Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 22

Sponsored Links

Page2️⃣2️⃣

 

 

 

Bayan barinta dakin ne yakoma ya kwanta Yana ajiyar zuciya Yana tuna abinda yafaru tsakaninshi da fanan karo nafarko kenan arayuwarshi daya taba wata mace murmushi yayi aranshi yana fadin ” mara kunya kawai”

In serious tone fanan tafuskan ci Zeenat kafin tafara magana “nikam dan Allah intambayeki mana zee!?” Kallonta zeenat tayi taga yanda tanutsu tana jiran amsanta tasan dole abinda zata tambayeta is very important gyara zama tayi tabata attention sannan tace ” inajinki” ” nikam yayankun nan wayan nan matan dukansu biyu ze aura ne danaga suna fada akansa!?” Ajiye wayar hannunta zeenat tana fadin ” wallahi kekam ah ah ita nusaiba yar abokin Abba ne wato alhaji badamasi me ruwa kuma hajiya Hussaina kawar ummi ce tom nusaiba yarinyar kishiyar hajiya Hussaina ce to itace take mugun son ya azaad inde kinganta tazo gombe to danshi tazo Amma inbanda yau inagama inkin tambayi ya azaad ya kamaninta yake besaniba dan ko kallo bata isheshi ba bare yatsaya magana da ita gashi tanada mugun rawan kai kamar wata amaryan kare , itakuma aneesa babanta yayan mommy ne Kuma suna mutunci da Abba tom time din da ya azaad yatafi US ne yin wani meeting akan business shine suka hadu da ita time din tana final year a university tunda tasa idonta akansa nanike mishi kamar chew gum kwata_kwata ya azaad baya sonta saboda bakaramar marajin magana bace inkina neman shedaniya ta gidan gaba to kisamu aneesa da ta lura bata gaban ya azaad kawai taje tasamu baban tana kuka kamar zata mutu tace mishi ita duk duniyar nan bataga mijin aure ba sama da azaad ba, shikuma tsaban son da yake mata ne yadaure mata gindi yasamu mommy da maganar nan sukayi kulla kullansu sukama Abba magana duk da abba bewani maraba da maganar ba amma ganin suna mutunci yace mishi bakomai dama gashi sun dade sunabin ya azaad yayi aure Amma se kakkaucewa yakeyi , ummi dataji maganar ko kadan hankalinta be kwanta da yarinyar ba amma bazata iya musu da mijinta ba , adaren ranar Abba yakira ya azaad yasanar dashi abinda ya yanke mishi dan ba shawara yabashi ba umarni ne. Babu yanda ya azaad ya iya haka yabi umarninsu amma bawai Dan yanason taba bayan wata uku aka musu baiko tunda nusaiba taji labarin tadinga rashin lafiya nan ne tadau aniyar tarwatsa aurensu dan bata shakka agaban kowa tasha fadan inde ita bata auri azaad ba to wlh aneesa bazata auresa ba inde tana raye bazaayi auren ba to kinji abinda yahadasu” tunda tafara magana fanan take kallonta bako kyaftawa ganin yanda take magana kamar wata yar jarida dariya fanan tadanyi “Kai zeenat kin iya bayani irin wannan dogon jawabin haka sannu ” murmushi zeenat tayi tace ” to ai namiki dalla_dalla ne saboda kigane ” ” aikuwa nagane yanzu” cewar fanan data tafi duniyar tunani “gaskiya taga wautan su aneesa yanzu ji yanda suke zubar da kima da daraja irin nasu namata sunzo suna nacewa Wanda bemasan sunayi ba balle yakula su, hmmm nide banga abinda zesa innacewa namiji haka ba wai dan inasanshi sede inmutu da sonshi araina ballema Azaad banga abin so atare dashi ba bugu da kari Dan Iska ne wata zuciyar tace mata amma ai yanada mugun kyau tsaki tayi dan yanada kyau Kuma seme ai Hali me kyau akeso ba kyaun fuska ba” “fanan tunanin mekikeyi haka tundazun fa nake miki magana” kwanciya fanan tayi akan lallausan gadon zeenat kafin tace” hmmm kede bari kawai dear inata mamakin su nusaiba ne ” “ohhhhh kyalesu wahala ce bata ishesu ba saboda nide da hankalina ba namijin dazanwa irin wannan son haukan ” girgiza Kai fanan tayi” karkice haka Suma bason ransu bane babu yanda zasuyine saboda naji ana cewa so mugun abune inya rikeka ni wallahi tausayi suke bani ” hmmm kede fanan haka kikace de ke kintaba soyayya ne!?” “Ah ah bantabayi ba” da mamaki zeenat takalleta saboda batayi tunanin yanda fanan take da kyau da hankalin nan ace wai bata taba soyayya ba “Amma meyasa baki tabayi ba !?” Rike Kai tayi dan tagaji da da surutun zeenat bacci takesonyi” saboda babu wanda yataba cewa yana Sona mana bantaba tsayawa dawani namiji da sunan muna hiran soyayya ba” girgiza Kai zeenat tayi tana mamaki sosai, ahaka sukaci gaba da hira har bacci yayi gaba da fanan ganin haka yasa zeenat barin dakin taje gun ummi tasameta tana waya da yan dubai cikin harshen larabci take magana zama tayi tana jiran ta tagama saboda akwai abinda takeson fada mata,ajiye wayar ummi tayi bayan ta kammala tana kallon yar autar tata yanda ta nutsu tasan abu me mahimmanci takeson fada ” zee ya akayi akwai labarine ” zeenat kamar wacce take Jira ummi tamata magana ta fara fadin ” ummi intambayeki Dan Allah fanan bata burgeki!? ” Tana burgeni mana” cewar ummi , Jin haka daga bakin ummi yakarawa zeenat karfin guiwa ta cigaba da magana ” wallahi ummi fanan tanada hankali sosai gata da nutsuwa ga ilimin addini dana boko” murmushin ummi tayi irin nasu na manya dan tariga da tasan inda zance zeenat din yadosa amma seta ce mata “cigaba inajinki” ” ummi Zakiyi matukar Jindadi inta zama surkanki bakaramin farin ciki zamuyi ba ” tagama maganar ta tana kallon ummin nata da itama kallonta takeyi ” tom hajiya zeenat naji bayananki amma waye kikeson ta aura din ” dan fari da ido zeenat tayi tace ” Matar ya azaad mana ummi” dariya ummi tafashe dashi ” nikam klau dinki kuwa bakisan yayanki yanada wacce zai aura ba ko kuma ita fanan din cemiki tayi bata da wanda take tare dashine ” sanyi jikinta yayi jin maganar ummi duk dahaka de bata karaya ba tasake cewa ” to ai ummi ya azaad yanada daman daze auri mata daga daya har hudu kinga ze iya auren fanan Kuma wlh bakaramin dacewa zasuyi ba ” maganar zeenat ba karamin tasiri yayi azuciyar ummi ba tabbas tana son fanan har ranta saboda kyawawan halinta zataji dadin hakan inde fanan tazamo surkanta amma zata gwada tuntuban abbansu da maganar taji mezece dukda tasan bazaa samu matsala tagunsa ba sede ko in azaad din, ganin ummi tayi shuru ne yasa tace ” ummm ummi nikam natafi tunda baayi accepting din request dina ba” cikin zolaya ummi tace ” gaskiya kam baayi ba tattara ki koma inda kika fito” komawa dakin tayi ta tadda fanan tagama shiryawa zata tafi fitowa tare sukayi taje tama ummi sallama ta tafi.

 

Tattaunawa sukeyi tsakanin su duk Wanda yaga yanda suke maganan nan yasan babu alkhari acikinsa. Alhaji sambo daurayi ne yace ” nide inzaku bi shawarata dase ince wani Abu” duk hankalinsu suka dawo dashi kansa hannu alhaji Ibrahim tijjani yadaga masa alamar yafadi abinda ze fada, cigaba da magana yayi ” nide aganina karmu ce zamu kashesa saboda inde mukayi hakan idon duniya kanmu zata dawo aganina kamata yayi muhada mishi target wanda idan ya fada tashi tagama ” tafi alh Ibrahim tijjani yayi Yana fadin” good point alh sambo tabbas ka kawo shawara mafi dacewa amma yanzu dameye yakama muhada mishi tarko” shuru sukayi dukkansu suna tunani can cikin sauri alh lamido yace ” mace! Tabbas da mace zamu hada mishi tarkon dakuwa tabbas ze kamashi ” kallonsa alh Ibrahim yayi ” eh hakane wannan ma point ne amma sanin kankane azaad shidin ba manemin mata bane kwata_kwata mata basa gabanshi” alh Umar baita ne yayi gyaran murya wanda tunda suke magana bece musu komai ba yafara fadin” azaad ba manemin mata bane abinda ze faru zamusa asa mishi idone adinga bibiyarshi dama daya kawai zamuyi amfani dashi domin cika burinmu bamuda matsala da koma wacece aka gansu adauka mana hoto kawai” raf!raf!raf tafi kawai sukeyi saboda bakaramin dadin maganar alh Umar baita sukaji ba, cikin farin ciki alh Ibrahim yadaura da ” sharri zamu hada mishi wanda ze matukar taba career shi wanda ze taba mishi kasuwanci domin babu Wanda zeso siyan kaya agun mazinaci me lalata yayan mutane koya kuka gani !?” Hahahahahah babu abinda sukeyi inbanda dariyar mugunta yanzu kam sunsamo hanya mafi sauki dazasuyi maganin taurin kai dakuma jiji dakan azaad ahaka suka watse.

Yau sati daya kenan rabon da fanan taje gidansu azaad saboda alluransa yakare tagama mishi duk wani treatment dinsa Kuma alhamdulillah yasamu sauki sosai dan bayama Nigeria kwanansa uku da tafiya Germany gabatar da wani business daga nan Kuma zewuce Malaysia sudawo tare da Abba . Su ummi kuwa bakaramin missing din fanan sukayi ba adan zaman dasukayi da ita sun shaku sosai.

MAINASARA’S family

Yau gidan se girke_girke da gyare_gyare akeyi duk wani me aiki agidan basu zauna ba sunata faman aiki kamar ba gobe saboda tarban Abba da azaad dasuke hanyar dawowa ummi dakanta take kitchen se masu tayata aiki sunata girki, Basu suka samu kansu ba se around 2 suka jera komai akan dinning area kulolin abinci sunfi goma ga drinks kala_kala dukansu suna zaune afalo ummi tayi kyau sosai tana sanye da dakekkiyar lace me matukar tsada tasha gold’s zeenat ma tayi kyau sosai abunta sanye take da abaya baka fawwaz ne yakalli agogon hannunshi yamike Yana fadin” areef tashi mutafi sunkusa landing” mikewa sukayi suka tafi airport din tsayuwar mintuna 10 sukayi kafin jirgin su yayi landing, mutane nata fitowa daya bayan daya , wani farin dattijo ne yafito sanye da shadda blue color da gare (malum_malum) bafulatani kyakyawa me gwarjini gashi atsaye yake kallo Daya zaka mishi kasan cewa kudi da hutu sunzauna ajikinshi Abba kenan ALHAJI MUHAMMAD B MAINASARA bakaramin kama sukeyi da azaad ba ta bangaren zubin halitta , azaad nahango abayanshi suna fitowa tare yanayin jikin su da tsayinsu kusan daya sede azaad yafishi murdewan jiki dakuma tsayi kasancewar shi saurayine…

 

 

Nafada mukuma zansake fada yawan comment dinku yawan read more dinku kusha karatu lafiya,se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by (MRS ISHAM )

 

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

 

 

Free book

 

 

 

 

____________________________________________

 

Back to top button