Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 33

Sponsored Links

Dakin baba suka shiga tazauna akan sallaya fuskanto ta baba yayi kafin yafara magana ” Fatima ni nafi kowa sanin halinki kin kasance me hakuri da juriya dakuma sadaukarwa , to ayanzu ne wayan nan halayen zemiki amfani ke yanzu ke bakamar sauran yan mata bace karki dinga hada kanki dasu domin ke yanzu kinzama babba tunda kika zama matar aure kikama mutuncinki amatsayinki ta matar aure , wani shiga shirgin daba naki ba babu ruwanki! Sannan aure yar hakuri ce duk wasu ma’aurata dakika gani dukkansu hakuri suke da juna domin anriga da anzama daya, yazama dolene se anyi hakuri da juna kiga misali da mahaifiyarki yau shekara ashirin da biyar da aurenmu amma dede da musu wannan bata tabamin ba balle bakar magana mara dadi hakurinta yazarce misali itadin matace tagari to zanso kiyi koyi da ita kiyi hakuri da mijinki ako wani irin hali kikasance meyi mishi biyayya kibishi sau da kafa nan ne zakiga ribar auren dakuma hakuri rashin kunya ba naki bane, inyace kiyi , kiyi inyace bari kibari karki tsaya yana fada kina maida masa magana , sannan mudin kika fita zuwa wani wajen batare da izinin mijinki ba duk taku daya mala’ikun Allah tsine miki zasu dingayi ! Wannan gidan bekai gidan mijinki ba domin mace da gidan mijinta take tunkaho duk abinda ze hadaki da mijinki kizama mace me sirri karki yarda sirrin mijinki yafita sede in abinda yakeyi yazarce ka’idan addinin musulunci nan ne zaki kai kara domin neman solution, Karki manta aljannarki na karkashin kafarsa seya daga zaki shiga dan haka kiwa mijinki biyayya karki saba mishi Allah yamuku albarka yabaku zaman lfy zaku iya tafiya” tunda baba yafara magana taketa sheshekar kuka gaba daya maganganunshi ya ratsata sosai rarrafawa tayi har gabanshi tarungumeshi tana kuka bubbuga bayanta yakeyi yana shafa kanta tare da samata albarka . Haka anty firdausi tafito da ita falo tana kuka mikewa su anty Amina sukayi da niyyar tafiya fitowa mama tayi hannunta rike da wata yar karamar box riko hannayen fanan tayi tabude box din awarwaro ne guda hudu aciki na zinari alamun sundade ba design din zamanin nan bane se sheki sukeyi zurawa fanan tayi ahannun kafin tace ” wannan awarwaron dakike gani gadon alhalinmu ne kakar kakatace tabawa kakata lokacin datayi aure itakuma kakata tabawa mama na dazatayi aure nima sanda zanyi aure mamana tabani kinsan metace min ” dago manyan idonta dasukayi jaa tayi takalli mama ta girgiza Kai, yar murmushin yake mama tayi tacigaba” cemin tayi duk sanda nahaifi yata tayi aure itama inbatasu, ki kula dasu sosai kinji? Kizauna da mijinki lafiya fanan kimishi biyayya kizauna dashi da akwai da babu Allah yamiki albarka yabaku zaman lafiya ” fashewa da kuka fanan tayi ta rungume mama kam_kam kamar zata koma cikinta kuka takeyi kamar ranta zefita, na mijin kokari mama tayi bata bari hawaye yafita a idonta ba sosai sukaji tausayin fanan amma dolene wannan akan kowace ya mace dole tabar gidan iyayenta , kokarin raba jikinsu takeyi amma fanan taki saketa ganin takine yasa su anty shayida sukazo suna kokarin rabasu suna bata hakuri Abu kamar wasa sunfi 30mint ahaka karasowa gunsu ya usman yayi yamata magana akunnenta sake maman tayi tarungumeshi shida kanshi yafara tafiya da ita zuwa motar bayansu sukabi zama mama tayi hawayen rabuwa da yarta dakuma farin ciki na kwarara daga idonta. Motarshi yashigar da ita back seat anty firdausi da anty amina suma suka shiga tana kuka suna rarrashinta su amira dasu anty shayida suka shiga motar suhaima natsaye tama rasa ina zata shiga fawwaz lura da hakan ne yabude matar gaban motarshi yamata alama da hannu yace ” princess let’s go” cike da kunya tashiga anty zainab dake motar dariya tayi kasa_kasa aranta tana fadin “ohhh wato su fawwaz ma ankamu kenan ” tada motocin sukayi sukahau titi tafiya sukeyi ahankali harsuka iso gidan wangale musu tangamemen gate din akayi suka shigo fitowa sukayi dukansu suka tsaya suna jiran afito da fanan rungume da ita anty Amina tafito suka nufi part din ummi abakin kofa anty Amina tatsaya tace mata tayi adduah sannan tashiga da kafar dama haka kuwa akayi afalo suka samu abba, ummi da areef mikewa ummi tayi tazo ta rungumeta tana mata lale marhaban zaunar da ita tayi akan lutsa_lutsan kujerun falon abba se murmushi yakeyi yaso ace azaad na gida daya mishi tsiya dazun yafita da car key ahannunshi ko inazeje oho . Budewa fanan fuska ummi tana Masha Allah dukda tabata kwalliyar da kukan datasha fuskan nan yadan kumbura zama sukayi afalon gaba daya suna hira duk dan susamu fanan tasaki jikinta ya usman ne yashigo falon yana rike da akwatin kayan fanan dayan kuma wani security narike dashi anty Amina ce tamike tacewa security yabiyota da akwatu nan part din Azaad tanufa security nabiye da ita abaya shiga tayi falon nashi dakuna ne manya guda biyu banda na azaad se babban falonshi da dinner table da kitchen komai akwai a part din se corridor sunji furnitures dakin dake manne dana azaad painting dakin fari ne se makeken gado da wardrobe me girman gaske ga mirror da aka cikashi da kayan shafa and kayan make up,dade sauransu , bude wardrobe tayi wanda yake shake da kaya nagani nafada babu abinda babu komai ansaka matasu aciki kaya kala_kala bangaren takalma da jaka daban bangaren kana nan kayama haka se bangaren dogayen ruguna su hijab pants and bra sleeping dress, atamfofi, waje tasamu ta ajiye akwatu nan tarufe wardrobe din layin ummi takira tace su anty firdausi da suhaima suzo da fanan part din Azaad aikuwa haka akayi shigowa sukayi dakin datake toilet ta nunawa fanan tashiga tayi wanka tana mika mata doguwar rigar abaya da gyalensa karba tayi tashiga toilet din tayi wanka tasa abayar milk color ta yafa gyalen tafito tasamu anty Amina da anty firdausi basa dakin zeenat tashigo tana masu suhaima masifa ” wato shine zaku taho bazaku kirani bako” hararan wasa suhaima tamata ” to aigaki kinzo ” magana zeenat zata kara fanan dake gaban mirror tana shafa lotion tace ” to anty masifatu Allah karku dameni tam”
Zama zeenat tayi tace ” wace ni rufamin asiri amaryar yaya guda nina isa indameki matarmu” dariya sukayi kara bata fuska fanan tayi tacigaba da abinda takeyi tana gamawa kuwa batace musu komai ba ta tadawo main falo tazauna ganin hakane yasa suma suka fito . abu me aikice ta sanar da ummi angama shirya komai a dinning ” to kutashi dukkanku food is ready ko ” mikewa sukayi dukansu suka zauna akayi serving dinsu fried rice da kaji se farfesu , masa da Miyan kifi. Yaseer ne yafara gamawa yamike yakoma falo yana kiran layin azaad seda yamishi almost 5miss called kafin yadaga ” haba ango wannan wani irin iskancine akawo maka amarya kawani fita kayi sauri kadawo” yana jiran abinda azaad din zece yaji dogon tsaki Mr azaad yaja yakashe wayar dariya yayi dan yasan zaa rina bayan sun gamacin abincin suka dawo falo wayar suhaima ce tafara ringing dubawa tayi taga number yaya inlaw ne murmushi tayi kafin tamike tafita a falon taje compound tadaga wayar ” hello yaya Ina wuni ” adayan bangaren aka amsa ” lafiya da nayi fushi dake bansan ya akayi nakiraki ba babynmu ne takeson jin muryanki shine mimi tace inkiraki ” dariya yabata wai babynsu ce takeson jin muryanta kai ya amir sarkin zolaya ” uhmmm kuda kuka manta dani ma aini yakamata inyi fushi bakuba” tafada tana murguda baki ” yanzu bawa mimin ” amir mikawa matarshi mimi yayi sunkusan 10mint suna waya kafin sukayi sallama yakashe, juyawa tayi zata koma ciki kawai taga mutum atsaye abayanta yaharde da hannunshi tadan tsorata ganin fawwaz ne tace ” laaaaah ya fawwaz wannan aisekasa inzura da gudu ” murmushin gefen baki yayi yace ” hmmm ai hankalina ne yakasa kwanciya shisa nabiyoki a tunanina ma wanine yakeson min kwace ashe yayanmu ne ” daure mata kai yayi da kalamansa ” bangane mekake nufi ba ya fawwaz” daga mata giran sama yayi kafin yace ” lokacin da wayarki tayi ringing ganin irin murmushin dakikayi yasa zuciyata tsinkewa dan nadauka wani ne yakesonmin kafa agun matar danake buri tazama uwa ga yayana ” sosai tazaro kyawawan idonta tana kallonshi wura mata iska yayi a ido kauda kanta gefe tayi hannunshi yasa yakarbi wayarta yayi dialing din number sa ya mika mata murmushi yayi yace” naji kinyi shuru kifada mini namiki ne ko ko banyi ba ?” Dariya tayi jin yanda yake magana da wakar dan musa tafiya sukeyi suna yar hira harsukazo falo ja tayi tatsaya tace” ya fawwaz kabarni infara shiga ” gyada mata kai yayi tashige tazauna sedaga baya yashigo yazauna akan kujera dake facing dinta daga sun hada ido se yasakar mata murmushi itama tamayar mishi babu wanda yalura dasu se fanan wani irin dariya tafashe dashi wanda rabon datayi irinshi tun ranar agida itada suhaima seyau kuma dariya takeyi ba qaqqautawa harda rike ciki zuba mata ido sukayi suna kallon iKon Allah suna mamakin meye yasata irin wannan dariya haka sedata kai kusan 5mint kafin ta dakata ganin suna kallonta ne yasa taboye fuskanta ajikin ummi tana yar dariya basu kawo komai aransu ba su a tunaninsu wani abun ne yasata farin ciki amma yawan da dariyar yayine yabasu tsoro .
___ Abba ne yace ” fanan daga yanzu kidaukemu kamar iyayenki bawai surakanu ba domin ke yace awajanmu matsayinki daya da zeenat so dan haka kisake jikinki nanma gida ne kinji ko ?” Fitowa tayi daga jikin ummi tace ” in sha Allah abba nagode ” mikewa anty firdausi tayi tace ” kutashi muyi shirin tafiya ” tashi sukayi suna musu sallama fanan jitayi kamar tayi kuka rungumeta suhaima da amira sukayi atare kasa_kasa amira tace ” to besty azage akula da miji abashi kulawa atarerayeshi kamar kwai nan da 5 months muzo sunan yan hudu” tsaki fanan taja ” kefa iskancin kine yake hadani dake kifita a eyes dina tam” kafin tajuya kan suhaima ” kekuma dama kin iya kallon love haka inyaah ” amira de batasan akanme take magana ba suhaima kuwa hararanta tayi tace ” to ina ruwanki yarsa ido kawai ” jarare jikinta fanan tayi tana ” uhmm jeki can da yawar soyayyarki ni karkimin rashin kunya” cewar fanan ahaka suka dingayi harsuka je bakin motar suka shiga daga musu hannu tayi tana musu bye_ bye tafiya sukayi suma suka koma ciki Abba kam already yawuce part dinshi su fawwaz ma haka anty shayida da anty zainab kuwa ko wacce mijinta yaturo driver sun maidasu gida, yazamana daga ummi, zeenat,anty amina se fanan din ne afalon ummi ce tayi magana ” fanan kitashi kije ki kwanta kihuta kinga gobe kunada program zaku fita karfe 10:00am nasafe ! Sannan a part dinku duk wani abinda zaku bukata akwai aciki kayan girki kidingawa mijinki girki koda bazeci ba kimishi de yasan kinyi kinji ko ” “to ummi” cewar fanan dake mikewa zata wuce part dinsu seda safe tamusu tashige atare ummi da zeenat suka sauke ajiyar zuciya dan yau burinsu na fanan tazama sirka agidan yacika sunyi farin ciki sosai.
Ita atunaninta yadawo gida dan dazun taji su fawwaz sunce baya nan dakinta tawuce cire rigar tayi tadaura towel tashiga toilet tayi wanka da ruwan zafi tayi alwala tafito goge jikinta tayi da towel din tashafa turare masu dadin kamshi wardrobe din tabude kayan baccin tazubawa ido ganinsu da yawa wani me riga da wando black silky tadauko tasaka tasa hula akanta takwanta taja blanket tana adduah bacci aikuwa bacci barawo yayi awun gaba da ita.

Se karfe kusan 12:00 nadare tukun yadawo gidan kowa ya kwanta yashiga part dinshi toilet yafada yayi wanka yafito towel daure a kugunshi shafa lotion yayi ajikinshi yafeshe jikinshi da perfume kayan bacci yasa ajikinshi yakwanta.

Back to top button