Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 30

Sponsored Links

30
Ababa na fitowa daga Asibitin Kai tsaye Asibitin su alh Bilal din ya nufa Yana addua da fatan dd babba ya samu sauki ya Dan dawo Kansa.

Yanda ya dauka Asibitin ba Hakan ya sameta ba sbd tin a gate ake Hana shiga saika Fadi Abinda kazo Yi,

Idan Kai patient ne bangaren da zaa nuna Maka kabi daban,
Idan dubiya kazo Kuma in ba time na dubiyan bane baa barinka shiga sai time na dubiyan yayi.

Ma’aikatan Asibitin ne kawai ake budewa Kai tsaye su shige harma da barka da zuwa sbd Asibitin kusan duka manya da masu abin duniya ne sukeda files da kati a cikinta.

Dan haka tin a gate Bai samu shiga ba bare qarasawa gurin dubiyar dd babba.

Guri ya nema Yana kokarin zaunawa zaman Jira securities na Asibitin suka hanasa Dan haka baida zabi dole sai komawa gida yasha baccin Rana kafin da yamma ya sake shiryawa ya fito ya nufi Asibitin Dan yasan ankai abincin Rana daga hotel din kaantes shiyasa Bai tsaya yaci abincin gida ba ya fice.

Kaman yanda suka San halinsa da Abinda zai iya biyowa baya idan suka taba duk Abinda zaa kawo batareda izininsa ba tinda yanzu yasan komai yasa tinda aka kawo Basu taba ba Yana Nan aje sai Ababan yazo yabasu Wanda zasu ci.

Yana zuwa kuwa abincin yafara sakawa benazir ta zuba masa yaci ya koshi kafin ya bar musu sauran Suma suka ci anan yace su Basa numbern Alh Bilal ta waya tinda yasan bazasu riqeta Akai ba tinda sun Dade da zama tsofin munafukai akansa.

Shiru sukai suna shakkar fada masa Basu da ita,
Benazir data shirya daukan marinsa ta Bude baki ahankali tana Dan sauke Kai qasa tace

“Bamu San numbernsa ba,bamu taba karba ba.”

Kaman yanda suka sani su dukan harbeta yayi da qafa Saida tayi baya Amma Bata Fadi ba
Cikin takaici yace

“Kwadayi kawai Kuka iya ya Baku kayan Dadi kuci ku shiga motarsa
Gashinan kun kwasa mana kayan wahala ko?”

Shiru sukai cikeda kunya da radadin kalmominsa babu Mai iya ko dagowa.

Yana cikin fadan aka buga dakin aka shigo ga mamakinsu su duka Alh Bilal dinne gabaki days sauya a cikin dare Daya damuwa Mai tsanani da rashin sanin mafita yasa idanuwansa har Wani zurfi sukai sbd kaman komai ya lalace masa ne.

Ababa na ganinsa ya miqe tsaye Yana masa barka da zuwa fuska a Dan sake kafin daga baya yakoma kalan jimami Yana tambayar ya jikin dd babba.

A hankali ya amsa masa tareda tambayan ya jikin sumayyah.

Kai tsaye Ababa ya amsa da tanajin sauki itama.

Sumayyahn Bilal ya kalla ta kasa dagowa ta kallesa daga ita har benazir sbd Ababa dake gurin.

Shi Kansa bazaiso su dago su kallesa ba a wannan yanayin Dayake ciki na rashin kwanciyar hankali ko Daya da tsananin damuwa.

Shiru dakin ya dauka har Ababa Mai son yin magana kasawa yayi yai shiru sbd sosai da gaske Bilal din yake cikin mawuyacin hali a bayyane.

Ajiyar zuciya Bilal ya sake bayan tsawon lokaci da shirun ya ratsa dakin zaiyi magana Ababa ya katsesa da kora benazir waje Shima ya fice Dan bawa Bilal din Daman magana da sumayyah

Suna ficewa sumayyah ta dago ahankali ta kallesa da idanuwanta dake cikowa da hawaye a duk lokacin da zata gansa sbd batasan meye matsayarta ba,
Ina rayuwar zata kaita da wannan cikin na jikinta,
Yaya alumma zasu karbeta da Abinda zata Haifa,
A wane matsayi Abinda zata Haifa yake da mahaifinsa.

Kallan datake masa idonta na cikowa da hawaye Shima shi yake mata idanuwansa na cikowa da hawaye sbd  Wani radadi ne shi da Abinda zaa Haifa masa zasu kasance aciki Mai kaifi,
Dd babba bai taba karbansa kaman yanda ya karbi sauran jikokinsa,
Bai taba kaunarsa kaman yanda yake kaunar DD,
Baa taba basa matsayi da mahimmancin da aka bawa DD ba tin suna Yara har suka girma matsayin DD daban yake dashi,
Duk Wani aikin wahala da rashin Hutu shine ake damqawa ahakan baa taba nuna godia ko Yabawar da zata saka yajisa Dan asalin kaantes ne Shima,
Ya taso da girmamman tabon rashin soyayyar gaskia ta asalin Dan gadon iyayensa a cikin kaantes,
DD shine hasken idanuwan dd babba,
Shine abin alfaharinsa,
Shine Wanda dd babba kadai kejinsa cikin tsakiyar zuciyarsa fiyeda ma yayansa duk da kasancewarsa jika,
Tin suna qanana banbancin da ake nunawa tsakaninsa da DD a bayyane yake Wanda Hakan Bai taba damunsa ba sbd irin kaunar da DD ke masa tana rufe gurbin da ake bar masa a zuci na nuna masa shi din ‘dan gaban fatiha ne bayan iyayensa nada tabbacin da aure suka haifesa.

A duniyarsa kaf tin tasowarsa mahaifiyarsa ce kawai sai DD suke masa Wani irin son Dayake basa qwarin gwiwan ci gaba da rayuwar cikin jarumta da karfin halin da a bayyane kawai yake dashi Amma a zahirin zuciyarsa shi din me tsananin rauni ne Wanda yake saka sa Jin duniyar na isarsa lokuta da dama,

Tin Yana qaraminsa ya taso cikin mawuyacin halin samun tinanin daidai na yanayin da aka sakasa,
Har girmansa Yana cikin wannan yanayin shiyasa tin daga ranar Daya fara kaunar sumayyah ya fahimci kusan ciwo Daya ke damunsu,
Nata ya shiga kwakwalwanta sabanin nasa da Bai shiga ba Amma dai ya sakasa cikin rauni sosai na zuciya.

A yanzu da wannan abin ya faru yasani ya qarasa ficewa ne a ran dd babba hakama zai saka mahaifiyarsa damuwa da kunqi DD kuwa zaiyita samun sabanine da mahaifinsu harma da dd babba sbd bazai taba yarda a tozartasa ba ko kuntata masa akan Abinda yayi.

Gangarowan hawayensa kan kyakkawan fuskarsa yasa sumayyah Kai hannunta hawayen ya sauka hannunta tana Jin zuciyanta narkewa
Take nata hawayen suka gangaro ahankali itama batareda ta iya cewa komaiba sbd basai yayi magana ba daga ita har shi tasan kowa na cikin mawuyacin halin da basusan meye makomarsu da Abinda zasu haifan ba.

Hawayensa Daya kasa riqewa ne suka koma Kuka ahankali mara sauti sai dai radadin zuci da jikinsa Daya gama sanyi da mutuwa.

Itama kasa tiqe nata Kukan tayi ta sunkuyar da Kai tana tsiyayo hawaye masu zafi.

Ahakan suka share lokaci Mai Dan tsayi babu Mai magana sai Kukan dasuka sha kafin ya Ciro handkerchief ya share hawayensa ya goge fuskarsa ya Ciro glass dinsa ya saka kafin ya share mata nata hawayen ya Kalli cikin idanuwanta ya Bata tabbacin inshallah komai zai tafi daidai,
Duk tsanani bazai taba rabuwa da itaba zai Samar musu rayuwar kwanciyar hankali Koda babu kowa acikinta.

Tambayanta yayi babu matsalan Dayake damunta ko babyn
Ta gyada masa Kai tana kallansa kaman Wainda ke bankwana sbd kukansa ba qaramin Bata tabbacin suna cikin tsaka Mai wuya yayiba.

Juyawa yayi ya fice a dakin bayan ya ajiye mata wayarsa Daya da layinsa da komai aciki.

Yana fitowa Ababa dake tareda benazir a zaune miqewa sukai tare tsaye Yana cewa harya fito.

Kasa kallon Ababan yayi sai kawai yace benazir tazo suje yabada Sako Koda zaa nemi Wani abin baya kusa.

Kasa motsawa tayi sbd Bata ma fahimci me yake nufi ba dan haka Ababa ya kalleta yace

“Kije ki karbo Sako akace”.

Bayan Bilal din tabi babu Mai magana a cikin su
Suna Isa ya Bude motar ya shiga ya Ciro rafar 1k guda biyu ya miqa mata yace yabar waya a hannun sumayyah duk Abinda ake buqata benazir din ta kirasa.

Yana barin Asibitin ta juyo ta dawo ciki,
Tana shigowa dakin a tsaye ta tadda Ababa Yana jiranta.

Kudin ta Ciro Kai tsaye daga cikin hijabinta ta miqa masa.

Karba yayi yana sakawa aljihu sbd yasani Kai tsaye dubi Dari biyu ne.

Wayar da Bilal din ya bari ya kalla yana kokarin Hana zuciyarsa fasa wayar sbd shi Sam bazai dauki wannan wayar dayakeson su rinqa Yi ba Amma zai Basu kwana biyu daga Nan zai dakatar sai yasan matsayarsa da cikin jikin ‘yarsa tukuna Dan shi a mutu a dawo so yake tabbas tinda Akai mata cikin sai sun aureta,
Sai sun shiga cikin ahalin kaantes Suma da yardar Allah.

Barin Asibitin yayi Bai sake dawowa sai dare ya sanmusu abincin Daren da aka kawo sauran yayi gida dashi acan yaci ya koshi har hande ta samu taci ciki itama Anne Kam saidai ta wanke kayan da akaci abincin dashi.

Washe gari Koda Ababa ya iso Asibitin an sallamesu Dan haka Yana zuwa kwasowa sukai suka dawo gida.

Anne gurin rawar jikin farin jikin ganin ‘yayanta har faduwa tayi taji ciwo a Dan yatsar qafa Amma Bata damuba,
A rayuwarta Bata taba farin cikin ranar ba sbd sai yanzu ne ta sake tabbatarda bazata iya rayuwar babu su ba Dan haka suna shiga dakinsu ta fasa Kuka ahankali da batasan ko na menene ba Amma dai tasan ganinsu ya dawo mata da rayuwarta ne.

Su kansu jikinsu mutuwa yayi ganin yanda tayi wata mummunan rama kaman wadda ko ruwa Bata taba sha ba tinda suka tafi.

Rungumeta benazir tayi tana sauke numfashi ahankali sbd ita yanzu haka kawai taji batajin Dadin komai,
Yanda zasu Rena babyn kawai take tinani
Idan Kuma su Bilal suka karbe babynsu Yaya sumayyah zata rayuwar batareda ciwonta ya dawo ba,
Nakudar haihuwar kawai tayar mata da hankali takeyi sbd radadin ciwon kawai zai tayar da ciwon sumayyahn.

Dan haka benazir ta shiga Wani tinani daya sanyaya jikinta tinda ta lura Ababa yanzu akan cikin babu Abinda bazai iyaba tasan sumayyah data Rai ko lafiya baida baqin cikin ko Daya.

 

*******Ahalin kaantes gabaki Daya hankalinsu ya tashi da Jin ciwon dd babba katsam Kuma wai attack ya samu,
Take duk na kusa Dana nesa suka hallaro a cikin kwana biyu Kuma har lokacin Yana Jin jiki sosai gashi an rasa meya samesa sbd Bilal ya kasa fada Dan haka yafi kowa shiga damuwa Daya San shine sanadin
Fatansa dai kada Wani mummunan abin ya faru ya zama Sila.

Lokacin da labari ya Isa ga DD kaante Kai tsaye yasan ba qaramin abu bane ya bawa dd babba attack sbd jajirtaccen tsoho ne Mai tsananin karfin zuciyar Dan haka koma menene yasan babba ne.

Take ya saka su ummensa fara Shirin tafiya zasu taho a cikin satin Suma sbd zuwansa kawai zaisa dd babban Jin sanyi ya sani Shima.
#MAMUH#
#DD KAANTE
#BENA ABABA
#SAFNAH ABABA
#CRAZY IN LOVE
#MARRIAGE
#AMNAH KAANTE
#ZAFIN KAI

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Back to top button