Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 32

Sponsored Links

Page 3️⃣2️⃣

 

 

_____ ” babansu yakamata kafada musu komai dangane da fanan kar azo daga baya abu yazo yacabe ” cewar mama dake zaune tana facing din baba , Maida hankali baba yayi gunta yace ” haba sumayya ta taya kike tunanin zan boye musu wani abu dangane da yarmu nafada musu komai domin me martaba Shima ashe yanada labarin amma besan wacece takamemmen sarauniya ba ” yafadi hakan ayayin da yake bude wata locker dake jikin wardrobe dinshi kudi yafito dasu akalla sun kai dubu dari hudu ” Kinga wannan kudin ki kira firdausi kibatasu taje kasuwa tasiyowa fanan kayan sawa dakuma akwatin da zaa sasu amma banda atamfa shi innaje shago zabayar wa tela yamata dinki ” yamika matasu ahannunta karba tayi tana jujjuya kudin ahannunta hawayen dake kokarin zubowa a idonta ta mayar dasu tana fadin ” yanzu kenan fanan ayau zatabar gidan nan tun kafin ta tafi nafara kewarta bansan wace irin rayuwa yata zatayi atare da wanda bayason taba ” shikanshi baba abin yadameshi amma hakan shine ze samo musu sauki , girgiza kai yayi kafin yace ” karki fadi haka aure anriga da anyishi amatsayinki ta mahaifiyarta adduah kawai zaki mata na zaman lafiya agidanta ” jiki asanyaye mama tace” hakane Allah yabasu zaman lafiya ” ameen.

____ ” haba azaad sekace baka da tausayi dan saboda kaine fah wannan abun yafaru da yarinyar nan Yakamata da akayi maganar auren nan kabada goyon bayanka dari bisa dari amma ko kunyar iyayenta bakaji ba afili kace bakason yarsu ” cewar yaseer da dawuwansu kenan yashigo part din Azaad, duk wannan maganganu dayakeyi azaad najinshi kalla bece mishi ba shikadai yasan abinda yake damunshi duk bazasu fahimmce shi bane, tashi yayi yazauna yana kwabe fuska yace ” yaseer nasani nasan saboda nine sunan yarinyar yabaci kuma am willing to do anything daduk karfina wajan ganin nawanke sunanta amma aiba dole seta hanyar aurenta ba ! Can you imagine wai kamar ni azaad muhammad mainasara the billionaire nizaawa auren dole unbelievable, bana sonta kwata_kwata kuma banajin zan iya sonta saboda she’s still kid to me akwai sauran yarinta akanta and tamin karama , duk inda aka ambaci aure yashiga tsakani to andauki amanarta ne anbaka kulawa da ita, lafiyanta rashin lafiyanta dakuma tarbiyanta se adalci nikuma yanda banasanta banajin zan iyayin daya daka cikin wayan nan abubuwan shisa bazan iya zama da ita ba ” tabbas abinda azaad yafada haka shin ze iya kula da fanan ne ko baze iyaba mutumin da ko kadan mata basa gabanshi be masan tayanda zekula dasu ba wani irin tausayin fanan ne yakamashi amma yasa aranshi in sha Allah seyayi iyayinshi naganin ya dedeta tsakaninsu da iKon Allah.
_____ ” to yanzu de ba wannan ba kashirya ayau zaa kawo maka amaryaka kazama cikin shiri dan acikin daren nan Yakamata ka angonce ” cike da shakiyanci yaseer yake maganar dan yasan yanzu ze fusata azaad, uhmmm kawai azaad yafada yana aiyanawa aranshi inya kusanci wannan jaririyar aiseta kusan mutuwa, Yaseer de tashi yayi yabarshi adakin dan yaga azaad inya fusata zasuyi dauki ba dadi.

Anty firdausi ce da mama, suhaima,Amira,auta afalon suna zaune sunata bubbude kayan da anty firdausi tasiyo da kudin da baba yabada kayane nagani nafada akwati biyu masu kyau abaya ne da akalla zasu kai guda ashirin se wasu fitinan nun kana nan kaya nahutawa dakuma liffaya suma sunkai 20 da takalma da jaka se jewelries nagani nafada kaya de masu matukar kyau suna zaune suna kallon kaya ya usman da ya al ameen suka shigo suma hannunsu niki_niki rike da manyan ledoji na kayan cosmetics daga abinda yayi kan turare, kayan make up, lotion,soaps shower gel, shower perfume etc. Shirya kayan akayi duka a akwatu nan se aka fitar mata da wanda zatasa yau suka gama shiryasu tsaf. Ana kiraye_kirayen sallah mangrib mama tace ” firdausi yakamata kitashi kuje ki shiryata kinga lokaci natafiya kar babansu yashigo yasamu baa kammala ba” Daukan kayan dazata sa anty firdausi tayi takai dakin tasameta tana kwance tabawa kofa baya zagayowa tayi gabanta idonta biyu ba bacci takeyi ba , hannu anty firdausi tasa tadagota tazauna murya asanyaye tace kitashi kije kiyi wanka tare da alwala inkikayi sallah sena shiryaki ” babu musu tamike tashiga wanka, tayi wankan tadauro alwala tafito daure da towel amma ta rame fuskanta fayau dogon rigar jallabiyarta tasa tadau hijab ta tada sallah seda tayi adduah sosai kamin tadan jabaya tajinginu da jikin gadon . Matsowa kusa da ita anty firdausi tayi tarike kafadarta sannan tace ” fanan kidena sawa kanki wasu irin tunani ki karbi komai ayanda yazo miki kuma kikara da godewa Ubangiji yasa hakan shine mafi alkhari domin duk abinda kikaga yasamu bawa to muqaddarine daga Allah , nasan tunaninki ya karkata akan wani irin zama zakiyi da mijinki da bayasonki to kisani wannan abu ne me sauki inkika kara mika lamuranki ga Allah sannan ahankali hankali zakike cusawa mijinki sonki azuciyarshi mu mata inde mukaso babu tayanda bama bi da namiji duk yanda kikaso zaki iya lankwasashi domin namiji zumane seda wuta kisa aranki zakuyi rayuwar farin ciki kedashi ko bakuyi ayanzu ba zakuyi nan gaba zanyi duk iya kokarina wajan tallafa miki kina dani kidenajin wani kunya kinji ko ” gyada mata kai tayi domin kalamanta sun kwantar mata da hankali tadanji relief, karajin kwarin guiwa tayi.

Jin datayi anshiga sallan isha ne yasa ta tashi ta tada kabbarah bayan ta idar ne anty firdausi tace mata tazauna agaban mirror zama tayi kamar yanda tabukata miko mata wasu mayuka masu bala’in dadi tayi dan tashafa shafawa tayi tana jin kamshin har tsakiyar kanta light make up anty firdausi tamata karkuso kuga fanan yanda tayi kyau da make up din nan, Mika mata wando na jeans dakuma yellow din body hook me dogon hannu tayi karba tayi tasa bakaramin kamata sukayi ba tab sukamata sunzauna ajikinta sosai hips din nan kamar zasu faso wandon sufito , liffaya anty firdausi tadauko fari sol medan touch din yellow ajiki nada matashi tayi mekyau ajikinta ta mata dauri da dolface yellow gashin kanta kuwa dauresu tayi seya zama kamar gammo dan kunne da sarka tasa mata se awarwaro da abin hanci me dan karamin stone rufa mata liffayan tayi ajikinta tako Ina harda fuskanta sannan tafesheta da wasu mayun turare masu kamshi sosai tabata takalmi white color se hand bag dinta,shiryata tsaff tayi wani irin kyau da fanan tayi mara misaltuwa tafito sakk amarya , rikota anty firdausi tayi tazauna akan gadon tana kokarin rufe mata fuska kenan segasu amira, suhaima sunshigo suma sun gama shiryawa cikin atamfa sunyi kyau sosai zama sukayi akusa da ita suna yaba irin kyaun datayi kamar su saceta sugudu duk yanda takai da basar dasu seda suka dan sata dariya, dan dazunma dasuka shigo dakin dataga zasu dameta kawai tasharesu tajuya musu baya.

Anty amina, anty shayida anty Zainab se zeenat ne zasuje dauko amarya su yaseer da fawwaz ne zasu kaisu duk sunci ado abunsu suka nufi anguwarsu fanan motar uku kawai suka dauka dan baason ayi yawanda zaa gane,bayan su isone suka shigo falon mama suka zauna suna Kara gaisawa mikewa anty firdausi tayi tashige dakin tariko hannun fanan da fuskanta yake arufe dakin baba sukayi domin yamata nasiha

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story Written by…
MRS ISHAM

 

 

 

 

 

Check Also
Close
Back to top button