Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 30

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na talatin_

____________

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

________

……Kurɓarta kusan uku ta fara jin yunƙurin amai. Ita dama zazzaɓinta kenan. Bata son abinci, dan ko an takurata taci zata iya amansa. Da sauri ya amshe mug ɗin tare da riƙota. A bazata, matuƙar bazata ta jita a jikinsa hannunsa saman bayanta yana shafa mata kamar yanda akanma yara idan ana son lallashinsu. Wani irin yuuu ta sake ji saboda tasowar aman da shaƙar ƙamshin turarensa. Jikinta taja da sauri tana toshe bakinta da hannu, kafin ma yay wani yinƙuri ta dire ƙasa. Ƙofar da ta gani a falon kawai ta nufa da gudu fatanta kawai ace bayi ne a wajen. Takoyi sa’ar hakan, dan kuwa ƙaramin toilet ne dake tsaf-tsaf yana ƙamshi alamar ana kula da shi yanda ya kamata. Bama wani aman kirki tayi ba saboda babu komai a cikin nata sai shayin nan da ɗan malt.. da Gwaggo Safina ta matsa mata tasha sanda suka iso. Yanda take yunƙurin aman ya haddasa mata rashin ƙwarin jiki. Daga duƙen da take ta dinga jin kamar juwa zata kwasheta, baya tai da nufin jingina da bango taji an riƙota. Bata da zaɓin daya wuce kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke numfashi guda-guda.
A hankali cikin nuna damuwa da yanayin nata ya furta, “Sannu! Kin gama”.
Kanta ta ɗan ɗaga masa tana lumshe idanunta. Sosai jikinta ya sake ɗaukar zafi. Taimaka mata yay ta wanke bakinta, a bazata kawai taji ya ɗauketa gaba ɗayanta. Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta maidasu da sauri ta rumtse sakamakon haɗa ido da sukai da shi. Bata sake gigin buɗe idonta ba sai da taji ya direta akan wani lallausan abu, ga sanyi da wani irin ƙamshi mai shegen daɗi na ratsata. Kaɗan ta buɗe idon tana dunƙule jikinta waje guda. Gado ne babba da yaji shimfiɗu na alfarma, sai dai rashin yawaitar hasken ɗakin yasa bata iya tantance sauran abinda ke cikinsa ba. Dan shi kansa ba wani ganinsa take sosai ba da ƙyau. Jin ya yafa mata ƙaton blanket ɗin gadon mai shegen laushi ta sauke ajiyar zuciyar da har sai da yaji sautin hakan. Baice komai ba yaje ya kashe ac ɗin gaba ɗaya. Wani ƙaramin freight dake a ɗakin ya nufa. Madara ya ɗako mara sanyi sosai da ruwa ya dawo bakin gadon ya ajiye, sai kuma ya sake fita a ɗakin babu jimawa sai gashi ya dawo da tarkacen maganin da doctor ya bada da allura da zai mata da kansa dan ya iya. Zama yay a bakin gadon saitin cikinta har tana iya jin kamar ya jingina da jikinta kaɗan, dan haka ta sake ɗan takurewa waje guda a cikin bargon. Allurar ya haɗa sannan ya yaye bargon batare da yayi magana ba ya ɗaga farar rigar ƙasan ta fulanin dake sama kaɗan, ya kuma zama zanin shima. Wani irin dukan uku-uku zuciyarta keyi amma ta dake da son tabbatar da abinda zai yi. Jin shigar allura jikinta yasata rumtse ido sosai, dan akwai ɗan zafi kaɗan. Shi da kansa ya murza mata wajen dan haka ta kasa buɗe idanunta har ya ɗagota ya zaunar. Madarar nan ya saka mata a baki cikin lallashi ya ce, “Daure kisha kaɗan sai kisha maganin”. Sam bata so, amma girmansa da yanda ya cika mata ido ya hanata iya masa musu. Haka ta daure ta ɗan sha kusan kwata ɗin robar sannan ta kauda kanta. Baice mata komaiba ya ajiye ya bata maganin. Tana gama sha kanta a ƙasa muryarta na rawa ta ce, “Bara na koma can kar su Gwaggo suga na daɗe”.
Idanu ya ɗan zuba mata kamar bazaice komai ba, har sai da ta tsargu ta ɗago ta kallesa. Maidawa tai da sauri cikin dabircewa. Ɗauke nasa shima yay tare da miƙewa ya kauda kayan maganin daga gaban gadon sannan ya dawo inda take. Batare da yayi magana ba ya kamata ya kwantar a hankali, blanket ɗin yaja ya rufa mata zuwa ƙirji, sai kuma ya ɗan zuba ma fuskarta datai takwaf-takwaf kamar zatayi kuka ido. Kamar mai raɗa ya furta, “Miyasa baki son nan ɗin?”.
Kamar mai jira da rawar murya tai saurin faɗin, “Su Gwaggo duk suna nan fa. Kuma ance musu kawai zanga doctor ne na koma kaga babu daɗi suji shiru ko?”.
Yanda ta ƙare maganar cikin sigar tambaya ya sashi sakin ɗan murmushi, sai kuma ya saki bargon dake cikin hannunsa har yanzu ya ɗan shafo black beauty face ɗinta mai santsi da laushi. Rumtse idanunta tai da sauri tsigar jikinta na wani irin tashi. Hannunsa na akan fuskar batare da ya janye ba ya ɗan ƙara duƙowa kanta sosai har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskar tata. “Su Gwaggo bazasu taɓa jin rashin daɗi ba sai dai ma suji farin cikin kwananki a nan tare da mijinki, in dai nine ki kwantar da hankalinki zan baki isashen lokaci na hutawa, sai dai ba hakan na nufin bazan iya canja shawara ba okay”. Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga kumatunta kaɗan ya miƙe daga ranƙwafar da yay a kanta.
Da kallo ta bisa zuciyarta na wani kalar tsitstsinkewa, sam tama kasa fahimtar kalamansa na ƙarshe balle gane ina suka dosa. Bayi ya shiga, babu jimawa sosai sai gashi ya fito. Ya shimfiɗa sallaya tare da daidaita tsaiwarsa ya kabbara salla. Ajiyar zuciya ta ɗan saki kaɗan tana gyara kwanciyarta, a haka barcin dake rinjayar idanunta yaci galaba a kanta. Can cikin barci sama-sama taji hawowarsa gadon, bargon ya gyara ya shiga, tana ɗan jiyosa sama-sama yana addu’ar barci, harya kammala ya shafa mata itama sannan ya kwanta a gefe yabar ƴar tazara a tsakaninsu. Daga haka bata sake jin motsinsa ba barci mai nauyi yay sake sureta…..

_____________★

Abin duniya ya gama dabaibaye Kainaat, ta rasa ta inama zata ɓulloma mayen yaron nan daya zame mata akwatin maciji. Tayi haukan, tayi kissar, tayi lalashin amma kamar tana ma ƙaramasa ƙarfi ne. Har sallamarsa tai daga Company aiki amma ya tabbatar mata bata isaba. Idan kuma ta dage to wlhy zai tona mata asiri wajen staffs dinta game da aurensu. Kainaat mace ce mai son girma, sannan tana da son adana sirrinta ga na ƙasa da ita shiyyasa ta kasance mai matuƙar taka tsantsan. Hakan yasa ta janye maganar sallamarsa dan sam bata buƙatar abinda zai zubda mata daraja a wajen staffs nata. Sai dai ta sake kasawa ta tsare akan komai na Companyn ta yanda Dafeeq bazai iya mata suruf bahana ba.
A tare kullum suke zuwa aiki su kuma dawo tare, dan sun adana matsalarsu a iya gidansu batare da wani a gefe ya sani ba idan ka cire Nadwa da Kainaat kan sanar mata domin ta bata shawara. Sai dai ma kamar Dafeeq ɗin na gani har hanji ne, dan duk shawarar da Nadwan ta bata sai ya wargazata. Yauma kamar kullum a tare suka baro office ɗin. Dafeeq ne ke tuƙi ita kuma tana gefensa tana danna sabuwar wayar data saya, tuni ta maido komai nata na waccan tsohuwar wayar dake a hannunsa anan. Ta kuma sami nasarar dawo da kuɗaɗenta na bank da Dafeeq ya kwashe ta hanyar wani ɗan uwan su Nadwa Manager ɗin bank ɗin da kuɗin ke a ciki. Dan sun kai report bisa shawarar Nadwa akan cewar ɓarayine suka sace mata bag. Sa’ar da aka samu shi Dafeeq bai kwashe kuɗin daga account nashi ba. Baifi kwana uku kenan da dawowar kuɗin ba, sunci uban faɗa kuwa dan harda marinta yay ta rama. A yau ne ma suka ɗan shirya har suka nufi office ɗin tare. Dafeeq kuwa ya sakko ne saboda wani shiri da yake ƙullama zuciyarsa, yayinda ita kuma ke faman masa shan ƙamshi.
Kallonta ya ɗan yi yana mai sakin murmushi, sai kuma ya sake damƙe steering da ƙyau tare da maida idonsa ga titi yana faɗin, “Dan ALLAH bamu birgeki ba, jibemu shar damu kamar ka sace ka gudu. Hajjaju mu kauda wannan abubuwan mu zauna lafiya mana Please”.
Shiru kamar Kainaat bazata kulashi ba sai kuma ta ɗan ɗago ta kallesa. Ganin hankalinsa na akan hanya ta maida kanta ga wayarta da faɗin, “Wani abun kake shiryawa kenan?”.
“Oh oh, ke shikenan baza’ai zaman lafiya ba sai ana shirya wani abu. Hajjaju karfa ki manta soyayya ce ta haɗamu, kece kuma kika fara min tayinta, sai da na zurma sosai kike neman mani illa kuma”.
“Oh saboda ni na fara maka tayinta shine ka amsa da manufa?.”
“Ko ɗaya baki canka dai-dai ba. Da zuciya ɗaya na amshi soyayyarki, tunda ke shaidace saboda ke na rabu da matata da nake tsananin so da ƙauna. Idan ma kina faɗin hakane saboda kwashe kuɗinki na banki da takardu ni nayi duk wannan ne saboda gano kece kika aureni da manufar rabuwa da ni bayan cikar kwana bakwai. Haba hajjaju, wane sakaraine zai sami zuƙeƙiyar mace irinki ya saki. Da ace tun farko kin sanrmin auren kisan wuta zakiyi bazamu kai ga wannan matsalar ba, amma kika shirya mun rufa-rufa. Ni kuma shiyyasa na kwashe kuɗi da takardun Companyn danna ɗaureki. Nasan dai suna hannuna bazaki taɓa rabuwar dani ba zaki ce saina baki”.
Tsaff kalamansa suka tsaru akan Kainaat, dan kamar wadda jikinta yay sanyi ta ɗago tana kallonsa. A bazata yaji ta furta “Yanzu a ina kaji wannan zancen haka Dafeeq?”.
Murmushi yayi mai bayyana haƙora, sai kuma ya ɗan kalleta da faɗin, “Zancen duniya ai baya ɓuya Hajjaju. Amma karki damu in dai nine ban ɗauka da zafi ba duk da da farko naji haushi. Amma yanzu na yafe miki. Fatana kawai shine ki janye ƙudirinki nima zan janye nawa harma na baki sauran takardun hannun nawa. Amma zan baki lokaci kiyi tunani dai”.
Kai kawai ta jinjina masa zuciyarta na wani irin rawa kamar zata faɗo. Amma batace da shi komai ba ta fita a motar dan sun riga sunzo gida. Da kallo ya bita yana wani cije lips, sai da ta shige falonsu ya kwashe da dariya yana buga sitiyari da faɗin, “Shegiya zaki gane kuranki tsohuwar guzuma kawai kin sa na rabu da ƙyaƙyƙyawar mamata ƴar shilax, wlhy kika yarda kika faɗa a wannan tarkon nawa kin gama kaɗewa. Khadijah kuwa tana gab da dawowa gareni. Dan wani zan nema ya aureta ya saketa batare da shi da ita sun san plan ɗina ba. Zan saida Companyn naki na ɗauke Dijoh na mu bar ma ƙasar gaba ɗaya”. Ya sake ƙyalkyalewa da dariya harda ƙyaƙyƙyawa na ƙeta..
A falo ya samu Kainaat kwance tana hutun gajiya, ido suka haɗa, a bazata ta sakar masa murmushi. A ranta kuwa faɗi take (shegen kaya kenan, ai nasan wannan kwantar dakan naka na sabon shiri ne. Amma babu komai zanyi amfani da shirin naka na gama da kai cikin sauƙi batare da ka kawo min wata tangarɗa ba. Kafin ka farga ka dawo tafin hannun Kainaat. Zan tabbatar maka ni da kai CUTA CE TA ƊAU CUTA… shegen yaro mai wayo kamar ɗan dila).
Martanin murmushin ya mayar mata, tare da takawa a hankali inda take ya zauna. Ɗagota yay ya rungume a jikinsa. Hakan yasa itama rungumesan suka saki ajiyar zuciya a tare. Daga haka labarin ya fara canja salo. Duk da Kainaat taso dojewa daga baya ya hanata kowacce irin dama.. Sai da ya tabbatar ya samu abinda yake so sannan ya barta yana dariyar ƙeta. Danne zuciyarta kawai tai tana biye masa da murmushin fatar baki, a haka sukai wanka tare, sannan suka dawo ƙasa ta dafa musu noodles sukaci a tare. Bayan sun gama falo suka sake komawa suka kunna kallo, tana zaune shi kuma yana kwance yay filo da cinyarta. Lokaci-lokaci sukan kalli juna su saki murmushi, a ƙasan rai kuma kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa, dan su duka babu wanda hankalinsa ke akan kallon..
Dafeeq ne ya katse shirun da faɗin, “Bakice komai ba Baby. Dan ALLAH ki ajiye makamanki mu zauna lafiya mu rungumi junanmu. Na tabbatar miki zan koma miki fiye da bawa a gidan nan”.
“Humm Dafeeq ina tsoron na sallama ne kaci amanata”.
“Babu wannan maganar ki yarda dani”.
Ɗan jimmm tayi kamar mai nazari, sai kuma zuwa can ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Okay shike nan na amince. Amma zamuyi komai a rubuce ka yarda”.
“In dai nine baki da matsala dani a yanzu. Tunda kin san gidanmu, kin san iyayena, mi kuma ya rage to”.
Cike da gamsuwa ta ce, “Hakane”……..✍️

_Ni dai nace Humm. Kufa masu karatu kuna da abin faɗa?._

_________

Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846

Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria

Ummu khalifa 01017018846

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button