Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 69

Sponsored Links

PAGE* 6⃣9⃣

Yarima koda sukaje 6angarensa da mamakinsa yabi ko’ina da kallo yaga angyara sosai duk anzuba masu sabbin ma’aikata da bayi, koda yaje part d’insa tsaye yatarar da guards d’insa nan suka zube suka kwashi gaisuwa, amsa musu yayi cikin sakin fuska sannan yawuce yashiga ciki komai a gyare yake fes, murmushin jin dad’i yayi dan shi kansa yasan memartaba yana sonsa sosai.

Zarah ma koda tashiga part d’inta nan kuyanginta suka kaure da murna da jin dad’in ganinta harda d’an kukansu.

Zama Zarah tayi suka gaisa cikin mutunta juna sannan tatashi tashiga bedroom d’inta ko’ina a gyare yake fes nan aka shigo mata da kayanta, saida tayi wanka tai sallah sannan tashirya nkayanta cikin watdrobe daganan tabi lafiyar gado takwanta nan bacci yai awon gaba da ita.

 

Sumayya ma wajen sultana bilkisu tacigaba da zama inda sultana bilkisu tacigaba da kula da ita cike da tausayinta.

 

Yarima bayan yagama shirinsa cikin shigarsa ta alfarma yafito a yarimansa sak fitowa yayi inda yatarar da shaheed yana jiransa saida suka k’ara gaisawa cike da jin dad’in ganin Juna sannan suka d’unguma zuwa fada.

Suna shiga nan duk mutanen da suke ciki suka zube Suna kwasar gaisuwa haka yacigaba da amsa musu cikin sakin fuska daga k’arshe da yagaji sai yakoma d’aga musu hannu ahaka suka isa har chan wajensu memartaba da waziri sai iyayensa da suke zaune, cikin girmamawa yaduk’a yagaishesu suka amsa masa sannan yaje yazauna kujerarsa da aka tanadar mashi sai kujera ta kusa da tashi shaheed yazauna.

Bayan jama’a sun nutsu memartaba lasifika yakar6a ahankali yai sallama sannan yafara yi musu godia akan addu’o’in da sukayi masa daga k’arshe yak’ara bayyanar masu da Yarima da yadawo sannan yak’ara shaida musu akan shine magajinsa ko bayan ransa.

Nan fada tarud’e da murna da kabbara cikin jin dad’i, bayan ya gama bayani yatambayi Yarima ko yana da magana nan Yarima yagirgiza kai.

Waziri ne yakar6i lasifikar yak’ara yi ma jama’a godia sannan yanuna farin cikinsa akan samun lafiyar memartaba yakuma yi murna akan bayyanar Yarima daganan yaba wasu fadawa umurni akan suje susa akawo abincin da yasa ashirya a gidansa saboda gaggarumar walima yahad’a yanaso kowa yaci yanuna farin cikinsa.

Haka akaje akazo da abincin me rai da lafiya aka zuba ma kowa na cikin fadar hatta su memartaba saida akasa masu nasu, bayan angama nan akaba kowa umurni yaci nan jama’a aka shiga ci ana jinjina ma karamcin wannan masarauta hatta su memartaba da shi kansa waziri sunci.

Shaheed ne ganin suhail baya ci yasa yata6osa yace kaci man.

Murmushi Yarima yayi yace na k’oshi, harararsa shaheed yayi yace ammah kasan bazasuji dad’iba idan sukaga bakaciba.

Jin haka yasa Yarima yad’ebo abincin cikin izza yaci, cokali biyar yayi yature abincin yajanyo wayarsa yashiga dannawa.

Bayan kowa ya gama nan sarki ya amshi lasifika yanuna godiarsa ga waziri sannan yad’auko wata alkyabba da rawani masu kyau yadamk’a ma Yarima.

Kar6a Yarima yayi cikin jindad’i sannan yanuna godiarsa, daga k’arshe yayi ma su memartaba sallama yaja shaheed suka fita, motarsa suka shiga suka nufi hospital d’insa.

Lokacin da ya isa sosai staffs d’insa suka nuna farin cikin dawowarsa, dr khalil ko rungumesa yayi cikin jin dad’i.
Yarima farin ciki yayi sosai alokacin da yaga komai yana tafiya daidai nan yanuna jin dad’insa tare da godia ga manyan staffs d’insa.

Bayan sallar isha’i bayan ya gama shirinsa na bacci saman gadonsa yahau yakwanta kad’an kad’an ya duba lokaci yayi tsaki ganin har wajen k’arfe tara ammah zarah batazo part d’insaba, daga k’arshe mik’ewa yayi yasaka alkyabbarsa sanan yafito yanufi part d’inta.

Koda yashiga babu kowa a parlour dan haka yawuce bedroom d’inta, kunna gloves yayi nan yahangota tsakiyan gado ta baje sai baccinta takeyi, murmushi yayi sannan yai light off yawuce yanufi saman gadon yahau yakwanta a gefenta.
Janyota yayi jikinsa yarungume ahankali tabud’e idanunta cikin muryar bacci tace bakayi bacci ba daman?

Uhm taya zanyi bacci bayan baki lek’aniba tunda muka dawo nifa ban yadda adinga nisa da niba dan ina buk’atar kulawa,

K’ara shigewa jikinsa tayi tace kayi hak’uri d’azun saida naje lokacin ka fita insha Allahu bazan dinga nisa da kaiba yanzu ma dan a gajiye nake saisa nakwanta.

Kina gudu kar inyi miki wani abu ko saisa bakijeba?
Marairaice murya tayi tace bahaka nake nufiba kawai dai baccine da gajiyar tafiya ammah nima naso inzo.
na k’i wayon naki yanzu dai kiyi baccinki babu abinda zanyi miki
K’ara tura kanta tayi cikin k’irjinsa tana murmushi.

 

Washe gari zarah part d’in yarima taje tagyara fes ko a gyare yake sannan tahad’a masu breakfast, bayan sun gama breakfast a part d’in yarima fitowa tayi tabarosa yana waya takoma part d’inta,

wardrobe d’inta tabud’e tad’auko wayanta takunna cikin jin dad’i tahau saman gadonta takwanta sannan tayi dialing d’in number d’in abbah ammah har ta k’arashi ringing baiyi picking ba dan haka talalubo ta mama, tana fara ringing mama tayi picking cikin Jin dad’i zarah tagaisheta nan mama ta amsa tace d’iyata ba dai kun dawoba.
Eh mama mundawo dafatan kuna lafiya? Ya su yaya rauda? Na kira wayan abbah ammah baiyi picking ba
Murmushi mama tayi tace duk muna lafiya nima sa’a kikayi wayartana hannuna kinsan yau ake d’aura auren Aisha.

zumbur zarah tayi tatashi zaune tace yau kuma mama? Shine baku fad’amana ba.

Haba zarah ke ai mun d’auke miki zuwa tunda kinyi nauyi yanzu, kuma shi suhail ai yana sane da maganar bikkin tunda kusan kullum muna gaisawa, kima tayamu godia a wajensa dan ya turo mana gudunmawa dasu mukayi ma Aisha siyayyar kayan d’aki kedai kinyi sa’ar miji mekirki saidai muce Allah yabiyasa.

Zarah kwallah ce tacika mata ido koda taji dad’in abinda yarima yaima iyayenta saidai abun yaimata ciwo da ba’asanar da ita yau ake bikkin Aisha ba, cikin fushi tace gaskiya mama ba’a kyauta minba ace ana bikkin ‘yar uwata ammah ba wanda zai iya fad’amin.

Haba zarah kuda bakunan kiyi zamanki kawai kihuta, yanzu dai bari inje inji da bak’i munyi waya anjima,,,,mama batajira jin abinda zarah zataceba takashe wayarta.

Nan zarah takira yaya rauda waya, yaya rauda tana yin picking zarah cikin fushi tace haba yaya rauda yanzu saboda Allah kun kyauta min ace yau ake bikkin Aisha ammah banda masaniya.

dariya yaya rauda tayi tace toh sarkin tsogumi kuda baku gari taya zamu fad’a miki bayan babu waya a wajenki kuma mijinki ai ya sani tunda har gudunmawa yaturo, abbah ne yace kar yafad’a miki dan ya san halinki matsamasa zakiyi sai kunzo.

Hawaye suka fara fita daga idanun zarah cikin muryar kuka tace toh ai yanzu mundawo kuma sai nazo ko bakuso.

Dariya rauda tayi tace wannan tsakaninki da mijinki ne mudai babu ruwanmu.

Cikin jin haushi zarah takashe wayarta nan takife kanta tafara rera kuka.

 

Wajen k’arfe d’aya yarima yagama shirinsa yafito yanufi part d’in zarah a bedroom yasameta ta kife kanta, kallonta yayi yace baby bacci kike?

‘Dagowa tayi takallesa sanye yake cikin galilarsa maroon colour ya yi gwanin kyau, fuskarta a d’aure tace ina zakaje?

Da mamaki yake kallonta yace ikon Allah yau kuma tambayata ake inda zanje saikace mace?

Shuru zarah tayi tare da janye idanunta daga kallonsa cikin muryar kuka tace gaskiya baku kyauta minba wai ana bikkin Aisha ammah banda masaniya alhali kai kana sane, koda ace ba barina zakiyi injeba indai kafad’amin ko addu’a nayi musu ai yayi,,,tak’arashe maganar cikin kuka.

Takowa yarima yayi yazo kusa da ita yazauna cikin sauri zarah tajuya mashi baya.
murmushi yayi cikin rashin damuwa yace zarah kinsan dai babu yadda za’ayi mudawo jiya sannan aganki yau kinfita kuma ga ciki.

Toh ai fitar kamawa take kuma ko yayane nad’an lek’a ai yafi banjeba.

Kibari bayan bikki sai inkaiki kiyi mata wuni.

mak’e kafad’a tayi tare da k’ara sautin kukanta.

Dafe kansa yayi da hannu biyu dan babu abinda yatsana sama da jin kukanta ahankali yace toh shikenan yanzu tashi muje kilek’a da an d’aura aure zan d’aukoki mu dawo.

Juyowa tayi tana share hawayen fuskarta tace dagaske kake?

Murmushi yayi yace toh ya zanyi.

Rungumesa tayi cikin jin dad’i tace nagode sosai hearty ka gama min komai.

Janyeta yayi daga jikinsa yace yanzu dai yisauri kishirya kinsan k’arfe biyu za’a d’aura auren mik’ewa zarah tayi tahau cire kaya tace please bari ind’an watsa ruwa ba zan dad’eba.

Yanzu har sai kinyi wanka ina nan?
Turo baki tayi tace duka fa minti ukku zanyi.

Hmm toh shikenan ammah indai kika dad’e saidai kifito kitarar baninan.

Bama zan dad’eba insha Allah,,,,cikin sauri taje tashiga wanka, bata wani dad’eba tafito d’aure da towel dan tasan halin kayanta zai iya tafiya yabarta,,,d’ago kai yayi yakalleta sannan yamaida idanunsa akan wayarsa da take hannunsa yana dannawa.

Gaban dressing mirror tazauna tayi simple makeup sannan tamik’e tanufi wajen wardrobe d’inta kallon kayan da suke jikin yarima tayi tai murmushi sannan tad’auko shadda marron gown wadda tasha aiki da pink d’in zare tasaka, gaban dressing mirror tazo tamurza d’aurin kallabi sannan tad’auko veil da hand bag da takalmi duk pink colour tasaka, k’ara feshe jikinta tayi da turare sannan tayi masa gyaran murya.

juyowa yayi yakalleta nan tasakar masa murmushi, zuba mata ido yayi yana kallonta bai ko k’yaftawa, kashe masa ido d’aya tayi tare da d’aga gira tace nayi kyau ko?

Janye idanunsa yayi daga kallonta tare da mik’ewa tsaye yace muje, rik’o hannunsa zarah tayi tare da langwa6e kai tace bakace nayi kyauba.
Cize le6e yayi sannan yace ba laifi ammah da hijab kika ssnya da zakifi yin kyau.
Jin haka yasa zarah tawuce gaba gudun kar yace sai tasa hijab, murmushi yarima yayi sannan yabiyo bayanta.

Cikin motarsa suka fita, suna cikin tafiya zarah kallonsa tayi tace sunfa tashi daga wanchan gidan na mance ban tambayesu inda suka komaba.

Batare da ya kalletaba yace ba sai kin tambayesuba na san gidan abbah yaimin kwatance.

Gaban wani madaidaicin gida yai parking ganin mutanen da suke shige da fice yasa yagane nan ne gidan.

K’ik’irin bud’e k’ofa zarah take cikin zumud’i, rik’ota yarima yayi yace zan fa dawo ind’aukeki da and’aura aure.

Langwa6e kai tayi tai kalan tausayi cikin kwantar da murya tace please kabari sai dare.

Ta6e baki yarima yayi yace na dai fad’a miki.
Toh naji,,cewar zarah tare da bud’e k’ofar tafita nan kallo yadawo wajenta daman jira ake aga wanda zai fito daga motar, ratsa mutane tayi tashiga cikin gidan nan suka gaisa da mutane, yanayin tsarin gidan ya burgeta koda flat house ne med’auke da d’akuna ukku, dakyar tagano mama nan tarungumeta tana murna itama mama murna tayi sosai nan tatambayeta jikinta da mutanen gida.

Alhmdllh duk suna lafiya cewar zarah, nan tagaishe da abokan mama daganan tawuce d’ayan room d’in da taga abokan amarya suna shiga rumgumeta su yaya rauda da Aysha sukayi cike da jin dad’in ganin ‘yar uwartasu itama zarah rungumesu tayi cikin jin dad’i, nan suka baje suna hira, Aisha kamar ba ita bace amaryar dan sakin jikinta tayi sukai hira sosai da zarah saida taji ana gud’a ana shelar and’aura aure sannan tadawo hayyacinta harda d’an kukanta.

Bayan sallar la’asar akasa amarya tashirya nan zarah tazage taimata kwalliya tashiryata sosai tayi kyau sannan aka tafi da ita wajen su mama dan suyi mata nasiha, zarah komawa tayi takwanta saman gado sukacigaba da hira da yaya rauda.

wajen k’arfe biyar akace amarya tafito atafi da ita dan dama abbah ya ce dakansa zai kai d’iyarsa saisa ba wanda yasa ran tafiya.

zarah fita tayi suka gaisa da abbah nan tatarar da yarima wajensa, bayan sun gama gaisawa yarima yace tafito sutafi, ba dan ta so ba haka tashiga tayi sallama da su mama taja yaya rauda gefe tad’auko cheque d’in 1 million tabata tace taba su abbah gudunmawarta ne.

Koda suka kama hanyar gida fushi kawai take a mota dan taso yarima yabarta takai dare.

Dariya yarima yake ciki-ciki har suka isa, yana yin parking batajirasaba tashige gida.

Bayan sallar isha’i yarima kiranta yayi a waya, zarah tana kallon wayar kamar bazata d’aukaba saida takusan tsinkewa sannan tayi picking batare da tayi maganaba.

Baby please kikawo min coffee insha yunwa nakeji.
umhum kawai tace takashe wayarta.

Nan tatashi tashiga kitchen saida tasoya mashi kwai sannan tahad’a mai coffee tad’aura saman tray, komawa tayi bedroom d’inta tak’ara gyara jikinta sannan tad’aura alkyabba saman sleeping dress d’inta.

Kuyangarta d’aya taba tray d’in tad’auka nan suka nufi part d’in yarima.

Guards d’insa tun kan ta iso suka bud’e mata k’ofa nan suka russuna cikin girmamawa suka gaisheta, amsa musu zarah tayi takar6i tray d’in da yake hannun kuyangarta tashiga.

Ganin baya a parlour yasa tanufi bedroom d’insa tare da yin sallama ciki-ciki, yarima da yake zaune yana waya ganin yadda tahad’e fuska yasa yad’anyi murmushi sannan yacigaba da wayarsa.

Wucewa zarah tayi chan gefensa tad’aura saman bedside sannan tajuya zatabar d’akin.

Janyota yarima yayi tafad’o jikinsa nan yai sallama yakashe wayar tare da kallonta yace baby haka ake ba miji abu?
Fuskarta a d’aure tace toh me kakeso inyi maka bagashinan na aje makaba ni kabarni intafi.

Hmm ammah ai kinsan agajiye nake kuma ga yunwa ina ji indai kinaso insha saidai kibani dakanki,,,yak’arashe maganar tare da kashe mata ido d’aya.

Kallonsa zarah take cikin k’ulewa tace chab ashe ba yunwar kakejiba.

Shima yarima idanunsa a kan fuskarta yace indai ba zaki baniba kid’auki kayanki kiyi tafiyarki na k’oshi.

Jin haka yasa zarah tad’auko cup d’in takai masa a baki, yarima kallonta yake yadda take cika tana turo baki, hannunsa yad’aura saman cikinta yana shafa.

sharesa tayi tacigaba da bashi nan tad’ebo wainar kwai takaimasa a baki, ahankali yake ci, ta k’ule sosai ganin yadda yake ci kamar ba ya so kuma ahaka wai yunwa yakeji.

Bai wani yi cin kirkiba yajanye kansa alamun ya k’oshi.

harararsa tayi tace daman ba wata yunwa da kakeji dukafa rabin cup d’in kasha.

Toh baby naga kamar ba’aso insha saisa nahak’ura yanzu dai tashi muje toilet kiwanke hannunki.

Tashi zarah tayi sukaje toilet saida yai brush ita kuma tawanke hannunta sannan suka fito.

Suna fitowa yarima janyo zarah yayi jikinsa yace baby kayannan sunyi miki yawa bari inrage miki ko alkyabbarce.

Harararsa tayi tace ni kakyaleni tafiya zanyi.
Tallabo fuskarta yayi yace baby please yakamata fushin yak’are hakanan Indai gidane kibari insha Allahu idan kin haihu zan kaiki kinga fushin nan da kikeyi yana ta6amin zuciya nasan shima babynmu bayajin dad’in yadda mummynsa take ma dadynsa yakamata kitausayamin,,,yak’arashe maganar tare da cire mata alkyabba sannan yarik’o hannunta yace muje kiji wata magana.

Turo baki tayi tace ni nasan ba wata magana da zaka fad’amin wayau kakeson yi min, kwanciya yayi tsakiyan gadon sannan yamik’a mata hannu alamun tazo.

Rik’o hannun nasa tayi nan tahau yajanyota a jikinsa yakwantar da ita nan yashiga shafa mata baya, a kunnenta cikin wata irin murya merikitar da ita yace baby please fushin yak’are hakanan kinji?
‘Daga masa kai tayi alamun toh, nan yacigaba da shafa mata baya yana lasar kunnenta cikin wata irin siga da yasa zarah tafara sakin layi, ahankali yasalu6e mata riga.

Sanin halinta yasa yadinga binta ahankali ammah duk da haka saida tayi masa raki.

washe gari koda suka tashi yarima tarairayata yayi sosai har saida yaga gabad’aya ta safka daga fushin da take.

Bayan sungama breakfast zarah d’aid’aya tayi bisa yarima tana ta zuba masa shagwa6a akan kar yafita, kan dole yahak’ura yazauna nan sukaita soyewarsu, sai wajen azuhur sannan memartaba yakirasa yafito fada nan zarah tasamu talalla6asa ya amince akan zataje tagaishe da su ummi, nan kuyanginta suka take matabaya zuwa wajensu ummi.
Saida tafara zuwa turakarsu dada sosai dada tanuna mata kulawa, daganan tawuce wajen sultana sadiya nan ma sultana sadiya tarasa inda zata sanyata saboda farin ciki, duk nok’e-nok’en zarah saida sultana sadiya tasamu tad’an saki jiki suka yi hira, kwad’on zogale sultana sadiya tasa akayi mata nan Zarah tazauna taci sosai, tarairaya tasamu sosai ita kanta zarah tajidad’in yadda tayi mata ta dad’e a nan sannan tayi mata sallama taje wajen ummi a chan parlour tagamu da sumayya tayi matashin kai da cinyar ummi suna hira dan gabad’aya sumayya tadawo wajen ummi ammah duk da haka tana lek’awa wajen iyayenta da dada koda a yanzu ba kamar da ba sun sake mata.

Ganinta yasa sumayya tatashi zaune cikin jin kunyarta.
Zarah cike da girmamawa tagaishe da sultana bilkisu, cike da so sultana ta amsa mata tare da tambayarta jikinta da gida.
cikin jin kunya tace Alhmdllh sannan tajuyo tace Aunty sumayya ina wuni?
Amsa mata sumayya tayi batare da ta d’ago ta kalletaba saboda kunyarta da takeji.
ummi ce tace Zarah kizauna saman kujera man kin zauna k’asa.
Ummi nan ma ya yi nafi jin dad’in k’asan…tafad’i hakan cikin jin nauyinta.
Murmushi sultana bilkisu tayi tace toh lafiya lau, ya gida da hidima? Ashe bikkin k’anwarki akayi wlh bamusaniba ai da mun lek’a.
Eh ummi daman saida mama tayi min magana tace lokacin taji ance memartaba baida lafiya saisa bata aiko maku da invitation card ba.
ayyyah Allah sarki toh Allah yabada zaman lafiya.
ameen ummi.

nan ummi tak’walama wata kuyangarta kira tace akawo ma Zarah kayan motsa baki.
Duk’ar da kanta zarah tayi tace ummi subarsa kawai ak’oshe nake.
a’a zarah baridai sukawo miki.
kafin kace mi nan aka cika gaban zarah da kayan marmari da abinci, mik’ewa sultana bilkisu tayi tace ina zuwa nan tawuce tashige bedroom d’inta.

sumayya kallon zarah tayi a karo na biyu ahankali tace zarah zan k’ara rok’onki akan abubuwan da nayi miki dan Allah kiyi hak’uri.
kallonta zarah tayi cike da tausanta tace wlh Aunty sumayya ko kad’an ban rik’ekiba kuma ai komai ya wuce please kidaina tunawa.
k’wallah ce tacika ma sumayya ido tace hmm zarah taya kike tunani zan iya mance cin mutuncin da nayi muku, wane irin makircine banyiba akanki ammah daga k’arshe kinga yadda rayuwa takoma min nayi wasa da damana ni kaina ina jin haushin wannan halin da najefa kaina.

girgiza kai zarah tayi tace Aunty sumayya kidaina cewa haka kema fa wasu abubuwan kowa yasan ba laifinki bane, kuma ko ba hakaba ni wlh tuni na yafe miki.

Share k’wallar idanunta tayi tace nagode sosai zarah Allah yasaka da alkhairi, Allah yasafkeki lafiya.
Nan suka d’an ta6a hira kad’an-kad’an ganin marece ya yi yasa taje tayi ma ummi sallama tafito sukai sallama da sumayya tawuce part d’inta.

cike da sha’awa sumayya tabita da kallo tanaji ina ma ace itace da cikin hawayene suka shiga gangaro mata alokacin da tatuno zuwa hospital d’in da sukayi da ummi aka tabbatar mata bazata ta6a haihuwaba saboda pills d’in da tasha da injections d’in da take na tsawon lokaci sun6ata mata mahaifa, kukane yaso yakubce mata cikin sauri tatashi tashige room d’inta tafad’a saman gado saida tasha kukanta me isarta sannan taje tawanke fuskarta tare da d’auro alwallah, nan tashimfid’a darduma tad’auko alk’ur’aninta takaranta.

Zarah koda takoma part d’inta a parlour tayada zango nan kuyanginta suka zagayeta suna mata hira, haka tabiye musu har aka kira sallah sannan tamik’e taje tayi alwallah tai sallah.

 

Haka rayuwa tacigaba da tafiya yarima yana tafiyar da aikinsa, a gefe guda kuma ga mulki dan memartaba yanzu bai cika bari yai nisa da shi ba dan a kullum cewa yake nan ba da dad’ewaba ko rai yayi halinsa kokuma insafka daga kan karagar kahau dan gabad’aya yanzu shekaru sunja sosai,,,a duk lokacin da yake maganar yarima yanaji babu dad’i a ransa, shi kansa waziri idan yaji memartaba yai furucin cewa yake a duk lokacin da mulkinka yak’are toh nima nawa ya k’are dan haka dole waziri mejiran gado shima yadinga yawan zaman fada, haka ake matsama yarima da shaheed suna zaman fada sosai.

Zarah sosai take samun kulawa daga wajen dangin yarima, dan sultana sadiya da sultana bilkisu kullum sai sun kirata a waya sun tambayi lafiyarta dan wani lokacinma sultana sadiya da kanta take zuwa tadubata takawo mata abubuwan da tasan meciki tana buk’atar ci dan Zarah kulawa take samu sosai a wajenta kamar yadda zata kula da sumayya.

A 6angaren Dada ma tana aikowa aduba mata lafiyar Zarah kuma tanayi mata aike da kwad’on ganye iri-iri.

su kansu su rahama yanzu wani irin kulawa sukeba zarah dan nan da nan zarah tasaba da rahama.

Yanzu sumayya danginta sun sake suna nuna mata kulawa sosai shima saida sultan ahmad yak’ara tunatar da su akan batada laifi fa sosai tunda da sa hannun zinat take wasu abubuwan, nan suka fara janta a jiki ammah duk da haka sumayya tayi sanyi sosai dan yanzu batada yawan magana.

 

*BAYAN WATA ‘DAYA*

Sumayya ce tafito daga room d’inta dasafe da mamakinta taga su ummi suna ta zirga-zirga da shirye-shirye cike da girmamawa tagaishe da ummi, fuskar ummi a sake ta amsa mata.
murmushi sumayya tayi tace ummi bak’i zamuyine naga kuna ta shirye-shirye?
Kedai bari sumayya wlh wani d’an yayanane zaizo daga agadaz zaikawo min ziyara dan rabonsa da garin nan tun yana k’arami lokacin da nahaifi husna akazo da shi.

Murmushi sumayya tayi tace Allah sarki Allah yakawosa lafiya.
ameen daughter yanzu dai je kiyi breakfast muma ai mungama komai dan ina sa ran nan da awa biyu zai safka.

Bayan ta gama breakfast d’inta zaune take ita kad’ai a parlour hannunta rik’e da hisnul muslim tana dubawa, sallamar da akayine yasa tad’ago kai takallesa tare da amsa masa sallamar.
Wani matashi ne wanda ak’allah bazai gaza shekaru talatin da shidda ba sanye yake cikin manyan kaya yanayin kamaninsa yasa tagane shine wanda ummi tace mata zaizo, ido yazuba mata yana kallonta, ganin kallon ba mai k’arewa bane yasa tagaisheshi.
tattare nutsuwarsa yayi sannan ya amsa tare da tambayarta ya gida?
Lafiya lou sumayya tace sannan tamik’e zata wuce room d’inta.

Gyaran murya yayi yace am ummi fa tana nan?
Batare da ta juyoba tace eh bismillah kazauna bari inmata magana, tana fad’in haka tawuce tanufi part d’in ummi tasanar da ita zuwan bak’on sannan tafito tawuce room d’inta.

ummi koda tafito cikin jin dad’i tace oyoyo yau ga salim mutanen agadaz dakansa ya kawo mana ziyara.

Murmumushi wanda takira da salim yayi tare da d’an zamowa daga kujerar da yake zaune yace ummi ina wuni.

Lafiya lou salim ya gida da mutanen gidan dafatan kowa yana lafiya.
lafiya lou ummi.
masha Allah toh ya k’arin hak’uri? Ayi dai hak’uri ban samu nadawo ba bayan sadakar ukku, ni ina ji tun ma lokacin rabona da agadaz.
Alhmdllh ummi ai bakomai.
masha Allah toh Allah yajik’anta, Allah sarki khadija mutuniyar kirki Allah dai yasa ta huta, ina yaran naku ina fatan suna lafiya?
Duk suna lafiya.
toh masha Allah, Allah yaraya mana su,

Ummi kira tashiga k’walah ma sumayya, fitowa tayi sanye da hijabi a jikinta tace ummi gani.
murmushi ummi tayi tace sumayya wannan shine bak’on nawa matsayin yaya yake a wajen su yarima kije kisa su kuyanga zinnira sushurya masa abinci.
Kallon bak’on tayi da a yanzu ma yatsareta da ido ahankali tace sannu da zuwa ina wuni?
Murmushi yayi yace lafiya lou ya gida?
Batare da ta bashi amsaba tawuce taje tabada umurni akawo masa abinci daganan tawuce wajen dada.

 

Cika masa gabansa akayi da abinci iri-iri ci yake ammah gabad’aya hankalinsa yana ga k’ofa.

Bayan ya gama kallon ummi yayi yace ummi wai ina prince? Kinsan bana k’asar akayi bikkinsu shi da rahama.

Murmushi ummi tayi tace duk suna nan lafiya lou yanzu ma zaka ganshi dan na fad’a masa zakazo, ina fata dai ka dawo k’asarka ta haihuwa kenan bazaka koma india ba, haba salim mutuwa ai bata wuce kowaba yakamata ace zuwa yanzu ka cire khadija aranka tunda wanda yabaka ya kar6i kayansa shekara biyu da wani abu fa kenan yanzu, kadaure kayi aure karik’e ‘ya’yanka ukku wajenka suma sutaso hannun iyayensu, dan su yaya munir hankalinsu ba a kwance yakeba basuda buri dayawuce suga ka saki ranka ka canza aure, d’azun koda yakirani a waya cewa yayi ink’ara kwatanta maka, kaifa salim ba yaro bane kai yakamata kakwatanta ma wasu.

Ajiyar zuciya salim yasafke yace insha Allahu ummi zanyi aure dan a lokaci guda wata ta fara canza min tunani.

Cikin jin dad’i ummi tace masha Allah wace me sa’a ce haka?

Dariya salim yayi yace ummi kuma a wannan garin naku daga zuwana yau d’innan.
Gyara zama ummi tayi tace salim fad’amin inda take insha Allahu zanje dakaina insami iyayenta.

Dariya salim yayi yace ummi kima kwantar da hankalinki ba wata bare bace nidai fatana Allah yasa ba matar aure bace.
Toh Alhmdllh tunda ‘yar gida ce wacece ita?

Duk’ar da kansa yayi alamun jin kunya sannan yace ummi ba wata bace face wadda nagani nan wlh ummi tunda nashigo taburgeni Allah dai yasa batada aure.

Murmushin jin dad’i ummi tayi tace in na fahimceka sumayya kenan kake nufi?
Eh ummi ita indai zaku bani ita toh wlh na amince zanyi aure.

Cikin jin dad’i ummi tace toh sumayya dai ta ta6a aure ammah a yanzu basu tare sa mijin nata Indai har kana sonta tsakani ga Allah toh nikuma insha Allahu zan sameta muyi magana.

Shima Cikin jin dad’i yace wlh ummi ina sonta kuma zan kular muku da ita, da gobe naso inkoma ammah a yanzu na canza ra’ayi har sai ta amince sannan zan bar garin nan.

Jinjina kai ummi tayi alamun gamsuwa sannan tace toh Allah yashige mana gaba.
Salim yace Ameen.

Koda yarima yashigo zama yayi sukasha fira cikin jin dad’in ganin d’an uwannasa kuma babban yaya dan dama tun yana karatu a india ummi tahad’ashi da shi.
Yarima fita sukayi tare suka zagaya gari yanuna masa wurare sai dare suka dawo gida.

 

Bayan sallar isha’i sumayya zaune take ta gama shirin bacci tana duba wasu addu’o’i.
Ummice taturo k’ofan tashigo tare da yin sallama.

Murmushi sumayya tayi ta amsa mata tare da fad’in sannu da zuwa ummi.

Yauwa daughter nan tazauna bakin gadon tare da kallon sumayya tace daughter daman bakiyi bacci ba?
Eh ummi ammah yanzu nake shirin yi.
Ohk ya yi kyau ammah inaso kitaimaka kiban aron hankalinki zamu d’anyi magana, gyara zamanta sumayya tayi tace toh ummi.

Ummi ma fuskantarta tayi tace sumayya aganina yakamata ace wannan lokacin kinyi aure indai kina da wanda kikeso yake sonki saidai idan babune shine sai kizauna har sai Allah ya kawo.
Murmushi sumayya tayi cikin jin kunya sannan tace ummi ai har yanzu babu wanda mukeson juna.
Murmushi itama ummi tayi sannan tace toh sumayya Allah yakawo, sai kuma tayi shuru kamar metunani sai chan tace am yauwa sumayya d’azun salim ya tuntu6eni akan maganarki ya nuna min yana sonki sosai indai zaki bashi dama sai yagabatar miki da kansa.

Gaban sumayya saida yafad’i cikin damuwa tace ummi ya za’ayi in amince masa daga ganinsa ba irina bane ko kin mance abubuwan da na aikata kuma fa doctor ya ce ba zan ta6a haihuwa ba taya kike tunani zai iya aurena,,,,tak’arashe maganar hawaye suna zuba daga idanunta.

Ummi cike da tausayinta tarungumota jikinta tace sumayya kidaina cewa haka tunda kin tuba ai Allahu gafururrahim ne, sannan da kike maganar haihuwa kikwantar da hankalinki nasan salim Indai yana sonki toh zai iya aurenki ahaka dan shima yana da yara ukku marayu da mahaifiyarsu ta mutu tabari shekara biyu da wani abu kenan kizauna kiyi tunani ko ma ince zuwa gobe kibashi dama kuhad’u kuyi magana dan jibi yakeson barin garin, ammah Indai baiyi mikiba kar kiji komai kisanar da ni kinji ko?

‘Daga kai sumayya tayi nan ummi tamik’e tace kikwanta kiyi bacci kar kisa damuwa a ranki kinji ko?
Ahankali tace toh ummi.
Murmushi ummi tayi tace sai dasafe dota.

Bayan ummi ta fita sumayya zama tayi taita tunani akan maganar ummi ta dad’e ahaka sannan dagabaya takwanta tai bacci.

Wanshe kare wajen 11am bayan ta gama breakfast fitowa tayi parlour dan tayi kallo, zaune ta tadda mutum shi kad’ai yana kallo, ganinta yasa salim yazuba mata ido, sumayya bataji dad’in had’uwarsuba ahankali tace ina kwana? Amsa mata yayi fuskarsa d’auke da fara’a.
Juyawa tayi zata koma room d’inta nan taji muryarsa ya ce please sumayya in ba damuwa kiban dama yanzu muyi magana.

Tsaye tayi tai shuru batare da ta juyoba, ahankali yak’ara cewa please.

Juyowa tayi batare da tayi magana ba tadawo tazauna bisa d’aya daga cikin kujerun da suke parlourn.
Salim tashi yayi yakoma bisa kujerar da take saitinta yazauna, kallonta yayi da take wasa da yatsun hannunta yai murmushi sannan yace hajiya sumayya ina fata dai ummi ta yi miki bayani akan komai.

Shuru sumayya tayi, ganin haka yasa yace toh ammah duk da haka bari ink’ara miki bayani da kaina agaskiya sumayya tunda naganki jiya naji k’aunarki ta shiga raina, ina sonki tsakani ga Allah idan kin amince sai kiban dama in nuna miki irin son da nake miki dan ni har ga Allah aurenki nakeson yi.
Batare da ta d’ago kantaba tace ummi bata fad’a maka na ta6a aureba?
Kar kidamu indai wannan ne toh ba matsala dan nima na ta6a aure shekara tara kenan rasuwa matata khadija tayi muna da yara ukku, Al-ameen shine babba shekararsa takwas sai Amina shekara shidda sai autansu Sadiq shekara ukku, indai har kin amince zaki zauna da marayu kikasance uwa agaresu toh insha Allahu bazaki ta6a samun matsala daga garemuba zamu zauna da ke tsakani ga Allah, dan ni tun mutuwar matata ban ta6a tunanin zan k’ara son wata maceba ammah sai gashi cikin k’anganin lokaci na fad’a tarkon sonki.

Cikin tausayi sumayya tace Allah sarki Allah yajik’anta su kuma Allah yaraya su,
Ameen nagode saura inji daga gareki.
Sai a lokacin tad’ago kai takallesa tace ammah fa ni bana haihuwa zaka iya zama da ni ahaka.
Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace kar kidamu sumayya ni naji na amince ina sonki kuma muna da su Sadiq gasunan zan mallaka miki su sugama ‘ya’yanki halak malak.

Sumayya har cikin ranta taji dad’in maganar da yayi ko bakomai itama yanzu zata fara sabuwar rayuwa….murmushi tayi masa a karo na farko sannan tace kabani lokaci zanyi tunani.

Marairaicewa yayi yace please kitaimaka kizartas da hukunci yau dan gobe nakeson barin garin saboda wani aiki da nabaro kinsan ‘yan kasuwa.

Shuru tayi nad’an lokaci sannan tace shikenan zuwa anjima zaka ji ni.
Murmushin Jin dad’i yayi yace toh Allah yasa inji alkhairi.
Ameen tace tare da mik’ewa zata wuce d’akinta har ta fara tafiya yakira sunanta, a nutse tajuyo takallesa,
Marairaicewa yayi yace please ataimaka atausaya min kar ayanke min hukuncin da ba zan iya d’aukaba.
Yanayin yadda yai maganar ya bata dariya nan tajuya tashige d’akinta.

A ranar taje tasamu ummanta tafad’a mata maganar da sukayi da salim, sosai sultana sadiya tanuna farin cikinta tace na tabbata sultana bilkisu bazata ta6a za6a miki abinda zai cutar da keba koda salim d’an uwantane kuma jiya sun shigo tare da yarima mungaisa na yaba da hankalinsa, Indai ya yi miki toh ki amince ki auresa.
Cike da gamsuwa da maganar mahaifiyartata tace toh ummah nagode sosai Allah yaza6a abinda zaifi zama Alkhairi
Ameen sultana sadiya tace nan suka d’an ta6a hira da d’iyartata sai bayan azuhur sannan sumayya takoma part d’in ummi.

Bayan sallar la’asar sumayya ta shaida ma salim ta amince sosai yanuna farin cikinsa tare da yi mata godia, nan suka zauna sukasha hira sama-sama dan rabin hirar duk shi yakeyinta, musanyar number waya sukayi.

Koda akayi sallar isha’i haka yakirata sukasha hira saida yasan yadda yayi tad’an saki jikinta da shi har wajen k’arfe goma na dare suna tare.
Ummi taji dad’i sosai da taga sun amince ma juna.

Hatta memartaba, dada, sultan abbas, sultan ahmad aranar sukasan da maganar salim nan sukayi musu fatan alkhairi.

Washe gari saida suka k’ara gaisawa sosai da sumayya sannan yai musu sallama yakoma tare da yi mata alk’awali zai dawo ba da dad’ewaba, a mota koda yarima zai kaisa airport labarin sumayya kawai salim yake bashi shidai yarima saidai yayi murmushi nan yai musu fatan alkhairi shima.

Tun daga ranar soyayya mai k’arfi ta k’ullu tsakanin sumayya da salim dan ko da yakoma saida yasanar da danginsa nan suma sukayi murna tare da yi masa fatan alkhairi.
Kusan kullum sai ya bata yaransa a waya sunsha hira sosai da sumayya, ita kanta har mamakin kanta take dan bata ta6a tunani zata iya son waniba bayan yarima ammah sai gashi lokaci guda salim ya canzata.

_________________

A lokacin da cikin zarah yacika wata tara cif kulawa sosai take samu a kowane 6angare yarima ko bayaso yana nisa da ita ko da ace yana wajen aiki toh suna manne da juna a waya, bayan 30 minutes batare da ya kirata ya tambayi lafiyartaba.
Kuyanginta ma basu yin nisa da ita indai yarima baya nan dan idan yadawo yaganta ita kad’ai fad’a yake musu sosai, saidai idan bacci zatayi shine take sallamarsu takwanta.

_*BAYAN SATI BIYU*_

Zarah zaune take gefen yarima inda gabanta plate d’in apple ne aje ammah ba ci takeba kad’an-kad’an ta cije le6e, kallon yarima tayi da yake cike wasu files, rik’o file’s d’in tayi nan yad’ago kai yakalleta, murmushi tasakar masa tace hearty ka aje hakanan kahuta man tun d’azun fa kaketa abu d’aya kaga dare ya yi kazo muje mukwanta zuwa gobe sai ka ida..

Shima murmushin yamaida mata sannan yace sorry baby ai na kusan gamawa gobe nakeso inje inyi submitting d’insu kiban minti goma kinji?
Kwantar da kanta tayi a kafad’ansa tace toh shikenan hearty ammah minti goma kawai nabaka,
Ohk angama ranki yadad’e.

Bayan ya gama kallonta yayi yace baby muje mukwanta.
Mak’e kafad’a tayi tace ni saidai kad’aukeni mutafi.

Hancinta yaja yace shikenan baby as you wish.

Koda sukaje bedroom Kwantar da ita yayi sannan shima yakwanta, juyawa tayi chan gefen tana murmushi bata ankaraba sai ji tayi ya rungumota ta baya, cikin kunnenta ahankali yarad’a mata baby yau guduna akeyi?
Juyowa tayi takallesa tare da marairaicewa tace bahaka bane hearty wlh ji na nake yau duk wata iri,
Kwantar da kansa yayi a k’irjinta yace baby daman tun d’azun da naga yanayinki nace bakida lafiya ammah kikace lafiyarki lau.
Shafa sumar kansa tayi tace ni lafiya ta lau hearty.
Toh bari ingani idan kina da lafiyar ganin ya d’age mata riga yasa tayi saurin cewa dan Allah kabarni kar kayimin komai.
Murmushi yayi yace toh sarkin tsoro ni ba abinda zanyi miki lafiyar babyna kawai zan duba.
Nan yashiga shafa cikinta tamaida idanunta talumshe tana jin sauk’in ciwon da takeji daman tana daurewane dan kar ta tayar mashi da hankali, ahaka bacci medad’i yai awon gaba da ita.

Yarima ma gefenta yadawo yakwanta tare da rungumota jikinsa.

Cikin baccin ne taji kamar wani abu yana tsikararta firgit tayi tafarka tana jin wani irin ciwo tun daga cikinta zuwa mararta, ahankali tazame jikinta tasafko k’asa tazauna tana murk’ususu nan da nan tafita hayacinta sai hawaye, jin ciwon ba mek’arewa bane yasa tafara kiran sunan Yarima da yake baccinsa.

Cikin bacci yaji ana kiransa ahankali yabud’e idanunsa ganin zarah yayi a k’asa tana ta murk’ususu cikin sauri yasafko daga saman gadon yazo inda take tare da rik’ota cike da tashin hankali yace zarah lafiya?

Hawaye suna fita daga idanunta tajawo hannunsa tad’aura saman mararta, dak’yar tabud’e baki tace ciwo.
Cikin tashin hankali yace bari inzo muje hospital ina tunani haihuwar ce,,,tashi yayi yacanza kaya sannan yad’auko mata zane da hijab yasaka mata, jakkar da suka tanada ta haihuwa yad’auko cikin sauri yax’auko key d’in motarsa sannan yad’auki zarah yafito.

Guards d’insa k’arfan jakkar da take hannunsa sukayi nan suka take masa baya har wajen mota, a back sit yasakata sannan yabud’e mazaunin driver yashiga, kallon guards d”insa yayi yace kar su biyosa, wuta yaba motar tun kan ya isa gate yafara horn cikin sauri megadi yazo yabud’e masa yafita daga masarautar.

Gudu yake sosai cike da tashin hankali ga zarah da take kwance baya tana ta kuka da salati, cikin k’ank’anin lokaci ya isa hospital d’insa, tun kan ya isa yakirasu yasanar da su zuwansa dan haka suna isa yatarar da su suna jiransa nan aka fito da zarah cikin sauri aka turata zuwa labour room.

Dr leemah ce tatsaya kanta, yarima ko gefenta yatsaya yana taimaka mata cike da tausayin matar tasa, zarah ta sha wahala dan gabad’aya gidansu babu sunan wanda bata kiraba, yarima waje biyu yaraba hankalinsa da wajen lallashin zarah sai wajen ceto babynsa, cikin ikon Allah batafi minti sha biyar tana nak’uda ba tahaifo shantalelen d’anta, Dr leemah ce tayi saurin d’aukesa tamik’a ma wata nurse dan tagyarasa, inda yarima yakoma wajen zarah yana mata sannu batare da ya ga abinda aka haifar masaba.

Hawaye suna fita daga idanunta tana maida numfashi sama-sama ahaka dr leemah tagyarata.

Koda nurse d’in tagyara yaron Dr leemah tafara kar6ansa tana yaba kyaunsa tana cewa wannan prince ne sak yabiyo.

Sai a lokacin yarima yamik’a hannu yakar6esa murmushin jin dad’i yayi tare da furta Alhmdllh, nan yai masa addu’a da kiran sallah, zuba ma yaron ido yayi cike da so, zarah ahankali talek’o yaron da yake hannun yarima saida gabanta yafad’i batasan lokacin da ta furta masha Allah ba dan yaron kyakkyawane kamar daddynsa, kallonta yarima yayi yana murmushi yace kinga kyautan da ubangiji yabamu ko?

Itama murmushin tayi tace masha Allah yanzu nan ni na haifesa?

Yanayin yadda tayi maganar ta ba yarima dariya, murmushi yayi yace eh man kece, ammah ai da ni yake kama.

Itama murmushin tayi cikin jin dad’i tace saidai kai d’in dai.

Nan su Dr leemah suka taimaka mata tatashi tayi wanka, a cikin daren yarima yakira sultana bilkisu yashaida mata, da har ta ce gasunan zuwa asibitin nan yashaida mata ai ta haihu cikin k’oshin lafiya yanzu dan dare yayi ammah tun da asuba zasu dawo.

Sosai ummi tanuna farin cikinta tare da addu’an Allah yaraya.

A nan hospital d’in su yarima suka kwana, tun asubar fari sultana bilkisu takira sultana sadiya tashaida mata sosai sultana sadiya tanuna farin cikinta inda tasa ma’aikatanta su d’aura ruwan wanka kafin su zarah su iso.

Dada ma koda taji labari murna tayi sosai har da hawayenta zataga jinin suhail d’inta shi kansa memartaba ya nuna farin cikinsa sosai,
Kan kacemi gabad’aya masarautar ta san da maganar haihuwar zarah.
gabad’aya su dada suka taru bayan sunyi sallar asuba suna jiran dawowarsu yarima cike da tsaguwa da son ganin babyn.

 

_Comments_
*Nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_
[5/3, 7:55 PM] Sis Naj Atu:

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Sak’on gaisuwa da jinjinar bangirma agareku masoyana, nagode sosai da soyayyarku agareni, hak’ik’a kun nuna min kulawa sosai banda abinda zance maku saidai addu’a Allah yasaka da alkhairi Allah yabar k’auna._

_*Yayata ko ma ince Auntyna jiddah mumyn zarah bazan ta6a mancewa da keba a rayuwata ke d’in tadabance saidai ince Allah yabar wannan zumuncin namu*_

_~M.B.A nd Mu’az banda abinda zance maku saida addu’an fatan alkhairi~_

“`My dala dole ingaisheki kuma in jinjina miki da namijin k’ok’arin da kike Allah yabar k’auna“`

_Intelligent Writer’s ni kaina bansan abinda zan ce ba akan k’warin guiwar da kuke bani saidai ince Allah yak’ara d’aukaka mana k’ungiyarmu ya albarkaceta, Allah yak’ara had”a kanmu gabad’ayanku na gaisheku, Aunty maryam Allah yaraya mana newborn baby muhammad_

 

_*S.A.N 4EVER na jinjina maku tagwaye ukku ku d’in na daban ne acikin zuciyata*_

Back to top button