Hausa NovelsRainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 13

Sponsored Links

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

 

Page 13
______________________
*Alhamdulillah mun dawo daga ɗan gajeren hutun da muka tafi na kawo maku Cigaban wannan littafi Mai taken rainon soja…ina fatan Ubangiji Allah ya bani ikon kammalawa cikin aminci kaman yanda muka fara. Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba…ga masu buƙatar payment regular group ₦500…Vip group ₦1000… Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*
________________________

Ware dara-daran idanun ta Ma’eesha tayi tana zuba su bisa Kyaƙyƙyawar fuskar shi Wanda har a lokacin Lulun idanun sa basu ɗauke daga Kallon ta ba. A hankali Zuciyar ta tafara mata magana da cewa “Shine fa ya dawo”. Ma’eesha..! Ya kuma kiranta a wannan karon har ta fuskar sa ya sauya yana shirin rufe ta da wannan faɗar nasa da take bala’in tsoro. Saurin muskutawa tayi tana juyi tare da Faɗi ƙasss timmmm daga Gadon. Saurin miƙewa Ma’eesha tayi tana Furta “ Uncle a’aaa Kai kaine?”. Ɗan janye idanun sa yayi daga kallon ta kana yace “ maza ɗauro alwala ki taho morning exercise ”. Shiru tayi tana kallon sa idanun ta na ciko da ƙwallah kaman zata sa kuka , Kawai sai kuma ta juya tana nufar wurin Waldrop ɗin ta , hannun ta tasa tana buɗewa a hankali tare da fiddo da Towel, kawai sai hawaye rau-rau suka fara zubo mata. Jan shashsheƙa tayi wannan yasa shi fahimtar kuka take yi. Ɗaure fuska yayi tamau kamin cike da Muryar sa wanda ita kaɗai yake yi mawa magana a hankali cike da taushi da shi … kukan me kike yi? .

Da Sauri Ma’eesha ta juyo tana kallon sa tare da saurin goge hawayen nata tana Girgiza kai tare da cewa “ A’a Uncle ba kuka nake yi ba. Mura ce take damuna shine idona ke hawaye.

Kallon ta yayi yana ɗan sauke idanun sa , don tarrr yake kallon ta kuma ya fahimci dalilin kukan nata. Kallon sa tayi shima yana kallon ta ba tare da yace mata komai ba a fuskar sa ta fahimci mai yake nufi . Wannan yasa ta a hankali kai hannun ta tana cire ƙaramar Wandon kayan barcin nata tare da ƙoƙarin cire rigar jikin ta . Keeee!!!

Muryar sa ya katse ta cike da tsaawa wanda sai da Hantar cikin ta ya kaɗa . Sam bata san lokacin da ta saki rigar barcin nata ba jikin ta na ɗaukar kyarma kawai sai ta fashe masa da kuka tana ɓarin jiki don ko ina nata rawa yake kar-kar-kar .

Miƙewa taga yayi Daga inda yake yana takowa ixuwa inda take. Baya Ma’eesha ta fara yi cike da tsoro tana fara kiran sunan Mami….a gabanta ta gan shi nan take tsoron ya ƙara kamata hawaye na sauko mata babu ƙakƙautawa . Wayyo Ya Khalil Uncle zai duke Ni…..Ya khalil kazo! Idanun Haidar ne suka kaɗa suka yi jahhh a lokaci guda kiran sunan Khalil da tayi shi ne yafi ɓata masa rai . Bama cire kayan da take ƙoƙarin yi a gaban sa bata jin tayi wani Abu . A hankali Zuciyar sa na raya masa cewa “ A gaban Khalil ma haka take cire kayan ,duk ya gama ganin jikin ta , shiyasa yake damuwa da ita ashe yana kallon na bulus ne. Wannan sakacin waye ? Nawa ne ? Ko na Mami da har bata san darajar jikin ta ba?”. Zuciyar sa ce ta basa amsa da cewa “ is your fault, sakacin naka ne. Muryar ta ya kuma ji tana furta “Don Allah Uncle ka tafi yanzu zan fito naje wurin Ya Khalil muyi exercise ɗin tare…..Yi mun shiru ko yanzu na ƙarairaya Miki ƙafa ɗaya kuma a haka kiyi mun exercise ba tare da an ɗauraki ba…Waro ido Ma’eesha tayi tana kama kan ta na nashiga uku, tana taɓe baki cike da shagwaɓan nan nata tana ƙoƙarin fashe masa da kuka ya ƙara matsawa jikin ta ….wannan yasa ta yin shiru don yanda ya gwamitseta har shi kan sa yana jiyo bugun numfashin ta.

Wani irin gumi taga yana tsartsafo ma saman Goshin sa…Uncle sorry kayi hakuri zan rinƙa tashi da wuri daga yau ba zaka sake zuwa ka ga ina barci…..Rufe mun bakiGumm ta kame bakin ta . Tana raba idanu tare da cigaba da tsiyayar hawaye.

A haka kike cire kaya a gaban kowa saboda rashin hankali? A gaban Khalil ma cire kayan jikin ki kikeyi kenan? Haka ne? Yayi maganan yana watsa mata dulu-dulun idanun sa. Saurin gyaɗa masa kai tayi alamun eh . Don ita sam rainon nasa ne bata san ya ake ƙarya ba bare tayi masa .

Wani irin sarawa kan sa yayi da ƙarfi …. Zuciyar sa na masa zafi , ji yake kaman yaje ga Khalil a halin yanzu. Cike da wauta tana shashaƙa ta furta “ Kayi haƙuri ban san babu kyau Na cire kaya a gaban mutane ba Uncle amma ba zan ƙara ba ….Kuma cire kayan kawai nake yi bai taɓa mun wanka irin yanda mami tace a da kaine kake mun wanka har kwalliya… Yanzu me yayi saura ? Ko zaki je ne shima yayi Miki? Mara Wayo wuce ki bani wuri . Saurin sunkuyawa tayi tana Ɗaukar Towel ɗin tare da nufar Toilet.

Ma’eesha!

Muryar sa ya katse ta inda cikin sauri ta tsaya cak tare da juyowa tana kallon shi . Cikin wani irin murya tamkar bana shi ba taji ya furta “ Khalil yaga jikin ki komai da komai?”. A’a ta furta tare da Girgiza kai tana saurin cewa“Uncle sai kuma tayi shiru tana kasa masa maganar ganin yanda fuskar sa ya haɗe kaman hadari ”.

Ina sauraren ki ,tun da baiga jikin ki ba ya kike yi a gaban sa ?.

Kallon shi tayi tana Ɗaura Towel ɗin daga saman ƙirjin ta wanda ya sauko mata har cinya. Kana ta janye rigar barcin nata a hankali wanda ɗaura Towel ɗin bisa kan sa . Kallon shi tayi tana murmushi tare da cewa “ Uncle ka gani ko? Ai kaima baka ga jiki na ba ko Uncle?”. Dan sassauta fuskar sa yayi don tabbas indai haka take yi to jikin ta babu mai ganin shi sai dai ƙafafu. Kallon yan lukutayen cinyoyin ta yayi zuwa ƙasa . Kana yace “ Kin tabbata haka kike yi ,ƙarya fa babu kyau faɗa mun gaskiya ba zan Miki komai ba Ma’eesha ”. Wangale masa baki tayi cire da gasgatawa tace “ Da gaske ne Uncle ƙaima da ka tsaya haka zaka ga nayi”. Murmushi taga yayi yana faɗin “Good girl , Ashe Ma’eesha na ta fara hankali tasaan yanda ake sitirtaa jiki. Wani sabon Annuri ne ya bayyana a Fuskar ta don jin daɗin yabon da yayi mata. Gyaɗa masa kai tayi tana cewa “ Ai yanzu na girma ne Uncle ” .

Wani irin dariya taga ya shaƙe dashi wanda tun da ta fara girma ta taso Bata taɓa ganin irin wannan dariyar nasa ba. Oya yi sauri ki fito ina jiran ki Back yard. Okay uncle. Ta furta tare da saurin shigewa Privacy.
**
Mami ne ke kai kawo tsakanin kitchen da Dinning area. Sanye take cikin shigar wata doguwar riga irin na english wears ɗin nan masu ƙaramar hannu. Gani nayi Shakaru sun ja ta ƙara ƙima dama kun san yanda take. A wannan karon idanun ta cikin medical Glass ne na ƙarin ƙarfin ido . Wannan gayun nata har yau yana nan . Don gashin kan ta yasha gyara an zubo shi baya , daga sama kuma ta sanya wata hula mai kyau na mata na zamani. Ƙafarta cikin room slippers tana kai hannun ta tare da cewa“ Ba zan soya mawa ma’eesha ƙwai yanzu ba ,saboda ba zata tashi ba nasan sai 9:00am.

Motsin fitowa falon yasa ta juyawa tana kallon ƙofar Bedroom ɗin Ma’eesha da take tahowa tare da kallon Mami. Rungume Mami Ma’eesha tayi tare da cewa“Mami ina ƙwana ?”. Kasa amsa ta tayi don mamakin sunyi da ita yau ba zata fito da wuri ba , sai kuma gata da kayan exercise riga da Wando mai yalwa irin masu kaman Jessy ,ƙafarta cikin kambass na mata baƙi irin manyan nan. Fuskar ta ta shafa tana kallon idanun Ma’eesha kana tace “ ina zaki je haka da sassafe ?” . Hummmm inda na saba zuwa da sassafe idan Uncle ya dawo mana! Ta ƙare maganan tana farrr da idanun ta tare da shagwaɓe ma mami fuska ”. Au yanzu da asuba ne ya shigo miki? Wannan wacce irin damu ne? Jiya fa da karfe goma na dare suka dawo shine yaki barci ko Hutawa baiyi ba shine Kema zai hana mun ke sukuni? Maza koma ki kwanta bari naje na sam……Aaahhh Ma’eesha ta bude baki tare da saurin riƙo Mami tana cewa “ A’a ina mami kinji zauna nima ina so na motsa jikin sai na dawo”. Tana furta haka tayi saurin ficewa daga falon ba tare da ta jira jin mene Mami zata ce ba”.

Bin bayan ta da kallo Mami tayi kana ta Girgiza kai tana furta “ Ma’eesha kenan na Uncle,wato duk wahalar da zai bata ta gummaci tayi koda bata son hakan . Ba zan ɗauki wannan exercise ɗin ba yarinya ta yar lukuta ce ba so nake ta tsiyaye a wahala ba ,macace ba Namiji ko Soja irin sa ba . Mami ta yi zancen tana ɗaga kai tare da kallon Upstairs inda Bedroom din jidderh yake. Itama jidder Bara na tada ita yanzu , tun da ƙanwarta ta tashi itama ta miƙe hakanan, ace mutum ba zai shiga Jami’a ba sai karfe tara ko Goma just because your father general yelwa shi yasa wani gatan baya da amfani. Mami ta ƙare maganan tana nufar Upstairs.

**
Tun da suka fara exercise ɗin a idon Khalil dake daga saman bene yana hango su , hannun sa riƙe da mug na Cofee yana sha da Wannan safiyar don gari yayi shaaa bai haske ba sosai . Kallon ma’eesha Ali haidar yayi inda take tsallen da igiyar nan don yafi bata Wannan training din tamkar wanda zata je atisayen zama Soja ko police . Ma’eesha yau zamu sauya exercise ɗin namu gudu zakiyi kije ƙarshen can ki dawo a minti ɗaya. Saurin kallon nisan wurin tayi kana ta Girgiza kai don babu yanda ta iya ta juya tana fara gudun tun kamin ta kai ta siƙe amma a haka taji yana faɗin “Ƙi ƙara gudu ….don dole tana haki ta isa tana dawowa zuwa inda yake tare da Sauke numfashin gajiya. Kin san minti nawa kikayi kuwa ? . Girgiza kai tayi ta haɗa gumi sharɓan…..Kallon timer⏲️ yayi kana yace “Ni da nace minti ɗaya ke mintuna biyar kika ɗauka har da ƙarin sakan talatin . Kamin Ma’eesha tayi magana ne ya furta “ Maza Juya ki ƙara ki dawo daga farko….Wayyo Uncle I’m tired . You are what? Ya Furta yana kallon ta babu wasa . Sauke idanun ta tayi ƙasa cire da yarinta a galabaice ta furta “ na gaji ba zan iya ba”. No impossible in life , Oya koma ki sake a minti ɗaya zakiyi kije ki dawo . Muje tare…..a tare suka fara gudun yana na wuce ta ya dawo yana furta “ Kina so kiyi kuka a safiyar nan kenan? . A’a Uncle. To ki ƙara sauri . Da gudu tayi gaba tana ƙarawa dai dai Gyefen benen da Khalil yake tayi baya Numfashin ta na ƙoƙarin ɗaukewa luuuuuu tayi zata zube ƙasa da sauri Aliyu ya kai hannun sa yana riƙota tare da rungume ta jikin sa….Numfashin ta ke sauka da ƙarfi da ƙarfi tana jan shi da ƙyarrr. Shafa bayan ta yake yi cike da kulawa a hankali cike da miskilalliyar Muryar sa ya furta “ I’m sorry , Zaki iya kinji Ma’eesha ”.

Yanda yake shafa mata baya yana mata magana yasa Khalil sakin cup din ba tare da ya sani ba . Nan take ya fashe yana tarwatsewa ruwan Cofee din yana fallatsa har inda suke. Wannan yasa Aliyu Haidar ɗagowa daga jikin Ma’eesha yana kallon saman. Kallon kallo suke yi tsakanin su . Kamin Ma’eesha itama ta ɗago tana saurin kallon daga inda taji ƙaran nan .

Gani tayi Khalil ya kama karfen benen daga sama yana dirkowa ƙasa sam bai tsaya bi ta hanya ba. Bude ɗan ƙaramin bakin ta tayi don ta dauka yanda ya dirko to fa ya karairaye ya gama. Tun kamin ya ƙariko Aliyu ya kalli Ma’eesha yana cewa “ Go and rest”. Da sauri ta furta “ Ya Khalil baiji ciwo ….cewa nayi kije ki huta……!!! Yayi maganan yana ɗaga Murya . Da gudu tayi baya tana cewa to.

Isowa inda Aliyu Yake Khalil yayi kana ya furta “ Ali haidar meye na ga kana mawa ma’eesha yanzu? . Wani irin kallo Aliyu yayi masa ba tare da yace komai ba. Kasan nasan ka fiye da kowa a cikin gidan nan . Ɗan ɗaga gira Aliyu yayi kana yace “ Go direct to the point ”. Cike da fushi don Ali dan rainin hankali ne nan Khalil ya furta “ nasan ka nasan yanda kake lalata ƴammata da ko wacce mace ta shigo gonarka. Kai din ɗan iska ne ba mutumin kirki ba , kai Ƙwarto ne shahararre….Don haka daga yau kar ka sake hugging ɗin Ma’eesha bare har ka shafa wani ɓangare na jikin ta……….!

*To masu masoyana makaranta littafin rainon soja anan na dasa aya….✍ Sai mun hadu a night update….Ina sake faɗa don Allah kar ki karanta mun idan baki biyani zufa na ba , rubutun ba sauki ne dashi ba bare kuma tsara labari….ga masu buƙatar karanta littafin Regular payment ₦500 vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932….Maman teddy’s write✍*

Back to top button