Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 25

Sponsored Links

Abangaren gidan su fanan kuwa yanzu shirye_shiryen saukan fanan akeyi haka gidansu amira ma Dan makaranta daya sukayi DHARUL_HUDA.
Dukansu suna zaune afalo harsu baba yau basu fita kasuwa ba saboda shirye_shiryen saukan gobe dazaayi, fanan nazaune itada suhaima atsakiyar falon hannunta dauke da jotter da pen tana rubuta list din mutanen dazasuzo tana sanye da wando falazo black me manyan fulawi fari tanason falazo sosai dan tafi sakewa acikinshi, se farar riga kanta da hula ita kuma suhaima list din abubuwan da ake bukata take rubutawa,
Dago Kai fanan tayi tace “mama nagama rubutawa bansan ko akwai wayanda suka rage ba ” suhaima ce tace ” kin saka gidansu ummi a list kuwa ” ” ah ah bansa ba basuma san zanyi saukan ba shisa bansa ba” cewar fanan dake kokarin rubuta sunan nasu a jotter ta, mama ce tace ” aikuwa de yakamata asa inyaso tunda basu saniba anjuma al ameen seya kaiku gidan kubasu kati ” to shikenan, mikawa ya usman list suhaima tayi dan tagama rubutawa karba yayi yana dubawa can kuma yace ” iyakacin abinda ake bukata kenan !? Naga kamar list din yayi guntu” Yana magana yana kallon list din Jin abinda yafada ne yasa mama tace ” inga ni” tashi yayi yaje yabata yadawo yazauna , duddubawa takeyi pen tadauko ta kara rubuta abubuwan dabata gani aciki ba bayan tagamane tamikawa baba yakarba yace” shikenan ko ” eh sukace, mikewa baba yayi yadauki car key dinshi yace ” Usman tashi ka tada mashin dinka ka kaini indauko motar muje kasuwa kaikuma Al ameen seku shirya kuje ka kaisu ” dukansu Mikewa sukayi mazan su ya al ameen sukayi waje sukabi baba , ya usman yatada mashin baba yahau suka fita daukan motar saboda gidan baze dau motar biyu ba shisa baba yake baro nashi a inda ake gadin motoci yacewa ya al ameen yadinga packing din nashin kawai, fitowa fanan sukayi harda auta itama zatabisu dogon hijab duka sukasa , suka sameshi a motar shiga sukayi yatada motar suka kama hanyar gidansu azaad, fanan kwatance tadinga yimishi harsuka iso fitowa baba me gadi yayi ganin bakuwar mota yasa yazo dubawa dan leko kai fanan tayi tagaisheshi washe fuska yayi ganin itace yakoma yawangale musu gate shiga cikin gidan yayi , bayan yayi packing suka fito, hango zeenat da fawwaz fanan tayi alamun fita zasuyi karasowa wajan su sukayi mikawa ya al ameen hannu fawwaz yayi sukayi musabaha idon fawwaz ne yasauka acikin na suhaima dake gaisheshi murmushi yayi ya amsa kafin ya amsa na fanan cike da farin ciki ganin fanan zeenat tace” Allah kawata gaskiya nayi missing dinki naso zuwa sekuma Abba suka dawo jiya yanzu kuma ya fawwaz ne zekaini shopping segaku nan tom muje ciki ” dariya suhaima tayi tace ” ummm nadauka nikadai akecewa inada surutu yau naga wanda tafini ” dariya zeenat tayi cikin yauki tace ” yanzu dan Allah ni inada surutu yar shuru_shuru dani” fanan de shuru tamusu dan wayan nan biyun intace zata biye musu suta hiran basu taba gajiya ba , kallon suhaima da auta tayi taga suna kama da fanan nan tagane yan uwanta ne riko hannun auta tayi tace ” zo muyi gaba fine girl tunda antynki taki kulani yau ” wucewa sukayi ya fawwaz sukabi bayansu afalon kasa suka samu duk yan gidan harda su abba banda azaad dake can yana kwance shigowa sukayi da sallama abakinsu bismillah fawwaz yamusu basu zauna ba se suka tsunguna har kasa suna gaishe da Abba kafin suka gaida ummi da anty Amina bin mazan falon ya al ameen yayi yana basu hannu suka gaisa cikin mutuntawa kafin yazauna, ummi ce takalli fanan ” su fanan tunda patient dinki yasamu lafiya aka guje mu ko !?” Cikin jin kunya ta sunkuyar dakai sannan tace ” ah ah ummi bahaka bane shirye_shiryen sauka nane yasha min kai shisa kuka jini shuru ” Abba tunda fanan tafara magana yake kallonta Jin yanda take magana cikin nutsuwa seta burgeshi sosai cikin barkwanci yace” ah ah umminsu kice wannan itace nurse din tamu kenan !” dariya suka danyi kafin ya cigaba ” yaushene saukan naku ?” Cikin nutsuwa da kunya fanan tace ” gobe ne yanzuma kati muka kawo muku ” gyada kai abba yayi yace ” Masha Allah awata makaranta ne!? Cikin zakin murya da yarinta auta tace” sunan makarantan Dharul_huda gobe da karfe 9 na safe zaafara atashi karfe 3 in akayi nasu anty semuma inmun je ajiya 6 muma zaayi namu yanzu ina aji uku ne” tagumi fanan da suhaima sukayi suna ganin iKon Allah yanda auta ke zaro zance sekace an tambayeta batasan mutane ba tazo tana musu surutu kamar wata parrot, ya al ameen de rike baki yayi , bakaramin dariya auta tabasu ba cikin dariya ummi tace” fanan kanwarki ce ko naga kuna kama sosai ” karaff auta zatayi magana fanan tadaka mata harara aikuwa ba shiri tayi shuru harda sa hannu abakinta,nanma dariya suka karasawa dan sunga hararan da fanan tamata bakaramin nishadi auta tabasu ba mikewa fanan tayi tamikawa Abba katin karba yayi Yana karantawa kafin yace ” fateema amma ya akayi makarantanku se yanzu takeyin nata saukan bayan yanzu wata biyu kenan da haddace Al qur’ani!?” ” Eh Abba dama haka tsarin islamiyarmu take inmuka gama aji shida semunje hutu mundawo zaayi saukan ” jinjina kai Abba yayi cikin gamsuwa da bayananta, ummi tace ” in sha Allah zaki ganmu” mikewa zeenat tayi tace ” kuzo muje daki ” dukansu mikewa sukayi sukabi bayanta Abba ne yace ” ohhh to zaku gudu dakin zeee kenan to ke zomuyi hira ko ” yafada yana nuna auta da hannu zuwa tayi tazauna akusa dashi ya tambayeta sunanta aikuwa nantake tafara zuba zance se dariya sukeyi dan sun lura auta ita kanta comedy ce girgiza kai fanan tayi Jin yanda auta tacigaba da zuba kamar ba dazun ta hanata ba aranta tana cewa Allah yashiryeki auta, fitowa azaad yayi yawucesu afalon yatafi garden dan yaseer yafada mai yana wajan, mikewa Abba yayi yacema auta ” karki je ko Ina kijirani anan indawo yanzu nan ” gyada kai tayi shikuma yawuce yabi bayan azaad dan akwai abinda yakeson su tattauna harya kusa shiga garden din yaji kamar ana binshi abaya juyawa yayi yaga Abba ne tsayawa yayi abba yakaraso suka shiga garden din tare gaida Abba yaseer yayi Yana mishi ya hanya suka zauna akan kujerun wajan . hira suke tasha adakin zeenat tana basu labarin time din datayi graduate nata se kallon photos sukeyi awayarta can zeenat tace “kutashi muje garden muyi pics ” ” nide sekun dawo ba inda zani ” fanan tayi maganar tana kokarin kwanciya, riko hannunta zeenat tayi tace ” wlh Baki isaba sekinzo munje munyi pics din nan ” mikewa tayi tace ” nide bazaku taba barina inhuta ba koh semuje ai ” tagama magana tana hararansu da dara_daran idanunta, ta corridor suka bi yakaisu bangaren azaad daga nan suka gangaro kasa sukabi ta kitchen suka shiga garden din basuma lura da su azaad ba da Abba se yaseer dasuke zaune suna magana ba, suhaima da zeenat suna gaba seda suka shiga tukun suka lura dasu Abba dake zaune zeenat ce tace ” laaaaah Abba ashe kuna nan Kuma ” juyowa sukayi suna kallonsu ” eh gamu nan munadan magana ne ” cewar abba, murmushi yaseer yayi yace ” ku karaso mana kuka tsaya agun” shide azaad ko tanka musu beyi ba suka karaso wajan, shigowa garden din fanan tayi cikin tafiyanta me kama dana mahauniya tana kallon flowers din bakaramin burgeta sukayi ba hartazo zata wuce taga wani kyakyawan bunch of flowers din masu kaloli daban daban tafiya sukayi da hankalinta tanufi wajansu duk abinda takeyi batasan su Abba na garden din ba suna hiransu suna kallonta, gaban flowers din taje ta tsaya can Kuma tasa hannunta tafara shafa su cikin nishadi tafi 5mint agun kafin ta juya zata tafi,cikin rada taji ance ” muna godiya sosai agareki da kika tabamu da hannunki me cike da karfin ikon jaaazana ” asukwane tajuyo Dan taga wayeke magana gani tayi bakowa awajan dan duk tunaninta bekawo mata akan maganar daga gun flowers din bane ganin bakowa ne yasa aranta tace” kila kawai gizo ne kunne na kemin” tafiya taci gaba dayi abunta sannu ahankali flowers din data taba suka fara girma sunayin tsayi harsuka fi tsayinta duk batasaniba tafiyanta kawai takeyi amatukar razane su Abba suka mike dan duk wani motsinta suna lura dashi ganin flowers din sunzo dabb da itane kamar zasu tabata suhaima tafasa ihu tana fadin ” wayyo fanan bayanki” jin ihun da suhaima tayine yasa azaad dagowa yana kallonsu ganin sun kafe waje daya da ido ne yasa yakai idonsa direction din dasuke kallo ” ohhh shit ” yafurta lokacin da yake kokarin tashi itakuwa fanan jin abinda suhaima tafada ne yasata zurawa aguje dan tamaki juyawa taga meye abayan nata, taku hudu zuwa biyar azaad yayi yakaishi inda take yarikota, rungumeshi tayi kam_kam kamar wacce zata koma jikinshi karasowa su yaseer sukayi inda suke suna ganin iKon Allah, azaad kallonshi yamayar kan flowers din dasuka girma suka zama kamar wasu bishiyoyi yayi ganin har time din basu koma ba suna tsaye kiqam yatsaya yayi wani tunani bakinshi yakawo dede kunnenta yace mata” kibude idonki sannan kijuya kikalli abinda ke gabanki ” lokaci daya taji duk wani tsoron datakeji ya yaye ahankali tabude manyan idanunta tadaurashi akan cute face nashi dashima kallontan yake runtse idonta tayi dan bazata iya kallon cikin idonshi ba danji take kamar lantarki najanta, su Abba de suna ta kallonsu ,juyawa tayi kafin tadanyi step kadan tanufi flowers din tafuskance su, nan take yayi wani irin girgiza kamar ze fado kasa furanni ne suka fara zubowa akanta suna zubewe akasa ga dadin kamshi seda suka zubo duka flowers din gaba daya seda suka kare ajikinta yanda suke zuban abun burgewa kamar a India ,seda yazamana wajan bakomai kasa kuwa kamar anyi ruwan fure tsaban yanda suka zuba, wani irin juyowa tayi kamar wata robot seda sukadan ja baya da irin juyin datayin kamar ba lafiya ba banda azaad dako motsawa beyiba, kanta akasa kafin slowly tadago fuskanta idonta arufe eyelashes dinta yayi zara_zara kamar wanda ruwa yataba shi , Abba de tunda yake arayuwarshi betaba ganin irin wannan Al amarin ba se a film yau gashi yafaru agidanshi mamaki kamar yakasheshi, haka suhaima da yaseer suma mamakin sukeyi banda zeenat da azaad dansu abinda suka gani ranan ma yarufe komai tunda TV yatarwatse wannan ai kadan ne, ganin dasukayi komatsawa batayi ne yasa Abba yace ” azaad jeka daukota ” zuwa yayi yakai hannunshi kan kafadarta yadan tabata , slowly tafado jikinshi ganin tasake nauyintane yagane ta suma cakk yadagata kamar yar baby yayi falo da ita su abba sukabi bayanshi, ganin azaad yashigo da fanan ahannu ne yasa duk suka mike kwantar da ita yayi akan kujera yadauko bottle water yabude goran yashafa mata afuska , da mamaki ummi take tambayar abba meya sameta bece mata bakomai ba yadauko wani zancen Yana cewa zeenat tamiko mishi agogonshi ,sauke ajiyar zuciya tayi kafin taware idonta ganin mutane atsaye akantane yasa tamike tanabin falon da kallo tunawa tayi da abinda yafaru a garden kokarin tashi takeyi anty Amina ta taimaka mata tazauna ya al ameen ne yakaraso kusa da ita yarike hannunta yace” yar kanwa dama bakida lafiyane!?” Yagama maganar yana jiran amsarta girgiza mishi kai tayi alamar ah ah ” to mutafi gida kinji ” nanma still gyada mishi kai tayi, azaad nazaune yana binsu da kallo musamman fanan din Aransa yake magana “tabbas wannan yarinyar akwai wani boyeyyen al amari atare da ita wanda iyayenta sunsan da haka suke boyewa , wani zuciyar tace kila ba mutum bace ita din kila aljanace amma ita bata saniba Kara kallonta yayi dakyau yaga de babu wani alaman daze nuna aljan ce, can wata zuciyar tacemai ko kuma rabinta mutum rabinta aljana ce, can kuma yayi tsaki jin shirmen da zuciyarsa kefada ” jin tsakin dayayi ne yasa suka juya Suna kallonshi ganin sunzuba mishi idone yasa yadaure fuska , gyaran murya Abba yayi yace ” al ameen zaku tafi amma sedan anjuma kaji” shikenan to Abba cewar ya al ameen. Hira suka zauna sunayi babu wanda yadauko maganar abinda yafaru balle fanan taji, kallon time abba yayi yace kuntashi mutafi masallaci duka mazan mikewa sukayi suka tafi masallaci, sukuma suka haura sama danyin sallah bayan sun idarne suka fara shirin tafiya gida, saukowa sukayi sukaga kowa na falon harsun dawo mikewa ya al ameen yayi yace to mutafi ko sallama suka musu Abba yace ” auta yanzu tafiya zakiyi baraki tsaya kimana hira ba haba auta ” cikin dariyarta tarufe fuska tace ” to ai abba zanzo kawo muku katin saukana nima ” dariya akayi jinwai zata kawo musu katin saukanta saukan daba nan kusa ba , fanan de girgiza kai kawai tayi manyancen auta har tsoro yake bata kamar wata babbar mace, shikanshi azaad seda yaji yarinyar ta burgeshi dukda bayason yawan surutu, fitowa ummi tayi Abu me aiki nabiye da ita rike da ledoji niki_niki tace ” yauwa autana ga chocolate ” zaro ido tayi takalli fuskar fanan taga ya reaction dinta yake karta kabar tayi laifi ganin murmushi akan fuskantar ne yasa ta kalli ummi tace” angode sosai ummi Allah yasaka miki da alkhari yakara budi ” amsawa sukayi dukansu da Ameen Ameen suna jinjina irin tarbiyan da yaran suka samu dan kallon azaad tayi dukda dazun bata ganshi ba dasukazo, kamar zata tafi kuma setace “bye_bye Yaya balarabe” kallonta yayi kafin cikin daddadar muryanshi yace ” bye bye ” bakaramin mamaki sukasha ba dan dukansu basuyi tunanin zebata amsa ba, seda tabi kowa na falon tana musu bye_bye , seda sukaji kamar karsu tafi dan dukkansu sunada saurin sabo barinma auta data dinga basu comedy yau, fawwaz da areef se zeenat da yaran anty amina ne suka fito rakasu suka shiga motar suna musu bye_bye fawwaz se satan kallon suhaima yakeyi (in yeeeh su fawwaz kenan love at first sight) seda suka tafi tukun suka koma cikin gida duk suna shiga falon suka tadda abba na waya da wani abokinshi bayan yagama ne yacewa ummi” Amma wannan yarinyar aina kuka samota” bashi labarin yanda takula da azaad dakuma abubuwan dasuka faru na tv dakaita gidansu dasukayi ummi tayi , jinjina kai Abba yayi sannan yaci gaba ” wannan yarinyar akwai wani abu atare da ita tabbas amma koma menene Allah yakawo musu shi dasauki dan yarinyar takwanta min arai yanayin nutsuwarta dakuma irin tarbiyan dasuka samu agidansu abune na ayabawa iyayensu” anty Amina ce takarbi dacewa ” abbana nifa anawa ganin yarinyar nan akwai wani abu ajikinta ne” azaad dayamike zewuce part dinshi kamar Wanda akawa dole seyayi magana yace ” babu abinda yake jikinta itadince dakanta ” ya haura stairs abunshi , cike da Al ajabi sukebin bayanshi da kallo dan yasasu aduhu meyake nufi da itadince dakanta.

Shigowa gida sukayi nan suka samu su baba ma sun dawo anyo cafenen Abubuwan dazaayi amfani dasu harda rago saboda yanka dakaji shiga cikin falo sukayi sukasamu mama tana fifito da wasu kayan aleda sallama sukayi suka zauna suka gaisheta kafin ya al ameen yace “mamanmu ina usman yayi!? ” “Ah ah ameenu yaron nan gaskiya tunda suka dawo banganshi ba kakirashi kaji mana ni kwana biyu nan narasa gane meke damunshi gaba daya yazama wani iri ” tana maganar tamikawa fanan wata farar leda me girma ta karba kafin tabawa suhaima ma nata fita yayi dan, yadubo ya usman din , budewa tayi taga sabuwar abayace aledarta me matukar kyau da tsada dark maroon jikinshi yasha stones ga hijab dinta fari dogo harkasa me hannu dakuma takalminta da nikaf me hawa uku murmushi ne yasubuce akan face dinta tana kara godewa Allah daya kasance suna da rufin asiri dede gwargwado dan baba dan kasuwane yanada shaguna guda uku a main market (babban kasuwan gombe) Daya shagon atamfofi daya shagon cosmetic nan ne ya usman yake ciki dan yamallaka mishi shagon sekuma dayan shagon provision ne babu abinda baa siyarwa aciki , suhaima ma bude nata tayi taga itama abayarce sak irin na fanan sede color ne ya banbanta nata pitch color ne se hijab dinta gray color dasu takalminta cike da murna take godiya cire hijab dinsu sukayi suka fara taya mama aiki har dare kafin suka samu suka huta sun rage aiyuka sosai.

 

 

 

 

 

Hakikanin gaskiya jiya nayi matukar Jin dadi da adduah ku agareni nagode sosai da sosai allah yabar zumunci Kun nunamin kauna matuka. Shisa nace yau bari ingwangwajeku da read more dari

Wayanda sukasan basa comment section suyimin magana ta private. Sannan Batu akan comment Yana nan daram yawan comment dinku yawan read more dinku, tsakanin jiya da shekaran jiya naga comment galan galan duk dama wayanda suka bini private sukayi sunfi yawa, godiya mara adadi.

 

Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & Written by (MRS ISHAM )

 

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

 

Free book

 

꧂꧂꧂꧁꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁

 

&______________________________________&

 

 

 

Back to top button