Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 35

Sponsored Links

35
Ajiyar zuciya Bilal ya sake saki a hankali tareda sake rungume DD yana Jin nutsuwar daqiqun.

DD dayasan Bilal ciki da Bai a take ya Jiyo damuwa a tare da Bilal din daga rungumar kawai sbd Allah yayi masa wata fitinanniyar baiwar karantar mutane ko a yanayin Aiki da jininsu.

Sakin juna sukai ahankali
Naseer yayi saurin miqa hannu babu kamewar komai DD ya miqa nasa hannun Naseer yayi saurin kamawa Yana cewa

“Munyi kewanka sosai Sir D,barka da dawowa”

Idanuwansa dake sake rudar da Naseer din cikin farin cikin ganinsa ya dago ya kallesa tareda gyada masa Kai a hankali cikin nutsuwa kafin suka wuto zuwa motocinsu.

Umme Kallo Daya tayiwa Bilal bayan tsayuwarsu gurin taji jikinta gabaki Daya na Neman sanyi murnarta na Neman komawa ciki sbd rama da sanyin dayayi.

Tabbas akwai qunci ko damuwar dake damunsa Dan haka daga ita har Zeenah jiki a matiqar mace suka rungumesa Shima yanajinsa jikin mahaifiyarsa Mai tsananin so da kaunarsa jikinsa ya sake mutuwa Yana kokarin danne damuwar dake shimfide cikeda ransa.

Kaman Umme ba zata sakesa ba Amma haka suka nufi motacin hannunta na riqe cikin na Bilal din Wanda ya kasa hada Ido da ita sbd tausayin Kansa da nata da ranta zaiyita Baci yanzu akan duk Abinda akeyi masa na nuna bambamci da rashin kauna kaman sauran.

A qa’idar DD ko motocinsa na Hawa gabaki Daya black ne,
Black Mercedes beymach Naseer yazo daukansa shikuma Bilal da tasa motar yazo daukan su Umme.

Luggages dinsa Naseer ya zuba a motarsa yafara wucewa dasu gidan DD din Kai tsaye shikuma ya shiga motan Bilal sbd su tafi kaantes tare daga baya zai tafi gidan idan yaga dd babba da dad dinsa.

A hanyarsu ta Isa gidan gabaki Daya motar babu me magana sai ummen dake kokarin fahimtar Abinda yake damun Bilal.

A rayuwarta ita Kuma kusan tafi so da kaunar Bilal din fiyeda komai da kowa,
Ya taso a wata gurguwar rayuwar rashin gata da zallan banbanci da ake masa tareda ganin kaman alfarma ce Akai masa yake zaune acikin kaantes din shiyasa yake ‘dan wahalarsu duk Wani wahala da aikin da babu Mai iyawa akansa yake Kuma duk a banza babu Mai nuna godewa ko daukan Hakan a matsayin kokari da fasaharsa saidai a alfarma da ake masa Dan haka ta fifita soyayyarsa itama akan sauran ‘yayanta kada abin yayi masa yawa ya samu matsala.

Suna Isa kaantes take securities suka Bude musu gate motar ta shige suna daga hannuwansu Dan isar da sakon barka da zuwa ga Sir DD kaante.

Babu me matsayi ko muqamin da dd babba ke iya fitowa tarba a gidan bayan Dawood Dan haka Koda sukai parking harabar gidan dd babba Yana tsaye Yana jiransu kaman yanda ya Saba tarbon Dawood duk zuwan Dayake Yi.

Abbakar ne yayi saurin qarasawa ya budewa DD kofar motar bakinsa a washe Yana masa barka da zuwa cikin girmamawa.

Fitowa DD din yayi Yana nufar dd babba Wanda ba kasafai kake ganin dariyarsa ba saidai murmushinsa Amma bayyanar Dawood gabansa baya iya riqe ko taqaita farin cikinsa Dan haka hannu ya ware Shima Dawood din qarasowa yayi a natse ya rungume dd babban.

“Welcome my Lion”

A hankali ya saki Wani qayataccen murmushin Daya saka dd babba dagosa Shima Yana murmushin.

Gaisuwar Umme dake gaidasa cikin girmamawa da sakewa ya amsa kafin ta Zeenah dake gefensa itama tana gaidasan.

Motar Dad kaante ce ta shigo harabar gidan suka tsaya duka suna kallansa driver ya Bude masa ya fito ya nufosu Kai tsaye Shima fuskarsa dauke da farin cikin ganinsu musamman DD duk da basa doguwar jituwa kaman ba Uba da ‘da ba akan banbancin dasuke nunawa Bilal yasa Sam basa jituwa da dad din.

Yana isowa Zeenah ce ta Isa gurinsa da gudu ta rungumesa tana Kiran sunansa.

Da farin ciki ya riqo hannunta suka qaraso Yana kallan DD da sai alokacin yake zare facemask dinsa idanuwansa akan dad dinsa dashima shi yake kalla.

“Dad”yafada cikin kauna Yana miqawa Dad din hannu suka damqe hannuwan juna kowannensu na bayyanarda farin cikin ganin Dan uwansa.

Dunguma sukai zuwa ciki dd babba da Dawood din na gaba harma da dad suna magana DD din na sauransu kawai sbd yasan zancensu ba qarewa zaiyi ba.

Bilal dake bayansu tini suka manta dashi Dan haka yake biye dasu kaman bodyguard nasu.

Umminsa zuciyarta sanyi tayi Wanda Abu ne da suka Saba dashi shekaru matsu tsayi Daya kamata ace sun Dena Jin ciwonsa saidai ciwon Hakan ba Abinda zaka iya cirewa ko Hana ji bane saidai kawai koyaushe kayita dannewa sbd haka Allah ya tsarowa ‘dan nata.

Hannunta na dama takai a hankali ta riqosa ta bayansa ya tsaya ahankali tareda juyowa ya kalleta sai yaga idanuwanta na Neman sauyawa
Ya girgiza mata Kai ahankali Yana sake murmushin yaqe.

Juyawa sukai zuwa part din su ummen Wanda Zeenah tini tayi gaba masu Aiki sun ja kayansu sunyi can dasu.

 

 

*********
Lamari yayi tsanani ya Baci,ya lalace komai ya kuncewa benazir da Anne dake cikin daki an sakasu karban haihuwar,

Benazir Bata taba Jin kanta Yana Neman juyewa gadan gadan ba sai a yau din Datake ganin ran sumayyah na Neman fita a gabansu,

Sumayyah tabar mata maganganun dasuka Fi mata kama da wasiyya Wanda ya sakata kasa riqe kanta ta fasa kukan tashin hankalin Daya saka Ababa leqowa dakin hankalinsa tashe qafafunsa na rawa Yana cewa

“An mutu ne?”

Daga benazir har Anne babu Wanda ya iya dagowa bare iya amsa zancensa da bama su ji sa ba Dan babu Wanda yake hayyacinsa.

Wani irin ciwo da nauyi zuciyar Anne takeyi Wanda ya sakata rarrafowa ta dawo gefen sumayyah takai hannuwanta ta rungumota jikinta a hankali tana rufe Idanuwanta dasukai jajir hawaye masu zafin gaske sune tsinke mata batareda ta iya cewa komaiba Amma da Wani zai iya dauke ciwon Wani da ayau ta dawo da ciwon sumayyah jikinta ta haife mata cikin.

Benazir kuwa da hannunta na cikin na sumayyahn data riqesa da kyau cikin nata duk da tana cikin azabar ciwon da ficewar hayyaci benazir a cikin tsakiyar zuciyarta take,
Tana Jin tsananin halin qunci da tashin hankalin da benazir ke ciki cikin zuciyarta.

Benazir datake zaune gaban sumayyahn hankalinta ya Dade da barin jikinta Kuka takeson Yi Amma masifar data qamar da zuciyarta ta tashin hankali mara misali ta hana ko hawaye taruwa cikin idanuwanta.

Jinin dake zubowa ne ya sake gudu idanuwan sumayyahn na Neman juyewa sbd zuwa lokacin numfashi ma Bata iyawa da kyau
Wasu siraran hawaye masu dumi ne ke gangarowa gefen fuskarta Wanda yake sake qamar da benazir da itama zuciyarta ke kokarin Dena bugawa dukkanin jikinta na Dena motsawa.

Anne dake rungume da sumayyahn har lokacin tana ganin yanayin sumayyahn rasuwar sameerah ta dawo mata sabuwa a cikin zuciyarta take taji itama tata zuciyar na kokarin tsayawa ta fashe da Wani irin Kuka Mai radadi da ciwo tana sake riqe sumayyahn tace

“Sumayyah Dan Allah duk tsanani karki barmu,
Kece sanyin idanuwanmu, ba zamu iya babu ke ba babu Abinda kika bari,
Karki tafi ki barmu,
Benazir rayuwarta lalacewa zatayi itama hankalinta zata rasa idan ta rasaki,
Idan na rasu waye zai sharewa benazir hawaye da baqin cikin wannan rayuwar mara Dadi……

Kalaman Anne suka saka benazir fasa Wani irin Kuka tana cusa kanta cikin qafafunta,
Bata taba yiwa kanta fatar mutuwa sai ayau,
Idan tafiya sumayyah zatayi ta barsu ya Allah ka dauki ransu a tare su tafi dukkaninsu su bar wannan duniyar da Basu San meye acikinta ba bayan Kuka da baqin cikin rayuwa.

Kukan dasuke Yi a kanta kaman ransu zai fita yasa Ababa kasa riqe Kansa yaje jikinsa na rawa ko gabansa baya Gani ya dauko wayarsa ko ganin numbers daidai bayayi ya Nemo sunan Bilal ya saka kiransa.

 

Bilal dake zaune gaban ummensa Yana Jin zuciyarsa na tsinkewa Tin safiyar yau din sai yanajin Hakan damuwar yanda zai iya sanar da mahaifiyarsa da ‘dan uwansa Abinda yake faruwa na qaruwar haihuwar da zai samu ta qaddara.

Ummensa da itama tata zuciyar ke tsinkewa tinda suka shigo kaantes kallan Bilal tayi tana sake Jin jikinta na mutuwa ta riqo hannunsa tana Kiran sunansa ahankali tace,

“Bilal….kafin tayi magana wayarsa tayi ringing Ya saka hannu cikin aljihunsa jiki a mace Shima ya Ciro wayar Yana dagowa yaga sunan Ababa take gabansa ya Fadi jikinsa ya sake mutuwa.

Kallan ummensa yayi yaga itama shi take Kallo jikinta a mace.

Wayar ya dauka tareda Dan janyewa daga gabanta.

Murya na rawa hankali tashe Ababa yace

“Kayi sauri kazo yanzu da gaggawa Sumayyah da Abinda yake cikinta na cikin mummunan hadari tin jiya take nakuda ba haihuwa har…..

Bai qarasa ba Bilal ya katsesa hankalinsa a matiqar tashe jikinsa na daukan rawa yace

“Meyasa ba’a kirani ba tin jiyan?
An kaita Asibiti ne?
Ganinan zuwa yanzu.

Kashe wayar yayi ya juyo ya nufi kofa zai fice
Umme tayi saurin riqesa hannuwanta na rawa a tsorace tace

“Waye ne?
Waye Kuma ba lafiya?
Meyake faruwa ne?
Ina zakaje?

Kasa amsawa yayi sbd hankalinsa Daya matiqar tashi
Kasa magana yayi idanuwansa na sauyawa da tsoron Daya kasa nutsuwa dashi.

Sake jero masa tambayoyin Umme ke kokarin Yi Amma Bai gama ji ba yayi gaba Yana sake saka Kiran Ababan yaji a gida suke ko asibiti Amma yakasa samunsa sbd Ababan Yana can ya kira dd babba ganin Bilal baigama sauraronsa ba ya kashe wayar.

Dd babba dake zaune a palonsa na alfarma suna magana da DD da dad kaante Kiran Ababan ya shigo wayarsa yaqi dauka.

Bai gama dauke idonsa daga kan wayar ba Wani Kiran ya sake shigowa kaman bazai dauka ba Amma tinanin zai iya Kiran Bilal ya fada masa Kuma Bilal din zuwa zaiyi a samu matsala idan Wani ya gansa can Dan haka ya dauki wayar a natse ya daga Kiran.

Ababan Bai iya tsayawa ko sallama ba a rikice yace

“Alh babba ‘yata mutuwa zatayi daga ita har Abinda yake cikin nata nakira Alh Bilal nafara magana ya kashe wayar,kunce idan haihuwa tazo a sanar ma…

Shima Bai qarasa ba dd babba ya katse Kiran hankalinsa na tashi ya miqe Dan tsayar da Bilal Dan kuwa matiqar Ababa ya kira Bilal to kuwa babu Abinda zai hanasa zuwa saidai komai ya faru Dan haka Bai tsaya Bata lokaci ba ya miqe da Kansa ya nufi kofa Yana saka Kiran wayar Bilal Wanda harya shiga mota.

Daga DD har dad kaante bayan dd babba suka biyo cikin mamakin meya daga masa hankali ya fice haka cikin sauri da bacin Rai.
#MAMUH#
#DD KAANTE
#BENA
#AMNAH
#ZAFIN KAI
#MAMUHGEE

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button