Hausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 31

Sponsored Links

U……31

Zaks Yaga nan da nan fuskar tasa ta hade baki kirin kmr hadari, be taba ganinsa a yanayin da yakansa ba yanzu, har wani duhu fuskarsa tayi saboda zallar azabar matsifa da jaraba dasuka masa dirar mikiya a zuciya, ya Kure su nabeelah da Alhaji Sadi da ido, se huci yakeyi kmr kumurcin maciji mesa a rami. “Da Aurena,,,,da Aurena take tsayuwa da wani namiji,,,wallahi wallahi Zaks yau sena kashe wancan tsinannen! Wlhi yau nine ajalinsa,! Zan nuna masa waye ni, dan mecin uwar ubansa, shege tsinanne kawai!” Aeezad ya fadi da muryarsa wadda ke barazanar tarwatsa motar da dodon kunnen Zaks din. Laluba aljihunsa yashigayi domin yaji akwai Karamar bindiga ciki, yaji babu , nan take duk yabi ya rikice idanuwansa sun rufe, lalubar gaban motar yashigayi tako ina yasan baza a rasa bindiga a motar tasa ba, ko gani bayayi sbda bacin rai,ji yake kmr zuciyarsa zata buga ta tarwatse, Zaks kam ya rasama yazeyi ya kasa cewa komi , shide yasan be isa ya dakatar da Aeezad daga aikata abinda yaga dama ba, Gashi da alama mommy Ma ta gansu danse kallonsu takeyi, gaskiy mommy bata kyauta ba, Zaks be taba ganin lefin mommy ba se yau, tasan da Aurensa a kanta kuma ta tsaya da wani namiji, ta gansu yanzu taga motar tasan sune a ciki koda motar ba a ganin na ciki, amma ai kaf motocin Aeezad tasani kodan lambar motar jiki, amma ta kallah ta dauke kai, taci gaba da sakarma Alhaji sadin murmushi, inside kam ba karamin bugu zuciyarta keyi ba, tinda taga ba ayi packing dai-dai ba, hkn ya tabbatar mata da yau akwai matsala, ta sadakar yau zatasha marirrika, kawai tunano irin Marin daya mata a asibitin tashigayi,.”yau natashi aiki!” Ta fadi a zuciyarta, dukda iskar dake kad’awa amma seta Kama zufa, kawai murmushi takeyi a zahiri, amma ko abinda Alhaji sadin kecewa bata fahimta. Ba bata lokaci Aeezad yaga bindiga karama a gaban motar, ganin yaga bindigar yasa Zaks shiga tashin hankali sbda yasan komi na iya faruwa. “Dan Allah Aboki karka Aikata abinda be dace ba in rai ya baci hankali ke nemosa…” Zaks ya fadi yana RIKO hannun Aeezad me lafiya wanda ke rike da bindigar yana kokarin ficewa a motar. Ina Ai Aeezad bebi takanma me Zaks ke kokarin sanar dashi ba, ko gani bayayi sosai, ya fito daga cikin motar, Zaks ma ya fito, nabeelah na ganin Aeezad ya fito daga cikin motar kuma taga bindiga a hannunsa, taga yana tinkarosu gadan-gadan da bindigar, zumbur ta tashi tsaye, Tana fadin “Alhaji kashiga mota ka gudu,,,kashiga motarka ka gudu! Nashi uku yau!!!” A rikice take mgnr, Alhaji Sadi shima mikewa tsayen yayi ba tare daya fahimci me nabeelah ke nufi ba, yashiga tambayarta “kamarya? Bangane ba?” Kasancewar ya bawa Aeezad baya Sam be Gansu ba, shifa bemaga shigowarsu da motar ba, in yana gaban nabeelah baya fahimtar komi kyaunta na makantar dashi, shifa Allah yasani dan kyaunta ze Aureta, (kunsan cikakkun kanawa dasan mata masu kyau, musammanma in farar mace ce) “kashiga motarka ka gudu dan Allah Alhaji!” Nabeelah ta fadi cikin magiya still idanuwanta na kan Aeezad da Zaks dasuke tinkarosu. Ganin inda ta tsurewa ido sannan ga alamar fitar hayyaci ya bayya kan fuskarta, yasa Alhaji Sadi juyawa yaga me take kallo ne daga bayansa, daya gigita ta har haka. Juyawar dazeyi yaga Aeezad da Zaks , ganin ya juyo Yana kallonsa yasa Aeezad dago hannunsa dake dauke da bindiga sama , ya shigo nuno Alhaji Sadi da bindigar yana kokarin sakin harsashin Zaks ya rike kan bindigar. “Ka barni in kashe shi, wlhi yau nine ajalinsa, daga kan matata baze kara marmarin kusantar wata mace ba in har matan Aure ce,…karamin mazinaci neshi,, wlhi sena zama ajalinsa yau!” Sune kalaman dake fitowa daga bakin Aeezad, Alhaji Sadi ya shiga firgici, Jin kalaman bakin Aeezad Sam be fahimci me yake nufi ba, sbda shide yasan nabeelah ba matar Aure bace, Alhajin ya fara tunanin Anya bayan ciwon hannun da yakeyi ciwon hauka be shafi Aeezad dinba, tini ya ganesa tinda ya daura idanuwansa a kansa ya fahimci kanin matar baban noor ne. “Ka fita a gidannan dan Allah’’ Cewar nabeelah da hankalinta ya kara mummunar tashi, ta shiga ture Alhaji Sadin da hannayenta biyu, ko gezau Alhajin beyi ba, sbda shi kansa ma ya kulle. “Bura ubannan!” Aeezad ya fadi a bayyane ganin nabeelah na ture Alhaji Sadi da hannayenta , hannayenta nasa na Auren sunnah, shine take taba jikin wani d’ana miji dashi yau garjejen kato. Hankalinsa da zuciyarsa da lissafinsa suka kuma baci, sbda tsabar bacin rai ko ganin gabansa bayayi sosai,. “Ka kyaleni Zaks , ka sakar min bindigata, in baka sakarminba na kashe mutuminnan to tabbas Kai zan kashe!’” Aeezad ya fadi cikin kunar zuciya, Zaks ya kara rike bingidar sosai da hannayensa biyu yace “Naji aboki zan dauka ka kasheni ,…” da karfi Aeezad ya fisge bindigar daga hannun Zaks yana fadin “Ka kyaleni ba ruwanka!!!” Ya fadi hadi da nufar kam Alhaji sadi da firgici ya hanasa tafiya, nabeelah sece masa takeyo ya wuce amma yaki wucewa se tambayarta yakeyi meke faruwa. Cikin hanzari Zaks ya kara binsa ya rikesa yayinda sukazo daf da Alhaji sadin, Aeezad na kokarin harbin Alhaji Sadi Zaks ya rike kan bindigar again, saura kiris a hannun Zaks din Dan Allah ya rufa asiri zaks din ya maida kunamar bindigar ciki. “Ka kyaleni!! Wlhi ka kyaleni in kashesa ko kai in kasheka,! Wlhi sena kashesa koda Nima daga hk za a kasheni!” Aeezad ya sake fadi cikin fitar hayyaci kishi ya rufe masa idanuwa, idanuwan nasa na kan Alhaji sadi. Zaks ya kalli Alhaji Sadi da zufa keta keto masa bakinsa se rawa yakeyi sbda tsoro ya kasa guduwa duk yabi ya firgice Gashi ga mutuwa real aini dole ya rude ya rasa uwar ubansa. “Ka bar gidannan !inba haka ba wlhi ze harbeka….” Cewar Zaks da yayi mgnr da Alhaji sadi, se kokawa yakeyi da Aeezad wanda ke kokarin amshe bindigarsa daga rikon da Zaks din yayi mata, so Zaks yakeyi ya amshe bindigar daga hannun Aeezad amma ina ya kasa, ya tabbatar da ace Aeezad nada lafiyar Dayan hannu da Zaks be isa ya iya masa ba, a haka ma ya kasa amsar bindigar a hannunsa, dukda shi hannu biyu garesa shi kuma hannu daya garesa, se zufa kawai Zaks keyi, gogan kam jikinsa har kyarma yakeyi idanuwa nan nasa sunyi ja-jawur kmr jan gauta. Nabeelah kam tini ta fara kuka sbda tashin hnkli , maaikata gidan na ganin abinda ke faruwa amma ba wanda ya isa ya we uffan ko gurin basu isa su karaso ba , baban noor na part dinsa ya kule a karshen bedroom dinsa yana wayar iskanci da karuwarsa. (Kaima baban noor Allah baze barka ba, ana nan ana maka talala,,) aunty hafsat na saman upstairs Tana dakinta ita da yaranta suna wasan yaushe gamo, big hajiya kam na dakin kasa tana baccin asara na bayan la,asar ta hangame baki, duk ba wanda yasan meke faruwa a tsakar gidan, kowa nacan yana sabgar gabansa.

Ba bata lokaci alhaji sadi ya isa ga motarsa jiki na rawa ya shiga, ya tada motar ya isa bakin get da motar da kyar sam hnklinsa baya jikinsa yake driving din ya raba motar Aeezad da akayi packing dinta ba dai-dai ba, yana kokarin ficewa a gidan Aeezad ya sakarma Zaks bindigar ya isa ga motar Alhaji Sadi dake kokarin ficewa a gidan a guje, already daman glashing motar tasa a bude yake ta fannin me tuki, wani irin mahaukacin naushi Aeezad yakai masa ta Cikin window din motar dai dai a saitin bakin Alhaji sadin. “Bakina !” Alhaji Sadi ya fadi a gigice sbda zafin dayaji a bakinsa ya matukar kara rud’asa nan da nan jini ya Balle daga bakin Alhaji sadin dai dai hakoransa guda biyu suka fito daga bakin nasa na gaba, suka fado gaban rigarsa, nan hnklin sadin ya kuma tashi, ya tabbatar Aeezad de mahaukaci ne. Aeezad na kokarin kara Kai masa wani naushin Zaks ya karaso a guje ya rikesa nan yaga Alhaji Sadi baki na jini. “Kaga abinda mahaukacin nan yamin kou ?” Alhaji Sadi ya fadi nan take wawulon bakinsa ya bayyana na gaba wanda keta jini. “Innalillahi! Ka gudu dan Allah …” cewar zaks dake kici kicin rike Aeezad, wanda keso ya kara kwacewa ya farma Alhaji sadin danya tabbatar shidin mahaukacin gaskene bana wasa ba. Ganin Zaks ya rikesa a guje Alhaji Sadi ya fice a gidan ya Danna motarsa kan titi ya shiga sharara gudu sbda gani yake kmr Aeezad din ze biyosa ne ya kashesa, Gashi ba a shara’ah da mahaukaci.

Ganin Alhaji sadin ya gudu Zaks ya saki Aeezad duk karfin Zaks din ya kare da kyar yake rikesa. Aeezad na huci yadawo ga securities din dake gadin get din kusan su biyar yace “wlhi in wannan mutumin ya kara zuwa gidannan kuka barshi ya shigo, koda gidan ba nawa bane amma wlhi dukse naci kutmar uban ubanda ya haifo ubanku a garinnan, dukse kunyi nadamar zuwanku duniyar gabaki dayanta wlhi…” “sorry sir…” suka hada baki gun bashi hkri. Ba tare da Aeezad yabi ta kansu ba ya juyo se huci yakeyi , ya nufo inda nabeelah ke tsaye ko motsin kirki ta kasayi, ganin yadda Aeezad ya zama kmr tsohon mahaukaci a lokaci kankani. Ganin ya juyo yayi kanta, yasata saurin juyawa zata nufa hanyar dazata sadata da cikin gidan. Taku uku Aeezad yayi ya damko dai-dai saitin wuyar hijjabinta, sede kawai taji an dankota, nan take hijjabinta ya zame ta kai, sumar kannan tata baki wuluk ta bayyata ta nade sumar da ribbon ash, nan take Aeezad yasamu damar ganin wuyanta, ya saketa amma ta kasa guduwa sbda tsoro da ace hannunsa Dayan lafiya yake da nabeelah tashiga uku yau, ubangiji ne ze kwace ta a hannunsa. “Dan kutmar uba, Da Aurena kike tadi, da Aurena, dan iskanci da wulakanci da dacin mutumci, wlhi yau zan nuna miki ke Karamar yar iska ce, nine babban…kina karyar maitar maza ne…” ya fadi cikin zafin zuciya, ya daga hannunsa me lafiya ze sharara mata Mari tayi hanzarin yin kasa da fuskarta, ta kulle fuskarta da tafin hannunta, ta rintse idanuwa, kalamansa nacinta, wai yau har ita yake cema yar iska Lallai ta zubar da kanta over a gurinsa, ta tabbatar duk sbda jikinta ne daya gani ya kara rainata, shiyasa bahaushe yace da wasa da yaro kwara kwana da yunwa, ita ma daba wasa take dashi ba amma ya mata irin wannan rainin me cin zuciya, dadin dad’awa danyaga tana kasansu ne shiyasa duk wani rainin ya karu. Zaks ya RIKO masa hannun dayake kokarin marin Mommyn dashi. “Aboki pls kayi hkri , bazata kara ba dan Allah kayi hkri…” Zaks ya fadi yana rikosa sbda inya barsa ya mareta ya tabbatar yana iya sumar da ita. “Dan Girman Allah ka kyaleni in koya mata hankali, bade bata dauki Aurena a bakin komi ba Dani kaina, yau zan nuna miki Aurenki nakeyi wlhi! Ko dan kinga na barki a banza ban miki abinda ze nuna Miki ni mijinki bane kou?” Ya karashe da zafin zuciyata ya kwace hannunsa daga rikon da Zaks ya masa ya fisgota, takalman kafafuwanta suka cire sbda janta dayayi da karfi, nan take ta Taka wata yar kwalba abinka da farar mace kuma kafarta nada Azabar laushi, nan Kwalbar ta fasa cikin kafafuwanta tashige , nabeelah ta fasa wani irin ihu Sam Aeezad bebi ta kanta ba, ya kara jawota kiiiiiiiiii! kafarta na zubar da jini amma Sam be Lura ba shima Zaks be kula ba, a haka yana jawota harya karaso da ita bakin kofar motarsa ya jefata baya, se ihu takeyi Aeezad yasha zallar iskanci ne da wulakanci yasata ihun dan hk bebi ta kanta ba yashiga gaban motar, zaks yashiga ba bata lokaci yaja motar Aeezad ya kafa ruwan matsifa da bala’i. “Baki daukeni a bakin komiba Dani da Aurena dake kanki,Ina kallankine kawai nabeelah, nasan a bnza kk kallona, kawai sbda kin raine ni, bafa kaina ko kanki aka fara Aure mace ta girmi namiji ba, wlhi tinda bake kk haifanba sena nuna Miki waye ni meye matsayin Aurena a kanki yau….ka kaini sabon gidana, wlhi yau sena nuna ma nabeelah ni cikakken namiji ne nafi gaban raini….” Aeezad ya karashe mgnr yana kallon Zaks sbda matsifa duk kamanni Aeezad din ya chanza. “Toh …” Zaks ya amsa da sauri, gudun kar yayi Lefi a dawo kansa. nabeelah ta kara fashewa da kuka jin yace a wuce da ita gidansa , cikin kukan take cewa “wlhi bazanje gidanka ba dan iska kawai, sena nuna maka na girmeki, bazan dauki raininka ba,,,banasanka!” Aeezad ne ya iya fahimtar me take cewa amma Sam Zaks be fahimta ba sbda kuka ya shake mata wuya sosai. Bakin cikin kalmar datace bata sanshi ya kara harzuka Aeezad a kanta, dabadan karfin San da yake mata ba tabbas babu abinda ze Hana ya rufeta da danbura uban duka yanzunnan, ji yakeyi kome ya mata ma be huce ba. , da kyakyawar hannunta data zama mallakinsa ta dauka ta taba wani namiji dashi kuma a gaban idanuwansa, wannan abu yaci masa zuciya. Be kara cewa komi ba sbda bakin ciki har suka isa katafaren gidan nasa. , sabone dal haka komi na cikin gidan sabo ne , tin daga kofar get din gidan abin kallo ne, gidan zagaye yake da matakan tsaro, duk wani gidansa zagaye yake da mata kan tsaro musammanma gidannan nasa yafi kowanne gidansa kyau, yana tsananin ji da gidan tinda ya fara San Aunty nabeelah yasa aka gina gidan dasunan nan zasu zauna kawai be sanar da kowa ba ko Zaks be sani ba kawai de yasan gidan nasa tin ana gininsa, kafin aka gama komi na gidan sabone fil daga waje akayi order dinsu. Ko packing din kirki Zaks be gamayiba Aeezad ya fito daga cikin motar, ba tare da Zaks din yayi packing ba shima yayi sauri ya fito Aeezad na kokarin bude inda nabeelah take Zaks ya dakatar dashi dacewa “dan Allah aboki kayi hkri ka daure ka dai-daita zuciyarka aboki, karka mari mommy pls ko ba komi ita ta raineka, inka mareta zataga kmr dan Tana karkashinku ne yasa all this, last time ka mareta kayi nadama daga baya kuma, pls this time karka mareta , Annabi bece mu dinga dukan iyalinmu ba kmr yaranmu…” Zaks yayi masa mgna cikin sanyi, Aeezad yayi kmr bejisa ba , ya bude inda nabeelah take cikin zafin zuciya ya kara jawota kiiiii kmr tsohuwar mota , sam Aeezad beda control da zuciyarsa inta baci. Dole zaks seda ya dawo tausan mommy dukda tanada lefi. Nabeelah se kuka takeyi , tasake fashewa da wani kuka, saboda jan da Aeezad din yayi mata a kasa, ta Taka kafarta wadda ta kumbure tayi suntum har yanzu zubar da jini takeyi, ta kurma wani irin ihu Tana fadin kafana!! Amma ina Aeezad be fahimci me take cewa ba hk shima Zaks din dake biye dasu a baya be fahimta ba. Yana isa kofar dazata Sada shi da gidan yasa yatsanshi kofar ta bude, still yana jaye da ita har suka iso tsakiyar falon babban katafaren gidan “Aljannarh duniya…” Zaks ya fadi a ransa yana karewa falon kallo komi na falon Onion color ne light and dark. Suna isowa tsakiyar falon dai-dai kan carpet din dake tsakiyar falon ya watsar da Aunty nabeelah kmr kaya, ta fadi kwance kasan falon , Bom-Bom dinta ya matukar amsa sbda ta baya ta fadi ta kuma fashewa da kuka. “Da hannunki kike taba wani namiji daba muharraminki ba…” ya fadi cikin zafin zuciya yana kallon Aunty nabeelah dake kwance Tana kuka duk tabi ta zama abar tausayi a lokaci kankani har wani zazzabi taji ya rufeta ruf, zafin kafarta se ratsata yakeyi. “ ba wanda ze hanan na zaneki mommy , bakin Cikin da kika samin a zuciyata baze misaltuba mommy dole sena zaneki wlhi…” Aeezad ya fadi cikin zallar bakin ciki, ya dagota ze yaye mata hijjabin jikinta ta rike hijjabin, gam sbda ba komi inside ko pant babu. Aeezad yaga fararen cinyoyinta sun bayyana, dukda a cikin matsifa yake amma seda yawu ya cika masa baki na zallar shaawarta, yayi hanzari ya rufe inda ya yaye sbda Zaks dake tsaye, aeezad yasa kansa ta kasan hijjabim nata nan take yaga zindir take bakomi jikinta. “Kai! Wato haka kika fito gun d’ana miji tsirara, ba kaya, sbda jarabar san maza na damunki…!” Ya fadi a bayyane, yadda yayi mgnr ita kadai taji Zaks dake tsaye yana basa hkri beji komi ba, , nan ran Aeezad ya kuma baci. Bece komi ba ya mike zuciya a harzuke ya isa gaban TV daya mamaye bangon dakin yana fadin “ wlhi kin kara jama kanki mommy, sena zaneki yau mommy,,,duk duniya banga wanda ya isa ya hanani na zaneki ba yau mommy…Kai dole na zaneki wlhi mommy!…” ya karashe yana lumsar idanuwa zuciyarsa na tafarfasa, ya fisgo wayar connecting din TV din wato igiyar TV din. Zaks dake tsaye ya zubo masa ido shi mgnar tazama dariya ta basa da haushi wai ze zaneta kmr wani ubanta. Ya juyo a fusace Zaks yaga ba yadda ze hanasa ya daki mommy kuma gaskiya beso ya daketa sbda shi knsa seya dawo yayi nadama. “Pls aboki kayi hkri dan Allah …” Cewar Zaks , ina Sam Aeezad bebi ta cewarsa ba, idanuwansa sun rufe ruf ya biyewa dokin zuciya. Ya daga wayar ze zuba mata nabeelah ta rintse idanuwa sbda tsoro, har tajiyo zafin bulalan a jikinta dukda bata iso jikin nata ba, ta fasa ihu. dai-dai ze zuba mata bulalar idanuwansa suka sauka a kan kafarta data Taka kwalbar wadda jini keta zubowa har lokacin ta kumbura a lokaci kankani ta kusa biyun dayar kafar me lafiya, kasancewar kwalbar ta shige jikinta duka, a memakon ya zuba mata bulalar seya zubawa kansa ya wurgar da bulalar gefe daya ya karasa kan kafar tata a guje, ya dagokafar tata da hannunsa me lafiya , yaga yadda kwalbar ta shige cike se kadan yake hangouta shima seda ya goge bakin gurin inda jini keta bulbula da hannunsa. Me kika taka a kafarki? Meye wannan? Jini har haka,,,meya Samarmin kafarki mommyna,…” ya fadi a rikice yana dauke idanuwansa a kan kafar tata sbda ji yayi tin daga zuciyarsa yake jiyo zafin datakeji na Kafar a jikinta. Nabeelah ta bude idanuwanta ta zubo masa su kmr me iska taga kuma duk yashiga taitayinsa yanzu-yanzu, mamaki yake bata guy dinnan yanzu kmr mahaukaci beda maraba da mahaukaci, itafa tasha dukan ze mata kuma seta tsincesa yana sambatu. “A ina kika Taka wannan tsinanniyar kwalbar? A ina kika takata? A gidannan ne ko a gidan Aunty hafsat? Amma ba karamin zafi kkeji ba mommy….sannu mommy, Nima inajin zafin a zuciyata, sannu mommyna, sannu kinji zaks zoka gani Zaks mommy ta taka wata kwalba ta shige kafarta, zoka ga yadda kafar mommy ta kumbura…zoka gani…” yashiga fadi a haukace yakai harshensa ya lashi dai-dai inda jinin ke zubowa a kafarta, nabeelah ta tsuresa da idanuwa yadda ya lashi kafar tata ya bata mamaki ko tsoron cuta bayayi, kuma ya hadiye Jinnin daya laso zuwa cikinsa, ba itaba harshi Zaks yayi mamaki, zaks ya kara tabbatar da komi Aeezad na iyayi a kan mommy, ashe kalamansa ba iya baki suke ba,? Se yau Zaks ya tabbatar da duk kalaman bakin Aeezad tabbas ze iya aikata komi ya fadi a kn mommy. Karasowa Zaks yayi ya tsugunno yaga tadda kafar tata taketa kara kumbura shima ya tsorata sosai daganin yadda kafar keta hauhawa. “Subhanallahi sannu mommy, amma a ina kika taka kwalbarnan mommy?” Nabeelah tayi shiru ba tare datace komi ba se kwallah kawai takeyi na zallar azabar zafin dake ratsa kafarta zuwa duk jikinta, duk Aeezad ne yaja mata, shi ya jawota ta taka kwalbar. “Kagani kou? Zaks wlhi Zafi takeji sosai, diba kaga yadda taketa kuka, wlhi zafi takeji na ratsata sannu mommy,,,bari in hura miki..” Aeezad ya kara fadi duk yabi ya rikice nan yashiga hura mata gurin da bakinsa. “Sannu mommy… inaga kwalbar na ciki ne ko Aeezad naga kafar nata kara kumbura?” Aeezad daya sunkuya se faman hura mata kafar da bakinsa yakeyi yace “A, kwalbar na ciki, yanzu yazanyi Zaks? Wlhi har cikin zuciyata nakejin zafin datakeji a kafarnan tata… yanzu yaxanyi?” ya fadi yayinda kwallah suka ciko masa idanuwa amma basu zubo ba, se faman hura mata kafar yakeyi da bakinsa. “Dole fa se an cire kwallar inba haka ba kafar zatayi ta kumburi ne…” Cewar zaks.

 

Am sorry sekun jini da next page insha Allahu.

Manyan mata adingayi ana gyaran kayan oga, 08101626484 is only chart, ko kin kira kashe take in zakise magani zaki iya kirana ta wannan lambar, amma pls masu siyan book Karki kirani kawai ku dubani a chart dan Allah masoyana ina kaunarku more… call 07034685493.

Saadatubintuabdullahi💖

Back to top button