Hausa Novelskawali Ne Hausa Novel

kawali Ne 16

Sponsored Links

*KAWALINE*

*Zahra Surbajo*

 

*Bissimillahirrahmanirrahim*

*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*

https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv

*16*

 

Rayhana ta isa abuja cikin ƙoshin lafiya,inda tasamu kawun nata yazo ɗaukarta a jabi garage.

Koda yayi arba da ita da ciki a gaba kamar wacce zata haihu yanzu kukane ya kubce masa,dan farin sani yasan rayhana me tarbiyyace amma ga iftilain daya afka mata.

Itama hawaye take haka suka shiga taxi zuwa inda yake ayki,a mota suka gaisa daga haka ba wanda yasake cewa komai.

Koda rayhana taga katafaren gidan da zasu shiga cogewa tayi awaje takai dubanta gun kawun nata tace asanyaye”kawu nan gidanfa?”

Murmushi yayi yace”kinsan de ba yadda zaayi na mallaki wannan na baroku a ƙauye kuna wahala,to nan gidan da nake gadi ne,ba nawa bane”ya bata amsar fuskarsa ɗauke da murmushi.

Sunkuyar dakai tayi ƙasa tana muemushi,suka shiga cikin gidan.

Tsabar kyau da haɗuwar gidanne yasa rayhana kasa ɗaga ƙafarta har saida kawu ya taɓota tai firgigit ta bishi abaya.

ɓangarenshi yamata masauki dan selfcontain ne,sosai gun yamata kyau,kan kujera ta zauna ta sauke ajiyar zuciya.

“ki zauna anan rayhana ni zan koma ɗakin maigadi na bakin ƙofar shigowa, masu gidan na faɗa musu a ƙauye kike kinzo nan ki haihune ki koma nasan baki da rawar kai dan Allah ki ƙara kiyayewa,”cewar kawu atausashe.

“insha Allahu kawu zan kiyaye.” ta faɗi atausashe.

Daga haka sallag ta fara yi sannan ya bata abinci taci tai godiya ga Allah sannan ta kimtsa ɗakin da yake amatsayin mallakinta a halin yanzu.

********

Siyama jitayi gaba ɗaya duniyar tai mata zafi,ta rasa inda zatasa kanta taji daɗi,ga wata irin mahaukaciyar soyayyar rayhan dakw ɗawainiya da zuciyarta.hakanne yasa ta haɗa yanata yanata ta diro nigeria,cike da kunyar haɗuwa da innarta da rayhana.

Direct daga airport drop ɗin mota ta ɗauka zuwa garinsu cikin shigar badda kama ta yadda bame ganeta.

mama tasamu a tsakar gida tana wanke wanke bakinta ɗauke da sallama ta shiga gidan.

Daga muryarta mama ta gane siyamace, jikinta har ɓari yake ta miƙe tana faɗin”siyama kece?”ta fashe da kuka.

Itama kukan tasaka ta tafi da gudu suka rungume juna,kuka suke sosai cikin kukan siyama ke faɗin “inna ki yafemin don Allah na tuba bazan ƙara barin gida ba”

“Siyama koda kike can ban taɓa kwana dake azuciyata ba kullum nema miki shiriya nake gurin ubangijin daya jarabceni dake”cewar mama cikin kuka

Sun jima a haka kamin su saki juna su samu guri su zauna tashi mama tayi takawo mata abinci,siyama tace”mama rayhana da naga bangantaba ko kin ayketane?”

Kuka inna tasa daga nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da siyamar.

Yanke jiki siyama tayi ta faɗi jin cewar ƙanwarta na ɗauke da cikin wanda takeso da burin yazama mijinta.

 

*Ku hanzarta siya 500 ne kawai dan vama ayi komaiba awannan labari*

COMPLETE ƊINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.

*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*

Surbajo for life.

Back to top button