi d’azun yace”waye driver d’inki? yasaka kai tsaye ta nufi front sit ta bud’e ta shigo da sallama”saidai batayi masa mgn ba “Anutse yaja motar yana kunnah karatun Alkur’ani me girma”Amaan ta lumshe Ido tana saurere”shidai yana driving d’in sa Anutse”saidai miskilin ko a bece mataba tunda ta shigo cikin motar”bayan sun iso *mmn khadija beauty saloon* yayi parking gaban shagon”ya kalleta ganin idanuwanta arufe yasaka yakashe karatun”da sauri ta bud’e idanuwanta suka sark’e da nashi “itace ta d’auke kanta da sauri”shi kuwa be dena kallontaba murya Akausashe yace”zamuje ciki bance bayan kin gaishetaba ki koma mgn”dato ta Amsa suna fitowa suka nufi bakin k’ofar shagon”shariff ya matsa yayi knocking,matar tazo ta bud’e suka gaisa”kasancewar ta sanshi yana kawo Ammi “gata nan Amata gyaran gashin daya dace”daga haka ya juya zai tafi, Amaan ta toge tak’i bin matar”yallab’ai tak’i zuwa fa”juyowa yayi ya kalleta”ta shagwab’e fuska tana fad’in nidai hamma bazaka tafi ka barniba bayan ban sansuba”rasa meye zaice mata yayi”yana dai ta kallonta kawai”kinga Amota zai tsaya yajiraki”muje Amiki kar yamma tayi”daga haka taja hannun Amaan suka wuce ciki “shi kuma yakoma mota yaja yabar wajen…..sosai matar tayi mamakin yawa da tsayin gashin Amaan”steaming tayi mata”bayan Angama Aka d’aure matashi”sannan Aka mata wankin k’afa “wanda bece Ayiba kawai dai matar tayi mata sbd tana zaton budurwarsace ita”sai gab da magrib Aka gama “Ahaka kuma shariff ya musu knocking”kinga gama ya nan yadawo ko?”nok’e kafad’arta Amaan tayi tak’i mgn balle ta tashi”matar na dariya taje suka gaisa yabata kud’in da shima bai san ko nawa bane yana fad’in tana Ina?”k’ilan saika shigo ta taso yallab’ai dan tayi fushi”had’e rai yayi yana tura k’ofar yad’an zuro kansa ciki ya kalleta”ta kauda kanta ta sunkuyyar”ya tab’e baki murya bbu wasa yace”idan kika bari na shigo ciki saina b’ata miki rai”yana fad’in hakan yajanye kansa yayi gaba”tanata turo baki ta taso ta fito”matar na mata dariya”koda ta shigo cikin motar batayi masa mgn ba”yana k’ok’arin tashin motar Ammi ta kirashi”badan yasoba ya d’auka yana fad’in Ammi gamu nanfa Ahanya zan maidota”sai kuma yace to yana yanke wayar”hamma ! kasan ko?”harda wankin k’afa tamun”na tambayeki ne?”sosai taji haushin maganar tasa saita sharesa”har suka iso gidan bata koma tankashiba…..bayan sallar isha’i shariff yashigo cikin parlourn “yana sanye da jallabiya da hula pasincap da suwaita Ajikinsa”hannuwansa duka na zube cikin Aljihun suwaita d’in”fuskar nan tasa A d’aure tamau” cikin shan k’amshi yayi sallama” Amaan na ganinsa ta tashi tabar parlourn”d’an cije baki yayi ya zauna gefen kujera zuciyarsa na tambayarsa fushi yarinyar nan keyi dashi kome?”be gama wannan tunanin ba yaji muryar Ammi tace”Akawo maka coffee d’in?”Eh Ammi “batace komai ba ta tashi ta wuce kitchen”bayan ta had’a masa ta fito dashi tadawo parlourn ta mik’a masa”cikin rashin sa’a daya Amsa cup d’in yasub’uce masa yafad’i yadaki center table ya fashe…kwalbar ta soki d’an gefen d’an yatsan k’afarsa babba,saiga jini na fita…. innalillahi wa inna ilaihir raju’un! wannan shi ake kira tsotsai”cewar Ammi tana nufar d’aki da sauri sbd ta d’akko masa cotton da hydrogen”tana zaton idan yayi Amfani dasu k’ilan jinin ya tsaya”Amaan na kwance saman bed d’in rub da ciki”kayan baccine Ajikinta riga da wondo masu sulb’i,sai suwaitar shariff data Aza saman kayan”yadda taji Anturo k’ofar ba’ayi sallama ba yasaka tayi saurin tashi zaune tana kallon Ammi data shigo ta nufi gaban mirror”Ammi! na’am Amaan”wlh kinga yayan kune yaji ciwo jini nata fita….bata rufe bakiba Amaan ta duro daga saman bed d’in ta fita da sauri kanta bbu ko d’an kwali”saidai kawai shariff daya lumshe idanuwansa yana jin rad’ad’in ciwon ya ganta gabansa tana hawaye tana fad’in” hamma nah! meye yaji maka ciwo ?”sannu! bara na dafe maka wajen kar jininka yak’are”ta fad’a tana kuka had’e da kok’arin dafe masa gefen yatsan”shariff dake kallonta da tsantsar mamaki ya janye k’afar tasa gefe da sauri, yana girgiza mata kansa beyi mgn ba “hakan yayi daidai da isowar Ammi”bayan ta mik’a masa ta kalli Amaan tana fad’in kukan meye kikeyi?”ba hamma bane yaji ciwo”Ammi na murmushi tace”bansan zaki damuba daban sanar miki ba Amaan”ta fad’a tana tsintse glass cup d’in daya mutu tabar parlourn “shariff kuwa Anutse yazuba hydrogen d’in jikin cotton yashafa Asaman ciwon”sai gashi ya tsane jinin kuma yatsaya”Amaan dai na duk’e gabansa tana kallon yatsar”Ahaka yaji sallamar Abdallah”yabi gashin Amaan da yaji gyara da kallo”kafin ya zare pasincap d’in dake saman kansa ya aza mata saman kanta da sauri yana fad’in taso kidawo nan ki zauna”to hamma kadena jin zafin ?”kansa kawai ya gyad’a mata “yah Allah kabama hamma nah lafiya! ta fad’a tana d’aga hannu sama”shi mamakinta kawai yakeyi”be tab’a zaton zata iya kuka sbd shiba”saiya kalleta murya can k’asa yace”keda kike fushi dani shine harda yin wani kuka sbd naji ciwo?”toba na hak’ura bako?”kumafa lafiyarka ta fimun komai mahinmanci hamma”sosai yaji kalamanta na dukan zuciyarsa yana kallon ta babu ko k’iftawa”dan wannan kalmar tata ta wuce ace yarone yayita….yaya shariff kanada bak’i suna a parlourn bak’i “okay yafad’a yana kallon Amaan”kamar bazaiyi mgn ba can yace”tashi kije ki kwanta”ki kuma saka hula ko d’an kwali”to hamma ka bani wannan hular?”,kansa yagyada mata”sai kuma tace”to yajikin naka?”nifa Amaan lafiyata qlau”yafad’a yana kallon gefen da Abdallah yake”yaga su yake kallo”harara ya watso masa yana mik’ewa tsaye “itama Amaan saita tashi tsaye ta nufi d’aki”shariff kuma yafita waje”sai wajen k’arfe 10:11 pm yadawo ciki”bbu kowa a parlourn”matsawa yayi yafara knocking Abakin k’ofar bed room d’in Ammi”jin shiru ba’a yi mgn ba yasaka ya murd’a handle d’in k’ofar ya shigo”d’akin da haske”Amaan na kwance gefenta na dama”ta saka hula ga wacce yabata rik’e A hannunta da Alama wasa takeyi da ita bacci ya kwasheta “tsaye yayi yanata kallonta can ya matsa yatofeta da addua,kafin yaja devut yarufe mata jikinta…..yana d’ago kansa Ammi na fitowa daga bath room”sosai yaji nauyin ganinsa d’akin datayi”saiya basar yana shafa kansa yace”Ammi zanje Abuja da safe insha Allah “Akwai Abinda zanyi ne Acan”Amma ta jirgi zan tafi da k’arfe 8 na safe zan wuce”wani abu zakayi Acan?”gidan mai na dake a can Ake kok’arin rufewa”subahanallahi! to Allah yakare”ya Amsa da Ameen yafita….washe gari da Asuba daya dawo daga masallaci ya shigo gidan”Abin mamaki Amaan na zaune parlourn da dogon hijab Ajikinta “tana ganinsa ta mik’e tsaye tana fad’in hamma ya jikin?”shifa harga Allah yama manta da wani ciwo da yaji saida yaji tayi maganar….hamma dan Allah kamun mgn kodai Asibiti zakaje??”girgiza kansa yayi cikin sanyayyar muryarsa yace”Amaan bakya gajiya da shirme ko?”nifa daga masallaci nake”karki damu tuni na warke”to Ina kwana?”lafiya qlau “kije ki koma kwanciya kiyi bacci….kafin tayi mgn Ammi ta shigo cikin parlourn”shariff yaduk’a ya gaisheta”ta Amsa da kulawa tana kallon Amaan tace”dama nace miki kidena damuwa shida ciwon ke jikinsa kilanma ya manta”ka ganta nan tunda na tasheta taketa faman tambayar ka warke ciwon?”shinefa muna gama sallah tace mun zataje ta gaisheka”shariff dai na duk’e yana sauraren kalaman Ammi”wanda Azahiri zaka d’auka bema damuba”Amma Abad’ini mamakin yadda yarinyar ta damu dashi har haka yakeyi…..tashi muje ki d’an kwanta ko?”muryar ammi ta katse masa tunani”Amaan batayi mgn ba tadai kalli shariff da shima ita yake kallo”saidai shi suna had’a Ido ya d’auke kansa ….shima be zauna a parlourn ba “side nasa ya wuce yafara shiri”sai wajen k’arfe 8:5 am ya sakko down stairs d’in”yana ta zabga daddad’an k’amshin sa me kashe jiki”kallon second 3 yayima parlourn ya lura bbu Amaan Aciki “wanda saida yaji fad’uwar gaba daya tunata”kuma shi kansa besan meyasa yatunata d’in ba”yana sanye da k’ananun kayan da sukayi matuk’ar dacewa da kalar fatar jikinsa “yayi kyau harya gaji”dukda fuskar tasa kamar koda yaushe d’aure take”Ammi dai na kallonsa Aranta tace”mutum har mutum Amma yak’i Ajiye iyali”ita yanzun rashin k’inyin Auren nasa harya fara bata tsoro”koda sadeeq be sanar mata yana soyayya ba ta fahimci shi yafishi kula mata da sunan soyayya….ganin yazo ya zauna yanata danne danne Awaya yak’i yin mgn yasaka ta girgiza kanta kawai tace”kaje kayi break fast mana”No Ammi zanyi Acikin jirgi ne”iya Abinda yafad’a kenan Atak’aice”tasan ba mgn zai komayi ba hakan yasaka tace”Acan zaka kwana ko yau zaka dawo??”idan matsalar batayi yawa ba yau zan dawo”idan kuma da matsala sosai Acan zan kwana”to shikenan Allah ya tsare hanya yabada nassara Ai bama fatan matsala shariff”koda kadawo bamunan muna wajen suna na hafsat(y’ar k’anwarta) kamar bazai tanka ba sai kuma yace” keda waye zakuje?”da Amaan mana”tunda kasan ba skul ko islamiya take zuwa ba”haka nan yaji beson Ammin taje tare da ita”sannan kuma zuciyarsa nason jin Ina Amaan d’in take?Amma miskilancin sa yahanashi ya tambayata”mik’ewa tsaye kawai yayi fuska bbu walwala yace”pls Ammi ki barta gida”zuwanku da ita wasu zasuyita tambayar ita d’in wacece?”daga haka yayi shiru ya nufi k’ofa”kamar tace” ya jira Amaan tazo suyi sallama Amma sanin halinsa tana iya masa mgn yace A k’yale Amaan d’in yasaka ta barsa……lokacin daya iso parking lot harma body quards nasa da driver nasa sun zama on ready”cikin girmamawa Aka bud’e masa back sit yashiga”yana zama kiran mus’ab na shigowa cikin wayarsa”ya d’auka da sallama”Ina tayaka murna Abokinah bisaga nassarar dakayi wajen bincike”kaji dai Alh Isa yau Anyanke masa hukuncin kisa ko?”d’an tab’e baki yayi yace”ban saniba! Okay Ai yau Aka sanar A news d’in safe”okay”pls sheriff dan Allah kaduba lamarin da Dr Mansoor yake ciki game da Amaan ka tausaya masa”wlh yana cikin wani hali game da soyayyar yarinyar nan”sannan bana so na sanar masa ta yadda kasameta sbd idan nayi hakan sai naga kamar na tona Asirin kane……✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button