Hausa NovelsRainon Soja Hausa Novel

Rainon Soja 10

Sponsored Links

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*

 

Free page 10

https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
YouTube link ku shiga kuyi mana Subscribe don samun audio novel na Mamanteddy ….
________________________
MAMAN TEDDY
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
Yar maula
Kwaryar sama
The virgin maid
Gidan Ƙwarata
The Sexy Boss
Yar aiki
Bafullatanan Ruga
X world duniyar shahara
Mr romantic
Dijama
Kwarton manya
Yar tsakar gida
Zuma da maɗaci
Sadaka yalla
Yar waye
Gidan zaurawa
Taɓarah
Fƴaɗe

A PAGE 12 FREE PAGE ZAI ƘARE ✍KU FARA PAYMENT https://chat.whatsapp.com/JLMzlJU65ZJ61TOzh7JHWY .
________________________
. Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500
Vip group ₦1000
SPC payment ₦1500
Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f free page ya fara nisa ya ku hanzarta wurin biyan naki ana ta payment.

•••••

Ganar Aliyu fa baya motsawa Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…..Cak General Saleh yayi yana dakatawa tare da jan wani irin numfashi mai nauyin fita , ji yayi kan sa na sara masa yana ganin duhuwa. Da gudu Mami da Khaleel suka isa ga inda Ali Haidar yake babu alamun numfashi kan sa na ambaliyyar fitar jini kaman a ƙwata. Fashewa da kuka Mami tayi yayin da Khalil yakao hannun sa yana Girgiza Aliyu tare da kiran sunan sa cikin sauri da Muryar tashin hankali “Aliyu Ali ….Aliyu….”! Saurin sauke Ma’eesha Khalil yayi yana kwantar da ita bisa Gadon Mami,don a yanzu duka bata kan ta suke ba ,ta kan ɗan su suke yi . Ita kuwa Jidderh saboda tsaban ruɗewa da kuka ta fita daga Bedroom ɗin tana isa Falon Mami tare da Ɗaukar Wayar da suke kiran Family dashi. Cike da Rawar Muryar tana makerkyata da shashashƙa numfashin ta tamkar zai ɗauke ta fara kiran sunan “Hajiya”….Hajiyar mu kizo Daddy ya kashe Ya Haidar, Hajiya don Allah kizo……..Sakin wayar tayi sakamakon Ihun Uwani da taji tana furta “ Hasbunallahu wani’imal wakeel Innalillahi wa’inna ilaihir raji’una….Wani irin duba Jidder tayi mata kana ta fara zabga mata harara tare da cewa “ Meye haɗin ki da mu ,ki tsaya a matsayin ki na ƴar Aiki , kina wani salati na munafurci bayan nasan yau Ya Haidar ya mutu sai kinyi farin ciki, don ki fi wahala dashi har matsa masa jikin da kike yi ai nasan yau ya mutu murna zakiyi Kice kin huta , to ba zai mutu ba zai rayu banza talaka kawai mtswwwww…” .

Kasa magana Uwani tayi ita dai sai hawaye dake tsiyaya mata , Tabbas Ali baya da kirki amma kuma yana da shuga ran mutane masumman masu hidimta masa irin su Uwani da Babba. Sunan babba shi yake bashi horo duk idan yayi laifi amma bashi da Wanda yake So a kaf yaran General Saleh Yelwa kaman Haidar, Matsalar sa ɗaya kafiya da faɗa saurin zuciya da fushi ga baƙar Miskilanci wannan sune halayyar Ali haidar. Shi kuma Khalil baya da Wannan sai dai shi Aƙwai shi da wulaƙanta mutum , ita kuma jidderh akan ta gadaran arziƙi ya ƙare da nuna asali da banbancin samu da Rashi ,wato mai kuɗi da Talaka ”.

**
Ku fara basa Ruwa .” Muryar Genar ya katse Mami da Khalil dake shirin ɗaukar Ali don su wuce dashi Asibiti . Ɗauke kai Mami tayi cike da nuna fushi bata tanka na Daddy ba , Sai Khalil ne yasa hannu yana Amsan ruwan Tare da kaiwa bakin Aliyu yana shafa ma fuskar sa na hannun sa . Ƙuuffull² tarin ma’eesha ya katse su , inda sai a Sannan mami ta tuna da Yarinyar . Kallon inda Ma’eesha ke motsawa tayi kana ta kalli Daddy da Khalil sai jidderh dake shigowa itama tana saurin ƙarikowa inda Suke.

Da sauri Mami ta miƙe tana Nufar Bed ɗin tare da kai hannu tana ɗago Ma’eesha, tana mai takowa zuwa inda Ali yake a ƙwance . Rigimar ma’eesha ne ya fara dawo dashi hayyacin sa. A hankali yake jan numfashi tare da saukewa kana ya ware Lulun idanun sa yana zuba su a bisa fuskar Mami dake riƙe da Ma’eesha . Hawaye duk ya ɓata fuskar ta , dukan su cikin tashin hankali suke. Kallon mal yayi yana sakin murmushin nan nasa da ba kowa yake samun damar yayi masa shi ba. Taho ma’eesha..”! Ya furta yana kai hannun sa a gajiye , Saurin kallon sa Mami tayi kana tace “ Baka da lafiyar ɗaukar ta , Khalil taimaka masa mu tafi Asibiti yanzu”.

Hannu Khalil yakai yana ƙoƙarin riƙon sa ,amma sai Ali ya zame jikin sa yana Mai cewa “ Mami bana Wani ciwo , idan ma ina wani ciwo to na warke tunda ga buɗe idanuna da nayi naga Ma’eesha a hannun ki ” . Daddy Don Allah kuyi hakuri ku bar Ma’eesha ta rayu damu ,Bata da kowa muyi wannan jahadin ladar mu bar shi gurin ALLAH .

A’a Ya Haidar ba zata zauna damu ba , kalli kaga fa sanadin ta Daddy yayi maka dukan da bai taɓa yi maka irin shi ba. Ko wannan zaka fahimci ita ba komai bace a rayuwar ka fache baƙar ƙaddara.

Keee yi mun shiru !!!

Mami ta katse ta cike da nuna ɓacin ranta tana Rungume ma’eesha tare da Girgiza ta bisa kafaɗan ta . Cike da isssa irin na Mami ta fara da cewa “ Banji tausayin wannan yarinyar ba sai a yau ɗin nan , tabbas ita ba baƙar ƙaddara Bace a rayuwar haidar, tun da a yau ya kalle mu yana bamu haƙuri bayan Haidar bai taɓa sauyawa daga ra’ayin sa ba ko ya durƙusa don Bama wani haƙuri baya wannan bai taɓa a rayuwa ,amma saboda ma’eesha kalli kuga jini ke zuba jikin sa , hawaye ke ɗiga daga idanun sa . Tabbas ita alheri ce ba’a rayuwar sa kaɗai ba Rayuwar mu duka . Na shirya Ni zan raini ma’eesha tamkar uwa , daga yau bana son ƙara jin Furucin ɗaya daga cikin ku kan cewa “ Ma’eesha ba’a gidan nan take ba , Bani na haife ta ba ko Daddy , yanda muka haife ku ina so ku sa a ranku itama mu muka haife ta . It’s impossible Mami…Dad kana jin mene Mami ke cewa ? . Ina wannan ba yar gidan nan bace….shiiiiiii ya isa Jidder.!

Muryar Daddy ya katse su inda yake rage Tsawon sa tare da dafa Aliyu , ƙurrrr yayi ma yaron nasa kammin ya Girgiza kai yana Cewa “ Haidar bana maka hukunci don ka raini ma’eesha bane ba ,a’a taurin kan da ka nuna mana ne , Amma daga yau ka sani ma’eesha zata rayu dani a matsayin mahaifi haka mami Khalil ina so ko bayan raina ku kula da yarinyar sosai tamkar yanda zaku kula Jidder. Ali ina ka mance da ma’eesha ka maida hankalin ka akan karatu , yanzu mune nauyin ma’eesha yake a kan mu . Fatan ka fahimce mu ….?

Gyaɗa kan sa Haidar yayi yana juyawa tare da kallon inda Ma’eesha take , Dad na gode Mami…. Girgiza kai Mami tayi kana tace “ Taso muje ka gasa jikin ka . A’a yanzu xanyi waya da Doctor Isma’il zai taho sai ya duba shi. Daddy yayi Maganan yana kallon mami….Ina Salihu yake??? Salihu ….yanzu Sojan naka ne ta banza zai saka kashe mun Miji? Zaka kashe Ali saboda zafin rai na wofi…? Muryar Hajiya Mahaifiyar General Saleh Yelwa ya katse su da take sababi tun daga falo . Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un waya kira Hajiya? . Mami ta furta tana kallon su duka . Kana ta mike cikin sauri tana cewa “ Muje muyi mata bayani nasan itama zata fahimce mu . Mami kuje zan shiga Privacy idan na fito ma gaisa da ita saboda bana sonta…..Shiru yayi don halayyar Ali ne fara magana sai kuma yayi shiru , kuma idan yayi hakan baya taɓa Cigaba da Maganan sai dai kai ke saurara kayi Haƙuri.

Okay mami ta furta Daddy ne yakai hannun sa yana Amsan ma’eesha dai dai Ali nace wa “ Bani muyi wanka tare ”. A’a ai yanzu ma’eesha a hannu na take duk wasu responsibilities dake tsakanin uwa da ƴa nice maiyi mata su . Kai dai shiga ka fito .

Ficewa duka suka yi daga Bedroom din banda Ali da ya motsa daƙyar yana nufar Toilet din Mami ”.

*After some years….. *
Taro ne ya taru hall babba na iya ɗaliban secondary school da primary a haɗe duba ga karshen zangon da ake ciki . A hankali Muryar ɗaya daga cikin malaman wannan makaranta ya fara magana da jawabi kamar haka “ ɗaliban da tafi kowa hazaƙa a ɓangaren Primary makin ta yafi na kowa wannan ƙyautar nata ce , itace Aisha Saleh Yelwa….Ihun yara da manya kaji ya cika hall ɗin suna kiran sunan ma’eesha…wacce a yanzu take ajin ƙarshe na primary wato Primary 5. Cikin wani irin sauri ta miƙe da gani kasan ta samu training da Raino cike da confidence wanda wannan ɗabi’ar nata ta same shi ne a hannun Uncle Aliyu. Fara’ar n ta shi yake ƙara mata masoya cike da Ladabi ta isa ga Uncle Anabeth. Tafi aƙa ƙara sakawa kamin ya miƙa mata ƙyautar ta tare da sakamakon ta . A hankali ta amsa Mick ɗin tana washe baki fara’ar ta na ninnkuwa dimples din ta na loɓawa , kyaƙyƙyawar yarinya tun a yanzu ina ga ƴammatanci kuma. Hular kan ta ta gyara zaman sa na sanyi irin na rigar jikin ta duka na makarantar ne. Cikin Sanyayyar zaƙakƙiyar Muryar ta tana dariya ta furta “ Hello good morning everyone, nice ma’eesha Saleh Yelwa, ina godiya sosai da Wannan babban ƙyauta kuma nasan Uncle ɗina shima da ya nann zai gode maku , amma makwafin sa na gode maku duka…….. Dariya aka ƙara sakawa har da masu kyakyatawa yayin da Su Na’ima wato class mate din Jidderh don yanzu a SS3 take ita ,nan su Na’ima suka sa ihu tare da cewa “ We really love you ma’eesha ❤️” . Daga masu hannu tayi tana murmushi tare da tafawa ita Bama ta jira a tafa mata ba duka da ita da ɗaliban da malaman suke tafawa a tare , itama ta tafa ma kanta kenan .

Sauka tayi tana komawa wurin zaman ta , yayin da ƙawayen ta kowa ke amsar ƙyautar nata .

Gyefe can Jidder ce take hura hanci da kumbura tayi da huƙeƙiya ta zama cikakkiyar budurwa yar shekara 17 . Fuskar ta sam ba Annuri don har iya yau tsana ce ke ruruwa mata na Ma’eesha a zuciyar ta . Jidderh me yasa bakya farin ciki ne ? Autar ku tafi kowa hazaƙa aa….. Enough please bana son Jin komai malama ki ɗan rabu dani” . Jidderh ta furta tana kallon Ƙawarta sadiya kana ta ja tsaki tana miƙewa tare da fita hall ɗin tana nufar inda moton drivan su yake . Kusan kaman mintuna Arba’in sannan daliban aka fara fitowa alamun Hutu ya kammala na karshen zango.

Ma’eesha… ma’eesha sunan kawai ma’eesha ake kira yayin da seniors din ta da yawa kyauta suke ƙara mata a haka har gaban moto suka kawo ta tana shiga tare da ɗaga masu hannu drivaer na jan moton tare da fara barin harabar Makarantar.

Tafiya ce suka fara babu mai cewa komai , sai dai ita ma’eesha akwai surutu cike da farin ciki take kallon Jidderh kana tace “ Anty jidderh kin ga Ƙyautar dana samu ? . Zanci uban ki kika ƙara kiran sunana? Ni tsaran ki ce Im i your mate? Ki kula kuma ki kiyaye…..!

Shiru Ma’eesha tayi tana kallon ta fuskar ta na narkewa idanun ta nan da nan suka ciko da ƙwallah . Anty jidderh Ni fa ƙanwar ki ce ,me yasa kike mun……Shiiiiiii huuuuuu jidderh ta saki huci tana caɓe baki tare da girgiza kai kana tace “ Ke bari na sanar Miki da Wani Abu da baki taɓa sani ba a Rayuwar ki , shin kin san me ake ɓoye miki a cikin gidan nan? A tunanin ki mu din ahali ne ɗaya? Humm yaro kenan! Tom Bara kiji idan su yayyun ki ne mami mamin Kice haka Daddy Ni ban haɗa komai dake ba .

Hawaye ne ya fara bin Kuncin ma’eesha don ita bata san wai mami Bama mahaifiyar ta bace gani take ita yar suce , kuma ko a yanzu bata fahimci inda jidderh tasa gaba bane , don har yau jidderh tsoro ya hanta bayyana mata gaskiyar.

Ke kin san bana son Hayaniya ko? Kai driver sauke mun yarinyar nan ta tako da ƙafa ta iso gida ,ba zan zauna tana mun kuka a moto tana cika mun kunne ba .

Kiyi Haƙuri jidderh. Drivern ya katse ta , inda ta hasala tana cewa “ A yau zaka rasa wallahi hanyar samun abincinka….ƙanwar kace ko kun haɗa jiɓi da ita ne matsiyaci ….kaga farin fata kowa wannan hasken naki da shegen dariyar ki na banza yake ribartar mutane don ban ga wani kyau da kike dashi ba . Sauke ta…..sauka ki fita …..!!! Tayi Maganan tana doka mata Tsawa wanda cikin sauri Ma’eesha ta fita , tana kallo moton ya ɓace mata, da sauri ta fara takawa tana gudu don lokaci daya garin ya fara kullluluɓewa da hadari ɓakin ƙirin. Sauri take yi tana tafiya tare da maida gift din ta cikin ƙaramin jakarta . Fuskar ta duka ya kacame da hawaye , a hankali ta furta “ Anty jidderh kiyi Haƙuri…..” tamkar wacce Jidder ke a gaban ta ….wani irin ruwa ne ya fara sauka mai bujaji da iska mai tafiya da mutane haka yake gaba da baya da Ma’eesha ruwan na sauka a jikin ta baki daya ..!

Sanye Mami take cikin wata irin tsadaddan material Golden , a yanzu ta zama cikakkiyar uwa mai kula da yaran ta . Tun da taga hadarin hankalin ta ya tashi ta fito barander tana jiran Dawowan ƴammatan nata . A haka ruwa ya fara sauka . Sunan Khalil da Aliyu yau suka dawo amma a yanzu bata ta kansu a ciki ta bar su ita dai burin ta taga Ma’eesha da jidderh sun dawo gida Lafiya. Hummmm wani sauke ajiyar zuciya tayi da sauri tana isa ga moton drivan da yake dauko su. Bude moton Jidderh tayi yayin da mami a ruwan ta isa da gudu tana furta “oyoyo my babies, Ina Baby ma’eesha………….?

Wani irin kallo jidderh tayi mata kana ta wuce ta fuuuu ba tare da ta tanka ta ba. Sam mami bata damu ba , hannu tasa tana murmushi tare da yar dariya tana ware jikin ta da cewa “ Oya come out my baby , taho na Rungume ki ruwan ba zai sauka miki ba ,ba zan bari ko kaɗan ya taɓa ki ba…..Ai Hajiya Ma’eesha bata a cikin moton nan………….

Ya kuke ganin tafiyar zata kasance a gabana bar maku tunanin.

*To masu karatu free page zai ƙare a shafi na goma sha biyu 12 maza ku fara payment saboda nan kusa zai ƙare . Regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Ayshatou Maman-teddy*

*Buxuwa Empire08126535394*
Tanayin ayyukan gyara sunna masu yawan gaske haka ƴammata , zawarawa masu shirin aure suna iya yi mun magana , sannan kina zuwa ki faɗi buƙatar ki kwai zamu baki amsa mutane sunyi yawa ne kuyi haƙuri don Allah…

Muna aikin rufe na miji a kwalba sai kin tabbatar da idan miji ki baya da hali karki zo mu rufe bawan Allah .

Muna aikin mallaka na Baƙin ruwa wannan muna ma saurayi da yaƙi fitowa ayi mgnn aure ko miji mara kyauta…

Muna kiranye ko mallaka na ramin tururuwa Hajiya ta idan kinason kiga mijinki yaƙi zaune yaƙi tsaye kula da tattali ya zame masa dole to don Allah kiyi aiki ramin tururuwa kiga yanda ake yi

Muna aikin kwai mai rubutu a jiki wa macen da takusa aure ko auren da yakai shekara goma ..

Muna aikin zuciya mai allurai a jikin zuciya baki ɗaya ki tambayi meye aikin da akace maki da zuciya za’a yi shi muna kiranyen sa , muna mallakar sa akan koma meye koda kinga wanda kk so ne inshallah indai ba zakiyi mugunta ko wani nufi a kansa ba kina iya Wannan aikin .sai dai aikin mu babu kauce hanya .

Mallkar tumfafiya da ganyen tumfafiya na turare aiki gagare ga wanda ta shirya.

Mallaka da kiranye na kan rago mai laya guda 84 kinga aikinnan bayanin sa bazai daɗi ba …aikin mu babu kauce hanya.

Aikin kifi da ake ratsawa a bushiyar Rimi

Aikin farin kyalle wanda ake zana Mutun na bar maku yanda yake aikin

Bugu da ƙari a kwai aikin da idan kinason shi ana bugawa a ranar aikin keyi idan kiranye ne a take takeyi .

Sannan akwai wasu ayyukan da Hajiya nayi maki alƙawarin idan bayyi ba kixo na baki kuɗinki

Sauran kalolin aikin suna da yawa gaskiya bazasu faɗu ba.

Kamar aiki :
Na yasiin
Na zobe farin jini
Na warwaro na farin jini ne
Na ƙasar ƙofar gida
Na ƙasar ƙafan kowani ɗana mijine ga masu buƙatar samun samari ta ko ina .

Na mallkar lilin kaza
Na gashin farantii ga maza marasa kyauta idan kinason ki rinƙa samun kuɗi hannun na miji to kina iya mana mgn :08126535394

Ƴammata masu buƙatar samari masu rufi asiri ko masu son su samu mijin su ko masu fama da matsalar jinnu suna iya mgn kuma zasu samu cikakkiyar bayani daga gare mu bi izinin Allah muna godiya sosai08126535394.

Back to top button